Showing 345001 words to 348000 words out of 495987 words

Chapter 116 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

ya juya zai bar gurin ta kira shi " bani takardar magani ya mika mata ya ƙara gaba ,ita kuma ta shiga ɗakinta ta soma neman layin aunty afra tana dauka tace "ga maganin fa a siyo " me kike jira ?" ki fara aiwatar da aiki kawai , " ki kiyi sauri dan bamu da isashen lokaci "to aunty nah maganin kuka nah tayi disconnecting din Kira ta fito ta shiga kitchen ta bude fridge ta d'auko karamin kwalin exotic ta ajiye sannan ta d'auko cup ta soma bude maganin har sai data balle rabin seachet sannan ta narka ruwa ta tsiyaya a cikin lemun ta mayar ta rufe haɗe da jijigawa sannan ta dumamasa sauran abincin jiya ta juye masa a plet ta nufo inda yake yana hangota ya hau washe mata baki daman kuma yana son ya samu karɓuwa a gurinta ita din ce taki sakar masa fuska , itama fuskarta a sake tace "sannu sanusi ga abinci kafin na kawo maka tukuici " sake washe baki yayi yana cewa "kai hajiya amman fa na gode sosai Allah ya saka da alkhairi Allah yasa ki gama da iyaye lafiya ". ya amsa ya shige d'akinsa ita kuma ta amsa da " ameen ta juya tana sake neman layin afra tana ɗauka Kisna tace "har fa na zuba masa na bashi har da abinci "kai haba ya fara ci ne ? "a'a naga dai ya shiga d'akinsa "yauwa ta wajena kinyi min daidai aikinki na kyau shiyasa nake sonki baki da sanya sai magana ta gaba idan an cire cikin nan karki sake yarda da muradi ,ki nuna masa kina da class saboda kin sakar masa dayawa shi yasa har ya samu damar banka miki ciki "Allah aunty bazaki gane ba shi fa yanayinsa ba kamar sauran maza bane , Allah yayi sa da kafirin karfi kamar Shari'a baka isa ya rikeka ka kwace ba dan ma ina masa hauka da yanzu ya tumurmusheni yafi sau babu adadi "shikenan idan an cire abinda ke cikinki ya za'a yi dashi ?"ya kuwa za'a yi baya na kawo masa abunsa yasan yadda zai yi dashi ni kuma na kama hau kamar farashi ina cika ina batsewa ina masa komai da izza da nuna isa ta karasa maganar tana kwashewa da wata mahaukaciyar dariya "kinsan wani abu aunty nah yau fa akwai kallon film a gidan nan dan wallahi sai yayi ƙaramin hauka "a she Zaki sha mazga "shi har ya isa ya taba lafiyar jikina "shikenan jiki duba wannan dan wahalar ko ya wula mu san inda dare yayi mana bari nima dai na tashi na shirya "okay " . aunty afra ta fada mata inda zasu hadu sannan ta katse kiran ...."


Bayan kamar minti arba'in kisna ta fito da shirinta cikin doguwar riga baka da hijab baki da nikaf shima baki ta kulle kofar falo ta zare key ta jefa a handbag dinta ta soma tafiya a hankali ta har ta karaso bakin kofar d'akin sanusi ta tura kofar haɗe da lekawa nan ta gansa kwance a kasa ya lashe abinci tass ga kwalin lemun bude ko bata tsaya dubawa ba tasan ya kwankwad'e dan haka ta saki murmushin samun nasara ta juya da sauri ta buɗe ƙaramin get din gidan ta soma tafiya cikin sauri sauri kamar zata tashi sama har ta karaso bakin titin unguwarsu bata haɗu da wanda ta sani ba hakan kuwa yayi mata dadi ta tsaida mai texi bata tsaya sun yi ciniki ba suka dauki hanya tana fada masa inda zai kaita a ikotun suna tafiya suna communicating da aunty afra har suka karaso daidai isalo jeactoin nan suka tsaya suka ɗauketa ."

suna isa asibitin atomos suka kira layin likitan da zata musu aikin , ta fito cikin fararen kaya irin nasu na likitoci ta shigar dasu ciki ta basu gurin zama a reciption sannan ta koma office dinta suna zaune suna tautaunawa akan zubar da cikin wata mashiyar mace kyakkyawa dake zaune kusa dasu ta sake matsowa sosai idanunta sun cika da ruwan hawaye saboda duk ta fahimci abinda ke tattare da rayuwar Kisna hajiya munirat ta tsura ma Kisna ido tana kallonta har kisna ta tsargu tayi shiru tana kallon matar "yar nan kiyiwa Allah karki zubar da cikin nan duk dai dana fahimci kamar auren dole aka miki baki son mijin shiyasa kike son zubar da cikin babu mai imanin da zai ce yana gabatar da rayuwarsa yadda yake so mai kudi ko talaka mutumin kirki ko akasin haka mutane dayawa suna son abinda zaki zubar ,wata ta dauki cikin taji yadda yake ajikinta ma tana so amman bata samu ba kuma badan Allah baya sonta ba , a tarihi akwai mata dayawa da suka fiki shiga kunci a dalilin auren dole amman sunyi hakuri sun yiwa iyayensu biyayya sun rungume qaddararsu har daga karshe sun zo suna alfahari da auren ,kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki ki bar cikin nan ki gode wa Allah acikin halin daya barki kada kiyiwa Allah butulci".

Kisna ta lumshe idanunta kawai dan bazata iya tankawa matar ba dan tayi mata kwarjini matuka amman bata so ta sanyo kanta cikin lamarinta , Hajiya munirat ta numfasa sannan ta cigaba da yiwa Kisna nasiha mai shiga jiki dan ta lura yarinyar bata san rayuwa ba daga ganinta tana matakin farko a rayuwar duniya batasan me gobe zata haifar mata ba ,dan kuwa da tasan karshen abinda zai biyo baya data fahimceta juyin duniya matar nan tayi da Kisna har afra ta mike ta bar gurin zuwa wani ɓangare itama Kisna ta mike zata bi bayanta matar tayi saurin riko hannuta cikin nata " da alamun diyata baki ɗauki shawarata ba kou ?" Kisna tayi saurin girgiza mata kai da cewar "abinda bazai taba faruwa bane dole kuma wajibi ne na rabu da cikin nan da nake dauke dashi wallahi bazaki fahimci yadda auren nan da cikin nan suka rusa min komai nawa ba " haka ne tunda auren dole ne zai iya rusa komai naki, ni abinda yasa kikaga na damu nasan zafin haihuwa da radadin cire ciki saboda haka nake baki shawara akan kudirinki hawaye ya fara zuba daga idanun Kisna da rawar murya tace "Hajiya kiyi hakuri ki kyaleni kada ki shigar da kanki cikin rayuwata ni cikin nan matsala ne kuma lalura ne agurina kiyi hakuri ki kyaleni nayi abinda ya kawoni "...

kiran da afra tayi mata ne yasa ta soma ƙoƙarin zare hannuta daga cikin na hjy munira amman ta sake damke hannunta sosai "wannan matar wacece agurinki data rakoki zubar da ciki ? Hajiya munirat ta tambayeta tana dubanta "matar yayana ce kuma cousing sister dina ce "amman duk duniya baki da makiyayar data wuceta kuma a gaba zakiyi kuka daita domin duk cikakken masoyi bazai so ka cire arzikin da Allah yayi maka ba" hjy munira na gama fadar haka ta sakar mata hannu tana zubar da hawayen tausayinta domin kuwa irin cutar datayiwa kanta kenan a karshe Allah ya barta haka babu wanda zata kalla a duniya a matsayin jininta , "duniya ina zaki damu ? wallahi da mutane zasu san abinda ke tattare da shafukan rayuwarsu da wani abu idan ance suyi bazasu yi ba " tana kallonsu likita ta sake fitowa ta shigar dasu cikin office dinta.suna shiga ta bawa kisna umarnin kwanciya akan gado kana ta bude gaban Kisna ta fara dubata bayan kamar minti goma tana dube dubenta ta d'ago ta kalli inda afra ke zaune tana dubansu " wannan cikin yafi karfin abotion fa sai dai ayi mata alluran nakuda ta haifi abinda ke cikin "afra ta kalli Kisna itama ta kalleta "kinji abinda likita tace me kika gani ?"ni dai bani da zabi ayi min koma menene indai cikin zai fita " take aunty afra ta bawa likita umarni ayi mata allurar nakuda."

nan take likita ta soma gudanar da aikinta ta nufi wani karamin duro dake ajiye a cikin office din ta dawo ɗauke da sirinjin allura , ruwan magani ta zuka a sirinjin "bani hannunki inji cewar likita Kisna tayi saurin mika mata duk da tsananin tsoron allurar da take amman haka ta ciza lip's dinta , a hankali aka fara sira mata allura tace " ash dan Allah likita kibi a hankali ko ta kanta bata bi ba cikin kwarewa likita ta cigaba da tsura mata allura nan take ta fara jinta a sama bayan kamar awa biyu bayanta da mararta suka amsa , likita ta sake zukar ruwan wani allurar tayi mata nan dakin ya fara juya mata ta fara fita haiyacinta ta rike mararta tana ciza lip's dinta da karfi tare da kiran "wayyyohhly Allah mutuwa ......."
" zan mutu aunty afra ki taimakeni wallahi mutuwa zanyi a she abun akwai zafi wayyyohhly Allah dana sani da ban yarda ba wallahi mutuwa zanyi ki taimakeni gabadaya ta rude sai faman zuba sambatu take gbdy ta fita haiyacinta sai jijiga take akan gado da azaba tayi azaba saukowa tayi tana kuka da idanunta cikin tsanani firgici da afra ta gani tattare a fuskar Kisna yasa duk ta rude Itama ta shiga tashin hankali sai zufa take fitarwa tana kamota tana yi mata sannu kisna ta durkushe a kasa tana wani irin numfashi tamkar ranta zai bar gangar jikinta , dan haka likita tace afra taje daga waje ta jirasu ita kuma ta k'arasa bayan Kisna ta shiga shafa mata baya a hankali tana mata sannu iya wahala kisna tasha sai gumi ne ke karyo mata jikinta na wani irin rawa ,tayi tsawo awa biyu durkushe tana fama da murkususun ciwo sannan a karshe taji wani fitowar wani abu mai sanyi daga gabanta yana bin jikinta tare da wani azababben ciwo ta rike karfen gadon da iyakacin karfinta tana jijiga amman har lokacin shiru babu fitowar abinda ke cikinta , awa biyu ta wuce babu labari tun tana fahimtar wacce ke tsaye akanta har ta dawo zuba sambatun da likita bata fahimta ,har bakwai na yamma Kisna na kan abu daya abu kamar wasa har taran dare .afra ta shigo d'akin yafi sau goma tana dubata sai dai da kuka take fita daga dakin ganin irin wahalar da kisna ke sha ,ga wayarta yaya badamasi sai faman kirata yake haka ma wayar Kisna muradi ya kira yafi sau hamsi babu damar d'agawa har cikin dare Kisna na kan abu daya .."

da misalin karfe biyar na asuba kisna ta saka wani razannaniyar ƙara likita tayi saurin rufe mata baki cikin tsananin tashin hankali can sai ga baby's har uku sun fito a jere har an kusan gama musu halitta suna fitowa taji kamar an cire mata duk wani ciwon sai numfashi kawai take saukewa da kyar tana kallon baby's din da bata ji digon imaninsu ba ko tausayinsu acikin zuciyarta tsanar mahaifinsu itace farkon abinda ta maye gurbinsu laifin ubansu ya shafe su dan bata ji digon soyayyarsu acikin zuciyarta ba hasalima farinciki taji ya mamaye ilahirin jikinta data rabu dasu .."
Yayinda wani irin tsoro mai tsanani ya shiga zuciyar likitan dake tsugunne a gaban Kisna ganin yara har uku maza masu tsananin kama da juna ,nan take jikinta ya dauki rawa ta zubawa Kisna idanu tana kallonta can sai ga hawaye ya fara zubo mata tunda take aikin zubarwa mutane ciki bata taɓa aikin daya daga mata hankali ba irin wannan gabadaya ji tayi kamar an zare mata laka, jikinta babu kuzari ta
kira afra , tare suka dawo d'akin tana nuna mata yaran itama tana ganin baby's har uku a kasa jikinta ya kama rawa a matukar gigitace tace "na shiga uku me zan gani haka yara har uku ?" wallahi dana san 'yan uku ne a cikinki Kisna da bazan saka hannuna gurin ciresu ba " ta karashe maganar cikin tsanani tashin hankali " aikin gama ya rigada ya gama aunty afra ni dai tunda na rabu dasu ai shikenan Kisna ta fada cikin karfin hali tana lumshe idanu "nima gaskiya dana san yara uku ne acikinta bazan saka hannuna gurin ciresu ba inji cewar likita "Kisna ta sake lumshe idanunta batare data sake tanka musu ba dan sun rigada sun gama mata mai wuya tunda suka taimaka suka cire cikin ,dan bancin su bata san yadda zatayi da cikin ba sai dai ta haifesu dole ai kuwa da an cuceta a rayuwa, yaya zatayi da yara har guda uku ?"
duk abinda ya kamata likita tayi mata dan jini ya tsaya "da alamun ma baki da bayan haihuwa dan da cikinki ya kai nine month's

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login