Showing 276001 words to 279000 words out of 495987 words
Chapter 93 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
basu tsaya a ko'ina ba sai a omole estate gidan wani kanin babansa dake zaune a Canada mai gadin ya sansa Musa sosai ya barsu suka shiga kusan awa daya suna tare daita suna abinda suka saba kafin daga bisani ya barta ya dawo unguwa dan gudun zargi .."
Can asibiti kuwa bakaramin tashin hankali yan gidansu kisna suka shiga ba a lokacin da suka nemeta suka rasa wasu na ƙaryata guduwa tayi yayinda wasu ke cewa guduwa tayi shi kuwa muradi tuni ya yarda ta gudu din ne dan babu inda basu duba ba acikin hospital din ba ko taje Shan iska ne sai dai wayam babu ita babu alamunta "ai sai dana fada maka kuskure kayi gurin fito da wannan mara jin magana na rantse da Allah wannan karon sai na balla mata kafa sambatu kawai Samir ke faman yi suna tafiya da muradi wanda ya rasa me zai ce illa furzar da iska " kenan duk plan ne sumar da tayi "? Ya tambayi kanshi a daidai lokacin da suka dawo inda su mumy suke, runtse idanunwansa yayi da suka sauya a take yana controlling natsuwarsa na wasu sakwanni kafin ya budesu akan inda ya barta gabad'aya ya rasa da wani kalma zai yiwa mumy dake gefensa tana girgiza kai da furta kalmar "Inna lillahi was Inna ilaihi raji'un bayani dan kuwa shine silar faruwar komai "kiyi hakuri mumy ban ..."babu komai muradi muje gida Allah ya shiryeta ranar kowa a gidan jikinsa yayi sanyi sukayi jugun jugun suna jimami tamkar an yi musu mutuwa ko girki ba'a daura ba ranar mumy da dady sun yi juriya dan ko dady ya samu labari "Allah ya kyauta yace tare da cewa rayuwarta zata cuta duniya ce tafi bagaruwa iya jema wanda bai zo ba tana nan tana jiransa yasa kai ya shige dakinsa da daddare yasa aka siyo masa nama yaci ya hayewarsa gado yayi kwanciyarsa ban da mumy data kasa shan ko ruwa ta zabga uban tagumi hawaye shabe shabe na bin kuncinta da muryar kuka tana addu'a "ya Ubangiji kana ganin halin da nake ciki ka tausaya min kayi min maganin damuwata da karfin ikonka ina rokonka Ubangijin al'arshi mai girma ka saisauta mana ka hadamu da abinda zamu iya ka kawo mana sauki cikin lamurramu ka duba rayuwar kisna ka yanke mata wannan wahala ina jin tausayin yarinyata dan tayi kankanta da irin wannan rayuwar idan da rabon sake haduwarmu ka dawo mana daita ka karkato da hankalinta zuwa gida Allah ka kubutar da ita daga wannan haramtacciyar rayuwar daka jarabeta sai wani kuka ya tsarketa ta kasa cigaba da fadin sauran abinda tayi niyyar fada ta dade zaune batare da bacci ya dauketa ba koda ake cewa bacci barawo ne a she marasa damuwa yake iya samun nasarar dauka washegari suka bazama neman kisna har gidansu Musa babu ita babu labarinta kowa a unguwar ya sheida musa ya daina kulata juyin duniya yace shi rabonsa daita tun ranar da abun nan ya faru amman zai tayasu nemanta duk inda ya ganta zai sanar dasu jiki a mace suka koma gida kowane na fadan albarkacin bakinsa .."
Washegari gari da rana Musa bayan ya gama abubuwansa ya bar unguwar zuwa omole kisna na ganinsa ta soma kukan ita tsoro take ji ya canza mata guri bazata iya cigaba da kwana ita kadai ba "bazai yiwu na kwana anan ba akwai idanu akaina abu singul mistake za'a iya fahimtar muna tare dan yan gidanku sunzo ta zaro ido "me suka zo yi kuma bayan sunsa mun dade bama tare ?"sun san baki da inda zaki daya wuce gurina shiyasa suka zo ni dai nace musu na dade banganki ba Allah ya taimakeni mutanen unguwa suka tsaya min ina ganin lokacin da kika shigo babu wanda ya ganki tayi saurin gyada masa kai alamun eh "to shine taimakon da Allah yayi min dan nasan wanannan yayan naki mai bakar zuciya sai ya kusan kasheni da duka suka sa dariya suna rungume juna a hankali suna hira yana romancing dinta ganin ya soma wasu abubuwa ta zaro ido tana kokarin fadin ",ifemi please mana dan Allah kada kamin banason kana samin hannu zafi nake ...."bai bari ta karasa maganar ba ya kara hade bakinsa da nata ko kadan baya ji baya gani dan wani iri yake ji a sansar jikinsa Musa ya fara wuce ka'ida dan yana kokarin shigarta kamar wacan ranar kin yarda tayi saboda tsoro ta turesa dan ko kadan bazata yarda ba tana son jikinta ta rasa dalili tana iya jurar wasanin da yake mata amman bata iya jurar ya shigeta gashi tana matukar bukatar kasancewa tare dashi kalonshi tayi ganin bai masan abinda take ba sai kokarin kamota jikinsa yake tausayinsa ya kamata shi kuwa burinsa ya kusanceta dan tabbas wannan shine damarsa akanta idan ya bari wannan damar ta subce masa a wannan shekarun nata sai yayi dayasani gaba dan a yadda ya lura danginta sun tsaneshi zasu iya komai ,sabon romancig ya fara aika mata dashi dan sake birkita mata brain ita kuwa duk lokacin da yayi yunkurin shigarta wani irin zafi take ji hawayen da suka fara sauka akan kuncinta ne take ya ji duminsa a hankali ya bude Idanunshi ganin tana zubar da hawaye ya fara ƙoƙarin controlling din kansa ɗan mikewa yayi ajikinta ita kuwa babu abinda take sai kuka ya zauna tare da mikar daita zaune ya matso jikinta ya manne mata yana tambayar ta "kin daina sona ko shiyasa bakya son na kusanceki ? "babu komai ai na dade da sanin kin daina so "no ina sonka mana ni dai zafi nake ji mu tsaya iya romancig kawai har sanda zamu yi aure "wani duniyar ke yanzu kina wannan tunani bayan yan'uwanki sun tsaneni ?"karka damu da tsanar da suka maka zan yi confused dinsu dole su yarda romancig juna suka cigaba da yi har la'asar ya fito ya siya mata abinci ya koma unguwarsu ranar ma haka ta kwana ita kadai shi kuma yana bayan uwarsa yana bacci..."
washegari a unguwar madu da wasu abokansa suka wuni Musa babu halin zuwa ko'ina dan da alamun suna timing dinsa ne har yamma ganin shiru shiru bai zo ba ga yunwa daya addabi kisna ta fito koda ta fito bata ga mai gadi ba dan haka ta dane get din gidan kasancewar yana da huji huji tana kokarin durowa mutanen unguwa suka hau ihun "ole !ole!! da kyar ta sha ta gudu gidan wata kawarta wacce itama budurwar abokin musa ce ramota ,ramota kam har ciki tayi as age dinta ya zube tace ta kira mata musa batare da bata lokaci ba ta kiransa sukayi magana yace ta zauna gurinta zai dinga aiko mata da kudin abinci kwanata biyu agurin ramota madu ya samu labari angata tana bin ramota kasuwa suka shirya dan kamota da magrib lokacin gurin yayi duhu suka shige cikin bukkan yan kasuwa wadanda suka tashi da wuri suka la'be bayan wani lokaci sai gata ta taho rike da leda sanye da wando da riga kamar wata iyamura muradi ne yayi nasarar cafketa aiko tana ganinsa tasa wata razannaniyar kara da ihu "yeeeeeeee egbami oooooooo ofe jimi gbe zai saceni ooooo sai ga mumy da madu da zee sun fito ganinsu bai sa ta daina ihu ba tunda ta fara ihun mumy ke tsaye tana kallonta cike da matsanancin mamaki tana zubar da hawaye gashi ta hana Madu dukanta kafi kace me mutane sun cika akansu har ana ƙoƙarin janyo taya a sakawa muradi mumy tayi saurin rike tare da Samir wani mutumi ya fito da gudu yace "saboda me zaka sace ta ka kyaleta ko nasa a konaka da taya yanzu sai da mumy taji abinda yace sannan tace "yata ce ta cikina ta gudu daga gida ne akan wani dalili ya haska fuskar mumy ya haska na kisna nan yaga tsantsar kamanninsu sannan mutane suka juya aka nufi gida daita ana zuwa gida ,kwanata biyu ta kitare katanga ta sake guduwa shima aka kamota da kyar aka kulleta a dakin mumy shima mumy na fita unguwa ta ciccire karfe kofa ta gudu shima da kyar aka kamota nan fa akace aljanu gareta ba yin kanta bane mumy ta tashi tsaye da neman magani haka dai mumy bata nan bata can neman magani duk inda akace ana bada taimakon masu aljanu zata wani lokaci tare da muradi suke zuwa......"
*******
Bayan shekara biyu wanda yayi dadi da shekarar kisna shabiyar a duniya abubuwa sun faru sosai ciki har da girman da Kisna tayi ,ta kara girma sosai qirjinta ya dan ciko da nono dan sun fi lokutan baya sai dai nonuwanta sun kasance masu gindin tasa ne gashi har lokacin bata fara period ba abun yayiwa mumy dadi sai dai da akwai alamun idan ta kara girma zatayi tsawo sosai komai bai gama ji ajikinta ba atakaice dai da sauranta da zama cikakkiyar budurwa kuma har lokacin zuciyarta na makale da soyayyar musa dan duk yadda mumy take taka tsantsar daita da yadda ake mata addu'a da yadda ake amso mata rubutu duk hakan bai sa zuciyarta ta saduda akan musa ba kullum zuciyarta cike da begensa take saboda lokaci suna waya dashi da wayar zainab duk sanda zainab tayi kuskuren ajiye wayarta zata dauka ta shige bayi su sha soyayyarsu .."
Mubarak bubakar tafida dan abokin dady yana yawon zuwa gidan dady saboda kisna tun da aka soma tashin hankali yake jin tausayinta kafin daga baya abun ya zama gagarumar soyayya a zuciyarsa , haka yaya nazir shima dan abokin dady ne dukkansu suna mata soyayya a karancin shekarunta na shabiyar a duniya kuma suna mata hidima sosai sai yaya taufiq shima yana zuwa shi kuma ɗan kawar mumy ne su dukkansu idan basu zo ba zasu kira mumy su gaisa sannan su bukaci a bawa kisna wayar, tuni muradi da Samir har ma da mumy suka fahimci manufarsu mumy tace ina ma kisna zata amince da ɗaya daga cikinsu wallahi da aure za'a mata mu huta da zaman datake a gidan nan ,muradi dake zaune yana sauraron mumy yace "aure kamar ya mumy ? " wai duka guda nawa take dan Allah ki share wannan maganar kowannensu yaje gaba ya nemi matarsa karatu zatai yi , ni so nake ma a canza mata school ina tunanin ko bording za'a kaita a yaba ta rubuta weac , naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke sannan tace "bari dadynku ya dawo muji abinda zai ce akai dan yace bazata cigaba da karatu ba a barta a gida har sanda zata samu miji , ko idan yaga wanda ya dace daita ya bashi samir yace "wannan mai bakar zuciyar ai karku soma aurar daita ga wani wallahi matsala zata bashi kar tazo tana guduwa dani har yanzu ban gama yarda daita ba Kallonta kawai nake yi" kamar kasani Samir kisna na bani tsoro kaga dai shekaranta biyu tsare a gida amman har yanzu jikina na bani duk randa ta fita daga gidan nan wani abu zai faru inji cewar madu .. Muradi ya nunfasa yace "ku fadi alkhairi ko kuyi shiru inshallahu babu abinda zai faru a ɗan mata sakin talala mu ga takunta sai lokacin mumy ta sake yin magana "kai muradi rufaana asiri a dai barta nan suka ci-gaba da tautaunawa akan kisna yayinda muradi yake ganin ai ya isa ta manta da wani musa a rayuwarta mutumin da gabadaya rayuwarsa ta kara burkicewa shine wiwi shine codin da kwaya ."
da daddare da dady ya dawo mumy ta fada masa irin sintirin da samari keyi akan kisna ya sha mamaki yace "shine baki fada min ba da tuntuni na aurar daita "to amman muradi yace abarta ta cigaba da karatu a maida ita boarding school "sai dai idan aurenta zai yi sai ta cigaba a gidansa ..." ? "Wa zai aura kenan wai kisna kake nufi ? Itama ta masa tambaya a rude ya gyada mata kai alamun "eh "a'a baya so kowa ya nemi mahadin rayuwarsa haka kawai baza'a hada dana da ciwon kai ba "to shinkenan zan tuntubi masu zuwa wanda ya shirya ayi dashi babu wani batun karatu "yafi sauki inji cewar mumy duk yadda taufiq nazir da mubarak Abubakar tafida suke zuwa gidan babu wanda ya taɓa mata maganar soyayya sai dai kowa ya gane take takensu har ita kisna sai dai a zuciyarta tace " babu wanda zata iya amince ma ,zuciyarta ta musa ce ..."
Muradi na zaune a kofar gida tare da abokansa suna hira dukkaninsu sanye suke cikin kanana kaya masu kyau da ɗaukar hankali mujahid na ƙoƙarin tashi ya shiga cikin gidan sai ga wasu yammata su uku zasu shiga gidan sanye da nikaf haka kafafunsa sanye da safa cikin zumbulelen hijab yace " yammata mutun ɗaya ta juyo idan kin shiga ciki kice zainab ko kisna wata daga cikinsu su kawo mana ruwan roba wani sanyi farinciki ya mamaye zuciyarsu dan sun dauka za'a hanasu shiga gidan ne , yayinda zinnira dake gaba taso ace muradi ne yayi mata maganar dan tana kwadayin sake jin muryarsa dan tuna yariya rabonta da jin muryarsa duk zuwanta gidan bai taɓa daga ido ya kalleta ba bare magana ta sake shiga tsakaninsu gashi ita yana bala'in burgeta ko ma tace tana maseefar sonshi suna shiga gidan sala ta fada dakin kisna ,kisna na ganinta ta mike "har kunzo ?
Sala ta daga mata kai sai dai kamar kofar gidanku da mutane yanzu ya za'a mu fita kin koyi musu amfani da magani ?"nayi tuni ma bacci ya kwashesu dan mutane kofar gida mai sauki ne ki bani nikaf dinkin da safa da hijab d'inki nayi amfani dashi "okay an gama ta fara cire kayanta tana mika mata "naso ko islamiyya su barki kina zuwa daga nan ku dinga haduwa dashi "ke bari shekara biyu fa ban saka shi acikin kwayar idanunta ba sai ta waya zinnira bata shiga dakin kisna faɗa mata sakon mujahid ba taje ta dauko ruwa mai sanyi guda uku ta fito sai dai bata ga wanda ta sake fitowa dominsa ba tayi shiru tana tunanin mujahid yace "kawo mana jiki a sanyaye ta bawa mujahid ta koma ciki ta iske kisna ta gama shiryawa "kisna karki manta da alkwarinmu fa "karki damu tunda kin min yadda nake so nima zan haduku da Aliyu aure ke kamar ya soki fa ya gama "ban son cika baki mutumin da bawani shiri kuke yi ba ."akanki zamu fara dan yadda kika faranta min nima zan faranta miki da zarar na dawo ku muje kawai Allah Allah nake mu bar gidan kar tsautsayi ya gitta ..."
Fitowa suka yi yayinda kisna ke sanye cikin hijab har kasa tasa safa da nikaf suna fitowa gabanta yayi mummunar faduwa sakamakon ganin Aliyu tsaye yana ƙoƙarin kulle kofar dakinsu sanye yake da gajeren wando niker da yar rigar kwallo kafarshi sanye da safa da takalmi canves na buga kwallo da alama zai je motsa jiki ne ko kuma zai je buga kwallon daya saba duk satin duniya sun zo zasu wuce ya dan kallesu yana jin faduwar gaba ,wani ƙatuwar harara ta banka masa ta cikin nikaf tana dauke kanta take ya gane harararsa tayi cikin nikaf ummana da zinira da sala ne suka gaishesa ya amsa mata da "lafiya atakaice Itama Kisna bude baki tayi tare da canza murya tace ina wuni ?shiru yayi yana nazarin murya yayinda kisna ta dinga Allah Allah su bar gidan dan kallon da yake mata yana sa gabanta na faduwa har sun gota shi kaɗan ya juyo da sauri yace "ku ......."Take gaban kisna yayi mummunar faduwa dan tasan dasu yake ,bai fiyye kiran sunanyen mutane ba daga "ke ku kai jikinta na rawa a ranta tace "kunga dan matsalar ko a fili tace " kuje ku kuji me zaice "mu dai je tare zai fi idan ba haka ba zai fahimci wani abu a hankali suka jero kan kisna na kallon kasa ummana da sala da zinnira da fuskarta ke bude sukayi karfin halin cewa " gamu bai yi masu magana ba har ya gama rufe kofar dakin ya matso daf da kisna ya tsaya suna fuskantar juna sannan ya zuba duka hannuwansa cikin aljihun wandonsa yayinda idanunshi ke Kallonta fuskarshi a daure ya tsira mata ido yana kallon onexpecting taga ya daga hijab d'inta cikin matsanancin tsoro ta zaro ido waje tana dubansa cike da matsanamcin firgici shi kuma ya kura mata ido kawai yana Kallonta.."
Sai Monday zamu hadu inshallahu
Mmm Sudais[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 40
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da