Showing 300001 words to 303000 words out of 495987 words

Chapter 101 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

ta  zaunar daita  a bakin gado  tana  kuka mumy   tace "mamana fada   min  abinda  kike so  nayi  miki  ki hakura ki rungume  auren  muradi ? Kisna tayi shiru taki yin magana illa shesheka" me za'a bata anan duniya da wuce a aura mata musa suje  suyi rayuwarsu muddin rai ".

"meye  ban  miki ba a rayuwa  tun kina ciki nake wahala dake  har  zuwa   haihuwarki dan inganta   rayuwarki   nayi miki  komai tunda nayi silar zuwanki duniya   nima a  karo na farko kiyi min  alfarma". mumy ta karashe maganar da kyar tana jan  numfashi   kisna ta d'ago  kanta hawaye na sake zuba mata ta tsurawa mumy idanu kafin daga bisani tace   "mumy  ke  uwace  kuma nasan  kin min komai a rayuwa amman nasan kin san yadda tasirin  soyayya  yake a zuciyar dan adam  ?mumy  tace "kwarai da gaske kuwa   nasani sai dai ita kanta  soyayyar zai fi kyau  ka ajiye a muhallin daya  dace  ba kowa zaka  iya sadaukarwa da zuciyarka ba ,  kisna  ta rike hannunwan  mahaifiyarta  cikin nata  tana  wani irin kuka  yayinda jikinta ke karkarwa "dan  Allah mumy   na  rokeki ki min rai   ki  taimakeni ki  fadawa  dady cewar  ya bar  zance aurena da muradi   saboda bana sonshi  ...."  da sauri ta mumy ta d'ago ta  tsura mata  ido  tana kallonta tare zare hannunwata dake rike cikin nata  "Wallahi  mumy  da ina sonshi  koda  cikin cokali ne  zan  hakura na auresa  amman  banason  shi kwata  kwata  idan ma na  ganshi  ji nake kamar na mutu   ......."
mumy  tace"subhanallahi  Kisna ta  goge hawayenta da bayan hannunta kana ta cigaba da magana cikin kuka "muddin  kina bukatar  ganinsa a raye ku  janye  batun auren nan  dan komai zai iya faruwa   "... mumy  ta sauke ajiyar  zuciya a daidai lokacin  da  aunty ummi ta  shigo  dakin bakinta dauke   da sallama "Assalamu  alaikum "
"Waalaikum sallam mumy  ta amsa mata  a can  kasan  makoshi  tare da cewa "gara da kika zo ki  ummi  tayani shawo  kan wannan  yarinyar  na rasa abinda ke damun  kisna  ana gabas tana yamma " aunty  ummi  ta zauna tana  huci  ita kuma kisna  ta cigaba da rera kukanta  mai ban tausayi qirjinta  na wani irin zafi mumy  ta bita da kallo  tana   share kwalla wani abu  na  takare mata a qirji adalilin kalaman kisna  "babu abinda zance  akan yaron nan musa  Ummi   sai  dai nace ubangiji  Allah yayi min  sakayya  akanshi saboda ya cuceni ya lalata min rayuwar    yarinyata " tayi shiru  tare da sauke numfashi  gaba-daya mumy  ta nemi natsuwarta  ta rasa ji take  kamar  zuciyarta  zata  buga  ganin rarrashin da  ake mata ma sake tunzura  zuciyarta yake tayi  tunanin sauyashi zuwa  wani sabon hakuri  ta hanyar rusuna mata dan haka ta fara  magana cikin sigar rarrashi     "kisna  kiyi  hakuri  ki  rungumi muradi a matsayin mijinki , muradi  zabin  mahaifinki ne  kuma zabinmu ne  gaba-daya ba zaki taba yin danasanin  ba  idan kika auresa , zai  kyautata  rayuwarki   ,kiyi hakuri  karki  bari wannan damar  ta subuce miki wallahi  idan  kika rasa wannan  damar har abada  kisna  bazaki  samu kamarsa ba mumy  ta karasa maganar  tana kuka tare da  zubewa kasa  a gaban  kisna ta rike  kafafuwanta " ni mahaifiyarki  ce gani a gabanki  na  durkusa miki   bisa  gwiwowina dana haifeki dasu   ina  neman alfarmaki   a matsayinki na  diyar cikina  ki amince  da  auren  nan zakiyi  alfahari  dashi wallahi  bazaki  ta'be ba muddin  kika  mana biyyaya  zaki ga haske a rayuwarki , kisna ta sake  rushewa  da wani gigitaccen kuka tare da tura  kanta  a tsinyar cinyoyinta  tana kuka ,aunty  ummi tayi saurin  durkusawa   ta  kamo mumy  tana kuka amman  ina mumy taki mikewa  tsaye so take taji abinda kisna zata fada  ,zuciyarta zata saduda ko kuwa zata wulakantata akan son zuciyarta ? Kuka aunty ummi  take sosai  kukan da bata  taba yin irinsa  ba a tsawon rayuwarta , kuka  mai cin zuciya domin  bata taɓa haduwa da abun tausayi ba a cikin  duniyarta irin mahaifiyarta,  ganin  abun take kamar a mafarki " wai mumy  ce durkushe   tana kuka tana  rokon kisna akan wani da nmj , kuka take sosai ta juya bayanta inda kisna ke rakube  ta soma dukan bayan  kisna a gigice "haba  kisna dan me zaki zabi  farinciki nmj  akan na  mahaifiyarki kalli kiga mahaifiyarki a durkushe a gabanki tana kuka tana rokonki kisna  sautinta ya hankarar da muradi cikin tsananin tashin hankali ya nufi hanyar dakin har zai shiga sai kuma ya fasa ya fito haraban gidan ya nufi jikin window dakin ya tsaya take qirjinsa yayi wani irin bugawa sakamakon ganin mumy durkushe a gaban kisna tana kuka yaji gaba-daya duniya ta tsaya masa shi kansa idan yace yana son rayuwa da kisna yayiwa kanshi karya bazai dai iya musawa dady bane sannan auren shi zai sake kwantarwa da mumy hankali kamar ya juya ya bar gurin dan kaucewa ganin bakinciki sai ya tsinci kansa da kasa daga kafafunsa dan haka ya cigaba da tsayuwa "zafa kiyi nadama  abinda kika aikatawa kisna   zakiyi dakinsani a lokacin danasanin bazai miki  amfani ba ina tausayawa ranar da hakin mumy zai bibiyeki ba'a nuna kiyayya ƙarara ga  bawa domin baki san me gobe zai haifar ba cikin  kuka aunty ummi  ta  sake yowa kan mumy "dan  Allah  mumy kiyi hakuri ki  tashi  ki  daina kuka kada zuciyarki  ta buga  ki tafi ki  barmu cikin tashin hankali , "hakika in haka ta faru nima bazan zauna  ba mutuwa zanyi  don Allah mumy  kiyi hakuri ", ke kuma  kinyi hasarar  rayuwa   wallahi , nan  gaba sai kinyi da kin sani dan  iyaye sun fi karfin haka "ki barni haka ummi har sai naji abinda kisna ta fada  zata auri muradi ta zauna lafiya dashi ko har yanzu tana kan bakanta ?" tsawon lokaci mumy na durkushe  a gaban kisna  amman kisna  taki saduda bare ta bude baki  tace  ta hakura  da musa mumy ta sake rushewa  da wani sabon  kuka don a ganinta shine ya kamaceta shima muradi hawaye yake zubarwa zuciyarsa na quna   sai da mumy tayi kuka mai isarta sannan tayi shiru, tunaninta yayi nisa cikin tunowa  kanta mafuta ,bazata iya bari a cuci rayuwar  marayan  Allah ba  ɗan  da   shi kadai ya rage  mata a duk fadin duniya tunda zuciyar kisna taki saukowa tana kan bakanta na kin aurensa  gara  kawai a hakura  kada taje  ta kashe  dan mutane a banza tunda gashi   ta furta  hakan a zahiri ta  mike cikin zafin nama ta juya ta fice itama aunty ummi  na ganin haka ta mike ta fita  kisna ta bi kofar da suka fita  da kallo batare da tace uffan ba dan kamar an kulle  mata bakinta illa dai siyayar da hawayen da take ilahirin zuciyarta a kuntace ,muradi ya dade tsaye yana zubar da hawaye sannan ya juyawa window baya yana taku a hankali yana tunanin aibunsa da yasa kisna taki amsarsa a matsayin miji inda mata bilaadadin suke kuka akanshi ga afra macen da kaf family Alhaji lukman suke ji daita a kyau da izza da komai amman yau an wayi gari tana binsa tana kuka tana rokonsa akan ya sota kullum ya bude wayarsa sai yaci karo da sakonninta bilaadadin na yadda ta makance akansa "bazai ce hakin mata ke bibiyarsa yasa kisna taki shi saboda shi yasan bai yaudari diyar kowa ba tun tasowarsa bai taba tsayawa da wata mace da sunan soyayya ba shi dai yasan zai yi aure idan lokacin yayi jiki a sanyaye ya nufi dakinsu kansa na masa wani irin ciwo ya fada kan katifa tare da runtse Idanunshi ....."

har  yamma kisna na kunshe  a daki tana kuka  idanuwanta sun sake jemewa  zee  ta shigo  dakin  ita da kawarta naima da wasu kaya a hannunta dan ita tun da'aka ce aure a satin ta soma shirinta cikin tsananin farinciki   zee tace "a'a hajiya kisna  anan  kan sana'ar ? Kisna tayi mata banza tamkar ba da ita take ba "wai meke damunta ne haka  duk tabi ta  lalace inji cewar naima "barta kawai naima damuwa tasanyawa ranta  wai  aure  za'a  hadata da ya Ali shikenan  ta damu rayuwarta  kan wani can banza wai  shi  Musa "wani  Musa kenan ?"na gidan olegele mana dan  yaron nan mai kama da (tana)  naima tayi saurin zaro  ido tana zama kusa da kisna  ta riko hannunta "haba kisna me zaki da wannan  tana ?kisna ta d'ago tana zabga mata harara.
"tana mana dan  anyi magana kina hararar mutane  "meye marabansa da tana ? "Allah ya baki giwa mai zaki yi da tana ?"wallahi ki zabi  Giwa ki bar tana  dan wannan tana babu abinda zai miki ?" Kisna  ta mike a fusace tana cewa  "ubanki ne tana ba Musa  ba  kuma wallahi kika  sake ce masa tana sai muyi barauba dake  kafin ki bar gidan nan shegiya yar iskar ki tsaya matsayinki bana son shishigi  da neman suna ta fito tana zagin naima  "ba tana ba ko maciji  ne haka nake son shi kuma babu wanda ya isa  ya hanani aurensa  ta karasa maganar tana ihu  kamar wata mahaukaciya  gaba-daya mutanen  gidan suka fito har  mumy  da dady da uban  gayya  muradi  kowa   yayi  tsuru tsuru yana kallonta  tana surfa maseefa ta inda take shiga bata nan take fita ba  "banason aliyu na fada  na sake fada banason shi "kiyiwa mutane shiru da wannan haukan naki ," kisani ko mutuwa kika yi wallahi sai na daura aurenki da Aliyu karewar kiyayya kenan dan haka kiyiwa mutane shiru bana son jin komai daga bakinki "i have to talk   dady ,I really has to talk before everything could mess up with me dole na bayyana rashin son da nake  masa  musa nake so, i say it in from of him and  everyone   "
"ni Kuma bazan aura miki wannan yaron ba bare na  cigaba da ganinku kuna rayuwa tare , ke din diyar cikina ce ,kuma dole kibi umarnina  kuma dolenki ki zauna da Aliyu  ......"

Suna cikin wannan halin suka ji  sautin muryar mumy "dady dan girman Allah " kayi hakuri ka hakura da wannan hadin saboda kasan halin kisna bana ji ta muradi ko wuta  mukace ya fada  zai fada saboda shi dan albarka ne ada can naci burin kisna bazata auri wannan yaron ba amman a yanzu  na yarda ta aureshi "
"Kin yarda ta aureshi mumy ?  Samir ya fada yana kokarin matsowa kusa da mumy "eh na yarda Samir tace ya turo iyayensa kawai a daura musu  aure sai dai akwai sharadi  muddin ta aureshi  wallahi babu ni babu ita har  karshen rayuwarta ciwo mutuwa  duk wani abu da zai sameta karta tako  kafarta zuwa gidan nan  babu ni babu ita har abada  kuma babu ku babu ita duk wanda ya taimaka  mata a rayuwa ban yafe  ba  dady ya numfasa  yana cewa "ni kuma muddin ni ne mahaifinta bata da miji sai  aliyu magana ta kare lokaci kawai muke jira karki dawo da hannun agogo baya uwar marayu kowa yaje yayi abinda ke gabansa daya bayan daya suka juya kowa ya kama gabansa  dady cikin sanyi jiki ya juya yabi bayan mumy saboda lura da yayi ranta a bace yake da maganarsa ta dai ƙasa mutsa masa ne , koda ya shiga dakin kuka ya same tana yi "kiyi hakuri da hukuncina uwar marayu ban haɗa wannan auren dan musgunawa rayuwar Aliyu ba ko cutarwa garesa nayi haka kafin komai ya rincabe mana kema nasan kina son wannan hadin kina dai jin haushin yadda kisna ke nuna tsanarsa a fili ne ,salaha you really has to carry over the tears in my eyes rarrashinta yayi sosai da kyar ya samu ta saki ranta ta dawo daidai  yayi Murmushin jin dadi daga gobe za'a fara shirin buki duk da ba wani event za'a yi ba diner ne kawai shima dan Samir ya bukata ne "Allah ya rufa asiri yasa auren ya zamo silar kwamciyar hankalinm da muke fata  ."dady ya numfasa tare cewa ameen ..

Da daddare Dady na zaune a dakinsa ya rafka tagumi yana tunani kisna ta shigo cike da sanyi jiki ta zauna a gabansa bai kyalleta ba ya juyar da fuskarsa wani gefe zuciyarsa na zafi a duk sanda ya tuna rayuwar da suke ciki lamarin na kona masa rai "wai yau shine yana fada diyar cikinsa na fada akan wani namiji "dady ta kira sunansa cikin raunanniyar muryarta mai shiga jiki "uhmmmm meye kiyi maganarki ina jinki ? " yayi maganar batare daya kalleta ba "dan Allah dady ka kalleni  ina son yin magana da kai "kiyi maganarki ba dole sai na kalleki ba "tayi shiru tana tunani maganar da zata fito daga cikin bakinta yayinda dakin ya dauki shiru yadda bata yi magana ba haka shima bai yi magana ba illa iskar da yake furzarwa qirjinsa na dokawa da matsanancin karfi saboda zuciyarsa cike take da tsoro abinda ya kawota tsawon minti goma sannan ta cigaba da magana cikin sanyi murya "dady ka min alfarma   ka  barni naga musa   yau  ina son  zanyi magana dashi mai mahimmanci daga nan shinkenan  na hakura kuma zan yarda da hukuncinka  amman rashin ganinsa wani gagarumin maseefa ne atare dani yayi mata banza tamkar badashi take magana ba  "wallahi nayi maka alkwari zan bi umarninka "bafa zan yarda da wannan banzar uzurin naki ba zan aura miki Aliyu ina jiran naga abinda zai faru bayan aure maza ki tashi ki bar min daki shasha kawai simi simi ta mike ta fito daga dakin tana zance zuci "yadda kuka rusa min tsari kusani nima zan rusa muku tsari zan kwantar da hankalina ayi biki amman abinda zai biyo bayansa sai ya tarwasa zuciyar kowa  " tana shiga daki ta fada toilet ta kira number musa sun dade a cikin bayi suna waya   tana  masa kuka shi kuma yana rarrashinta da daukar  mata alkwarin baza'a yi auren ba ..."
Tun ranar laraba aka fara gyara gidansu mumy da gidan da kisna zata zauna batare da saninta ba ,daya daga cikin gidan je dady ne dake cikin gra gida biyu ne a hade sai dai get din kowane bangare daban yake , ba zaka ga wanda ya shiga bangaren Samir ba haka zalika bazaka wanda ya shiga bangaren muradi ba dady ya kashe kudi sosai tamkar bai san ciwonsu ba duk da muradi yaso ace ya barsu sunyi komai a aljihunsa amman yaki ."


    Washegari  mumy  na zaune  a ɗakinta sai ga madu da wasu abokansa su uku suna shigowa da akwatunan  lefe suka ajiye suka sake fita tun   tana kirgawa har ta dawo ta daina akwatuna kashi da kashi har kusan set bakwai   kowanne set kalarsa da daban sai dai  duk   iri desing daya ne babu wani bambanci sai na colours take ta fahimta wato akwanan auren kisna ne tana tsaka da kallon akwatinan muradi ya shigo sanye da bakaken kaya da facin cap baki hatta takalmin ƙafarsa baki ne kasancewarsa fari sai kayan suka amshesa fiyye da duk kayan daya saba sakawa  sai kamshi yake zubawa fuskarsa ta sake fitowa sosai saboda gyaran fuskar da yayi , ya karaso har gaban mumy ya durkusa yana cire facing cap dinsa cike da girmamawa ya gaisheta "mumy anyi lafiya ?"lafiya lau muradina ya fama da hayaniya ?tayi maganar tana daura hannunta a kanshi ,murmushi yayi sannan yace "alhamdullahi "wadan nan kayan  fa "kayan kisna ne " ya fada yana mikewa tare da zama    akan kujera idanu ta tsura masa   for two second tana masa kallo mai cike da tsantsar mamaki shima ita yake kallo  hawaye ne suka fara turereniyar zubowa akan fuskarta yayi saurin mikewa ya dawo gabanta ya   kamo hannuwanta duk biyu "no mumy farinciki ya kamata kiyi ba kuka ba wallahi bana son ganin hawayenki yana daga min hankali ganinsu yafi kiyayyar kisna  gareni ya kai hannu yana goge mata hawayen sannan ya mikar daita tsaye yana kallonta "bani da uwar da zan kaiwa kayan bare wasu dangin da zasu kawo dole kice uwar ango hannunki suka fi dacewa suzo kai tsaye saboda kece uwata kece komai na rayuwata sai ki nemowa amarya mamanta muje kiga kayan muradinki  abinda bai  yi ba a karo take fuskar mumy ta bayyana murmushi da tsananin farinciki "wai ma a yaushe ka soma hada kayan lefe ban sani ba  ?"jiya zuwa yau ne fa  mumy ya karasa maganar yana Murmushin karfin hali cike da shagwaba ya zaunar daita akan kujerar daya tashi "ki zauna a nan ki huta zan bude miki akwatin daya bayan daya yana gama fadar haka ya karasa ya soma budewa shiru mumy tayi tana jinjina kai murmushi ya subuce mata a lokacin daya bude akwatin  kayan  bacci ganin duk ya zabo hadaddun kayan zamani masu matukar kyau da daukar hankali "da kanka ka zabo wadan kayan bacci ? sai lokaci ya fahimci kuskuren da yayi na bude su agaban mumy duk ya rude cikin saurin murya yace "no !no "ta kalleshi tace "no ? Yayi saurin gyada mata kai alamun "eh " batare da yace mata komai ba da yamma  sai ga Samir danashi shima kusan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login