Showing 438001 words to 441000 words out of 495987 words
Chapter 147 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
abun arziki zai zama na tsiya yanzu meye laifina daga fadar gaskiya ?
yayi mata banza yana hura hanci a ransa yace "haka ne abun arziki ?
Kamar taji abinda yace a ransa tace ""tam shikenan nayi shiru bari ma kagani na kama gabana daman a shiryena nake mufeeda zahra kun tashi mu wuce tare ko kuwa anan zan barku ?, suka kwashe da dariya tare da mikewa tsaye "yau dai an ganku a rana akan kisna sai kiyi taka tsantsan aunty ummi ki fara neman gidin zama agurin uwargida sarautar mata inji cewar zahra ,suka sa dariya gbdy ban da muradi dake ciccin magani aunty ummi tace "ai kuwa naga alama sai na bige da neman gidin zama suka nufi d'akin mumy dan yi mata sallama ."
kisna dake tsaye ajikin kofar dakin tayi kasa tana manna bayanta da jikin kofar ,wani murmushin farinciki ya bayyana akan fuskarta lallai sai yanzu ta tabbatar da muradi ya soma sonta ko babu yawa ,sai dai hakan bazai sa ta fito su hadu ba sai tagama jinyar zuciyarta ta mike da kyar ta koma ta kwanta amman har lokacin tana jin bugun zuciyarta akan mijinta dan soyayyarsa ta zame mata abincin ruhinta , tunaninsa ta shiga yi yayinda sautin maganarsa dake tashi a hankali ke shiga kunneta kadan kadan ,yana nan zaune tare da Samir da zee su aunty ummi suka fito "to mu zamu wuce sai wani lokaci a gaishe da amarya ko kallonsu bai yi ba bare ya amsa suka fita suna masa dariya ."
Ita kuwa nawal jin shiru har kusan uku da wasu mintuna bata ji motsinsa ba , ta fito daga part dinta ta tura kofar falonsa ta shiga da sallama taga baya nan wani faduwar gaba taji, a hankali ta nufi kofar bedroom dinsa data gani tayi knowcking a hankali saboda tasan halinsa shi mutun ne mara son hayaniya yafi son duk abinda za'a yi ayi shi a natse ,jin shiru ta sake yin knowcking amman still shiru babu motsin komai alamun ma babu wani halitta a cikin dakin jiki a sanyaye ta murd'a kofar dakin dan gaba-daya a tsorace take dashi ta shiga dakin kallon dakin ta shiga yi zuciyarta na rawa babu kowa acikinsa kallon dakin ta cigaba yi komai a kimtse very niet sai kamshi turarukansa ke tashi , a hankali ta karasa bakin gadonsa tana kallon farin bedshit din dake shimfide tana tunanin inda ya tafi batare daya nemeta ba , ta zauna tare da kwanciya akan katifa ta janyo pillonsa ta rungume ajikinta gam tana jin tamkar shi ta rungume a hankali ta fara rera kuka "Please my norr karka guji rayuwata wallahi ba laifi bane yaudarata akayi ,rayuwa babu kai numfashina zai tsaya , kuka take sosai can ta zabura ta mike zaune tana sauke numfashi da kyar idanunta na cigaba da tsiyayar ruwan hawaye hannu na rawa ta kai ta dauki frem din hoton kisna ta tsira mata ido tana murmushi ta dauki hoton cikin wasu kananan kaya rigar da kadan ta wuce cibiyarta wanda kallo daya namiji zai mata yaji sha'awarta ta tsarga masa tana kallo hawayenta na dinga akan hoton a hankali ta jin wani abu na taso mata , bata da tantama kishin mijinta ne ya yunkuro mata ta lumshe idanunta tana jin zafi a ranta "why norr me yasa zaka ajiye hoton nan a nan alhalin kasan dole zan ji babu dadi idan nagani ?, ta sauko daga saman gadon tana jin kamar ta saki frem din akan tayis ya tarwatse tun kafin nata zuciyar ya samu matsala sai kuma tayi wani tunani ta fasa ,ta mayar dashi inda yake ta fito da gudu ta fada ɗakinta tana kuka tamkar ranta zai fita "me yasa na yarda na basu kaina gashi na jama kaina tashin hankali agurin mijina ?, wayyyohhly Allah ka taimakeni kada na samu matsala da mijina .."
har sanda karfe hudu ta buga muradi da Samir suna nan suna hira sannan suka fita tare zuwa massalaci ,bai dawo gidan mumy ba gida ya wuce dicret zuciyarsa na tuttukin bakincikin yana shigowa parlour ya iske nawal da wasu mutane guda biyu zaune a kasa ita kuma tana zaune akan kujera bai tsaya bi ta kansu ba ya shige d'aki ya zauna shiru can ya mike ya zare jallabiyar jikinsa da agogon dake daure da tsintsiyar hannunsa ya shiga bayi , cikin natsuwa nawal ta turo kofar dakin ta shigo gabanta na faduwa , ta hadiye wani abu data ji ya tsaya mata a makoshi jin saukar ruwa a bayi ta fahimci wanka yake tana kokarin juyawa taji an bude kofar bathroom ya fito daure da white towel sabo a kugunsa, murdadden jikinsa sai sheki suke zubawa ruwan wanka na yawo ajikinsa ga kwantaccen suma qirjinsa da yayi kasa har kasan mararsa gabanta na faduwa ta fuskancesa idanunta ya shiga cikin nashi saurin dauke Idanunshi yayi kamar bai ganta ba , ganin yadda yayi yasa gbdy ilahirin jikinta ya dauki rawa kamar mazari tare da juya masa baya dan ya samu damar kimtsa wa ,ta cikin mirror ya tsurawa bayanta ido yana jan tsaki "aikin banza kawai ko kunyar uwar me take ji ? yayi maganar a kasan zuciyarsa ."
turare ya ɗauka ya fesa sannan ya karasa inda kayansa suke ya dauki kaya marasa nauyi ya saka duk abinda yake tana tsaye batare data juyo ba gabanta na cigaba da faduwa ya raɓa ta gefenta ya fito zuwa parlour bátare daya ce mata komai ba tsayuwa ta cigaba da yi kamar wacce aka da sata cikin tsananin tashin hankali wasu hawaye suka yi nasarar zubo mata tana kokarin gogesu ya sake shigowa a dakin a zuciye ya karaso gabanta ya tsaya yana cewa "ke ....wadan can mutane dake falo su waye ?, muryarta cike da in Ina tace "ma ...masu aiki ne "
"Masu aiki ya maimata yana mata kallon sama da kasa ? ta gyada masa kai alamun "eh! "to bana bukatarsu acikin gidan nan dan haka maza a sallamesu su kama gabansu yayi maganar yana furzar da numfashi tare da juyawa ya bar daki jikinta na rawa ta fita zuwa falon ta sallamesu ."
ta zauna tana fuskantar shi tana sake danne kukanta gbdy yaki kallon inda take illa remut daya dauka ya kunna tv ta rasa abinda ke mata dadi a rayuwarta a dan fusace yace "wai meye haka ne da zaki sakani gaba da sheshekan kuka ? "wani irin bugu gabanta yayi da karfi ,take tashiga kokuwa da numfashinta dake barazanar daukewa tana kokarin tsaida sheshekan da take ta durkusa tare da jan gwiwowinta ta karasowa gabansa tana kuka " kayi hakuri dan girman Allah "me kika min da kike bani hakuri yayi maganar batare daya kalleta ba Idanunshi na kan tv .
ta share hawaye fuskarta " nasan laifina shiyasa nake baka hakuri , wallahi ban kasance mazinaciya ba tsautsauyi ne my norr kuma nayi ƙoƙarin na fada maka yadda komai ya faru a can baya sai dai tsoron karka gujeni yasa nace maka maza uku sun yaudareni "kenan karya kika fada min ?, a'a ta furta cikin murya kuka "gara ki fada min cewar mazan uku sun kusanceki kafin ni hankalina zai fi dauka , cikin rawar jiki ta shiga bashi hakuri akan wancan karyar da kika girba min "
Jikinta na rawa tace " fada maka komai daya faru bashi da wani amfani sai tarin bakinciki da damuwa ni dai ka yafeni dan Allah ka kuma rufa min asiri nasan kai mai hakuri ne kayi hakuri dan girman Allah ta karasa maganar tana rungumeshi ajikinta tare da fashewa da wani sabon kuka ta zagaye weist dinsa da duka hannuwanta ko motsi bai yi ba bare tasa rai zai yi magana sai data sha kukanta sosai sannan ya zareta ajikinsa yana fuskantarta "kace ka yafe min my norr yayi mata shiru "zaka ci gaba da zama dani ko kuwa zaka sallameni dan nasan ganina zai iya haddasa maka komai ?, nan ma shiru yayi mata kawai dan idan ransa ya baci baya iya magana ko kadan haka tayita masa magana batare data fada masa dalilin dayasa ta bawa samarinta na baya kanta ba ."
mikewa yayi ya koma d'akinsa ya dauki hoton kisna ya tsurawa hoton Idanunshi da suka kada suka ja ya manna hoton a qirjinsa yana jin wani irin buguwar zuciya ,bai taba jin yana tsananin sonta ba sai a wannan lokacin ta shiga zuciyarsa sosai "kisna kin samu kyakkyawan mazauni a zuciyata da rayuwata dan Allah ki bani dama na ganki i love you so much I really miss you ,nayi kewar komai naki , gangar jikina na bukatarki ,ki taimama ki bari na ganki ya kwanta rungume da hoton bai sake fitowa ba sai washegari shima yana gama abinda zakiyi ya fice a gidan ko tsayawa break bai yi ba ,bai dawo gidan ba sai byn isha'i ya shige d'akinsa ya kulle ya kwanta.
nan fa abun duniya ya damun nawal hankalinta ya daga sosai Cike da tashin hankali nawal ta dauki wayarta ta soma neman number mumynta tana dauka ta sakar mata kuka , murmushi ne akan fuskar hajiyarta amman bata san sanda ya koma zuwa damuwa ba "ya da kuka nawal?tayi maganar tana saka wayar a handsfree " ina missing dinku mumy hajiya Mardi ta kalli mijinta dake zaune kusa daita sannan ta sakar masa murmushi kafin tayi magana , nawal taji sautin Muryar mahaifinta "haba dai mamana jiya ne kawai fa bama tare , ki daure mamana ke din jaruma ce ban san ki da ragwanta ba "Allah dady kamar na dawo gida nake ji "ya numfasa kana ya cigaba da magana "ina kika taba ganin akai mutun gidan miji shekaranjiya yace kamar ya dawo gida yau ?, duka kwananki daya ne fa dariya suka saka mata "Allah dady bazaka fahimci halin da nake ciki bane a kwana dayan da nayi , gbdy na rasa meke damunna "kinga kiyi hakuri aure dan hakuri ne , ki rike mijinki ki zauna lfy da danginsa kinji idan an kwana biyu da kaina zanzo na ganki Allah yayi miki albarka mumy ta mike tana cire wayar a handsfree ta shiga bedroom dinta "ke sai naga masu aiki sun dawo lafiya dai ko "wallahi mumy cewa yayi baya bukata" ga dan iskan yaro to uwarsa ce zata miki aikin gidan ?
"kinga mumy mu ajiye maganar masu aiki akwai fa matsala nan ta shiga korowa mahaifiyarta komai dake tasan komai sai jan numfashi tayi "kina jina ki kwantar da hankalinki idan Allah ya kai mu gobe ki kira wacce uwar goyon tasa kiyi mata kuka amman karki kuskura ki fada mata komai ,nace kiyi haka ne dan nasan ita kadai ce wacce zata shawo miki kansa da sauri kafin ita wacece matar tasa ta tare "kin kawo shawara mumy zan yi kokari kiranta gobe yanzu ma dan dare yayi ne da yanzu zan kirata "ya za'a yi da masu aiki a sallamesu ne dan gsky ni bana bukatarsu ? "a'a mumy ki dan barsu zuwa wani sati muga yadda yanayin zai yi idan da hali sai su dawo idan babu na hakura kwa dinga aiko min da abinci nan suka shiga wata hira nawal har da dariya byn wani lokaci sukayi sallama ."
washegari ma kamar jiya da sassafe ya fita ko breakfast bai yi ba yana fita ta soma neman layin mumy bugu biyu mumy ta dauka cikin sanyayyiyar muryarta tayi sallama kawai taji ta sanya mata kuka cike da tashin hankali tace "nawal me ya faru ?,mumy ina yini ?,yasu aryan ?suna lafiya meke faruwa nawal kinsa hankalina ya daga "wallahi mumy ina cikin damuwa ta kare maganar tana sakin kuka "damuwa ubangiji ya rabamu daita " mumy laifi nayiwa muradi ya dauki fushi dani mai tsanani "subhanallahi to ya isa kukan sannan bana bukatar jin laifin dan mijinki sirrinki ne inshaallahu zan masa magana ke kuma ki kiyaye abinda zai bata masa rai kinji Allah yayi maku albarka "ameen mumy Allah ya qara girma suka yi sallama mumy na katse kiran ta kira muradi tace maza yazo tana son ganinsa cikin kankanin lokaci ya karaso bakinsa dauke da sallama ya shigo cikin dakin mumy tana zaune rike da waya ta karba masa sallama a hankali ya karaso ya durkusa har kasa gabanta "ya gida mumy cikin haɗe fuska mumy ta amsa yace "mumy lafiya yana ganki kamar kina cikin damuwa ? "dole ka gani haka har yaushe akayi daren muradi yau duka kwana biyu datarewar yarinyar nan har ka fara damun rayuwata ? .
naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana runtse Idanunshi "bazan dauki ka wulakanta musu yarinya ba kai baza'a maka laifi kayi hakuri cikin dadin rai ba sai ka dagawa mutane hankali ... " mumy ki tsaya ki fahimceni itace tace nayi mata wani abu ....?ban sani ba idan ba ita bace yaushe zan sani sauran kuma idan ka koma gida ka hauta da bala'i wallahi zaka hadu da fushina da baka taba gani ba , mumy ta inda take shiga ba ta nan take fita ba shi kuwa tun da ta fara magana ya sunkuyar da kanshi kasa bai d'ago ba har sanda ta dasa aya ..
Shiru ya ɗan ratsa dakin can muradi ya d'ago ya sake duban mumy sannan yace "kiyi hakuri mumy inshallah komai ya wuce hakan bazai sake faruwa ba duk abinda kike so shi za'a yi "ka dai ji abinda na fada maka banason jin wani tashin hankali sai zaman lafiya ka tashi ka bani guri "dan girman Allah mumy kiyi hakuri karkiyi fushi dani wallahi na hakura ki yafe min duk ya dawo kalar tausayi sanbna ta saki ranta tana sakar masa murmushi ta shiga yiwa yaronta da addu'ar zaman lfy sai lokacin hankalinsa ya kwanta ya mike ya fito yana fita mumy ta kira nawal tayi mata fada sannan tace itama ta kiyaye abinda zai dinga motsa masa zuciya dan fushinsa bai da kyau "inshaallahu mumy na gode sosai a gaishe min dasu aryan da mutan gidan tana ajiye wayar tayi wani tsalle ta fada kan gadonta ta kwanta lamo can ta mike ta fada bayi tayi wanka ta fito ta sauya wasu kaya zuwa kanana kaya gbdy ta dawo one babu wani tsari babu fasalin ta kira gidansu tace akawo mata abinci cikin kankanin lokaci komai yayi ready karfe biyar daidai ya shigo gidan ta mike tsaye ta isa kusa dashi cikin sanyi jiki tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya nufi hanyar d'akinsa ta bishi stil tana sake bashi hakuri babu yadda ya iya haka ya hakura yayi wanka suka dawo parlour tun kafin ya zauna ta kamo hannunsa zuwa dinnig ta bude wata hadadayar kula sai kyalli take ta zuba masa freidrice dataji kayan hadi ,abinci kadan yaci dan shi bai damu da abinci mara nauyi ba ya tashi ya koma daki ta bishi daki tana lallabashi da bashi hakuri , ya sanyawa zuciyarsa ya rungumeta suka cigaba rayuwarsa duk wani kulawa nawal tana yi masa amman hankalinsa da zuciyarsa sam basa gareta suna gurin kisna gashi ita kuma ta boye masa kanta ko yaje gidan baya ganinta gashi soyayyarta tattare da matsananciyar sha'awarta ta addabi ruhinsa duk zuwan da zai yi baya ganinta sai dai yaga yaransa hankalinsa idan yayi dubu to a tashe take ".
Tun daga lokacin bai kara samun walwala da sukuni ba har mamakin kansa yake kullum cikin damuwa yake baya wani cin abinci kirki gashi kowa ya gane halin da yake ciki yanzu gidan mumy da nawal ita kanta ,sai dai ko sun tambayesa sai yace musu babu komai yanzu haka aiki yake agaban system amman tunaninta ya hanashi aiwatar da komai ,ya ture system din gabansa ya mike ya fara zagaye cikin d'akinsa ya dauki lokaci a haka yana kai kawo sannan ' ya dawo ya zauna a gefen kujerar dake dakin yana jinjina girman alamarin kisna duk ilahirin jikinsa sunyi masa mugun sanyi , ahankali ya sake mikewa ya koma kan gadonsa ya zauna yana son ya cigaba da aikinsa idanushi suka sauka akan dan karamin fream dinta dake ajiye akan bedside ,ya zuba mata ido kawai yana kallonta shi kansa ya amince tun ba yanzu ba yana na matukar quanarta fiyye da komai, Itama kuma haka take matukar sonsa tamkar rayuwarta kamar yadda ta sha fada masa a cairo , " duk duniya byn mahaifiyarsa da mumy to ita kadai yake ji a gangar jikinsa , soyayyarta ta zarta na sauran matan duniya 'ahankali ya kai hannunshi ya dauki karamin fream din yana cigaba da kallonta yayi matukar kewarta sosai, yayi kewar komai nata ,kusan kwana bakwai Kenan rabonshi da sanyata acikin kwayar idanunshi wanda kuma hakan ya faru ne a sanadiyyar zuwan nawal , bancin haka yasan zuwa yanzu da tuni tana makale dashi tana bashi kulawa ,runtse idanushin yayi sosai Yana jin yadda kaunarta ke sake ratsa zuciya da gangar jikinsa"tsawon lokaci idanunshi na runtse sannan ya budesu fes yana sake kallon hotonta tare da sake jin haushi da takaicin nawal a ranshi. "
********
Bangaren mumy kuwa bata bar kisna haka ba kullum cikin tsuma diyarta take da kayan mata dana gyaran jiki , yanzu ma tsaye take a bakin kofar ɗakinta tana knowcking daga cikin dakin kisna ta amsa da waye ?,ki bude nice jin muryar mumy yasa ta taso ta bude mumy ta shigo hannuta rike da kula wacce ke dauke da hadin jijibi , naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke ta ajiye kular hannunta ta janyo karamar kujarar ta zauna tana fuskantar kisna dake zaune gbdy jikinta ya sake sauyawa , tayi kyau sosai farinta ya sake fitowa tamkar wacce take wanka da madara ita kanta mumy kisna tayi mata kyau sosai ,sai dai ta dan rame shima tasan hakan baya rasa nasaba da rashin mijinta, murya a sanyaye tace "ga jijibi nan a