Showing 228001 words to 231000 words out of 276165 words
Chapter 77 - GIDAN DAN LITI BOOK COMPLETE BY HAMIDA SANUSI AHMAD.txt
cikin parlourn, sigarin hannun shi ya zuƙa ya fesar kafin ya ce,
"Barka da dawowa sarauniyar mu,ai tin wancan satin nake ta zuba ido na gan ki kamar yanda kika yi alƙawari sai naji shiru, dole ta sanya na sake jinkirta aika kayan nan nace sai kin zo kin gani."
Hayaƙi Any ta busa sama sannan ta samu waje ta zauna,nan take wata matashiyar budurwa da ta sha ado da wasu ƙananan kaya ta tawo da ƙaramin faranti saman shi ɗauke da giya ta fara takowa inda Any take cikin yanga da yauƙi, Alhaji ne ya kece da wata mahaukaciyar dariya yana kallon Any, dan kuwa ya san dole ta yaba da wannan yarinyar da ya ware ta musamman dan tarbon ta,da ido Any ta kafe yarinyar tana jin wani irin tausayin ta a ƙasan ran ta,da ace ta san abinda ta sani da bata jefa kanta cikin masifa da bala'i irin na bariki ba,a zahiri kuwa sai ta lashi leɓen ta na ƙasa sannan ta kalli yarinyar ta nuna ta da hannu sannan tayi mata alama da ta juya ta gani, shewa wajen suka ɗauka banda masu gadin Any mutum takwas,cikin isa da gadara Any tace,
"Baby na ce bata da lafiya,tinda muka dawo tana asibiti shi yasa na ɗaga zuwan zuwa wannan lokacin,ina godiya da hospitality Alhajin Allah,na yaba da wannan kyautar dan kuwa ina buƙatar ta,baby zo mu je ki ɗebe min gajiyar dake tattare dani."
Miƙewa tsaye Any tayi ta kama hannun yarinyar da niyyar su wuce ɗakin da ake saukar ta a dik sanda suka zo resort ɗin,cikin wata iriyar murya suka ji an ce,
"Police !"
A gigice mutanen wajen suka hau guje-guje,nan da nan Alhaji ya hau waige-waige yana neman yaran shi,gani ya yi be ga kowa ba,shi kan shi an sace bindigar jikin shi,kallon Any ya yi ya saki wani shu'umin murmushi,nan take ya gane abinda tayi masa,cikin lokaci ƙanƙani ya haɗe fuska ya kama tauna haƙoran shi,a haka aka damƙe shi da mutanen shi aka cika mota da su akai Hisbah dasu,a wani ƙaton hall aka ajiye su aka kulle,dan kuwa dare ya tsala sai aka bar su anan kafin safiya tayi a waiwaye su.
Any na ganin an samu nasarar aikin da za ayi sai hankalin ta ya kwanta, tsoron dake cikin zuciyar ta ya kau,a daren ta wuce wajen Billy da ta fara jin sauƙi sosai, dan kuwa tana zama lafiya ƙalau ba tare da damuwar komai ba, ƙurajen dake gaban ta da bakin ta ma sun fara warkewa.
Any na zuwa inda Billy take sai ta faɗa jikin ta ta fashe da kuka ta ce,
"Bilkisu mun samu nasara alhamdulillah,an kama Alhaji da mutanen shi,Bilkisu hankali na ya kwanta, amma kuma ta wani ɓangaren ina jin tsoron abinda zai je ya zo."
Cikin farin ciki Billy ta sharewa Any hawaye sannan tace,
"Anam kar ki ji komai, Allah yana tare damu,inshaa Allahu babu abinda zai faru sai alkhairi,ni dai dan Allah gobe ki kira min su Baba su zo na gan su, ko kuma ki kai ni gida."
"Sai dai na kai ki gida Bilkisu saboda ni kaina dama mun shirya da an kama su zan tafi na ɓuya,saboda idan na zauna a gari akwai matsala,kar ki manta ƙungiyar mu babbar ƙungiya ce,na tabbata zai yi wahala Alhaji be kuɓuta ba,idan ya fito kuwa sai ya yi ajali na tabbas."
"Inshaa Allahu babu abinda zai same ki sai alkhairi."
Haka suka dinga tattaunawa har aka kira asuba, sallah suka yi sannan suka fara tattara kayan su dan fara shirin barin asibitin koda kuwa ba a sallami Billy ba. suna kammala shiri Man yazo da mota ya kwashe su sai ƙauyen Ba Mugu.
********************
Amarya Huzaimah ce zaune a ɗakin ta tana jiran ango, shiru ango bai shiga gidan ba balle ta gan shi a ɗakin ta,ta jima sosai a ɗakin tana zaune kafin taji ƙarar mota,sake rufe fuskar ta tayi tana wasa da yatsun hannun ta, fuskar ta ɗauke da murmushi,ba ƙaramin so take yi wa Abdul ba,ta yi alƙawarin zama da shi a yanda yake har Allah ya bashi lafiya,za kuma tayi dik wani ƙoƙarin da ya dace tayi dan ta ga ta taimaka masa ya samu lafiya.
Bakin shi ɗauke da Sallama ya shiga ɗakin,ledar hannun shi ya ajiye a gefen ta kafin ya cire babbar rigar shi ya zauna a gefen ta, cikin wata iriyar murya idanun shi na zubar da hawaye ya ce....................
[09/08, 10:39 pm] Aunty Hameeda: GIDAN ƊAN LITI
RUBUTAWA : HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 92:
"Bani da bakin da zan yi miki godiya Huzaimah akan amincewa da kika yi kika aure ni dik da kin san lalurar dake tattare dani,na gode,na gode Huzaimah Allah ya bani ikon kulawa da ke,Allah ya bani ikon faranta miki har ƙarshen rayuwar mu."
Cike da jin nauyin shi ta share masa hawayen idanun shi da hannu ɗaya,murmushi ya yi mara sauti sannan ya kama siraran yatsun hannun ta ya sumbata,hawayen shi ya ƙarasa sharewa da kanshi,sannan ya tashi tsaye ya riƙe mata hannu ta miƙe itama,hanyar band'aki suka je ya buɗe mata ƙofa sannan ya ce,
"Bismillah shiga kiyi alwala anan bari naje na dawo ko?"
Ɗaga masa kai tayi a hankali sannan ta shiga banɗakin bakin ta ɗauke da addu'ar shiga band'aki,Abdul kuwa yana fita sai ya wuce ɗakin shi ya rufe ƙofa,tsayawa ya yi yana tuna ranar da aka kai masa Mommy da alƙawurran da ya yi mata tin a ranar su ta farko,tabbas ya tafka babban kuskure a baya wanda yake fatan wannan karon ya kiyaye maimaita irin shi.
Alwala ya yi sannan ya fesa turaruka ya koma ɗakin da Huzaimah take,yana shiga ya tarar da ita tana zaune a saman abun sallah tana jiran shi,da alama ma sallah ta idar kafin ya koma,ba tare da ya ce komai ba ya hau abun sallah suka tada sallah,sai da suka yi raka'a biyu sannan suka yi sallama, addu'o'i Abdul ya yi wa Huzaimah sannan ya jawo ledar dake ɗauke da abincin amarcin da ya watsar a gefe tin shigar shi ɗakin,kaji ne manya guda biyu an naɗe su a irin ledar nan ta gashi mai ƙyalli,soyayyan dankalin turawan dake ciki kanshi ya naɗi romon da akai gashin kazar dashi,nan take cikin Huzaimah dake tattare da muguwar yunwa ya hau ƙara,dariya Abdul ya yi itama ta sunne kai a mayafin ta tana dariya ƙasa-ƙasa,sai a wannan lokacin ta tuna da rabon ta da abinci tin safiyar ranar da za a kawo ta,shima kunun gyad'a kawai ta sha da aka matsa mata sai ta karya,babu ɓata lokaci suka fara cin abincin su suna korawa da madara,dik yanda Huzaimah take jin kunyar Abdul bai hana ta zagewa ta ci ta ƙoshi ba.
Suna kammalawa Abdul ya tattare komai ya mayar kitchen,ragowar abinda suka ci ya sanya a fridge ya rufe,kafin ya koma ɗakin har Huzaimah ta sauya kayan jikin ta ta wanke bakin ta tayi shirin bacci,kame-kame Abdussaboor ya fara yi,ya rasa yanda zai yi da ran shi,ga mace har mace a gaban shi,kuma yarinyar da yake so amma babu halin taɓawa,wani irin malolon baƙin ciki ne ya takure masa waje ɗaya a ƙirjin shi,ganin tsayuwar da yake yi a bakin ƙofa tayi yawa ne ya sanya Huzaimah ta kalle shi,cikin siririyar muryar ta mai dad'in sauraro ta ce masa,
"Da alama dai angon Huzaimah bai gaji da kacaniyar biki ba shi yasa ya tsaya a tsaye kamar soja,ka zo ka kwanta ka huta dan Allah bacci nima nake ji."
Tana gama faɗin haka ta saki hamma ta gyara kwanciyar ta ta juya masa baya ta rufu da bargo,ganin hakan da tayi ne ya bashi ƙwarin guiwar hawa gadon ya zauna a bakin gadon,ya jima zaune a wajen har sai da ya ji ta fara sauke numfashi a hankali alamar ta samu bacci sannan ya tashi ya rage kayan jikin shi ya kwanta a gefen ta,ya jima sosai yana saƙa da warwarewa kafin bacci mai daɗi cike da mafarkan Mommy da Amir ya ɗauke shi.
***********************
Washegari da sassafe aka fitar da su Alhaji daga inda aka kulle su,bayan an sanya musulman ciki yin sallah ne aka sake maida su aka kulle,da misalin takwas na safiya aka kai musu abinci,wasun su ne suka karɓa suka ci musamman matan,wasu kuma sai suka tsaya suna kallon abincin a wulaƙance suna surutai,Alhaji kuwa ko kallon abincin ma be yi ba saboda ƙuncin da yake ciki na cin amanar da Any tayi masa,babu kalar azabar da bai ayyano yana gana mata ba daga daren ranar har zuwa wayewar safiya. Da misalin ƙarfe goma na safiya aka buɗe su,kwamandan Hisbah ne ya fara sanya su a gaba ya dinga yi musu wa'azi da nasihohi,dik wata aya da hadisi da ya kamata ya jawo musu ya jawo musu,daga ƙarshe an samu mutum shida da ba musulmai ba sun karɓi musulunci kuma sun yi alƙawarin sauya rayuwar su daga ta bariki zuwa rayuwar ƙwarai,wasu da dama suna da ilimin addinin takewa suke yi dama sai suka karɓi nasihar kwamandan suka yi alƙawarin sauya halin su daga mummuna zuwa kyakkyawa,kwamanda ya yi wa matan alƙawarin sama masu mazajen aure dai-dai da su saboda su samu wanda za su ɗauke musu lalurorin yau da gobe ba sai sun fita neman kuɗi da jikin su ba,masu taurin kai kuwa kamar su Alhaji,sai suka ƙi karɓar nasihar,tabbas zuciyar shi tayi rauni da nasihar da akai masu,amma ɗaukan fansa da son yin ramuwar gayya ita ta hana Alhaji risina,ya yi wa zuciyar shi alƙawari koda zai shiryu ya bar wannan muguwar ɗabi'ar ba zai bari ba har sai ya wulaƙanta rayuwar Any da dik wanda ke da hannu a yaran shi wajen kama shi,dan kuwa yaran shi da ya tarar an kama a wajen bai yarda da su ba, a ganin shi dik yana daga cikin shirin da aka ƙulla dan kawai a kama shi.
Ba a ɗauki wani dogon lokaci ba aka tura su kotu dan yanke musu hukuncin da ya dace da kowannen su, Alhaji kuwa lauyan shi ya kirawo aka hau jan shari'a dik da cewa ya san yana da laifi,kuma mutanen wajen sun shaida hakan.
Nan da nan ya fara yi wa mutanen kotun yayyafin nera,tin daga kan ƙananan ma'aikatan dake da hannu akan case ɗin har zuwa kan alƙali mai yanke hukunci. Sai da aka yi sati ɗaya ana shiga kotu akan shari'ar Alhaji,sai da Alhaji ya gama yayyafin nera aka yanke masa hukunci akan laifukan da aka kama shi da su na safarar miyagun kwayoyi,safarar mata da maza zuwa kasashen turai,da kuma laifin buɗe gidan karuwai da na barasa a cikin garin kano garin musulunci,Alhaji bai taɓa zaton zai rasa wannan case ɗin ba,dan haka daga karshe dole jikin shi ya yi sanyi ya dena jiji da kan da yake yi,a ranar da aka yanke masa hukunci akan laifukan shi a ranar Hajiya tazo kotu ta dage sai an raba auren su, dan dama babu abinda yake yi mata sai ta yi wata sama da shida bata sanya shi a ido ba,babu ɓata lokaci alƙali ya raba auren su a kotun,zage-zage ya dinga yi yana tonawa kan shi asiri akan irin maƙudan kuɗaɗen da ya kashe dan a murɗe case ɗin amma aka ci amanar shi.
Direct gidan gyaran hali aka wuce da Alhaji da sauran mutanen da aka yankewa hukunci a wannan ranar,Alhaji na zaune a motar da za ta kai su gidan gyaran hali ya fashe da kuka,kuka ya dinga yi har sai da ya baiwa wasu haushi a wajen ganin ai bashi kaɗai bane zai shiga bala'i to meye na yi musu kuka ya dame su?
Cikin tsawa wani riƙaƙƙen ɗan daba ya kalli Alhaji ya ce,
"Kai dalla malami rufewa mutane baki ko na yi maka kuya anan."
Kallon shi Alhaji ya yi ya ga yaro ne ƙarami ba wani babba ba,yara kamar shi sun sha zuwa suna neman taimako a wajen shi akan ya taimaka ya kai su ƙasar waje suma su nemo arziƙin Allah,sai ya wanke su ya gogar da su sannan yake saka kowa a inda ya dace,murmushi kawai ya yi ya hau goge hawayen shi.
A rayuwar shi bai taɓa zaton zai ƙare a haka ba,ya yi bala'in raina hukuncin mahukuntan ƙasar Nigeria,a zaton shi a kowacce kotu ce ake murɗiya har a ƙi yanke wa mai laifi hukuncin da ya dace saboda abun duniya,ya raina kotu da hukumomin tsaro na Nigeria gaba ɗaya,ganin su yake yi maƙasƙantan da ba zasu iya karya daular da ya gina ba, gefe ɗaya kuma ya yi mamakin yanda manyan ƙasan suka dinga barranta kansu da shi a lokacin da yake tsananin buƙatar taimakon su.
Suna isa aka hau gudanar da dik wasu formalities da ake gabatarwa kafin a baiwa firzina ɗaki,rigunan da aka baiwa su Alhaji su sanya sai da suka sake sanya shi fashewa da kuka,shi Alhaji mai daloli da nerori ne zai sanya wadannan wulaƙantattun kayan? Yana kuka yana komai aka tasa ƙeyar shi cikin ɗakin da zai zauna,wani irin amai yaji yana taso masa saboda tsananin wari da hamamin da ya ziyarci hancin shi,manyan maza guda bakwai ne a cikin ɗakin shine cikon na takwas ɗin,kallon Alhaji suka dinga yi suna kallon ogan su,umarni kawai suke jira ya basu su yi masa irin marabar da suke yi wa baƙi irin shi. Sun jima suna kallon kallo da Alhaji kafin matashin da ba zai wuce shekara talatin da bakwai ba ya sakko daga saman gadon shi ya tsaya a gaban Alhaji,sai da ya zagaye Alhaji sau uku kafin ya tsaya a bayan shi ya ce,
"Alhaji Tanimu Daloli barka da zuwa gidana !"
A matuƙar razane Alhaji ya ɗaga kai ya na ƙoƙarin juyawa dan ya sake kallon matashin da ya kira sunan shi,wani irin duka yaji an sakar masa a kan shi wanda ya yi sanadiyyar sumewar shi a wajen,Alhaji bai sake farkawa ba sai da duhun magariba ya gabato,sanda ya farko kuwa wata iriyar azaba ce ta ratsa bayan shi, ya ji kamar zai yi bahaya a wajen da yake kwance babu sutura a jikin shi,cikin sauri ya hau neman kayan shi bai gani ba sai a can ƙasan gadon da yake kai,a razane ya miƙe yana tafiya kamar ɗan shayi ya kwashe kayan shi ya fara suturce jikin shi,cikin wani irin tashin hankali yake bin mutanen ɗakin da kallo,gani ya yi suna binshi da wani irin shu'umin murmushi,cike da shaƙiyanci wanda ya daki kan Alhaji ya sumar dashi ya ce,
"Gaskiya Oga ban taɓa zaton za a samu wannan tsohon kwankwan ɗin a matsayin virgin ba,ka ji waje a matse malam babu wata hayaniya da ƙyar aka samu hanya?"
Dariya suka bushe da ita sannan matashin ya ce,
"Na baka shi Ɗan Saurayi,ka ci gaba da jin daɗin ka,dama ai shi ya fara kaini inda aka koya min wannan harkar,sai da na saba da dukiya da jin daɗi ya yi wa kwalawa shune na suka ƙundume ni,to gani ga ka yanzu a ɗaki ɗaya,a yanzu ne zaka gane kowa a gidan shi sarki ne,ni nan ne gida na kamar yanda kuka ƙulla min sharri kala wajen uku har hakan ya yi sanadiyyar zamana anan zan kuma ƙare rayuwar tawa anan,zan nuna maka cewa ni ne ke mulkin gidan nan dik wani me neman maza a gidan nan sai ya amfana da kai Alhaji Tanimu,sai ka zama karuwar mazan gidan nan ka rubuta ka ajiye wannan maganar tawa,hanya ɗaya ce zata cece ka kana so in faɗa maka?"
Cikin sauri Alhaji da ya gama sanya wandon shi ya zube a gaban matashin yana kuka ya ce,
"Ina son sanin hanyar Kailani,dan Allah ka sanar dani dan na kuɓuta,ka tausaya min na tuba na bi Allah da mahammadu manzan sa na bi ka,kaico na ni Tanimu,da na sani na ɗauki nasihar Hisbah da ban kawo nan ba, na tabbata da hukunci na ya yi sauƙi,dan Allah Kailani ka yi hakuri akan abubuwan da muka yi maka ni da Any."
"Ai babu hakurin da zaku bani na ji,ka san kuwa irin wahalar dana sha anan? Ka san azabar da na dinga sha har na zama jan wuya? Dole kai ma ka ɗanɗani mafiyin ta,hanya ɗaya ce zata kuɓutar da kai daga hannu na da yara na a gidan nan, wannan hanyar kuwa itace ka ɗauki ranka da kan ka,mutuwar ka ce kawai zata yi maka katanga daga azabar da zan yi ta baka."
Kuka Alhaji ya fashe dashi yana tuna irin yanda ya baiwa yaron horo na musamman daga karshe da kwaɓarsa zata yi ruwa a hannun hukuma shida Any kawai sai ya yi wa yaron shune aka kama shi da manyan laifuka ciki har da kisa.
Dik yanda Alhaji yaso ya samu ya gasa bayan shi bai samu ba saboda kurkuku ba gidan kowa bane balle ya yi mulki yanda yake so,ƙarshe a haka ya kwanta cike da azabar da yake ji tana ratsa shi a bayan nashi kamar zai rasu,tashin hankalin shi bai ninku ba sai da dare ya ratsa yaji wanda aka kira da Ɗan Saurayi yana lalubar shi cikin daren da sunan yana neman ƙari,duk yanda Alhaji yaso ya saka ƙarfin tuwo ya hana sai mazajen nan suka yi masa rumfa,wasu suka juya shi suka tale shi wasu suka rufe masa baki,a haka Ɗan Saurayi da sauran mutum uku dake bin maza a ɗakin suka ƙara neman Alhaji, kafin gari ya waye Alhaji ya suma ya kai sau huɗu,dik abinda ake yi Kailani na kallo yana jin wani daɗi da nishad'i a cikin zuciyar shi.
**********************
Motar su Any ce ta tsaya a ƙofar gidan Mai Dusa,Shamsu na zaune a shago ya kammala sanya cajin mutane yana turawa wasu mutum huɗu videos ya ga tsayuwar dalleliyar mota a ƙofar gidan su,cikin faɗin rai ya hau nunawa mutanen wajen ai ya san masu motar wajen shi aka zo,kafin ya miƙe ya nufi motar Billy da Any sun fito,washe haƙora ya sake yi yana sake baza kafaɗu yana cikawa mutanen wajen baki,tin daga cikin shagon ya ware murya dan son a sani ya ce,
"Ke dan ƙaniyar ki zaki zo gida shine babu ko waya ki faɗa min? Ku shiga bismillah gani nan shigowa gidan to."
Murmushi Billy tayi dan ta riga ta san halin yayan nata da fafa da son a sani,kayan su Man ya dinga fitarwa a bayan mota har ya kammala,bayan ya gama ne ya tsaya suka yi sallama ya d'aga