Showing 384001 words to 387000 words out of 495987 words
Chapter 129 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
kina kallona abinda kika ji na fada haka nake nufi har acikin raina muddin kina bukatar zama tare damu ".
ta lumshe idanunta dake zubar hawaye "wai duk akan muradi ne yasa iyayenta suke kinta har suke ƙoƙarin haɗa matsayinta dana yar aiki ? " ita ko me zatayi dashi a rayuwata har abada bata qaunar wata halaka ta sake shiga tsakaninsu koda ta gaisawa ce ". a hankali ta maida kanta ta kunshe tana wani irin kuka " babu shakka soyayyar dake tsakanin iyayenta da muradi tana neman katse mata rayuwar jin dadi da iyayenta , cikin yanayi na bakinciki dady ya cigaba da magana "wallahi tunda kikayi sanadin nisantani da ya'yana kema bazaki ji dadin zaman gidan nan ba , sai kin gwamaci zaman kurkuku da zama tare damu". ya k'arasa maganar yana fesar da numfashi mai zafi kana ya maida jikinsa ya jingina da kujerar da yake zaune ya ɗan kwanta tare da lumshe idanunsa zuciyarsa na tafasa " kinji duk abinda iyayenki suka zartar akanki yanzu me kike gani zaki zauna tare dasu ko zaki bini mu koma ?"
muryarta cike da kuka tace "zan zauna tare dasu ". alhamdulillah sai abu na gaba yaya kayi wa girman Allah kai da aunty ku yarda ku amince da auren kisna da yaron nan tunda ta nace ba'a san abinda Allah ya boye a tsakaninsu ba " meye shi abinda Allah ya boye banda wahala ? "wallahi wahala kawai zata sha a hannunsa " dady ya fada still Idanunshi na lumshe " koma dai menene ita tajiyowa kanta, idan dadi ne babu mai tayata sha haka zalika idan ma wahalar ce ita kaɗai zata sha abunta fatana dai ku hakura ta aureshi a wuce gurin ,da anyi auren tuntuni wallahi da yanzu ta girbi abinda ta shuka data soma nadama cikin tashin hankali dan dai kunki amincewa ne wallahi da yanzu ta zama abar tausayi ku dai ku bari ayi ku zuba ido kuyi kallon abinda zai faru "wannan ba matsalata bace ga mahaifiyarta nan zaune idan ta yarda ta amince babu ruwana suje su karata "alhj marwa ya kai dubansa ga mumy "aunty kinji abinda yaya yace kiyi hakuri ayi auren nan shine kwanciyar hankalinmu tsawon lokaci tun secondary School ana fama da abu daya babu irin kulawa da soyayyar da baku bata ba , kulawa gata sangarta so da qauna duk kun tattara akan ita kadai amman ta rufe idanunta tace lallai sai wannan yaron". numfashi mumy ta sauke kana tace" na soma tunanin akwai mummunar qaddarar dake biye da rayuwarta shiyasa muka ki auren da kuma rashin mutuncin yaron , yaron daya dibi kalazir ya watsa min a fuska har yana cewa abashi ashana ya kyata min wai shi kisna diyar cikina tanacewa aurensa har abada bazan manta wannan tozarcin ba taje tayi duniya ce duk abinda ka shuka shi zaka girba , baka yiwa iyayenka ba ya'ya sunyi maka ina ga kayi ? "kin amince kenan ?"na amince taje ta auresa amman babu hannuna babu kafata ciwo mutuwa rayuwa karta zo gareni ko mutuwa nayi kartazo kan gawata idan tazo ban yafe mata ba " ki dai yi hakuri haka qaddarar rayuwarta tazo killa rabo ne a tsakaninsu idan basu yi auren ba sa haifa a waje, dasu zo suna bin juna suna haihuwar shegu suzo su bata mana zuri'a gara an aura mata shi suje su karata ɗan nacin kisna yayi yawa ni kaina ban taba ganin yarinya irinta ba dady da mumy sukayi shiru suna kukan zuci ."
"Ke kisna bani number wayar musa zamuyi magana dashi ".babu kunya ta soma karanto masa yana daddanawa har number's suka cika , kira daya musa ya dauka Alhj marwa cikin harshen yoroba yace "kana magana da kanin mahaifin kisna ne ". cike da girmamawa musa ya kwantar da murya ya gaishesa cikin harshen yoroba kamar yadda alhji marwa yayi masa magana da yarbanci "kana son kisna har yanzu Kuma a shirye kake da aurenta ?" ina sonta har yanzu kuma a shirye nake muddin iyayenta sun yarda sun amince da aurenmu "to shikenan ka fada iyayenka su fara shiri nan da wata uku masu zuwa za'a daura muku aure sannan karka sake kiranta a waya dan idda take ba'a neman aure yayinda mace ke idda idan na samu labarin ka kirata komai zai iya faruwa "okay sir ..." Alhj marwa na gama jin abinda ya fadar haka ya katse kiran ". wani irin numfashi mai zafi kisna ta fesar tare da lumshe idanuwanta saboda wani farinciki daya ziyarceta take duk wahalar aikin da'aka daura mata ya fita akanta farinciki ya maye gurbinsa "ku sanyawa auren albarka yaron yace muddin kuka yarda a shirye yake shima da alamun yana sonta ". dady ya mike cike da tsananin bakinciki ya soma tafiya tamkar bashi da laka ajiki "wallahi bazan sakawa wannan auren albarka ba tsinuwata ta tabbata akanshi ina nan akan bakana ta aure shi tunda tana so amman albarkatace har abada bazan saka ba idan uwarta taji zata saka mata albarka ta saka mata bazan hana ba ya k'arasa maganar yana barin falon cikin tsananin bakinciki da tashin hankali yana Allah wadai da kisna ".
"hakuri dai zamu taru muyi yaro mai taurin kai da zuciya mara tausayin iyaye sai hakuri ,hakuri dai zaku cigaba da yi babu yadda alhj marwa bai yi da mumy akan ta sanyawa lamarin albarka tace" bazatayi ba "yadda ta nuna bamu isa daita ba haka banga wanda ya isa ya sanyani dole na saka albarka akan wannan tsinnannen auren ba, na tsinewa wannan auren na kuma na tsine masa muddin aka yi wallahi sai ta dawo tana tsince tsince a bola Kai abinda zasu ci ma sai ya gagaresu dan Allah baya kunyata iyaye akan ya'ya sai dai ya kunyata ya'ya alhj marwa ya sallami kisna ya sake fuskantar mumy yana cigaba da mata nasiha "ke uwace fushinki zai fi na mahaifinta tasiri akanta ki dai daure ki yaki zuciyarki sannan ki janye furucinki akanta tunda yaron muslimi ne kada mu saka qabilanci cikin lamarin "ai bana kinsa dan wani abu , ina kinsa ne dan bai cancanta abashi aure ba wallahi da wani bayarban ne ke son kisna irin hashim to wallahi zan tsaya tsayin daka abashi ita kaga dai yoroba ne amman mai hankali da natsuwa ba irin yama yama din yaron ba ". to shikenan Allah ya kyauta ya shirya mana shirin addinin musulunci sai mu dage da mata addu'a duk lokacin da kika samu dama ki dinga bata karshen ruwan alwalar sallah la'asar tana sha yana sanyaya zuciya sannan ki dinga karanta mata lailafi duk sanda tayi bacci a fuskarta da zumar Allah ya shiryata ya sanyaya zuciyarta da izinin Allah za'a samu sauki wata killa kafin lokacin da za'a daura musu aure kuga komai ya wargaje Allah ya kunyatasu tunda ita mai bukatar kunyata iyaye ce auren yaki yiwuwa ya k'arasa maganar yana mikewa yayi ma mumy sallama ta mike itama tabi bayansa tana masa godiya har haraban gidan ta rakashi sai dataga tashin motarsa ta dawo ciki zuciyarta ta quna ."
A wannan ranar haka kisna ta yini a daki cikin tashin hankali da tsinkewar zuciya da kuma farincikin zata aure masoyinta sai dai furucin iyayenta ya bala'in tsaya mata arai ta rasa ta ina zata fara rayuwar aure da musa iyayenta na fushi daita wani irin gumi ne ya wanke mata ilahirin jikinta ta kamo lip's dinta na kasa tana cizawa a hankali a hankali tana tunani yadda zatayi "zan yi duk abinda suke so zan kyautata muku kafin zuwan lokacin wata killa zasu yarda su amince da aurena da musa amman batun na hakura dashi never in history ". washegari taje har daki ta gaishe da mumy har zata wuce mumy tace "ke kisna taja ta tsaya "kin manta aikinki ne ?"sai lokacin kisna ta tuna da batun wani aikin da'aka sharada mata dan haka ta gyada mata kai alamun" a'a "To ki fara" ta mike ta fito waje dan ta bata waje jiki a kasalance kisna taja kafafunta ta karasa bakin gado ta fara da kakkabe gadon sannan ta shimfida zanin gado ta share dakin tass taje ta dauko abun moping ta goge dakin ta dawo parlour Shima ta share Tayi moping tana aikin tana hutawa saboda rashin sabo, duk dakunan gidan da falon dake gidan har sama sai data gyara tare da goge ko'ina sannan ta samu kanta, ba ita ta karya ba sai gurin daya saura ta shiga wanka bata jima da fitowa ba mumy ta kwalla mata kira tana fitowa tace "a daura girkin rana fuskarta da alamun gajiya tace "me za'a daura ?"ke ba mace bace baki san abinda za'a daura ba sai kin tambaya ? "Kiyi hakuri mumy "a'a kece dai da hakuri dakiyar banza wacce batasan ciwon kanta ba kalleki mace har mace santaleliya a tsaye amman ki kare anacin jinjiri mumy sai faman zaginta take tana muzanta musa. a hankali ta juya duk ilahirin jikinta ciwo suke ga bakincikin zagin mumy ta shiga kitchen tara tukunya batare data dauraye ba a she mumy ta ganta "haka ake daura tukunya ba'a dauraye ba saboda ke mahaukaciya ce dakikiya ki tsaya ki natsu ki koya a'a kafafunki nacan gurin nacin namiji shasha dabba kawai ki zubar ki dauraye sannan ki daura ".tana gama fadar haka ta juya tana kiran asabe mai aiki ta fito daga dakinsu ta tsaya a gaban mumy "hajiya gani ".
"Ki shiga kitchen ki dinga kula da wacce shashar karta girka abinda bazamu iya ci ba "to shikenan ta nufi kitchen ."
Tun dawowar kisna gidan , mumy bata d'aga mata kafa sai dai kuma akwai wani sirri dake tsakanin uwa da d'a tana jin tausayinta amman bata bayyana tausayin ,shi kuwa dady sam nuna yake kamar bashi ya haifeta ba da ita da yan aikin gida abu daya yake daukarsu har ma masu aikin sunfita daraja mumy na falo zaune yayinda kisna ke zaune a gefenta tana bare mata ayaba tana mika mata da apple da take yanka mata bisa umarninta dady ya shigo ya wani haɗe rai daga tsaye yana kallon kisna tun shigowarsa gabanta ke Fad'uwa ta gaishe dashi muryarta na rawa ya share bátare daya amsa ba "ke maza ki hada min farfesun kayan ciki da lemo kwakwa yanzu ki kawo min kanta a kasa ta amsa da "to". Kamar zatayi kuka dan a mutukar gajiye take tun safe take kan kafafunta bata zauna ta huta ba tana kallonsa ya juya zuwa d'akinsa mumy ta mike ta rufa masa baya ita kuma ta yunkura hawaye na zubo mata ta shiga kitchen ."
Cikin minti talatin kisna ta kammala komai da taimakon asabe mai aiki da yake akwai komai ta gama cikin fargaba ta kai dinnig sannan ta fito filin falon sosai inda mumy ke zaune suna hira da sadiq da madu saukowarta kenan daga sama gurin dady "mumy na kammala tayi maganar tana rike kugunta da yatsina fuska , mumy tayi mata banza sai Sadiq ne yace" sannu da kokari kanwata har naji kamshi da alamun zai dadi madu yace "Allah yasa dai yayi dadin idan bai yi ba ke da dad babu ruwana" zubo mana muci muji ko yayi kisna ta amsa da" to" kamar wata wawiya ita kanta yanzu tana mamakin kanta komai akace mata zatace to babu matsala ,al'amarin zaman gidan sam babu sauki sannan a ganinta har da rashin adalci tunda babu tausayi bare jin kai gbdy aikin gidan itace da zarar an ganta zaune tana hutawa sai asan yadda aka sakata aiki ta rasa inda zata tsoma ranta taji dadi ,zaman gidan tamkar zaman prison kana kallonta kasan tana cikin kunci da tashin hankali ga laulayi ciki daya sakata gaba dan ba wani abincin kirki take ci ba gashi komai taci sai ta amayar shiyasa ta gwamaci zama da yunwa duk ta fige ta lalace tayi baki wani lokaci sai taji kamar ta gudu ta bar gidan anman da zarar ta tuna nan da wani dan lokaci zata bar gidan gbdy zuwa na musa sai hankalinta ya ɗan kwanta ."
tana kwance tana bacci a dakinta mumy ta shigo dakin da niyyar tashinta taje tayi aiki ta tsura mata ido kawai tana kare mata kallo tun daga dan yatsanta har zuwa qirjinta gaba-daya ta qara canzawa kana ganinta kaga mai shigar ciki ".ke kisna ta kira sunanta ta farka agigice ta zauna tana mutsutsuke idanu mumy ta sake tsura mata ido "yaushe rabonki da ganin jinin al'adar ki ? " nan take ta diririce gabanta ya yanke ya fadi tayi shiru tana tunani "wajen wata biyu kenan tun wanda tayi a gidan muradi bata sake yi ba " gabanta na faduwa tace "ko last mouth nayi mumy "karki min karya ga ciki nan ajikinki ina kallo amman kice min kinyi last mouth". "Allah mumy nayi amman idan baki yarda ba idan nayi wannan watan zan nuna miki". shikenan ki tashi kije ki gyara kayan miya da nama gashi can an kawo ki yanka nama manya ta mike da kyar zuciyarta na rawa mumy na fita ta shiga kitchen tana aikin tana jin tsinkewar zuciya