Showing 366001 words to 369000 words out of 495987 words
Chapter 123 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
amman ya hakura ya danne zuciyarsa ke me yasa bazaki yi yadda yake yi ba". kin manta da komai ki rungumi mijinki shine aljannarki ki daina wani kunbure kunbure banza dan kinga komai kika yi masa yana kyaleki wallahi zan fada masa yanzu idan kin cigaba da kunbure kunbure nan ya mazgeki"cikin Muryar kuka kisna tace "yanzu aunty ummi saboda kin tsaneni sai kice ya bubugeni ?"ni zaki ce a bubuge wallahi kuwa zan yiwa dan'uwanki bori ta k'arasa maganar tana dariya "Shikenan bazan ce ya bubbugeki amman ki saki ranki "na daina inshallahu zan baki mamaki amman wallahi na rasa me yasa yake bani haushi Amman zan dinga kokari na rinka cire kiyayyarsa a raina zan cigaba da hidimar gabana ku ci-gaba da min addu'a sun dade kulle a daki sannan aunty ummi ta mike tayi mata sallama ."
******
Tunda kisna ta dawo gidan bata shiga harkokin muradi zamansu kamar da babu girki babu aikin komai sai tayi ra'ayi sai dai babu zagi babu kallon banza lamuran gabanta kawai take shima haka baya shige mata ya barta har sanda zai samu wacce zata soshi da qaddarar rayuwarsa, komai tayi ido ne nashi hatta wayarta da musa ta dawo babu ruwan ta ko a gabansa amsa kira take wannan dai ya kasa hakuri dan haka ya shiga ya fita har sai daya ga an kama musa an tsareshi a hannun ma'aikata kuma yace duk wanda yazo kar abada belensa hakan ya kwantar masa da hankali ita kuwa rashin samunsa ya daga mata hankali sai dai ba kamar yadda take ji ada ba wanda idan da ne bataji muryarsa ba sai tayi kamar zata mutu ya shigo ya isketa tana Zariya a falon rike da waya kallo ya fahimci inda damuwarta ta dosa bai wuce akan rashin samun number musa ba ya d'auke Idanunshi ya shige d'akinsa ".
watan hudu kenan da komawa kisna gidan muradi sai ga sadiq tare da madu ya kawo shi a wata safiyar asabar muradi na zaune a falo yayinda kisna ke zaune a dakinta sautin Muryar muradi dake fita da karfi ne yasa ta fito da sauri dan bata saba jin sautinsa haka ba shi din mutun ne mai magana cikin sanyi murya kuma a natse , tana fitowa idanunta ya sauka akan wani matashi kyakkwa mutun mai kyaun gaske kamar muradi sai dai shi dogo ne kuma baki sai dai fuskar da jikinsa da kwai alamun yana smoky ta k'arasa shigowa falon inda muradi ke faman dukan qirjinsa "irin rayuwar da za'bawa kanka kenan kou?" wannan shine alkwarin da muka yiwa mahaifiyarmu ?" ka maida kanka dan shaye shaye yanzu zuwan me kayi "? ka tashi ka bar gidan nan banason ganinka har sai ka dawo yadda nake son ganinka ta yadda shi kanshi makiyinmu zai yi nadamar abinda ya aikata mana madu ya shiga tsananinsu yana bawa muradi baki akan yayi hakuri "babu wani hakurin da zanyi madu kace masa kawai ya wuce banason ganinsa wai a kalli sadiq a kalleni ace uwa daya ce ta haifemu ? yayi maganar kamar zai yi kuka zuciyarsa na tafasa " na dauka shine wanda zai tallafi rayuwarmu a she Shima zai dawo tamkar wancan mashiririnci uban nasa ne ," shifa mahaifiyarmu ta danka amanarmu a hannunsa Amman kalli yadda ya dawo kalli yadda ya maida rayuwarsa kamar dan daba duk sadiq ya rude sai zufa yake fitarwa yana cewa "kayi hakuri dan'uwana nima ba'a son raina bane wallahi zan canza zan dawo tamkar yadda kake son ganina "ya Ali kayi masa hakuri kaji abinda yace dan Allah ka barshi ko zuwa anjima sai na dawo na d'aukeshi daman mumy bata ce ya zauna tare daku ba tace akawo shine ku gaisa " .nan take kisna ta fahimci d'aunwasa sadiq ne data take jin labari idan hirar ta dauro a bakin mumy "ni dai madu kace masa ya tashi ya wuce banason ganinsa nasan halin sadiq ya rigada ya dauko mugun halin ubansa ".
"saboda me zakace ya tafi ?"ya tsinkayi sautin Mmuryar kisna cike dakiyar zuciya ya juyo yana ffuskantarta ta tsareshi da kyawawan idanunta masu matukar haske."ya madu ka wucewarka kawai babu inda zashi muna nan tare wani sanyayyiyar ajiyar zuciya madu ya sauke bai taba jin kisna ta burgeshi ba irin yau yayi murmushin jin dadi tare da yi musu sallama ya juya ya wuce."ya sadiq ka zauna mana ya kake wani dari dari ka saki jikinka nan gidan tamkar gidanka ne zauna bari naje na kawo maka abun sha " mutuwar tsaye muradi yayi yana dubanta cike da matsanancin mamaki bai taba expecting zata so dan'uwansa har ta mutuntashi ba zama sadiq yayi yana kallon fuskar muradi kisna ta shiga kitchen ta fito da tire Wanda ke dauke da ruwa da lemu da cup ta fito ta ajiye a gabansa ta bude kwalin ta tsiyaya a cup ta mika masa ka fara sha kafin na gama maka abinci ya gyada mata kawai sannan ya amsa ya kai baki , shi kuwa muradi kallonta ya cigaba dayi , yaji kamar yace kar sadiq ya sha dan yasan halinta yadda bata sonshi din nan zata iya illata duk wani nashi ,sai dai kafin yayi hanzarin hanashi tuni ya shanye ya sake tsiyaya wani yai shiru tare da zuba masa ido suna zaune ta dawo da wani plet mai dan girma Apple da banana da ya'yan inibi ta ajiye masa" kaci kaji ya sadiq wai ma yaushe kazo ne ?"dazu nazo da asuba a gidan takwarana na sauka daga nan aka kawoni gurin mumy shine byn na dan huta tace akawoni nan "ai kuwa mumy ta kyauta nan dai suna hira tana tashi tana duba abinda ta daura ta burge muradi sai dai kuma a ransa yace duk na munafurci ne may be wani shiri ne daita akansa , dan haka ya tattara kayayyakinsa ya shige d'akinsa ya barsu cikin , kankanin lokaci ta gama dafa masa taliya ta kawo masa lomar farko da kyar sadiq ya hadiye saboda rashin dadin abincin ga yajin daga zabga amman haka yayita turawa yana mata godiya ko babu komai ta mutuntashi yana cin tana jansa da hira har ya gama tace ya tashi suje masaukinsa dakin dake bayan part dinsu ta Kai shi "ga daki nan ka shiga ka saki jikinka fa babu abinda zai faru yace "na gode "baka bukatar gode min ta juya ta koma ciki ai tana fita ya fada bayi saboda cikinsa daya murd'a dan baya son yaji ruda masa ciki yake nan ya shiga zuba zawo sai daya kusan minti goma sannan ya fito yana sauke numfashi "idan na cigaba da cin irin wannan abinci zan mutu nan kusa ya fada yana fadawa kan katifa ."
tun zuwan sadiq bai fi sati biyu ba ya fara fahimtar yadda halaiyyar matar gidan yake adalilin rashin kulawar da bata bawa dan'uwansa amman bai tofa nashi ba ya zuba ido tun safe idan yayi wanka yana side dinsu anan yake wuni kallo sallah ne kawai ke tayar dashi tun muradi baya sauraransa har yazo ya hakura ya rungumeshi ko babu komai zamansa tare dasu yanzu yasa shaye shayen da yake sauki da alamun damuwa ce da rashin galihu ya haifar masa dana shi shaye shayen , shima sadiq babu laifi yana da tsafta sosai shi ke share haraban gidan a madadin mai gadi hatta motocin muradi shi yake wankewa bai dauki girman kai yasanyawa kanshi ba shi yanzu rayuwar kaninsa ta zamo abar sha'awa agurinsa sai duk sanda muradi yagansa yana aiki zai haushi da fada "dan me yake aiki alhalin ga mai gadi duk lokaci da muradi ya dawo daga aiki tare yake iske kisna da sadiq suna hira ko tare da mai gadi hakan kuwa yana masa dadi dan haka yayi tunanin kisna ta canza dan haka ya fara shiga cikin lamarinsu ,sai dai duk sanda ya sanyo kanshi cikin hirarsu sai kisna tayi dip ta dauke wuta ta daina cewa komai sosai sadiq ya fahimceta sai dai bai mata magana ba sai dai kuma baya jin dadin yadda takewa dan'uwansa shi duk abinda zata masa muddin zata dinga wulakanta masa dan'uwansa a banza ne a gurinsa muradi ya gyarawa sadiq flat din daya ciki ya zuba masa komai kusan ma sunfi na bangarensa kyau hadadden kafet aka malala a falon sannan aka saka masa na tsakiya wato grass carpet ga ƙatuwar tv bango da speaker komai na part din lemo green ne da ratsin fari a kwana a tashi babu wuya har Sadiq yayi wata uku tare dasu komai yana tafiya normal wanda haka ke kara saka zuciyar muradi samun natsuwa dan har ya fara jansa zuwa officer". a daidai wannan lokacin zee ta haifi danta namiji santalele kyakkyawa mai kama da ubansa sak sosai dangi sukayi murna da wannan haihuwar a ranar muradi suka je tare da kisna wannan shine karo na farko da suka fita tare lokacin da muradi yaga baby tamkar yayi kuka duk zuciyarsa ta jaguke saboda tuno danashi ya'yan da yayi da yanzu nashi sun kai isa tafiya ita kam kisna ko ajikinta ba wai dan ta manta ta kashe ya'yan cikinta ba babu kunya zata kwace yaron Samir ya dakatar daita "karki soma taba min da jiki a sanyaye taja gefe tana kallonsu "Samir kamar na wuce da yaron nan ya shiga raina "ka wuce dashi mana ai danka ne ka masa huduba kafin ka wuce da duk sunan da kake so " wasu hawayen farinciki suka cika a Idanunshi yayi saurin maidasu tun kafin su zubo "na gode Samir na gode da wannan mutuntaka da ka min "karka ji komai muradi ka wuce duk yadda kake tunanin matsayinka a zuciyata soyayyarmu daga Allah ne yayi wa baby huduba da sunan badamasi ya d'ago adaidai lokacin daya gama "sunan yaro Muhammadu badamasi Allah ya raya mana shi yasa makarancin Alqur'ani ne yasa ya zamo irin sheik Aliyu isa pantami irin sheik lawan Abubakar "ameen suka amsa gabadayansu kwana nan su biyu a sabiti aka sallamesu dake lafiya lau ta haihu bayan sun dawo gidan ya cika makil da mutane hatta mumy da dady sun zo sanda kisna ta gaishesu mumy ce kawai ta amsa amman dady ko kallonta bai yi ya sake maida kanshi ga jikansa wanda yaji ya shiga ransa matuka kusan tun da akayi haihuwar kofa fita ta budewa kisna saboda kullum tana gidan kwakume da baby Junior wanda aunty ummi ce tace a dinga kiransa da haka .
da zarar ya Samir ya ga kisna rike da baby babu kunya zai kwace yace "kinsan kina so me yasa kika kashe naki ?"na rantse da girman Allah na sake ganin kin taba min d'a sai naci ubanki la'ada waje wani kallon rainin Sense take masa hakan bai hana idan ta shigo ta gansa ta d'aukeshi "ranar suna muradi ya kashe kudi kamar hauka komai na baby da zee shi yayi duk wanda yaji sunan baby sai yace an kyauta da'akayiwa ya badamasi kara ,walima na musamman muradi ya shirya wa abokansu a white place dake nan cikin gra , suna zaune a kofar gidan akan fararen kujeru dasu jahid Samir ne kawai baya cikinsu ya shiga cikin gida suna hirar suna duban masu aikin gyaran sa da raguna guda biyu "wai kai bazakayi wani abu akan matsalarka ba haka zaka zauna kana kuntata rayuwarka ?"me zanyi jahid da wuce hakuri da addu'a kuma kullum cikinsa nake fatan dai Allah ya kawo min sauki "malam ka bude idanuka sosai ya kake yi kamar baka san duniya ba kota karfi ne ka dinga kusantarta inji cewar habib "idan tayi ciki ta cire ko ?ni kuma na yita hasara ya'yana a'a ta sha zamanta itama ai tana jin jiki dan ba itace bace" .
"ta dade bata zubar ba daka zauna kana takure rayuwarka kai ba mata ka iya bi ba ai gara kayi abinda nace idan taje ta karar da ƴaƴanta ai kanta ta cuta kai ba sai ka qara wani auren ba kuma ka haihu ka barta da mugun halinta "dan Allah ka saki jiki ka kwashi gara ya k'arasa maganar yana kwashewa da dariya tunda suka fara maganar muradi yaji yanayinsa ya dan sauya dan sam shi ya dade da cire batun wani sex a rayuwarsa ko jiya sanda ya shigo gidan da daddare ya lura da yadda kisna ke faman juyi akan kujera tana mika ga plet din abinci a gabanta da alamun abinci ta gama ci kallo daya yayi mata ya fahimci ba komai take bukata sai sex Amman dan mugun hali irin nata take tauye kanta suna cikin tautaunawa sai ga afra ita da wata kawarta sun karyo kwanar unguwar da fari bai gane ko su waye ba sai da suka yo kusa dasu saboda lalacewar datayi tamkar ba afra ba suka shiga gidan take gaban muradi ya yanke ya fadi ga afra tazo ga kisna na ciki ai suna shiga da kisna suka fara arba cikin wata dakakkiyar shadda pich colour mai shegen kyau sai kyalli take ai kisna na ganinta ta bar abinda take ta kwasa da gudu ta rungumeta "aunty afra nah oyoyo "afra ta shafa bayanta tana cewa "baby nayi fushi ko ki nemi?" Kika sa ina ta tunanin ashe haka duniya take "wallahi aunty afra kina raina kullum dake nake kwana dake nake tashi gashi kona kira layinki baya zuwa ya kwana biyu ?"lafiya wayata ce ta samu matsala ga tashin hankali kawai na tattara na ajiyeta "shiyasa amman Dan Allah kiyi kokari ki gyara "inshallahu zan gyara ko dan saboda baby nah ya labari? Kisna tace "akwaisu lodi lodi na tara miki suka sa dariya sannan ta kalli matar dake gefen aunty afra tace "ina yini aunty ?"lafiya lau ya taro alhamdulillah "mu shiga ciki suka nufi part din zee nan hira ta barke sam cikinsu babu wanda ya nunawa afra kyama daga mufeeda har zahra da zee kowa ya sake daita bayan wani lokaci kisna da afra suka samu kebewa " wai aunty afra meye gaskiyar lamari abinda muradi ya fada a wancan ranar ?" karye me ne duk abinda ya fada " to me yasa baki ƙaryata ba a sanda yake maganar ?" ina Ni in Kare kaina mu da muke cikin tsaka mai wuya ai na rantse da girman Allah sai muradi yasan ya taboni sai yasan ya qulla min sharri zan nuna masa nafishi iya wasan "ki barshi kawai aunty afra ni zanji da komai banason wani abu ya sake faruwa dake saboda ina son naga kin koma gidan ya badamasi ki karasa rayuwarki bana son ki fita cikin family din mu "dawowata da wuya kisna har yanzu bana gaban yayanki duk yadda dady ke fama dashi akan ya mayar dani yaki tayi mgnr kmr zatayi kuka "karki damu inshallahu zaki dawo "ya labarin musa kuwa kuna tare kin hakura dashi ?"ina wannan soyayyar ai daga Allah ne ina mugun son dan yarbawan nan tamkar raina sai dai gurin wata uku kenan bana jinsa kuma jikina na bani ba lafiya ba "okay zan bincika miki duk yadda ake ciki zaki ji ai da dai wannan number kike amfani ?"kisna ta gyada mata a nan suka tsaida maganarsu suka mike suka shiga cikin jama'a anyi taron suna lafiya sai muce Allah raya Muhammadu badamasi ".
*****
A wata safiyar asabar tun safe kisna ta tashi ta fara soye soye har ta gama sannan ta dafa shayi wanda ji kayan hadi over ta zuba a flask saboɗa sadiq musamman komai dan sadiq take yi saboda yana yaba mata sosai tana tsaye tana shirya dinnng table sai ga muradi kamar an jihoshi riga ce shirt a jikinsa ta motsa jiki sai wando three quater kanshi cike da suma sai dai daga bayan keyarsa an aske rabi wato dai askin apro gashin sai kyalli yake koda yake daman shi maaboci kula da gashin kansa ne kamar danshi aka haliccnsa , ya tsura mata ido saboda ganinta daga ita sai rigar bacci iya gwiwa suna hada ido gabanta ya yanke ya fadi saboda ganin irin shu'umin kallon da yake aiko mata dashi dauke kanta tayi shi kuma ya fada kan kujera yana cewa "washhhhh sannan ya cigaba da magana a natse "ki daina tsayawa a falo haka kin dai san yanzu bamu kadai bane a gidan " ya dan saci kallonta tana cigaba da abinda take bata ce komai ba ganin haka yace "hado break din sadiq na kai masa tayi saurin cewa "a'a zai shigo ai yayi break anan muradi ya sauke wani sanyayyiyar ajiyar zuciya jin dadi sai dai tana bashi mamaki zai ga inda ba'a son kani ace ana son yaya , mikewa yayi ya shiga d'akinsa yayi wanka ya sauya wasu kayan ya fito alokacin da tuni sadiq ya shigo falon yana zaune tare da kisna yana kwasar girkin kisna mara daɗi ya d'ago ya kalli muradi dake shirin fita yace "dan'uwa kazo kaci abinci mana bai kai ga cewa a'a ba kisna tayi saurin cewa "a'a nifa ban yi girki dan shi ba kai dai kaci idan kuma bazaka ci ba ka ajiye min kayana na zubar gbdy sukayi shiru suna dubanta muradi ya tabe baki sannan ya karaso dinnig table din ya dauki arish kwaya daya ya kai baki ai da sauri ya furzar yana kallon sadiq "yanzu kai wannan abinci kake ci ?"sadiq yayi saurin take masa kafa yana cewa," dadi kou ai kaf Nigeria babu macen da tafi kanwata iya girki kai dai ka zauna ba dan halika ba kaci , kanwata kiyi hakuri yaci ko kadan ne ",no bafa zan bari ba" yadda ta hade rai a lokacin datayi maganar ya kusan sa muradi dariya sai dai ya hadiye yana girgiza kai kawai