Showing 225001 words to 228000 words out of 495987 words

Chapter 76 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

kullum cikin damuwa nake akanki na gaji enough kisna kowa yaje yayi rayuwarsa ya juya zai wuce ta rungume shi ta baya tana sheshekan kuka babu yadda ya iya haka ya hakura sai dai ya rantse bazai bata masauki ba tace babu damuwa ita dai burinta su dinga haduwa shiru yayi na tsawon lokaci yana tunani inda zai samu kudin da zai sha we da kwaya a hankali ya jiyo daita suka fuskantar juna ,sosai idanunta na kanshi numfasawa tayi kana tace "tunanin fa ?" ya numfasa tare da girgiza mata kai sannan yace "ina cikin matsalar kudi ne wallahi , kudi nake so ifemi ko zan samu agurinki ? yayi maganar yana tafiya hannunsu tsarkafe cikin juna ", ban dashi sai dai ina da hanyar da zaka iya samu kudi idan zaka iya ? "me ye shi hanyar ki faɗa min dan ina samun kudin the next thing zan daukeki mu bar garin nan gabad'aya zuwa wani guri har sai munyi aure mun haihu sai mu dawo ya karasa maganar yana rungumota jikinsa farinciki ya kama kisna tace " me zai hana ka hadu kai da ganga dinka kuzo gidanmu akwai wata sabuwar motar da wani enemy dina da'ake rikonsa a gidanmu ya siyawa dad dina ku dauka kuje ku siyar kawai Murmushi Musa yayi yace "kema fa wasa wasa kin iya ta'adanci sata dai kike kokarin turamu gidanku "no ba sata bane cikar burinmu ne ". To shinkenan wannan ai mai sauki ne wace iri ce motar ?"kuma ta ina kike ganin za'a shiga cikin gidanku cikin sauki batare da an fuskanci wata matsala ba ? " ta daga kanta sama alamun tunanin har na tsawon minti goma sannan ta maida idanunta garesa tace *"land cruiser Prado ce "* Idan zaku shigo ku shigo ta katangar baya saboda itace bata da tsawo sosai amman kafin nan kuyi kokarin ku yanke wutar data bawa karfen dake kewaye da katangar , Murmushi Musa yayi yace " zan san yadda nayi amman ni bazani ba gaskiya saboda ina sonki sosai any single mistake ya faru zaki haramta gareni ni kuma abinda bazan so ba kenan nan dana rasaki gara na rasa rayuwata nan dai suka ci-gaba da tautaunawa daga karshe sukayi sallama da zumar zasu hadu gobe a wani lungun dake cikin kasuwa ..."

Bayan kwana biyu musa ya zauna da abokansa sun dauki dogon lokaci suna tautaunawa akan yadda zasu shiga gidansu kisna duk ta inda suka duba sai suga no way za'a iya kama su tunda basu da kayan aiki gashi su ba sana'arsu bace shiga irin wadan nan gidajen na masu kudi barsu dai da satar unguwa shima time to time ne sai sun nemi kudin shaye shaye sun rasa , duk yadda yayi dasu suka ce a'a a cikin abokansa ne wani mai suna sikiru yace zai hadasa da ganga din 'yan fashi da suke bola a munshi local government dake kusa da idiaraba dan su har bindiga suke da take musa ya amincewa sikiru washegari suka je tare akayi magana sannan aka fadi percentage din da kowa zai samu a idan an gama halkallar tare da basu full address din gidan kullum sai yan fashin sun kewaya zuwa unguwar su kisna batare da wani ido ya gansu ba kwatsam wata rana da misalin karfe 1:dot na dare suka fito zuwa unguwar su kisna cikin ikon Allah suka iske gidan babu wuta sakamakon an dauke wutar nepa basu tsaya bata lokaci ba suka hau yanke wayar wuta daya bayan daya suka dinga dane katangar gidan suna dira cikin gidan har suka dire duka ta kan direba suka fara suka wanda yayi kokarin fitowa ya kunna gen tambayesa mukulin motar data kawosu sukayi jikinsa na rawa yace "babu mukullin mota a hannuna ". nan suka rufesa da duka mumy dake zaune tana kaiwa Allah kukanta ta mike da sauri ta fito zuwa parlour inda ta cigaba da jin kukan direba nan take ta fahimci barayi ne suka shigo tayi saurin shiga d'akinsu zainab da tuni suma sun tashi har kisna wacce tafi zainab tsoracewa ta kamo hannunsu suka nufi dakin masu aiki asabe mai aiki da sauran ma'aikata suka nufi dakin mumy gabad'aya asabe ta mai da kofar dakin da sauri ta kulle tasa bayanta ta danne saboda dogon kofar shigowa parlour'n a bude take ba'a San wanda ya bar parlour'n last ba ita kuma mumy koda ta fito tsoro bai sa ta rufe ba suna cikin daki barayin suka shigo suka haska falo basu ga kowa ba dan haka kai tsaye suka nufi kofar dake facing dinsu suka murda aiko zee da kisna suka fasa ƙara nan barayi suka shiga dukan kofar da iyakacin karfinsu suna kiran a buɗe musu , idan kofar tayi kamar zata bude sai asabe mai aiki ta sake rufewa garam ta rufe haka suka dinga dukan kofar tana budewa yafi sau biyar asabe na maidawa ta rufe amman sai da suka samu nasarar balla kofar asabe tayi wacalau gefe har kugunta ya bugewa karfen labule , mumy dake tsugunne rungume da zee da kisna bata d'ago ba kallo asabe mai aiki sukayi suna huci bacin akwai abinda suka zowa da sai sun yiwa asabe dukan mutuwa kafin su bar gidan amman duk da haka sai da daya ya waska mata mafi a fusace daya wanda ya mareta yace "ina wayoyinku da zinari ?"da sauri asabe tace "bamu da waya bare zinari barawon ya daga karfen dake rike a hannunsa zai buga mata tayi saurin cewa "ga waya can ta nuna musu amman wallahi bamu da zinari ya sauke nunfashi ya dauki wayar yana dube dube , yayinda Kisna ta gigice ta rude dan tunda taji an ambaci waya da zinira ta d'ago a hankali b taga babu alamun ganga din musa ne nan ta shiga mummunar tashin hankali dan tasan wasu barayin ne dabam dan haka cikin ta maida idanunta ta rufe gam bata sake kokarin budesu ba babbar wayar mumy na jone a caji sai dai Allah bai basu ikon ganinta ba sai karamar a hankali mumy ta d'ago kanta ta kasan ido ta kare musu kallo sun fi su goma sha acikin dakin banda gidan da wadan da ke kofar gida da tsakar gida ya tambayeta kudi tace bata da kudi duk wayoyin masu aikin sai da suka kwace da manya da kanana mumy bata ce musu komai ba illa sake kamkame yaranta da tayi tsawa ya bugawa mumy a gigice ta mike jikinta na rawa yayinda Kisna ta nade kanta da bargo "ki bamu babbar wayarki tace ai kun dauka "Bama son wannan babbar waya zaki bamu "bani da big phone karama gareni kuma kun dauka kai tsaye gaban tv ya nufa kica kica ya hau kwance tv yayi waje dashi sauran sukayi layin dady .."

Can bangare dady kuwa yaji hayaniya yaki karewa yana farkawa yaji alamun barayi ne ya fito yá kulle kofa ya nufi saman gidan ya shiga bancloy daman akwai glass ya rufe ya fara ihun ayi masa gudunmuwa barayi sun shigo "ole barayi !!! Alhaji hamza ka min harbi ,alhj sani kamin harbi barayi haka ya dinga ihun neman taimako cike da tausayawa tsabar gigitacewa ya kasa dauko bindigarsa bare ya sarrafa yana ta ihu babu wanda bai ji shi ba dan har mutanen wasu unguwar ma sunji dai hunsa kasancewar dare ne sai dai babu wanda ya fito afra da ya badamasi suka tashi "kamar Muryar dady ? Inji cewar ya badamasi babu kama shine ta fa jikinta na rawa ya yunkura zai sauko ta riko shi tana kuka ina zaka ?." Zan fita ne mana ta fashe da kuka tana rokonsa kar ya fita kai tsaye ya fita zuwa falo sai dai ya nemi mukulin get din dake kai mutun gidan dady ya rasa ya dawo cikin rawar jiki ya shiga neman layin police da kyar suka dauka ya fada musu halin da ake ciki suka ce gasu nan zuwa Samir da muradi suma suka farka a gigice daga bacci saboda jin sautin dady alamun ihun barayi yake muradi ya zabura ya mike shima Samir ya mike jikinsa na rawa kamar mazari yana neman gurin buya muradi ya fara kokarin zare laptop dinsa dana Samir da manya wayoyinsu dukansu ya kashe ya samu guri ya boye yana jiran shigowar su yayinda madu tuni ya fita da sauri taf taf ya haye saman lalluki na gidan dan ya dauka anan dady yake ya kalli yamma shima ya fara ihun "ole yadda dady ke ihu haka barayin dake waje ke dukan direba suna tambayarsa makullin mota ai suna jin dady yace "ayi masa harbi nan take suka harba bindigarsu wanda karar bindigar barayin ne tasa alhaji hamza farkawa daga bacci ya dauki bindigarsa yayi harbi jin haka yasa sukayo cikin gidan zuga guda suka haye saman gidan suka dinga dukan falon dady na sama a tunaninsu daga ciki yake ihun neman dauki , ga mukullin falon ajiki amman Allah bai basu ikon gani ba idanunsu sun ya rufeb har mukkulin yayi tsalle ya fadi basu lura ba suka sa wani karfe suna kwakulo kofar dan ya bude suna bude falon suka ga babu kowa sai kujera da tv da kayan wanki dady da'aka kawo masa dazu sababbi da wasu kayyaki suka shiga bubbude abubuwa suna neman abun dauka suka leka ko'ina basu ga abinda zasu dauka ba suka fito suka raba kansu gida biyu wasu sukayi hanyar sama lalluki guda uku suka daga kafafunsu zasu daki glass din bancoly suka ji murya daga bayansu "a'a ku dakata dady karka bude kofar tare da cewa "lafiyarku ..? Shiru sukayi suna kallonsa tsaye cike da izza da kwarjini tattare da rashin jin tsoro nan take ya shiga zuba musu ruwan bala'i "kunzo kunata damun mutane a unguwa da hauka kuna kokarin dagawa mutane hankali akan karon banza me kuke so ne da zaku damu mutane ? Suka tsaya suna kallonsa gabansu na faduwa kafin daga baya suka ce mukulin mota land cruiser Prado "mukulli kuke so ai sai ku fada sai a baku " iya mukulli mota kawai suke so ko da wani abu dan banason ku lafiyar kowa a cikin gidan nan ? ya tambayesu zuciyarsa a dake babu wani alamar jin tsoro suka gyada masa kai yace "oya ku biyoni muje ya juya suka biyo bayansa abun ya bala'in bawa dady mamaki yana tafiya suna binsa a baya har ya shiga dakin dady ya bude durowa ya ciro mukkulin ya mika musu na land cruiser Prado , suka karba kafin su fito sunyiwa wadan da suke kasa alama suka bude get suna fitowa mutum daya ya shiga cikin mota yayi reves ya kunna ya fita da motar yayinda wasu ke biye da motar suna tafiya cike da iskancin samun abinda ya kawosu wadan da suke cikin gidan ma basu gama fita ba tuni motar tayi gaba tafiya suke suna wani karairaya akan titi har motar tazo gaban gidan Alhaji sani sannan suka bubbude murfin motar suka shiga sukar bar unguwar a guje babu abinda suka yiwa mutanen gidan duk da ihun da dady yayi shi kansa dady yayi matukar mamaki barayi ne zasu ji kayi musu ihun sata basu ɗauki mataki ba alhalin ga abun daukar mataki a hannunsu take jikinsa yayi sanyi ya fahimci duk yadda akayi turosu akayi domin tafiya da motar gabad'aya ahlin gidan suka hallara a falo har masu aiki kisna ce kawai bata gurin muradi ya kallesu daya bayan daya bai ganta ba yace "mumy ina kisna sai lokacin ta lura bata fito ba tace" tana daki kasanta da shegen tsoro tunda ta lullube cikin bargo ban sake jin motsinta ba"sai tsaya jin abinda mumy zata fada ba kai tsaye ya nufi dakin ya soma dubata da kyar ya ganta lullube cikin bargo ta haɗa gumi bata numfashi alamun ta sume ya tallabota jikinsa ya fito daita yana kallon fuskarta "ga tsoro ga ban tsoro sunan da baba mai gadi ke kiranta dashi ne ya fado masa akan doguwar kujera ya kwantar daita ya nufi kitchen yana cewa "suma fa tayi duk sukayo kanta suna kallonta ruwa ya dauko ya tsiyaya a hannunsa ya shafa mata a gigice ta sauke nunfashi da atishawa tare da kamkame mumy a jikinta tana karkarwa a hankali take jin hirar yadda satar ta kasance tun da taji ance an dauki mota tasan duk yadda akayi daga musa ne dan haka ta kwantar da hankalinta babu wanda ya runtsa a cikinsu har sanda police suka zo dady yayi musu bayanin komai suka wuce baba mai gadi kam tattarashi akayi a cikin daren akayi asibiti dashi da direba dan tun shigowarsu yake aikin zuba zawo ajiki yana jin harbi kuwa ya sume , washegari mutanen unguwa sukayita shigowa yi musu jaje tare da barka da arziki babu wanda suka taba sai dai kowa yaji sai yace turosu akayi .." tunda aka sheidawa ma'aikata suka shiga bincike sai dai babu wani bayani kisna ta masu ta samu hanyar fita zuwa gurin Musa taji bayani sai dai babu hali
yansanda na magana da dady a waje kisna ta fito dan jin mai zasu tautauna daga can nesa ta hango muradi yana waya har lokacin kamalarsa na nan sai ma sake fitowa datayi sosai ya fita dabam acikin mutane yana wayar bilkila suka shigo gidan ya karaso inda katanga take yana nuna musu abinda yake bukata "a kara tsawon katangar bayan sati daya police suka sake dawowa babu labarin anga mota sai dai sun tabbatar wa dady za'a ga motar muddin suka fita daita idan kuma sai daita zasu yi dole za'a bukaci takardun mota muradi ya karasa inda suke tsaye yace "idan kuma pieace's dinta sukayi fa suka siyar da part part dinta ?police sukayi shiru suna kallonsa dan sun san muddin sukayi haka baza'a ga motar Ba "dady abar zance motar nan mu godewa Allah da basu taba lafiyar kowa ba zan siya maka wata motar .. wannan maganar ma karaf acikin kunnen kisna tayi juyi har da tsalle tasan sunci bulus "..

**

Yau ma kamar sauran lokuta daga school ta zarce gurin Musa sun dade yana bata labarin abinda aka bashi ,sun balballe motar ne sun shaida part dinta har sun raba kudi ciki ya siya sabuwar waya da sababbin kaya yana bata labarin yana romancing dinta ita kuma tana murmushi dadin abinda yake mata yasa ta shagala har kusan magrib suna tare babu sallah babu salati sai faman tsotsar juna suke sannan tayi tunanin zuwa gida tana fitowa taga dare ya shigo tayi narai narai da idanu zatayi kuka ya kalleta yace " doulbe wahala ko "? Ta gyada masa alamun "eh "kije gida idan Kinga zasu taba lafiyar jikinki Kiyi abinda kika saba sai dai karki gidanmu zan samu inda zan ajiyeki "bazan ma koma gidan ba sannan bazan zauna gurinka na daura maka laifi ba azo ana tayar mana da hankali nasan inda zani suka sake komawa cikin dakin abokinsa fatai basu rabu ba sai gurin tara na dare kai tsaye gidan kawarta Farida ta nufa farida su kadai ne a flat din saman *mafeye hospital beside okekoto jeactoin* suna tare da babansu ne kaɗai dan mahaifiyarsu ta rasu dan haka kisna ta samu masauki kullum zata shirya da yamma taje su hadu da musa su sha soyayyarsu sai shadaya na

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login