Showing 162001 words to 165000 words out of 495987 words
Chapter 55 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
taimakonsa , tana bukatar kulawarsa tana bukatar ta ganshi a nagartaccen mutun kamili wanda zai jibanci al'amuran ita da dan'uwansa sai ya zubar da komai domin soyayyar mahaifiyarsa ta fiyye masa komai soyayyarta na makale a zuciyarsa duk inda zashi suna tare da wannan son da Allah ne ya dasa shi a zukatan iyaye da ƴaƴansu kuma babu mai iya fitar dashi sai wanda ya dasashi ,yana tsananin sonta yana son ya mutu da qaunarta bashi da wata soyayya data wuce ta Allah da manzonsa sai kuma ta mahaifiyarsa , yana makale a dakin da'aka bashi ya takure guri daya yana kuka yana felling din mahaifiyarsa hawaye na zubo masa hajiya aysha ta shigo dakin ta bishi da kallo "Aliyu lafiyarka kuwa ka dawo daki ka takure kanka ? Tayi masa tambayar duk da tasan bazai wuce tunanin mahaifiyarsa yake ba ,Aliyu ya sake sunkuyar da kanshi kasa tare da cewa "babu komai" .
hajiya aysha ta zauna kusa dashi cike da kulawa "sai yaushe zaka dawo kamar jikana wanda nayi silar zuwan iyayensa duniya ?"ina sonka aliyu ina son ka dawo tamkar jinina saboda tsananin son da zuciyata ke maka , takure kanka da kake yana matukar damuna dan Allah ka cire tunani da damuwa a ranka baka rasa dangi da yan'uwa ba tunda gani ,nice danginka nice mahaifiyarka daka rasa nice komai naka zan tsaya maka akan komai zan bawa rayuwarka kulawa ka hakura da rayuwar damuwa , kayi kankanta da daurawa kanka tunani ." cike da raunin zuciya tace" kayi min alkwarin zaka cire damuwar nan a ranka ta karasa maganar tana kamo tafin hannunsa cikin nata " na kasa hakura granny ya kirata da sunan daya ji jikokinta na kiranta dashi ,ta Lumshe idanunta tana mai tsananin jin farinciki " zai wuya na iya cire damuwar dake zuciyata ko zai ciru sai a hankali "nasan da haka Aliyu amman kayi kokarin kai yaro ne karami rayuwar tunani bata kamaceka ba ka cigaba da rayuwarka ka cigaba da walwala kamar sauran yara "inshallahu zanyi kokari gabadaya Hajiya aysha ta gama kashe masa jiki ta zuba masa ido cikin tausayawa "Ko zaka iya fada min sunan mahaifiyarka da mahaifinka ? Shiru yayi yana tunani kafin yace "benedicter rashida ya furta a hankali " shiru hajiya aysha tayi tana cigaba da kallonsa kafin daga bisani tace "mahaifinka fa "rashida Benedicter ya sake maimaitawa Hajiya aysha ta muskuta cikin damuwa tace "babanka nake nufi saboda karatu ya sake dubanta ya tausasa muryarsa yace "Aliyu benedicter rashida "wani irin suna ne haka? " mahaifinka ne Aliyu ko benedicter wanne aciki na dai san rashida sunan mace ne kenan sunan mahaifiyarka ne? ta karasa fadar haka tana sake tambayarsa still dai abu daya ya fada mata kamar farko "ko baka da uba ne ?da sauri Aliyu ya gyada mata kai alamun "eh bani da uba sai uwa da wannan sunan na kare karatun primary tausayinsa yayi mugun ratsa zuciyar hajiya aysha bata san sanda hawayen tausayi ya shiga turereniyar zubawa bisa kuncinta ba , ta soma kuka sosai " yaro kyakkywa kamar wannan ga natsuwa da ilimi sannan da gani idan ya cigaba da rayuwa zai yi biyayya da kamala amman bashi da mahaifi wannan wacce irin rayuwa iyayensa suka zaba masa ? "inna lillahi wa inna ilaihi raji'un ta dinga furtawa tana maimaitawa hawaye na sake zubo mata tamkar an bude fomfo jiki a sanyaye ta baro d'akin zuciyarta cunkushe da bakinciki marasa misaltuwa "hakika bata so Aliyu yazo ta hanyar zina ba amman babu yadda zatayi haka Allah ya qaddara masa daman kuma qaddara tana kan kowani bawa wuni ranar da bakinciki hajiya aysha ta wuni har sanda Alhaji marwan ya shigo ɗakinta shi da afra a dalilin bai ganta a falo ba afra ta samu guri akan kujera ta zauna shi kuma Alhaji marwan ya krasa da sauri ya zauna a bakin gadon saboda hango hajiya kwance da yayi ,hankalinsa a matukar tashe ya soma tambayarta damuwarta batare da ta lura da afra ba dake zaune akan kujera ba ta koro masa komai akan Aliyu tana fashewa da wani sabon kuka "banji dadi da yaro kamar Aliyu ya kasance dan zina ba mai yasa mutane suke biyewa son zuciyarsu su aikatawa rayuwar ƴaƴansu mummunar ta'adancinta ....."? "Wallahi iyayensa sunci zarafinsa " muryar Alhaji marwan na rawa yace "subhallah hajiya ki daina kuka haka bawa baya wuce qaddararsa shi babu ruwansa har agurin Allah shi din tsarkake ne yanzu yadda zamu tallafawa rayuwarsa zamuyi a qalla sun dauki sama da minti talatin suna tautaunawa duk akan idanun afra data cika bam tana sake jin tsanar Aliyu a ranta ...
******"
Bayan wata daya Inna jamila ta koma kauyen ilo tasa aka kira hajiya salaha a waya tayi mata bayanin abinda ya faru dasu ,gama jin bayaninta ke da wuya sai gani aka yi Hajiya salaha ta zube kasa sumammiya nan take aka kwasheta zuwa asibiti ,likitoci suka rufa akanta domin ceto ranta dake ƙoƙarin barin gangar jikinta ,da kyar likitoci suka samu ta dawo daidai, sai dai ban da kiran sunan muradin hajiya kayi babu abinda take ."
Alhaji realwan dake zaune a gabanta ya riko yatsun hannunta cikin nasa gam hankalinsa a matukar tashe "ki kwantar da hankalinki salaha, inshallahu Allah zai kubutar dashi daga hannun yan fashin nan ,babu abinda zai sameshi ki daina d'aga hankalinki dan Allah , Allah ya ga kinyi iyakar ƙoƙarinki akan yaron nan". "Alhaji bazan iya kwantar da hankalina ba d'a sukutun fa koda bani na haifesa ba dole naji zafin rashinsa , duk kuma ranar da mahaifiyarsa ta waiwayemu da batun yaranta me zance mata"? "Inshallahu gobe zan sa ma'aikata a cikin lamarin ayi bincike ."
"Dan Allah a taimaka a binciko min shi gara ace mutuwa yayi a hanuna akan ace yana hannun 'yan fashi azzaluman mutane ,Allah ka saka mana ka tona asirinsu a duk inda suke, Allah ka bayyana min muradina ....."ta karasa maganar tana kuka ."
Alhaji realwan na barin asibiti ofishin 'yan sanda ya nufa yayi musu bayanin komai da inda abun ya faru tashin farko suka bukaci hoton muradi sai dai babu sai kwatanta musu yayi da shekarunsa , abunka da mai arziki take labarin 'batan Aliyu ya karad'e ko'ina ,bangaren gidan tv , radio jarida da duk wani kafafen yaɗa labarai , yawan kukan da Hajiya salaha take babu dare babu rana yasa likitan dake dubata yayi mata allura saboda a samu hankalinta ya kwanta dan bp dinta ya hau sosai ."
zuwan hajiya Aysha biyu asibintin duba jikin Hajiya salaha sai dai bata taɓa zuwa da Aliyu ba ,sannan bata taɓa zuwa ta iske idanun hajiya salaha biyu ba , duk sanda zata zo tana bacci ,satin hajiya salaha ɗaya ta ɗan samu saukin rad'ad'in rashin Aliyu aka sallameta daga asibiti suka dawo gida kuma har wannan lokacin babu wani bayani akan batan Aliyu , hajiya salaha tayi baki ta rame ta fita haiyacinta, ta daina ci ta daina sha hatta magana taki yi da kowa daga sallah sai sallah ke ta da ita tsaye hatta kisna sai da tayi zazzabin rashin kulawar mahaifiya , kowa yazo kalma daya yake faɗa mata tayi hakuri Allah zai bayyana shi a karo na uku ne da Hajiya Aysha tazo tare da afra duba jikin hajiya salaha ta iske idanunta biyu "sannu salaha ya karfin jikin "? Sai data maida kanta kan pillow sannan ta buɗe baki da kyar tace "da sauki Hajiya na gode sosai hawaye na gangaro mata , kuka take sosai tana maganar zuci "wai ɗan waye ne acikin wannan yaron a cikin yanuwanki ? "Hajiya salaha bata tsaya boyewa surukarta komai ba saboda ta ɗauketa a matsayin uwa tunda itama matsayin diyarta ta ɗauketa,ta fada mata matsayin mahaifiyar Aliyu da irin rayuwar datayi da danuwanta haroon ,Sai lokacin hajiya Aysha tasan takamaiman abinda ya faru sannan sai lokacin tasan batun zuwan muradi daga ilo , haka nan hajiya Aysha taji gabanta ya fadi babu wanda yazo mata a lokacin sai Aliyu sai dai shi ai yace mata bashi da kowa a duniya sai mahaifiyarsa ..." cikin jimami tace " Allah ka shirya mana zuri'a ,shi kuma babakarami Allah ya karkato da hankalinsa gida shi ma yaron Allah ya bayyana shi a duk inda yake a hankali Hajiya salaha ta cigaba da amsawa da "ameen ameen hawaye na gangaro mata anan Hajiya aysha ta bar afra gurinsu mufida tace daga nan gidansu zata wuce daman kuma tana son zuwa gidan saboda Kisna ."
lokacin da hajiya Aysha ta koma gida tayita bin Aliyu da kallo wanda lokacin satinsa bakwai kenan a gidan, tsantsar kamaninsa da sarakuwarta ta gani sosai akan fuskarsa wanda bata lura da hakan ba a tun ranar da marwan ya kawo mata shi sai yau ,a hankali ta shiga tunanin bayanin da marwan yayi mata akanshi wanda Aliyu din ne ya fada masa da wanda shi kanshi yaron ya fada mata , shiru tayi tana kallonsa zuciyarta na tabbatar mata da lallai shi ne yaron da'ake nema dan a labarinsa akwai abinda ya shafi uwa da rashin uba haka a labarin da surukarta ta bata akwai abinda ya shafi uwa da uba sai dai uban bashi da amfani , tagumi ta rafka dan bata son rabuwa dashi ,ita dake shirin saka shi a makaranta ya cigaba da karatunsa tunda ya sheida mata ya kare primary ,duk ta daga hankalinta ta riko hannunsa cikin nata"Aliyu ta kira sunansa ya d'ago kyawawan idanunsa ya Kalleta kawai kasancewar shi din ba mai yawon hayaniya bane "idan kaga yan'uwan mahaifinka zaka koma hannunsu da zama "? Yayi saurin girgiza mata kai "ai bani da mahaifin ma bare wasu yan'uwansa yayi maganar kamar zai yi kuka ,"zaka zauna agurina kenan ka cigaba da karatunka ? tayi maganar tana fad'ad'a fuskarta da murmushi "zan zauna muddin rai agurinki sai dai idan na hadu da mahaifiyata ne to zan koma hannunta gbdy amman zan dinga zuwa ina ganinki ai ina sonki kina da kirki sosai "Allah sarki Aliyu nima ina sonka ina jinka tamkar jikana daura hannunta tayi a saman kanshi tana jin tsananin kaunar sa da tausayinta ..
Washegari
Aliyu na zaune a kusa da hajiya aysha suka ji sallama "assalamu alaikum Hajiya ta dago kanta tana duban kofar shigowa ". a'a afra ce tafe da yamma nan "?"Nice ina yini granny "? Ta gaisheta tana yatsina fuska saboda Aliyu data ganin zaune a kusa daita ga hannunsa cikin nata "Lafiya lau ya mammanki "? Shiru tayi kafin daga baya tace "wai da gaske rike wannan kazamin yaron dan tsintuwa kuma shege wanda bashi da baba zaki yi ? gaskiya ni idan yana gidan nan zan daina zuwa wallahi dan tsoro yake bani ".
"Kul na sake jin kin furta wannan kalmar hajiya ta dakatar daita tana daga mata hannu cikin ɓacin rai shi kuwa Aliyu ko ajikinsa dan bai damu ba , dama uwa tace bashi daita shine zai damu har ma ya daga hankalinsa kuma sai inda kkarfinsa ya kare amman dan wani uba bai shi da matsala da wannan azzalumi mutumin da shi kansa tuni ya kankareshi a rayuwarsa yama fi son ace masa bashi daita sai da hajiya taja kwafa tace "banason zance banza a ina ma kika ji kalmar shege ?"kin mata rana nan naji kina fadawa dady bashi da uba ? Tsam hajiya ta sha jinin jikinta tabbas sai bayan da komai ya faru ta lura daita " shikenan ki Saka ranki a inuwa ma gobe goben nan zai bar gidan zai koma gurin gidan Alhaji realwan "wani irin tsalle tayi cike da murna "dan Allah grannny kai naji dadi sosai wallahi amman can din ma ai gidan zuwana ne me zai hana ki kai shi gidan marayu kawai mu huta wallahi banason shi bana son bude idanuna na ganshi ".Aliyu ya waigo inda take tsaye ya tsura mata ido yana kallon yadda take farinciki dan zai bar gidan ,Hajiya Aysha ta Kai hannu ta shafo kanshi "manta da wannan mashiririciyar kaji ai inda zaka koma duk daya ne da nan din "Allah karki kai musu shege dan tsintuwa "?"Ke ban son hauka karamar yarinya dake sai shegen surutun tsiya wannan bakin bana marwan bane wallahi na wannan uwar taki ne maza ki bace min da gani kima tattara kayanki ki bar min gida da yake tana da wasu kayan anan gidan ida zata zo tayi kwana biyu bata zuwa da kaya ,tsimi tsimi ta shige daki tace "babu inda zata ta haye gado tayi kwanciyarta zuciyarta cike da farinciki da bakinciki farincikinta Aliyu zai bar gidan bakinciki still dai gidan yayan mahaifinta zai koma washegari Hajiya salaha ta shirya Aliyu cikin sababbin kayan data dinka masa ta rike masa hannu ,tare suka zauna a bayan mota direbanta ya jasu zuwa gidan Alhaji realwan .."
A parlou'n gidan ta iske yaran gidan gabad'aya sunyi jigun jigun ban da badamasi wanda yake karatu a Austarelia , damuwar mahaifiyarsu ta shefe kuzarin yaran gidan duk sun dawo tamkar marasa lafiya ,bakinta dauke da sallama ta karasa shigowa filin parlou'n ta samu guri ta zauna akan kujera sannan ta nunawa Aliyu gurin zama ya zauna kusa da Samir wanda ransa yake a bace saboda dammuwa ko yar sannu da zuwa da suke mata a duk sanda tazo bata samu ba daga garesu ,"Samir ina abbanku yana gida ko ya fita "?"Yana d'akin mommy ya fada muryarsa a raunane kamar zai yi kuka "maza tashi ka Kiramin shi a hankali ya mike ya nufi d'akin inda ya iske dadynsu nayi wa mummy faɗa "mai yasa kike son kashe kanki ne "? yayi maganar cikin tsananin ɓacin rai wanda yake tattare da tsantsar damuwar halin data ciki "bazaka fahimci yadda nake jin muradi acikin raina ba a yanzu in dai akwai abinda nake so bai wuce Aliyu ba kuma kai ma muddin kana sona kaso Aliyu tayi maganar tana juya masa baya juyo daita yayi suka hada ido "shikenan ki kwantar da hankalinki nima ina son shi ai sai dai bazan so wani abu ya sameki akan shi ba , yayi maganar yana goge mata hawayen daya gangaro mata ,"salaha ya kira sunanta ta d'ago idanunta dake cike da hawaye ta zuba masa "ina son kiyi hakuri ki ......"
Sallamar Samir ce ta dakatar dashi daga abinda yake son fada ya juyo yana amsa sallamar tare da bashi umarnin shigowa d'akin "dady granny tazo tana parloun tana jiranka wai kazo yanzu "Okay je kace gani nan zuwa ko cikakken minti biyu Samir bai yi ba ya dawo parloun yace "gashin nan zuwa cikin hanzari alhj realwan ya fito yana gama k'arasowa parloun ya daskare tsaye saboda ganin Aliyu zaune ,koda bai taba ganin Aliyu a rayuwarsa ba ai ya taba ganin haroon mahaifinsa sannan yasan garba yasan Bature uwa uba