Showing 279001 words to 282000 words out of 495987 words
Chapter 94 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
A matukar gigice kisna take kallonsa cikin tsananin tsoro da firgici sam batayi tsamanin zai daga nikaf dinta ba ganin asirinta ya tono no going anywhere yasa ta rushe da matsanancin kuka ɗan batasan menene zai faru daita ba idan Samir ko madu suka ji sannan batasan abinda zatace dan kare kanta ba agurinsu dan ta muradi mai sauki ne zai iya kyaleta taci bulus batare daya taba lafiyar jikinta ba gabad'aya jikinta ya kama rawa kamar mazari a zahiri yake iya hango tashin hankalin data shiga bata ce masa komai ba illa ta durkusa kasa bisa gwiwowinta dan tasan na lahira sai ya fita jin dadi a gurinsu samir idan suka ji abinda tayi kokarin yi sai sunci ubanta , hakuri take son bashi amman ta kasa magana ."
kugunsa ya rike da hannu daya yana cigaba da mata kallon mamaki yayinda tawagar tafiyarta kowacce tashiga rawar jiki da neman hanyar gudu yayi saurin kallonsu yana zare musu idanunsa yace "duk ku dawo nan ke kuma zinnira har dake a saka hannu gurin fitar kisna gida bayan kinsan komai ? "uhm ammm wallahi .... " ya daka mata wata razannaniyar tsawar data hargitsa ya'yan cikinta "yi min shiru stupid bana son jin komai daga bakinki na dauka kina da hankali a she kema ol the same ne daita nan zinnira ta fara kuka wiwi tamkar ance uwarta da ubanta sun mutu "ke kuma ina kike shirin zuwa ?ya tambayeta yana tsareta da idanunshi masu matukar firgitarwa a rikice tace "gidansu zinnira zamu ko zinnira ki faɗa masa gidanku zani wani gigitaccen mari ya kifa mata sai da jinta da ganinta ya tsaya na wani lokaci "you are very stupid ni zaki yiwa karya you better tell me where are you going to kafin na tatttakaki ?"Cikin Muryar kuka tace " gurin musa zani ..."
"What ? Ya furta da karfi qirjinsa na luguden bugawa take wata irin zufa ta shiga tsatsafo masa a gabad'aya ilahirin jikinsa kamar an watsa masa ruwa ya kamo lip's dinsa na kasa yana cizawa da karfi ko zai rage jin bugawar da zuciyarsa ke yi fuskarta dake tsiyayar ruwan hawaye ya cigaba da kallo "wannan wace irin maseefa ce ?"yaushe zukatansu zai hutu da matsalolin kisna ?shiru yayi na tsawon mintina yana tunani da kallon fuskarta yayinda kawayenta kowacce cikinta ya duri ruwa jira suke ya gama daita ya dawo kansu cikin haka sai ga Samir ya shigo da sauri dan shirin zuwa buga wasa turus yayi yana kallon muradi daya tasa kisna gaba da ido gefe guda gasu zinnira sun hada uwar gumi suna juya hannu kallo daya yayi masa ya fahimci yana cikin tsananin ɓacin rai kuma yasan ko yayi masa magana a lokacin da wuya ya bashi amsa dan haka ya sa kai ya shige cikin gida yadda muradi ya dauke kisna da mari haka ya juya ya dauke sauran yace duk su cire nikaf din fuskarsu
tsab ya gane sauran biyu din ummana da sala ne daman kuma ya lura suna da dan rawan kai har gara zinnira.
ya tasa keyarsu zuwa cikin gidan suna kuka suna rokonsa banda kisna da haushi ya taru yayi mata yawa har saman dakinsu ya kai su simi simi suka shiga yayinda kisna taki shiga aiko ya cicibeta ya shiga dakin daita ya direta "maza ki kama kunnenki kafin nayi miki ruwan kyankyasai take tayi saurin kamawa suma sauran sukayi tun kafin ya waigo ya tsare kisna da ido "kinsan Allah ko da wasa naji kin sake ambar sunan yaron nan zan mugun baki mamaki kinsan tunda kike wulakancinki a cikin gidan nan ban taba sa hannuna ajikinki ba tsakanina dake nasiha ne wallahi karki bari na nuna miki tru colour dina shekarunki shabiyar a duniya amman har yanzu kina hauka yanzu haka shi yana can ya manta dake a rayuwarsa me kike son maida rayuwarki yau shekara day day har biyar ana kan abu daya wannan wani irin naci ne ? fada sosai yayi mata kisna banda kukan bakinciki babu abinda take tana jan kunne ,zama yayi ya fasa zuwa inda zata shi dan tuni ya cire takalmin ƙafarsa da rigar jikinsa ya saura daga shi sai singlet da gajeren wando ya ja karamin table din glass din dake tsakiyar dakin ya daura kkafafunsa ya fuskanci su zinnira "ku kuma kananun yan iska har kun san kuyi wayon fitar daita kou ? a tare suka girgiza masa kai hawaye shabe shabe a fuskarsu suna bashi hakuri "you are very stupid da hakuri da kuke bayarwa maza ku canza zuwa frog jump marasa kamun kai kawai babu mutsu suka canza har kisna "dan Allah kayi hakuri "inji cewar zinnira "shiiiiiii kiyi abinda nace samir ya gama shirinsa ya fito "halan wannan uwar yan rigimar tayi halin nata yayi shiru yaki yin magana "ya zamu fita kuwa naga ka cire kaya ? "wallahi ina ganin bazani ko'ina ba Samir yace "shinkenan mu bari gobe kawai bari naje na fadawa jahid wai me kisna tayi ne ? "ka fa daina goya mata baya sam bata da mutunci duk yadda samir yaso jin abinda tayi kin fada yayi, muradi ya bala'in wahalar dasu jikinsu sai rawa yake ko'ina ciwo yake musu Samir kuwa sai kara zuga yake dan yasan duk abinda yasa muradi punish din kisna da kawayena abu ne mai girma suka masa dan haka ya dauki din madu ya shiga zabga masu ta ko'ina suna ihu suna susa duk inda belt ya sauka sannan ya fita.
kai tsaye dakin mumy ya nufa yana shiga yaga abun mamaki dan tarar da mumy kwance rashe rashe akan gado ga zee kusa daita ko wadataccen numfashi bata saukewa karasawa yayi cikin sauri ya kai hannu gurin hancinta yaji babu numfashi haka ma zee shi abinda ya daga masa hankali bai taba ganin mumy tayi bacci bayan sallahr la'asar ba da sauri ya juya ya bar daki jikinsa na rawa Yayi hanyar sama "tun daga kan step yake ihun kiran sunan muradi cikin tsananin tashin hankali " kazo na shiga dakin mumy na gansu gaba-daya a kwance kamar basa motsi wata irin zabura muradi yayi ya mike tsaye shi kuwa Samir tuni ya juya ya bar dakin da sauri , kulle kofar muradi yayi ya bar gurin da sauri cikin kankanin lokaci aka kira ya badamasi nan ya tabbatar da suna raye anyi musu amfani da maganin bacci mai karfi ne nan da nan yace a hada musu coffe har asabe dake zaune a kitchen tana bacci a basu cikin knkanin lokaci aka hada aka basu sai dai basu dawo haiyacinsu ba muradi ya juya ya nufi dakinsu domin jikinsa ya bashi aikinsu kisna ne yarinya kamar aljanna ya tsura mata ido yana hadiye wani kulli daya tsaya masa a makoshi kisna ta ɗan tsaya tare da bude idanunta da yayi mata nauyi taga shi ne wani sabon marayan kuka ta fashe dashi tana shesheka dan ya tausaya musu kawayenta na tayata murya a shake yace "duk ku biyoni suka mike da kyar suna rike kafafu har dakin mumy nan take gabansu ya buga ganin an cika a dakin har dady .
"kune kuka bawa su mumy maganin bacci ko gabad'aya suka yi tsuru tsuru tare da nuna kisna dake tsaye "wallahi itace itace tasa mata mu babu ruwanmu mu dai tace mana mu taimaka mata ita kuma zinnira wai sonka take shine kisna tace idan ta taimaka mata taje gurin musa itama zata taimaka mata ta hadaku aure inji cewar sala "ya subhallah muradi ya furta yana kallonsu daya baya daya, takaicinsu bai bari yabi ta kan maganarsu ba yace "ke ....a ina kika samu maganin bacci gashi kin illata mumy dasu asabe ? yayiwa kisna tambaya yana kallonta "cikin Muryar kuka tace "wannan makira ce ta kawo min" tayi magana tana nuna ummana da yatsa take jikin ummana ya dauki rawa ta fashe da kuka tace "ai kece kika ce na .."tsaya tsaya ya dakatar dai ta ta hanyar buga mata tsawa "me yasa da tace ki kawo mata baki fadawa daya daga cikinmu ba kika biye mata sai na police sun kamaku yau ke Kuma kinga rayuwarki ko "kina cewa wata makira bayan gaki ƙatuwar makira dan har yanzu mumy bata motsa ba a sanadiyyarki idan wani abu ya sameta sai kinga yadda zamuyi dake da kuka kisna takarasa inda mumy take kwance tana kuka "dan Allah mumy ki tashi karki mutu wallahi bazan sake ba ina sonki bana son ki mutu ki barni Samir ya cakumo wuyanta zai buga kanta da bango muradi yayi hanzarin hanashi dan yasan yana buga kanta ta tashi aiki "barta kawai Samir dukanta bazai sa mu huce bakincikinta ba da kyar muradi ya amsheta a hannun Samir dake tsuma sannan ya kora su zinnira zuwa gidajensu da kyar aka samu asabe da zee sun farfado a ranar amman mumy kam sai da'aka danganata da asibiti da kyar aka samu ta dawo daidai lokacin data tashi taji abinda kisna tayi ta rushe da kuka "wayyo Allah kisna zaki kasheni wannan wacce irin yarinya ce .."?" wallahi dana san irin kisna zan haifa da na cire cikinta a lokacin dana samu kuka take sosai tana zuba surutai yaranta suka zagayeta suna share mata hawaye , "wallahi mumy ko nan gaba kisna ta baki abu karki ci dan zata iya kasheki inji cewar madu .."
Tun daga ranar dady bai sake samun sukunin ko walwala ba haka itama mumy yayinda dady ke mamakin nacin irin na kisna yasa aka kira masa ita tana zaune a gabansa idanunta na kallon tayis din dakin" sakina ya kira complete name dinta ta d'ago kanta da kyar tana kallonsa "kina bukatar rayukanmu ko ? ta girgiza alamun a'a ",to me yasa kike son daga mana hankali da dagula mana lissafi ?"kin fi son yaron nan akan rayuwa damu ko "?ta sake girgiza kai " karki ce a'a kin fi sonshi mana tunda kin fi jin magabarsa akan tamu sosai ya dinga mata fada da nasiha daga karshe ya sallameta .."
Da fari dady kanwarsa Hajiya ummah ya soma tunanin ya samu da maganar kisna bayan kwana biyu da faruwar lamarin ya shirya direbansa ya kai shi gidan inda ya isketa tare da mijinta kasancewar weekend ce suka gaisa a mutunce Alhaji tijjani muhamud adam ya mike dan basu guri ya koma can nesa kadan dasu ya zauna yana duba magazine hajiya ummah tasa aka kawo dady ruwa da lemun chivita mai sanyi aka ajiye agabansa dady ya numfasa sannan ya fara magana a tsanake "ummah nazo ne akan ifitila'in daya samemu gabad'aya" jiki a sanyaye tace" Allah ya kyauta ya shirya mana kisna koni abun ya dameni addu'a dai zamu cigaba da yi "haka ne muna kanyi yinta na dade ina tunani yadda zan shawo kan matsalar dake faruwa da kisna sai gashi cikin sauki aka fada min cewar dana nazir yana cikin wadan da suka nuna suna son kisna abun yayi min dadi kwarai da gaske yanzu dai atakaice nazo ne na sheida miki idan da gaske yake ya fadawa mahaifinsa azo neman aurenta bana bukatar komai nashi sai sadaki kai sadakin ma zan biya cikin tsananin firgita da tsinkewar zuciya Alhaji tijjani muhamud adam ya juyo ya fuskanci inda suke zaune dan duk yana jin maganarsu cikin tsuma da karkarwa ya mike tsaye yana nade jaridar hannunsa ya soma takowa a hankali tare da murtike fuska yace "kayi hakuri Alhaji realwan dana nazir bazai auri wannan yarinyar ba sai lokacin hankalin Hajiya ummah ya kai garesa tace "saboda me zaka fadi wannan kalmar kuma a gaban dan'uwana kana son 'bata mana zumunci ne ?" bayan kasan kusan auren da'ake yi kenan a cikin family dinmu gashi da alamun naxir din yana sonta dan ya fada min da bakinsa kuma naji dadin haka jira nake kisna ta dan kara ayi maganar aure shine zaka ....."
"nazir danki ne ko nawa ? Ya katseta ta hanyar fadan haka tayi shiru tana dubansa kamar yadda dady yake kallonsa cike da mamakinsa tunda shi din ma kusan danuwa ne kakaninsu uwa daya uba daya ne jiki a sanyaye tace "dan ka ne "
"Alhamdullahi da kika ce dana ne to na dade da samar masa matar da zai aura nima lokaci kawai nake jira
"da ina da wani dan sai ya aureta amman kiga shi kadai gareni Allah yayi mata zabi mafi alkhairi."
juya maganarsa take a zuciyarta taji wani abu ya tsaya mata rai ta tsaya sosai tayi masa duban tsanake sannan tace "me yasa tun farko baka sheida min ba sai yanzu da kaga yaya yazo da bukatarsa sannan zakace ga zance ga magana ?"babu wani ga zance ga magana nayi haka ne saboda dana ne idan lokacin yayi zaki kisani dole ranta yayi mugun ɓaci ta soma magana cikin daga murya da zafin zuciya nan suka shiga fadawa juna magana ganin rayuka zai ɓaci a banza kuma ba'a samu biyan bukata ba yasa dady ya sauke naunauyen ajiyar zuciya yace "Alhaji tijjani ka zauna duk abun bai kai na tashin hankali ba d'a dai kamar yadda ka fada danka ne kuma inshallah baza'a sake maganar akanshi ba kuskure na ne sai dai na dauka a halin da nake ciki kana cikin mutanen da zasu rufa min asiri su tallafawa rayuwata amman babu komai Allah zai nuna min yadda zanyi "dady na gama fadar haka ya mike tsaye cikin sanyi jiki yayiwa hajiya ummah sallama ya wuce Alhaji tijjani ya ta'be baki ya zauna bisa kujera ya cigaba da magana "ina wallahi bazata sabu ba"
"Gaskiya ban ji dadin abinda kayi ba ai ba kai kadai ka haife nazir ba "muddin dai kinsan dana ne nazir ba shegensa kikayi ba na gama magana babu batun aure tsakaninsa da wannan yarinya mara jin magana , yarinya da ko aurar daita akayi sai ta gudu taje gurin saurayin da take so ke yanzu kinga dacewar su dan Allah ? "Duk mutumin daya san ciwon kansa bazai soma amsar auren wannan yarinyar ba shi kuma zai zo ya sameni sai naci mutuncinsa idan na sake jin labarin yaje gidan da sunan zance zai ga abinda zan masa Allah ya nuna masa yadda zai yi ya aurar daita amman muddin ina raye nazir bazai aureta ba "amman ka cika butulu wallahi ba yaya ya kamata kayiwa haka mutumin da ..."dakata gori zaki min ko me ?"shi din ma ai sai ayi maka fada sosai sukayi sannan ya fice daga gidan ,a kasalance ta koma ɗakinta ta kwanta dan ta huta ko ta samu zuciyarta da gangar jikinta su samu natsuwa ..
Daga gidan hajiya ummah gidan abubakar tafida shima dai the same thing ya iske abinda ya faru a gidan Alhaji tijjani muhamud adam shi ya faru jiki a sanyaye dady ya dawo gida tare da matsananci ciwon kai yaji kamar yayi kuka da kyar ya fito daga cikin motarsa yana tafiya babu laka, da sauri muradi daya shigo domin ganin shigowar motarsa ya biyo bayansa har ya kai daki "lafiya dady? ya fada sanda yake fuskarshi sai yaga kamar Idanunshi yayi ja tamkar garwashin wuta "babu komai dana kaina ne yayi dum muradi bai sake yin magana ba amman ya mika masa dukkan attension dinsa yana bukatar ƙarin bayani dan zuciyarsa bata yarda iya ciwon kai ke damunsa ba da kyar ya bude bakinsa ganin dady bashi da niyyar cewa dashi komai "dady nasan ni din dan riko ne a gurinka sai dai ban taba jinka amatsayin marikina ba ina jinka ne tamkar uban daya kawoni duniya dady baka taba boye min komai ba duk damuwarka na sani tun a can baya adalilin soyayya da yarda tasa damuwarka ta zama tawa saboda ka cancata kai din nagartaccen mutun ne ka cancata a shiga cikin lamarin damuwarka dan Allah kayi hakuri dady ka fada min damuwarka " ya karasa maganar cike da tausayawa .."
Dady ya nunfasa sannan ya fara magana cikin tsananin tashin hankali "damuwata bai wuce akan kisna ba nan take dady ya warware masa komai labarin daya tsuma zuciyar muradi saboda tsananin tausayin dady ya sake kamashi har kuka muradi yayi yana kallonsa cike da tausayawa tausayinsa ya mamaye zuciyarsa yaji tozarcin da'aka masa yayi yawa dady bai cancanci haka daga yan'uwa da abokan arziki ba ya cancanci su ji tausayinsa su kaunaci bukatarsa hannusa ya kamo ya zaunar dashi akan kujera yaje ya bude fridge ya dauko masa lemu mai sanyi ya tsiyaya masa a cup ya bashi "ka sha dady ya amsa ya rike kawai yana nazarin rayuwa batare daya sha ba " abinda bazai taba yiwa Abubakar tafida da tijjani ba a rayuwarsa shi suka masa sun nuna masa iyakarsa sannan sun fahimtar dashi kowa kansa ya sani Idanunshi suka sake rikedewa suka yi jazur muradi ya kwantar da kai ya fara magana cikin sanyi lafazi "dady kasanyawa zuciyarka hakuri duk abinda ya faru da bawa a rayuwarsa da sanin ubangijinsa tun daga haihuwa har zuwa mutuwarsa a tsare yake a rubuce a allon lauhul mahfuz bawa bai isa ya tsarawa kansa rayuwa ba iyakacinsa bin umarni duk inda aka kai shi da rungume komai aka jefa masa da hannu biyu biyu hakika Ubangiji na jaraba bayinsa mafiya siyowa a gurinsa ta fannoni da dama kuma yana murna da masu godiya a duk halin daya barsu da rungumar kowacce qaddara, Allah yana son bayinsa masu tawakalli da hakuri domin har yana fada acikin Alqur'ani mai tsarki cewa "innallaha ma'assabiri wato lallai yana tare da masu hakuri dan haka ka kara hakuri Allah na tare da kai ka manta damuwar da suka kunsa maka dan zai iya cutar da kai baka isa ka daukewa kisna rayuwar da take ba sai Allah ka cigaba da yi mata addu'a