Showing 228001 words to 231000 words out of 495987 words
Chapter 77 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
dare ta dawo gidansu Farida ta kwana gabad'aya akan soyayyar Musa rayuwar gida ya fita ranta har tsawon kwanaki ashirin ana nemanta daga baya aka san inda take tana fita mumy da aunty ummin da Zainba tare da Afra suka zo gidansu farida bata boye musu komai ba ta fada musu tabbas tana gidan kuma tana zuwa gurin Musa mumy ta fashe da kuka , suka ce zasu dawo da zarar ta dawo ta kira su a waya."
hakan ce ta kasance gurin sha daya mumy taga kiran farida daman a shiryantake suka fito gabadaya har muradi matan suka shiga gidan suka isketa a parloun zata gudu mumy ta kamota "dakata babu abinda zan miki ,ta zaunar daita itama ta zauna "kullum abu daya da zarar anyi magana sau kice bakya tare da musa yanzu fa da me zaki kare kanki "?" Me ma akayi miki kisna da zaki bar gida ? tayi shiru ungo waya ki kira shi kullum ke kadai ake duka yau shima yazo yaci dukan dan ubansa na gaji da zuwa police station Ai kisna na jin haka ta rud'e dan bata son a ta'ba mata lafiyarsa gara ita a doketa ta amshi waya ta kira number the way yadda tayi masa magana ya fahimci ta kamu a hannun iyayenta dan haka ya katse kiran Zainba ta kalleta tace "mumy tashi muje gida kawai dan wallahi bazai zo ba ",me yasa kika ce haka Zainba?"Allah mumy bazai zo baki ga yadda tayi masa magana a waya ba shi din idan ba dolo bane ai zai fahimci wani abu, mumy ta gyada kai "shikenan ai kya ci dukan ke kadai wallahi muddin baki fita hanyar wannan dan iskan yaron nan ba jikinki ba zai daina cin izaya ba muje gida tayi narai narai da idanunta tace "bari na dauko rigarta ta nufi dakin su Farida jikinta na rawa ta soma neman hanyar da zata bi dan bata son komawa gida tafi jin dadin rayuwar waje tare da Musa kullum zasu haɗu idan tana gida fa ? babu hanyar fita daga dakin sai falo ,ta kalli wakaken window dakin dake kan three building bata yi tunanin komai ba ta haye ta dira sai kan saikawe ta saki wani siririn ƙara mara sauti tamkar muryar mage saboda azaba ........ ..
madu da ya badamasi da muradi da Samir da suke tsaye suna jiran a fito daita suka ji fadowar abu kasa dummmmmm , afra da Zainba suma suka mike suka leka dakin data shiga wayam mamaki ya kamasu suka shiga nemanta acikin dakin "ina kuma ta shiga ? Afra tayi saurin leka bayi bata nan, a hankali idanun zainab ya kai kan window ta ganshi a bude take gabanta ya fadi "inna lillahi karda kisna ta window ta fita aunty afra tayi saurin karasowa jikin window suka leka a tare suna haska waya sai hangota sukayi a kasa bata numfashi aiko suka saka ƙara suna kokarin fito wa daga dakin "shikenan kisna ta mumy .." mumy najin abinda suka ce ta rushe da kuka tana furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "kashe kanta tayi ta tambayesu jikinta na wani irin rawa hanyar fita suka yi gbdy har farida suna mata bayani ta biyo bayansu da sauri tana kuka tana furta kalmar" inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "shikenan na rasa yarinyata nasan ta mutu duk mutumin daya fado daga gidan sama mai hawa uku mutuwa zai yi jikinsu na rawa suka karaso a lokacin tuni ya badamasi ya ciccibota hankalinsa a matukar tashe saboda bata numfashin shi kuwa muradi mutuwar tsugunne yayi numfashinsa na barazanar ɗaukewa Samir da madu suka tsura mata ido tana kwance rai hannu Allah ,"ku samo ruwa ina ganin suma tayi da gudu madu yaje ya siyo ruwa ya dawo ya mikawa ya badamasi ya shafa mata still Bata motsa ba 'mumy na kuka tace "ku daukota muje gida kawai ta rigada ta mutu fa tayi maganar tana juyawa ta soma tafiya tana ci-gaba da kukanta". naunayen ajiyar zuciya suka sauke gabad'aya ganin ta sauke numfashi da atishawa "mumy tana raye fa suka hada baki gurin fadar haka a tare mumy da muradi suka karaso kansu muradi yayi saurin dukawa a gabanta ya kai hannu ya amsheta a hannu ya badamasi ya tsura mata idanunshi yana Kallonta hawaye na tsiyoyo daga kwarnin idanunsa cike da tausayawa yace "sannu Kisna ......"iya abinda ya iya fada kenan yayi shiri ya kasa karasa magana cikin raunin ciwo taja numfashi da kyar ta sauke tana runtse idanunta tare da rike gefen kungunta da hannu "yanzu kisna kin zabi mutuwa akan a hukunta musa?"inji cewar mumy kafin kace me tuni mutane sun cika gurin kowa na fadan albarcin bakinsa "wani mutun yace wannan yarinya Allah kadai yasan ya'yan da zaki haifa a duniya sama ba daya ba,ba biyu ba har uku ki iya fadowa ,gaskiya ku kaita aikin soja kawai shi zai fi dacewa daita muradi ya d'ago ya kalli mutumi cike da bakinciki a fili yace sai kazo ka kai ta tunda kai ne ubanta zuciyarsu cike da rauni suka ɗauke zuwa gida "...
Mmm Sudais[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 34
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
....D'aki iya arfat ta basu babu kunya bare tsoron Allah musa ya mike tsaye tare da mikawa kisna hannu "tashi muje mu kwanta kinji ifemi kamar bazata mike ba sai kuma ta mika masa hannu ta tashi gudun ɓacin ransa suka shiga d'akin da iya arfat ta nuna musu, wata yar karamar katifa ce yashe a kasa da pillow guda daya , ya kalleta yace "ki kwanta mana ko zakiyi wanka ne ? " Ta girgiza masa kanta alamun "a'a ".
"Okya bari ni na watsa ruwa ya cire kayan jikinsa a gabanta ya saura daga shi sai singlet da boxers, tayi saurin kawar da idanunta har sanda ya fita sannan ta buɗe idanunta , bai ɗauki dogon lokaci ba ya dawo d'akin ya goge jikinsa kwanta a bayanta tare da janyota jikinsa ya rungumeta tsam , tayi shiru kawai tana tunanin mumy da tunanin halin da zata shiga na rashin ganinta na tsawon awanin nan ganin jikinta yayi sanyi yasa ya kai bakinsa cikin kunneta "tunanin me kike yi ifemi ?".
"Ina tunanin gida bansan me zai sake biyowa baya ba a dalilin rashin kwanana a gida ba ban taɓa kwana a waje ba ina jin tsoro halin da mumy zata shiga tayi maganar cikin harshen turanci hawaye na gangarowa daga kwarnin idanunta, bai yi magana ba illa harshensa da ya zira cikin kunnenta ya fara tsotsa take gabad'aya tsigar jikinta suka mike jikinta yayi bala'in yin sanyi ta lumshe idanunta saboda yanayin data tsinci kanta ciki na zallar qaunarta , sai daya tsotsa kunneta sosai sannan ya juyo daita suka fuskanci juna ya maida bakinsa kan lip's d'inta ,tana son hanashi abinda yake mata kamar koda yaushe sai dai zuciyarta ta kasa dan haka ta barshi ya cigaba da wasa da sansar jikinta da albarkatun kirjinta da basu gama bayyana ba a haka har bacci ya d'auketa ya zare jikinsa ya sanya kayansa ya fito zuwa tsakiyar unguwarsu inda ya kasance base ne na samari .."
Tunda kisna tasa kafa ta fita daga gidan hankalin kowa ya tashi matuka most especially aunty Afra kusan tafi kowa shiga tashin hankali , babu wanda ya samu kwanciyar hankali har sanda dady ya dawo ,hankalin mumy a tashe ta koro masa komai ,yayi shiru yana sauraronta kafin daga baya ya numfasa yace "me yasa kika ɗauki hukunci duka akanta da kin bari na dawo asan abun yi , yanzu ina muka san ta nufa bare mu nemota saboda Allah ?" yayi maganar cikin tsananin ɓacin rai , ya rage kayan jikinsa ya fito zuwa haraban gidan madu da ya badamasi da gabadaya mutane gidan har masu aiki suka biyo bayansa tare da raba kansu zuwa nemo kisna , babu inda ba'a je neman kisna ba amman Babu ita babu alamunta har unguwar su musa madu da zainab da aunty Afra sun je amman basu ganta ba sai musa suka gani zaune cikin tsakiyar abokansa suna hira madu yaji kamar yaje ya cakumi wuyar rigarsa har sai ya fito masa da kanwarsa sai dai tunanin rashin hujja ya hanashi tana gurinsa ne ko akasin haka tunda shi gashi a cikin mutane ,musa na kallonsu ya ɗauke kanshi yana hura hanci , ranar dai haka suka Karachi neman kisna basu ga ko mai kama daita ba babu wanda ya runtsa daga mumy har mutanen gidan kwana zaune sukayi ,mumy banda kuka babu abinda take gabanta na tsananta faduwa saboda tsananin tashin hankali , tayi da tasanin dukan kisna yafi sau babu a dadi, dady dai yayi dauriya sosai magana yake son yiwa mumy akan kukan da take sai dai kukan zucin da shima yake bai barsa yayi magana ba da zarar ya runtsa idanunsa da zumar yin Bacci sai yaga kisnarsa cikin tashin hankali sai yayi firgigib ya bude idanunsa haka suka raya wannan dari cikin tsananin tashin hankalin da basu taba tsintar kansu ciki ba ."
gari na waye suka sake bazama nemanta wasa wasa sai da suka jera kwanaki biyar suna neman kisna batare da sun ganta ba fadar tashin hankalin da mumy ta shiga ba'a magana , duk ta fita haiyacinta tayi kuka kamar ranta zai fita , tana kuka ta kira muradi da Samir ta sheida musu halin da'a ake ciki ,take zuciyar muradi yayi mummunar faduwa sannan ta cika da matsanancin mamakin kisna sam bai yi tunanin kisna zata iya aikata haka ba duk da yasan tana da rashin jin magana amman bai zaci soyayya a ɗan shekarunta ba har ma da guduwa ta bar gida to ina taje yayiwa kansa tambayar da bashi da mai bashi amsa ? gabad'aya daga shi har Samir suka ji kasar cairo tafi a ransu burinsu kawai su dawo gida , dan shi muradi yaso tahowa a cikin satin samir ne ya dakatar dashi "karka manta nan da kwanaki kadan zamu fara jarabawa ga buga wasa a gabanmu zuwa England muradi ya ja tsaki kana a fusace yace "mahimmanci rayuwar kisna agurinmu ta wuce duk waɗan abubuwan daka ambata ,ga mumy na cikin damuwa gaskiya bazan zauna ba tafiya zanyi idan kaga zaka iya kazo mu tafi tare idan bazaka iya ba ni zan wuce Samir ya kamoshi suna fuskantar juna cikin tsananin tashin hankali yace "ka kwantar da hankali muradi komai zai zo da sauki tunda ga dady ga ya badamasi nasan duk zasu yi komai dan gano inda take , shiru yayi kawai dan bashi da abun da zai sake cewa sai dai baya ji zai iya cigaba da zama alhalin mumy na cikin damuwa ..."
bangaren kisna da musa kuwa kasancewarsu guri ɗaya acikin kwanaki yasa wata muguwar shakuwa da soyayya ta sake shiga tsakaninsu wacce tafi ta da , har ta kai idan ya fita yawonsa sai ta dinga jin kamar ta rasa wani abu daya danganci rayuwarta ,sosai musa yake bata kulawa da matar yayansa har ma da mahaifiyarsa abunka da kuruciya sai kisna take ganin kamar sun ma fi sonta akan yan gidansu duk halin da 'yan gidansu suke ciki musa na kawo mata labari saboda shi yana fita ko'ina yaje yawonsa cikin abokansa ya dawo wasu daga cikin abokansa kamar fatai marly sun san kisna na gurinsa dan haka idan yan gidansu sunzo unguwar sai suyi kamar zasu faɗa musu amman tsoron musa olegele yasa basa iya faɗa sai dai suyita Kallonsu yayinda hakan ke sake bawa yan'uwa kisna haske akan lallai kisna na tare da musa .
yau ma daga massalaci dady ya wuce neman kisna yana furta "laila a illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumi zuciyarsa cike da faduwar gaba "ya Allah kasan ban taba lalata diyar kowa ba da sunan zina Allah ka tsare min da mutunci kisna ka karkato min da hankalinta garemu tafiya kawai yake yana karanta duk wata addu'a da tazo bakinsa har gari yayi haske ya koma gida batare daya ganta ba .."
musa ya siyo wa kisna kanana kaya wando legis dogo da t shirt, kullum zata shirya su fita yawo inda suka san idanun 'yan gidansu ba zai kai garesu ba ,kwasam madu ya jiyo labarin inda suke , jikinsa na rawa ya zo gida ya faɗa aiko gabad'aya yan gidan suka nufi gidansu musa zasu shiga da hayaniya , dady ya hana ya nemi iso a gurin mahaifin musa Alhaji abdulganiyu olegele ,dattijon ya dingiso ya fito waje sanye da gajeren wando da singlet ya mikawa dady hannu amman bakinciki yasa dady ya kasa mika masa nasa hannun ya fara magana cikin ɓacin rai akan abinda ya kawoshi bayan mahaifin musa ya gama jin komai ya shiga gidan ya tambayi alaja mutia , kai tsaye tace masa "ita batasan komai ba amman bari ta Kira musa taji ko da gaske ne ,ta shiga daki ta kirasa ta kora masa bayanin komai ,hankalinsa bai tashi ba kamar yadda na kisna ya tashi saboda za'a rabata dashi , Kuka tasa masa tare da cewa bazata ko'ina ba ya rabu dasu idan sun gaji da wahala zasu koma gida "ki kwantar da hankali ni kaina bazan so Ki koma hannunsu ba amman alaja tace lallai nazo yanzu dan haka kema ki wuce gida ta yadda ba'a fahimci muna tare ba dan alaja bata son ansan muna tare dake ."
tare suka fito ta kowannensu ya kama gabansa ta nufi hanyar gida shi kuma ya nufi gidansu ,koda ya iso unguwarsu ya tarar da dangin kisna tsaye cirko cirko a kofar gidansu ,ko