Showing 48001 words to 51000 words out of 276165 words

Chapter 17 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt

nuna wa kowa inda ya kamata ya bi kar ya taka ɗan uwan sa a yi faɗa, haka dai da zama ya haɗa ku haka za ku ci gaba da zaman, ko ɗaya ya kashe ɗaya ko mutuwa ta ɗauke mu baki ɗaya haba, uwar me aka yi yanzu kuma da gaba na ke ta fad'uwa ina waje?"

Cikin kuka Saddeqa ta sanar da shi duk abinda ya faru tsakanin ta da Ameerah da sharrin da ta qulla mata har ya yi sanadiyyar fad'uwar Yadiko,salati Ɗan liti da Baabaa suka saka Baabaa tace,

"Jikan nawa za a yi wa sharrin fyad'e daga zuwan shi hutu yau yau ɗin nan ko kwana be saka haqarqarin shi ya yi ba a qauyen? Amma dai Ameerah kin sha Maman sharri, ba zan taɓa yafe miki ba se Allah ya yi mana hisabi dake da uwar ki da ta koya muku mugun hali"

Da kyar Ɗan liti da Munir suka lallashi Baabaa ta koma d'akin ta, Innoh na surfa masifa tana ta zage-zagen da ba ma a gane da wa take yi, saboda can cikin ran ta danqare yake da haushin Ameerah akan abinda ta aikata, sannan ga takaicin Baabaa ta zageta har da ja mata Allah ya isa bata da ikon ramawa dan kuwa bahaushe yace, ɗan kuka ke jawowa iyayen sa jifa, to kuwa Ameerah ta janyo mata jifa kuma ta kasa tarewa.

Ɗan liti ne ya taimaka wa Yadiko ta shiga d'akin ta ya kwantar da ita a gado ya fita zuwa d'akin Innoh,duk da Yadiko ta ji gaskiyar abinda ya faru babu laifin Saddeqa da Munir hakan bai hana ta kiran Saddeqa ba ta yi mata nasiha akan kiyaye mutuncin ta, cikin nishi take faɗin,

"Tin kina k'arama nake yi maki addu'ar Allah ya kare maki mutuncin ki da ke da dikkan yaran, Allah ya sa mijin auren ki ne kawai zai san ki a matsayin 'ya mace, Allah ya tsare ku ya kare ku daga zina da ke da dikkan yara, Saddeqa shi mutuncin mace babban abu ne wanda idan mace ta rasa shi ta rasa qimar ta a idon mijin ta, har abada sai dai su yi ta zaman doya da manja ai ta samun sab'ani a rasa daga ina matsalar take, a yanzu mun zo zamanin da mata ke ganin kamar ajiyar budurcin mace ma babu wayewa a ciki, to ina so ki sani a idon 'yan duniya ne hakan yake rashin wayewa, amma a idon maza masu nagarta hakan tawaya ne, ballantana wasu daga cikin 'yan iskan ma suna son tagari,dan haka ina jaddada maki faɗin Allah subhanahu wata'ala ki guji kusantar zina da dikkan dangogin ta, ki tsare mutuncin ki ko hannun ki kar ki bari namijin da ba muharramin ki ba ya taɓa da sunan son ki yake yi ba da lalura ba,domin kuwa da namiji da mace su riqe hannun juna in ji Annabi Muhammad wanda ba muharraman juna bane ba gwanda a caka masu qusa ta huda hannun nan nasu shi ya fi masu alkhairi, Saddeqa ki kula da qanin ki, ki zama mace mumina, Allah ya yi muku albarka,"

"Inshaa Allahu Yadiko zan kiyaye dika nasihar ki, Allah ya baki lafiya, bari naje na yi sallah na kawo maki abinci ki ci, ko kin ci?"

"Ah ah ban ci ba, je kiyi sallah ki zo mu haɗu da Sadeeq mu ci gashi can na kife da ƙwarya,shi wancan yaron Munir Baabaa ta yi masa nashi girkin,"

"To Yadiko"

Fita ta yi ta d'ebi ruwa a bokiti dan kuwa ba zata iya sallah da wannan dattin ba,tana jiyo Ɗan liti a d'akin Innoh yana yi wa Ameerah faɗan ba zai ɗauki yi wa Saddeqa yarinyar kirki qazafi ba,yarinyar da idan gaskiya zai faɗa babu mai yi masa ladabi da biyayya na gaske ba na ha'inci ba sama da ita da uwar ta, bud'ar bakin Innoh sai cewa tayi,

"Ladabin banza ladabin wofi,biyayyar banza biyayyar wofi, yarinyar da kullum idan ta fita makaranta tun safe se yamma, rana d'ai-d'ai ne take dawowa ta ci abinci ta koma,ka ga kuwa Allah kaɗai yasan me take aikatawa a wajen"

Cikin ɓacin rai Ɗan liti ya kira sunan Innoh, babu kunya ko tsoro ta kirawo nashi itama gatsal, kasa cewa komai ya yi ya shuri takalman sa zai bar gidan, tsaye yaga Saddeqa da ta gama jin komai tana kuka, rasa me zai ce wa yarinyar ya yi sai kawai ya sa kai ya bar gidan.

Wanka ta shiga ta na yi tana kuka,a haka ta gama dirje jikin ta ta fito ta sake sanya guga a rijiya zata jawo wanda zata yi alwala, gugar ta ji an riqe an sake tsomawa a ruwan an fara ja, da sauri ta ja baya tana kare jikin ta da ta manta bata yafawa mayafi ba, dan kuwa ta manta da Munir gaba ɗaya a gidan.

"Ki dena kuka ki yi sauri ki yi alwala ki yi sallah ni na tafi sai da safe, Allah ya bawa Yadiko lafiya,dan Allah ki bata hakuri akan abinda ya faru,"

Murmushi ta d'anyi mara sauti saboda ganin sauqin kai irin na Yah Munir,shi da bai yi laifin komai ba yake bada hakuri,cikin sanyin murya tace,

"Zata ji na gode, sai da safe Allah ya hutar da gajiya"

Shima murmushi ya yi sannan ya sa kai ya bar gidan, yaso k'warai Sadeeq ya raka shi kwana amma yaron yace ba zai bi shi ba Yadiko na da buqatar shi a yau, duba da cewa yau Baban nasu yana d'akin Innoh ne.

Tana idar da alwala ta shiga d'akin su da sauri Ameerah dake lab'e tana kallon yanda Munir ke bawa Saddeqa kulawa tana kuka ta bar jikin window ta kwanta tana gursheqen kuka,bata kula ta ba ta wuce ta sauya kaya ta saka alimun a hammatar ta saboda turaren ta ya qare, wanda mommy ta bar musu kuma Ameerah hana ta ta yi,sallah ta tada ta fara yi, Ameerah kuwa na nan kwance tana jin zafi da tuquqin baqin cikin abinda ta gani na faruwa tsakanin Munir da Saddeqa.

Sai da ta idar da sallar isha'i ta yi shafa'i da wutiri sannan ta zauna ta na yin azkar ɗin ta da bata samu damar yi ba tun magariba, tana nan zaune Sadeeq ya shiga ya kira ta yace taje su ci abinci idan ta idar, da hanzari ta tashi dan gudun kar ta bar su da yunwa,tana so da ta gama cin abinci ta wanke uniform ɗin ta da suka sha cukuikuya ta samu ta d'inke inda ya yage idan sun bushe.

Fitar ta ke da wuya Ameerah ta samo reza ta ɗauki Uniform ɗin Saddeqa ta dinga yankawa, yanka irin na rashin mutunci, yankan da ba za su gyaru ba, ta na gamawa ta sa dariyar mugunta ta cukuikuye ta mayar inda ta ɗauka ta koma ta kwanta.................
[09/08, 10:38 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI







RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH










PAGE 18:









Suna gama cin abincin su Yadiko ta sanya su Saddeqa a gaba da nasiha har sai da suka zubar da hawaye saboda yanda jikin su ya yi sanyi, tana gamawa tace,

"Idan da mai wata magana a cikin ku yayi ina sauraren ku, kun san rayuwar nan idan yau mune gobe fa ba mu bane, dan haka ina sake jaddada maku ku yi hakuri da 'yan uwan ku, ku yi riqo da zumunci domin Allah, Allah ya yi muku albarka baki ɗayan ku har 'yan'uwan naku da dikkan yara baki ɗaya,Allah ya kare ku daga sharrin dake cikin wannan zamani na zinace-zinace da shanye-shaye da harkar nan ta dabanci da ta yawaita,Allah yasa a koda yaushe a kuma ko ina kuka samu kan ku ku yi hakuri da rayuwa kuma ku nemi halal ɗin ku,"

"Ameeen Yadiko inshaa Allahu zamu kiyaye dik abinda ki ka ce,kuma zamu kasance masu aiki da kyakkyawa da umarni da kyakkyawa, sannan zamu zamo masu hanuwa wajen aiki da mummuna kuma zamu yi hani da aikata mummuna gwargwadon iyawar mu,Allah kuma ya amsa dikkan addu'o'in ki akammu,yanzu ya kike ji a jikin naki?"

"Hummm Saddeqa ba zan iya misalta miki abinda nake ji ba,amma zan iya cewa alhamdulillahi ina godewa Allah da ya jarabce ni da jin wannan ciwon a jiki na domin na san kankarar zunubai ne, Allah ya bamu ikon cin kowacce iriyar jarabawa ce ta tunkaro mu,"

"Ameen Yadiko, gobe zan raka ki asibiti idan Yah Saddeqa ta tafi makaranta,"

"Ni ba inda zani ni zan raka ta kai ka tafi makaranta, ni da mun kusan sauka kai kuma yanzu kake farawa ma, sannan ni senior student ce ba lallai a dake ni ba kai fa dan primary mugun duka zaka sha idan ka yi fashi,"

Murmushi Yadiko tayi sannan tace,

"Dik kar ku damu zan je asibiti da kaina babu me dukar min masoya na,Allah dai yasa baban ku ya bari kawai shine fatan, kun san baya son a ce za a je asibiti,"

"Indai ba shi zai bada kud'in ba  kin san zai bari, ai dama damuwar shi ace masa miqo kud'in zuwa asibiti,"

Saddeqa ta qarasa maganarta tana dariya, dariya Yadiko tayi sannan tace,

"Qaniyar ki Saddeqa mahaifin naku kike yi wa tsiya ko? Bari yazo na faɗa masa me kika ce,"

Kama baki Saddeqa ta yi tace,

"Ki yi wa Allah ki rufa min asiri Yadikonaaa"

"To naji tashi kuje ku kwanta Allah ya albarkaci rayuwar ku, kar ku manta da addu'ar bacci,"

"To Yadiko sai da safe Allah ya qara maki lafiya,bari naje na wanke uniform d'ina,"

"Ni dai anan zan kwana,"

"To maqalematan Yadiko banda minshari dai,"

Dukan qafar Sadeeq Saddeqa tayi kafin ta bar d'akin suna dariya baki ɗayan su, Ɗan liti ta gani zaune a saman bokitin qarfe ya zabga uban tagumi, nan da nan jikin ta ya yi sanyi Allah yasa be ji hirar su ba, cikin in ina ta gaishe shi ya amsa sannan yace,

"Zo nan Saddeqa,"

Jiki na rawa ta je ta durqusa a gaban shi tace,

"Baba gani, dan Allah ka yi hakuri,"

Murmushi ya yi saida haqoran shi suka bayyana, sannan yace,

"Saddeqa baki yi min komai ba sai alkhairi,ki yi hakuri akan abinda ya faru kin ji? Na yarda da ke na san ba zaki taɓa lalata rayuwar ki ba,dan haka ki ci gaba da kare mutuncin ki, a yau na yi danasanin aika mommy aikatau birni ban san da wa zata haɗu a can ba, dama auren ta na yi mata ta dawo gida ta yi ta hayyafa ina ganin jikokina,amma babu komai duk sanda ta ɗauki albashin ta na farko ta dawo ba zata koma ba aure zan yi mata ko sadaka ne gwanda na bada ita kowa ya huta,"

"Ameeen baba na gode, Allah ya dawo mana da ita lafiya,"

Har ta miqe zata tafi taji yana faɗin,

"Sannan ni ba zan hana mahaifiyar ku zuwa asibiti ba, wannan karon da kuɗi na zan kai ta asibiti a duba min lafiyar ta saboda ni kaina na ji tsoron yanda ta faɗi lokaci ɗaya, ba zan jure rashin Yadikon ku ba ko wata nakasa ta kama ta ina son matata, ina fatan kin gane?"

Tsit Saddeqa tayi, kenan ya ji duk abinda suka tattauna a tsakanin su da mahaifiyar tasu, kuma da dikkan alamu nasihar ta har shi ta ratsa ba iya su da ta yi wa ba,dan kuwa Yadiko ta yi musu nasiha sosai mai ratsa zuciya wadda ta tabbata har ta koma ga mahaliccin ta ba zata manta kowacce kalma da ta sanar da ita ba.

Ko juyawa bata sake yi ba ta faɗa d'akin su ta na sauke ajiyar zuciya, Ameerah ta gani kwance da alama idon ta biyu kuka ma take yi, Ɗan liti ta sake leqawa dan ta ga shin ya bar tsakar gidan ne taje ta kwashi kayan ta ta wanke ko kuwa? Ya na nan zaune a saman bokitin qarfe ya zabga tagumi be tashi ba har ta gaji da tsaiwa ta koma saman tabarmar ta ta kwanta da niyyar idan ya shige d'aki ta je ta yi wankin ta.

Ɗan liti kuwa na nan zaune yana tunanin shiga d'akin Innoh ya tadda mita da masifa, tagumin shi ya sauya wa salon zama daga hagu zuwa dama ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya,Sadeeq ne riqe da hannun Yadiko zai raka ta ta zaga,ganin Ɗan liti zaune saman bokiti ne ya sanya ta tsayawa tace,

"Malam lafiya na gan ka zaune a waje a dai-dai wannan lokacin?"

"Lafiya qalou Yadikon Sule, ina zuwa haka?"

"Zan ɗan zaga ne kafin na kwanta bacci nake ji,"

"Allah sarki, to ya jikin naki? Ina fatan da sauqi ko? Ki shirya gobe da safe zan kai ki asibiti a duba min ke, Allah ya baki lafiya ya kiyaye mu shiga tashin hankali,"

"Ameeen malam Allah ya kaimu goben"

"Ameeen,"

Sadeeq ne ya gaida mahaifin nashi sannan ya tsaya a bakin qofar bayin Yadiko ta shiga da dafa bango,har ta gama lalurar da zata yi ta fito suka yi wa Ɗan liti sallama suka shige ciki suka barshi nan zaune.

Be bar wajen ba sai wajejen sha biyu da 'yan mintuna na dare wanda ya tabbatar da cewa Innoh ta yi bacci a wannan lokacin.

Jin ya shiga d'akin Innoh ne ya sanya Yadiko sauke ajiyar zuciya tare da faɗin,

"Allah ya kyauta,"

Addu'o'in bacci ta fara karantowa irin su Ayatul kursiyyu,suratul falaq, suratul nas, suratul ikhlas, sai addu'o'in da suka zo a sunnar Annabi Muhammad yana yi kamar su...

"Allahumma inni as'alukal'afiyah,
Ya Allah! Kai ne Ka halicci raina, kuma Kai ne Kake karbarsa,gare ka kaɗai mutuwarsa da rayuwarsa suke,in ka rayar da shi, to ka kiyaye shi,in Ka ɗauke shi, to Ka gafarta masa. Ya Allah! Ina rokonka aminci daga dukkan mummuna. Bismikallahumma amutu wa ahya,"

Rintse idon ta ta yi ta hau karanto  suratul ikhlas sau goma dan tana so ta samu falalar da ake samu ta samun gida a aljannah a duk sanda mutum ya karanta ta sau goma a lokaci ɗaya, a haka bacci mai daɗi ya ɗauke ta, Sadeeq kuwa ya jima da yin baccin shi.

A can d'akin su Saddeqa kuwa yanda ta kwanta tana jiran Ɗan liti ya shiga d'aki ta je wankin uniform a haka ta yi bacci cike da mafarkai kala kala.

A dai-dai wannan lokacin kuwa rana ce tarrr a wajen Sule saboda live da ya kunna a gidan shi na TikTok, duk yanda me rai yake tunanin abubuwan da wasu daga cikin yaran hausawa musulmi ke aikatawa a TikTok abun ya wuce tunanin su,wasu daga yaran hausawa rayuwa suke a TikTok kamar a gidan karuwai, wani lokacin ma gwanda gidan karuwai ana samun d'aki a keb'anta da juna, wannan kuwa a fili suke yin duk wani kalamai da nuna tsiraicin su ga junan su a haka har su gamsar da junan su, Sule shine shugaban haɗa wannan badaqalar a live ɗin da yake gabatarwa, ya haɗa mata da maza kala-kala daga garuruwa daban-daban,wasu ma dan lalacewa mace da mace ke neman junan su, wasu kuma namiji da namiji ne ke neman juna.

Wani irin daɗi Sule yake ji dan kuwa shima bana zai fara amfana da kud'in da ake samu ta hanyar yin wannan sabuwar harkar da ya fara,da ya ji kowa ya lafa zai san yanda ya yi ya sake kunno musu wutar sha'awar junan su.

Ana haka suka samu wai bawan Allah ya yi joining gidan bad'alar tasu ya hau yi musu wa'azi da nasiha akan su dena abinda suke yi saboda duniyar ma dika dika nawa take? Kar su manta akwai qananan yara dake tasowa idan suka yi karo da wannan videos ɗin fa tinda wasun su suna recording abinda ake yi har su watsa a kafafen sadar da zumunta na shafukan internet kala-kala,nan take kuwa Sule da jama'ar shi suka wanke bawan Allah'n nan da zagi ta uwa ta uba,suka yi masa tatas suka sauke shi akan live ɗin nasu, suka ɗora daga inda suka tsaya.

Cikin masifa da jin haushi Sule yace,

"Guys mu ci gaba da jin daɗin mu ai Allah gafururraheem ne, idan zai yi mana rahama wata shegiyar ko wani shegen se ya hana,"

Wani daga cikin matasan dake kan live ɗin ne yace,

"Rabu da jahilai munafukai ai duk masu wa'azin nan mun san su sai da suka gama jin daɗin su suka gama biyan buqatun duniya sannan zasu fake da yi mana wa'azi, matsiyaciyata kawai gaskiya Babban yaro ka dena d'akko mana 'yan yawa suna katse mana jin daɗin mu, Baby kina ji na kuwa ko kin yi bacci?"

Dariya Sule ya yi sannan ya sake maqalewa a jikin bangon d'akin shi da ya sanya wa labule me kyau saboda kare yawa, headphone na gani mai kyau da tsada maqale a kunnen sa, rigar sa mai datti ya dakko ya goge zufar da ke tsattsafo masa saboda rashin wutar lantarki sannan ya wurga ta gefe ya kunna fitilar da yake amfani da ita mai haske dan baida kud'in siyan ring light,camera ɗin sa ya kunna ya ci gaba da zantukan batsa dake sake kunna wutar sha'awa a tsakanin matasan.

Qarfe biyu da minti arba'in da biyar na dare 2:45am, Munir ne zaune a saman gado ya kasa rintsawa saboda wasu azababbun sauro dake ta sintiri wajen d'ibar jinin shi suna bushasha, zaune yake  ya sanya riga da wando na shadda fara qal dan a ganin shi idan suka gan shi da farin kaya za su kyale shi ya rintsa, amma inaa gaba ɗaya sun ishe shi da kuka da cizo,ji ya yi kamar shima ya fashe da kukan dan takaici.

"Da na san haka gidan yake da sauro da na siyo magani kafin na zo, amma abinda zan yi kenan gobe da sassafe wataqila na samu na koma baccin safe,"

Haka Munir ya kwana zaune har aka fara kiraye-kirayen sallar asuba, idanun shi sun yi nauyi sosai saboda baccin da ke cikin su, haka ya miqe ya shiga bathroom ya yi wanka ya yi alwala sannan ya fita dan zuwa masallaci daga nan ma ya samo maganin sauro ko kuma ya je dakin Granny ya yi baccin.

Ɓangaren Saddeqa kuwa yau ko tashin da ta saba yi da dare bata yi ba saboda ko addu'ar bacci bata samu damar yi ba ta kwanta,dan haka a firgice ta tashi saboda wani mugun mafarki da ta yi, nan take ta hau qoqarin tina abinda ta gani a mafarkin nata amma ta kasa,ganin ba zata tina bane ya sanya ta tashi ta yi sauri ta yi alwala ta yi sallah, tana idarwa ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login