Showing 492001 words to 495000 words out of 495987 words
Chapter 165 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
muguwa ce ina mata mugunta sai ka karanci halinta tukun zaka gane ta ko abu ta siyawa yaran bata bani ba sai taga idanun mijinta zaki ganta ta shigo suki suki cike makirci a hau basu , Kinga last week muna zaune ya tambaya ko yaran suna da sababbin kaya da wanduna ingaya miki kafin nayi magana ta tsigil " wai suna dashi akwai waondunan da basu saka ba ,na kalleta na hade rai nace" ni dai babu wandunan da basu saka ba duk sun gama sakawa sai cewa tayi "Ahmed dai na da wanduna sababbi ina kallonta ta gama kirge kirgenta dana ga zata bamin lokacin na barta ita dashi na wuce ina zan iya ga magana kmr aku kuturu ga makirci "Allah ya kyauta yasa ta gane ,ameen suka ci-gaba da hirar duniya wata tara kisna ta sake haihuwar namiji yaci sunan ya samir aunty ummi ta saka masa mahbub amman ita kisna dan uwa take kirasa
*******
Kisna na zaune a falonta sanye da riga da wando na bakistain farare sol kanta babu dan kwali gashin kanta dake cikin gyara kullum sun zubo bynta , yayinda mahbub ke kwance a gefenta yana shan hannu ,sauran yaran suna kasa suna wasa sai mother dake gefenta tana nuna mata assignment sai ga nawal ta shigo kamar zata fashe tana kunfar baki "nace a kawo min mahbub kince kar akawo min Allah yasa dai ba cinyasa zanyi ba sannan ba wani abu zan masa ba bare kince kar akawo shi ,ni bansan kince a kawo miki shi ba amman gashin nan yanzu idan zaki wuce ki tafi dashi inji cewar kisna ta fada tana dauke kanta ta maida kan assignment din da takewa mother ,
"bazan tafi dashi ba me gindin haihuwa dan na lura baki qaunar ganin yayanki angurin Allah yasa ba wani mugunta nake masu tsam mother ta mike ta shige dakinsu ta kulle dan sam kwakwalwarta bata son hayaniya haka bata son ana ihu brain din zafi yake mata."
kisna tace "naji ni me gindi haihuwa ce idan fitsari banza ne kiyi mana ko ni na saki shan maganin kwayoyin hana daukar ciki da kike yawon kasashen duniya , ki haihu mana ko na hanaki ne ,Allah ne ya bani kuma kema zai baki idan kin tsarkake zuciyarki kin cire mugun nufin dake ranki ,kaji min shegiya munafuka makira mata duk yadda nake kauce miki sai kin nemi sani magana, ban san me kawo wannan kananan maganar bare har kice min me gindin haihuwa yaro ne nace gashi nan idan zaki tafi ki wuce dashi ko bashi kenan ba amman dake ke din makira ce sai da kika nemi fada min magana duk take taken ki fa ina sane fa kawai dai na zuba miki ido dan bani da lokacinki, Idan kinga miji ki dinga nan nan da ya'ya kina nuna wai ke kina sonsu alhalin ba haka bane acikin zuciyarki daga yau ma karki kara taba min ya'ya muna fuka kawai wahalalliyar sai faman lashewa miji takashi kike amman bakya gabansa suna cikin haka muradi ya shigo aiko nawal na ganinsa ta fashe da kuka tana cewa "daga abun arziki zai zama na tsiya norr kaji fa daga na aiko ta bada mahbub akawo min shine tace...."shine nace me ? ki shiga hankalinki nawal , haushi ya kama kisna ganin tana kukan makirci daga yau kika sake jefa min magana sai na miki rashin mutunci na cire miki bakaken hakoran nan me katon baki kawai aiko nawal ta sake rushewa da wani kuka kamar wacce akace uwarta da ubanta sun mutu kisna ta bude baki kenan zata sake wanketa muradi yayi saurin daga mata hannu a tsawace "karki sake cewa komai anan ya isa .
ya kalli inda nawal dake tsaye tana kuka "ke kuma idan daukarsa zaki yi daukesa ki wuce tsabar mubafurci irin na nawal nan take ta hau goge hawayenta tasa hannu ta dauki mahbub dake kwance ta fice muradi ya k'araso ya riko kisna ya manneta da qirjinsa yana tafiya daita a hankali ya nufi d'akinta daita yana shiga ya zagaye hannuwansa a cikinta yana magana kasa kasa kmr me koyon mgn "haba kisna ban sanki da haniya ba banason kina yiwa nawal iyaka da yaran nan ita din abar tausayi ce ki dinga mata uzuri kinji , koda nawal ta girmeki amman kece babbar acikin gidan nan kin fita experience din rayuwa saboda kin haihu ita kuwa duk girmanta bazata qarar da wani abu daya danganci hakan ba , amanar gidana tana hannunki ko ina nan ko bana nan duk abinda nawal tayi miki ki sanar dani kafin ki dauki mataki , shiru tayi kawai tana sauraronsa ya numfasa tare da juyo daita suka fuskanci juna ya tsira mata ido yana kallonta cikin tsananin qaunarta ta bala'in hade rai kamar an aiko mata da sakon mutuwa har tasa gabansa faduwa sai dai haka yayi karfin halin cewa"ko babu komai hayaniyar nan zatayi affecting din mamana tana ina banganta ba ?da kyar ta bude baki" tana dakinsu ki qara hakuri akan wanda kike yi .
Ya zauna tare daita "idan kin gama abinda kike ki shiga dakina akwai wasu kayana da'aka kawo daga gurin wanki ki kai min part din nawal tafiya ta kamamu gobe zuwa spain nida samir gobe 12:dot jirginmu zai tashi yace ta kai wa nawal ne dan part dinta yake itace ya dace ta haɗa masa kayansa har ya gama maganarsa bata ce masa qala ba ganin taki cewa komai yasa shi juyawa ya fita zuwa dakin su mother tana kwance ta takure jikinta guri daya ta toshe kunnenta da hannuwanta tsura mata ido yayi na wasu mintuna yana matukar qaunar diyarsa zai iya karar da rayuwarsa akanta gyara mata kwanciya yayi sannan ya sauko ya shiga gurin nawal ta kwantar da mahbub tana wani irin kuka idanunta yayi ja saboda zagin da kisna tayi mata Ahmed yana zaune yana goge mata hawaye ta kamosa ta rungumesa ajikinta muradi ya k'araso cike da sanyi jiki ya zare Ahmed ajikinta "ahmed jeka falo kayi kallo kaji yaron ya fita daga dakin muradi ya zauna a gabanta "haba nawal menene abun kuka nasan kina kuka ne dan baki haihu ba kiyi hakuri kema inshaallahu naki yaran na zuwa nan kusa , zaki haifa min mace zaki haifa min namiji komai lokaci ne amman ki daina fadawa kisna duk maganar datazo bakinki saboda kinsan bazata kyakeki ba tana da hakuri da kawaici amman bata daukar irin wadannan abubuwan ya k'arasa maganar yana rungumeta har magarib ta shigo suna tare yana rarrashinta da fada mata kalamai masu kwantar da zuciya suna zaune a falon suka ji knowcking "waye? inji cewar nawal kisna tayi shiru, har nawal ta mike tsaye muradi yace ta koma ta zauna ya mike ya bude kofa kisna ya gani tsaye cikin riga da wando ba irin wacce ya gani d'azu ajikinta ba , sai kamshi take tana sheki ,nazo daukar yaro na ne tunda ba'a ga ya dace akawo min shi ba."
Muradi yayi shiru yana kallonta kafin daga bisani ya juya ya daukosa ya saba a kafad'ansa nawal na ganin haka ta fahimci kisna ce ta ta'be baki a ranta tana cewa" aikin banza kawai ki dai bari na fara haihuwa zaki sha mamaki ,muradi ya fita ya mika mata mahbub har ta juya ya janyota ya rungumeta tare da yaron ,"dan Allah ki ɗan saki ranki mana kin fa san idan akwai abinda na tsana bai wuce fushinki ba Please baby love ki saki ranki ,naji ta fada a takaice tana zare jikinta ya manna mata wani hot kiss guda biyu sannan ya saketa ta juya yabi bayanta da kallo har sai daya daina ganinta ."
Washegari karfe tara ya fito daga part din nawal cikin shirin tafiya ya shiga na kisna lokacin tuni yaranta sun wuce school ta gyara ko'ina sai kamshi airfresner yake tana sanye cikin dinkin atama riga da siket puppy da ratsin fari jikinta sai wani sihirtaccen kamshi yake fitarwa tana ganinsa ta mike tsaye ta rungumesa tana sakar masa Kukan shagwa'ba zuciyarta tayi matukar rauni dan bata so abinda zai nisanta ta dashi , ta kasa sabawa da tafiye tafiye da yake duk sanda zai yi sai taji wani iri a zuciyarta kissing dinta ya shiga yi babu kaukautawa ,baby I will miss you ,"I will miss you too ta fada ranta a jagule ji tayi kamar ya fasa tafiyar , dan Allah ki daina kukan nan idan kina zubar da hawayenki zan tafi zuciyata cike da damuwa wayarsa ce ta dauki kara ya ciro ya duba sunan Samir ya gani ya mayar da wayar ya ɗauketa cak bedroom dinta ya nufa bisa gado ya shimfideta sannan shima ya hau gadon ya daura kanshi akan cinyarta yana shafa yatsun hannunta" zanyi kewarki baby love irin sosai din ko zaki shirya mu tafi tare bana son nayi nisa dake ina tsananin qaunarki burina mu kasance tare a kowani hali ?ta sauke numfashi tana daura hannunta daya a sumar kanshi yayinda d'ayan hannunta ke gadon bayansa sai dai har lokacin bata daina masa kukan shagwa'ba wanda yake sake rirkita masa lissafi tun samir na kiransa har ya gaji ya daina dan yasan karsheta yana can gaban kisna yana faman aikin rarrashinta tunda ga nawal nan har ta fito masa da jakarsa."
ya cigaba da fada mata kalamai masu sanyi har sai daya ga babu hawaye ko daya a cikin idanunta sai dai hakan bai shi tashi daga kan cinyarta ba , daga qarshe ya tsurawa kwayar idanunta nashi idon cikin tsanani tashin hankali ''anya baby love ba haqura zanyi da tafiyar nan ba Samir ya tafi shi kadai ? ''da sauri ta girgiza kai tana cusa hannunta cikin sumar kanshi '' gara ka tafi tunda nasan abu ne me mahimmanci nayi maka alkwarin idan zaka sake tafiya zan bika ,Ina bazan yarda da wannan wayon ba koda yaushe haka kike fada min 'dariya ya bata "shinkenan ka tafi da nawal ,okay haka ma zaki ce shinkenan bari naje nace ta haɗa kayanta kawai mu tafi tare ? ai tana jin abinda yace ta sake sakar masa kuka yayi saurin tashi yana hade hannayensu''is Okay ! ya fada yana kallon fuskarta yadda tasha kuka sai yayi sha'awar tsokanarata
'"ga tsoro ga ban tsoro ta baba me gadi kina mutuwar son muradi kina wasa dashi ta kaiwa qirjinsa dukan wasa tana cewa" kai ko Allah sai na fada wa dady ,tunda dai ba granny zaki fadawa ba ai da sauki dan itace zata hadiye zuciya ta mutu tsabar kishi ta matsoshi sosai kamar zata shige jikinsa , Allah zanyi kewarka ,nasani baby love rabuwa da masoyi akwai ciwo Amman karki damu 2 0 7 muna tare akan waya idan kuma na kira ban sameki ba shinkenan na hakura tayita kiran nawal muna shan soyayyarmu ''yayi maganar cikin salo tsokana ,tashi tayi ta fara bubbuga kafafuwanta cikin shagwaba, baya ya dan ja kana ya kama baki ''eyeeee naga fa alamar matar nan kina kishin wannan abar over fa ya fada still cikin tsokanarta yana shafa gaban wandonsa ,anya da gaske bazan fasa tafiyar nan na zauna mu cgaba soyewa ba ?haka yayita tsokanarta sam ya manta wani samir na jiransa ta fada jikinsa cike da kukan shagwa'ba ,shima bai tsaya wata wata ba ya rungumeta tsam yana jin duminta da qamshin azababben turarenta mai tsayawa arai ".
"ki daina wannan kukan baby love Allah yana bala'in kashe min sana'ar jiki har yanayina ya fara canzawa tana jin haka ta zame jikinta ta fara share hawayenta yana tayata sai da yaga fuskar ta tayi fes sanann ya fara kising every part of her da kyar ta kwaci kanta ya kamo hannunta ya dauki hijab dinta ya saka mata sannan suka fito ta shiga kitchen ta dauki karami jaka wanda fararen roba ne set uku aciki dauke da cinci da dambun naman rago ta fito suka sauko tana kan kafad'ansa hannunta rike da karamar jaka suka jero har harabar gidan inda Samir ya cika yayi bammmmm kamar zai fashe ,bai damu da securities dinshi ko nawal da Samir dake tsaye ba ya sake kwakwame kisna babu kunya kisna ta motso shi a haka har suka isa jikin motar da zasu tafi airport acikinta batare da ya kalli Samir dake tsaye shida nawal ba yana zabga masa harara , sake janyota yayi ya mata kiss a kumatu da goshinta nan fa zuciyar nawal ta shiga rawa kamar ta buga tsabar bakinciki ruhinta yayi baki idanunta suka ciko da hahaye a hankali muradi ya saki kisna ya karaso inda nawal take ya rungumeta ,yasa ɗan yatsansa yana ɗauke mata hawayen da ya fara silalo mata''no baby karki min hasarar hawayenki ya janyota gefe guda samir ya sake zabga masa wata ƙatuwar harara ya sakar masa murmushin gefen baki ,kisna ta hadiye wani abu taji ya tsaya mata arai ta fuskanci samir tare da juya masu baya dan bata son ganin irin sallamar da zai yi da nawal .."
"My baby nawal karki karya min kwarin gwiwaa ,ki bar kukan nan haka, bari na gaya miki abinda zaisa ki yarda dani 'bakinsa ya sanya a kunnenta cikin kashe murya da iya salon magana tare da sace zuciya yace''ina sonki har yanzu kina cikin zuciyata burina na karshe yanzu bai wuce ki haifa min me sunan mahaifiyata ba.."wayyo Allah dadi kamar ya kashe nawal taji wani irin farin ciki ya mamaye ruhinta tasan muddin Allah ya amshi addu'ar sa ta haifi uwar masu gida soyayarsa gareta zata ninku ita dai burinta ya sota fiyye da kowa da komai, ta daura kanta kan kafadarsa tana sakar masa dariyar farinciki ''na gode na gode!! my norr wallahi ruhina yayi haske Allah ya amshi addu'arka itama tayi masa mgn cikin nata salon ,"ki sha kuruminki Allah ma ya amsa lokacin kawai muke jira ki hafawa hajiyarmu jikoki masu tsananin kama dani ''inshaallahu ta karasa maganar yana kissing dinta ''kaga malam ,idan ka fasa tafiyar nan ne ka gaya min na kama gabana , banza yayi masa yana sake bata hot kiss wanda yasa Samir dauke kansa kana ya kama hannunta yana fadin''ki kular min da kanki, zanyi kewarki sosai ''kai take daga masa tana murmushin farinciki har ya juya ya soma tafiya ya kawo daidai inda kisna ke tsaye ta kamo hannunshi ta sumbata , ita dai kisna na tsaye bata ce komai ba sannan bata sake yunkurin isa garesa ba dan ita bata cikin matan nan masu gasa da kishiya, dan ciwo taji ciwo a ranta tunda tana son mijinta kuma tana kishinsa ya kai bakinsa daidsi kunnen kisna " zanyi kewarki bayan tafiyata ki kular min da gidana amanar komai tana hannunki "
har ya shiga mota shi da samir motocin suka ka yi gaba suna kokarin ficewa daga gidan me gadi na kokarin rufe get din gidan amnan tana tsaye rungume da hannunta duk a qirji ta kai minti goma tsaye sannan ta juya domin komawa ciki karaf idanunta suka sauka akan nawal tana sakar mata murmushi sam hakan bai dameta ba kuma bata jin zai zama hujja da zatayi fushi da miji ba dan wani lokaci ka dauki lamuran makirci da kishiya take ka saka a ranka sai ta haɗaka da miji kuzo kuna samun matsala tana gefe tana muku dariya.
part dinta ta shiga a daidai lokacin da mahbub ya tashi a bacci ta d'aukesa ta zauna tana zuge zip din rigarta ta fara bashi nono tafiya ce da muradi yayi zuciyarsa cike da tunanin matansa most especially kisna tana makale a zuciyarsa daram yana sauka ita ya fara nema cike da sakin fuska da fara'a suka gaisa tayi masa ya gajiya .."Cikin kwanakin masoya guda biyu sun yi maseefar kewar juna barin ma muradi kewar kisnarsa kawai yake shiyasa duk bayan minti talatin yake kiranta ya baibayeta da daddar muryarsa da kalamansa masu sake dilmiyar daita cikin tafkin qaunarsa, da misalin karfe goma na dare byn a lokacin tuni yaranta sun ci abinci sunyi wanka sun kwanta a kiyasinta ma sun dade da bacci kiransa ya shigo ta d'auka muryarta a shagwabe "hello my world best ykk? ganin kwance baby love tunaninki ya sakani gaba ya hana zuciyata sukuni duk inda na motsa kece ke kawo min farmaki ,murmushi tayi "nima haka nake ji koma nace fiyye da naka ,ya zaro ido yana murmushi kmr yana gabanta "to bari na tattaro na dawo dan gaskiya na kasa jurewa kewarki na son kasheni ,"kayi hakuri ka kammala abinda ya kai ka duk da nima ina jin irin abinda kake ji ,na yarda amman ki ɗan min wani abu na samu natsuwa mana yayi magana muryarsa can kasa sarai ta gama fahimtarsa a hannu yake yaso kwarai ace tare daita yayi tafiyar amman yasan hakan zai da taba ruhin nawal shi kuma a gaskiya bazai zo daita ya bar kisnarsa ba ,ko bama haka ba inda suka je cakude suke da zaratan maza kuma babu wanda yayi ganganci zuwa da matarsa sai da suka dauki lokaci me tsawo suna faranta junansu har ya samu natsuwar da yake bukata sannan sukayi sallama kwansnsu goma suka dawo cikin koshin lafiya da nasarori masu yawa a part kisna ya kisna ya sauka nan fa nawal tace bata san da wannan zance ba part dinta zai sauka abu kmr wasa sai da aka kira aunty ummi tun kafin tazo kisna tace ya koma gurinta shi kuma yayi rantsuwa bazai koma ba dan shi ba jahili bane yasan abinda yake koda aunty ummi tazo mgb daya tayi babu son zugiya ,"nawal kiyi hakuri kinyi karatu daidai gwargwadon tunda dakin ya baro lokacin da tafiya ta kamashi dan haka yanzu a dakin kisna yake haka dai ta hakura ba dan ranta yaso ba ranar an yi kwana soyewa tsakanin kisna da muradinta har albarka ta dinga sakawa mahaifiyarta saboda dadi yayi dadi dan bakaramin shirya kanta tayi ba kafin ya dawo ."
*****
Suna zaune ya shigo yana sanye cikin laulausan yadin filtex ruwan madara da hula baki mai asalin tsada da silifas baki dan waje wanda itace ta dinka masa sannan ta takurasa ya saka dole a ranar wacce