Showing 42001 words to 45000 words out of 495987 words

Chapter 15 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

baya yarda da kowa sai yan gidansu ...
Nawal na ganinsu ta sake fad'ad'a fuskarta da murmushi ta maida hankalinta sosai a kan aunty zee tace "aunty zee sannuku da zuwa kun zo lafiya ya kuka baro mutanen gida ?
"Alhamdulillah aunty zee ta amsa mata atakaice ,nawal ta ɗan saci kallon kisna wacce gabad'aya yanayinta ya sauya sam bazaka ce ta taɓa dariya ba ,yanayin fuskarta yasa gaban nawal ya dinga faduwa amman ta sanyawa jikinta jarumta tace maman twins ina wuni ?
Sai da kisna ta gama shan kamshinta dan har nawal da Aliyu sun fidda rai zata amsa suka ji sautin zazzakar muryarta "lafiya " atakaice .
shiru dukkaninsu sukayi ,daga kisna har nawal babu wacce numfashinta bai fita da matsanancin sauri ,wani irin kishin Aliyu ne ya mamaye zuciyar kisna ,duk da a yanzu tafi kowa maraba da shigowar nawal gidanta a matsayin kishiya ta huta da wasu daga cikin iskanci Aliyu amman wani lokaci sai taji kamar ta kashe nawal din akan tsananin kishin mijinta dan Allah ne kaɗai yasan irin ciwo da rad'ad'in da take ji a zuciyarta a duk sanda ta tuna da aurensu , sai dai tana kokarin danne kishinta saboda bata son zubarwa Kanta da mutunci a idanun nawal din da Kuma idanun duniya dan ta lura da tsoronta dake tattare da zuciyar nawal din kuma tasan hakan bai rasa nasaba da kashedin data mata a wancan ranar ba , ita kuwa nawal gbdy jinta tayi duk a takure a gurin , mikewa tayi cikin sanyi jiki tayiwa mumy sallama ta wuce zuciyarta cike da matsanancin tsoron kisna , Aliyu ya so bita sai dai kunyar mumy yasa ya kasa Binta suka ci-gaba da hira da mumy da zumar anjima zashi gurinta ,yayinda kisna da aunty zee suka koma kitchen ..

"Kinji wani sabon salo kiran sallah da husir wai aunty zee a bakin guzuma abun ma babu dadin ji aunty zee ta karashe maganar tana kwashewa da dariya "ai naga yadda kika shaka dan gaisuwar ma da kyar kika amsa kisna ta fada tana dariyar mugunta "ba dole na bata rai ba mata ta girmeni nesa ba kusa ba amman ta bige da ce min wani aunty kinji kuwa yadda raina ya ɓaci ,dan wallahi ko shi ya Aliyu a girme zata iya girmansa idan kuwa bata girmesa ba zasuyi daidai daita amman tsabar iyayi wai aunty zee ta fadi tana jan tsaki "ke kuwa meye abun jin haushi bayan gindin zama take nema sgurinki "
"Ai kuwa idan dai agurina zata samu bazata taba samu ba sai dai gaisuwar fatan baki ,kisna tace "to ai shima aunty data kiraki dashi ba wani abu bane fa normal ne yanzu da wanda ka girma da wanda ya girmeka duk zaku iya kiran junanku da aunty Kawai dai ke baki son girma ne shiyasa kikaji haushi ",gaskiya bana son gara ma idan nasan na girmeka ina iya hakurin wannan amnan ita datayi kanwa ta biyu ko uku dani ta wani ce min aunty ..." Dariya suka yi suka ci-gaba hirarsu suna aiki batare da sun bi ta kan laidar da Samir ya kawo musu ba .."

******"

Tunda su mommy suka zo wasu abubuwa suka ragu kasancewar basa zama a gidan kullum sai sun fita yawo har da kukan murna kisna tayi saboda tun zuwanta kasar sau daya ta fita zuwa kasuwa sai gashi yanzu kullum sai sun fita , sai dai duk daren duniya sai Aliyu yasan yadda yayi ya bata mata rai har ya kai ta ga yin kuka , satinsu mommy uku a kasar suka fara shirin komawa Nigeria ita da yara ban da aunty zee zata zauna tare da mijinta duk abinda ya dace mommy tayi tsaraba dashi Aliyu ya siya mata Ana jibi jirginsu zai daga tace zata shiga kasuwa ta duba ta gani ko akwai abinda zata bukata dan haka washegari ta shirya da misalin karfe biyu na rana direban Aliyu ya bar gidan ita."

Aliyu da samir da nasir na zaune a haraban gidan akan fararen kujeru suna tautaunawa akan business da buga wasa dan wani sati zasu wuce spain domin buga wasa yayinda safiyya da aunty zee da kisna suke dakin mommy zaune akan gado suna kimtsa mata kayanta aryan da areef suna wasa a kasan tayis da kayan wasa, can aryan ya fita daga dakin ya tsaya abakin kofa kasancewar safiyya data shigo dakin bata rufe ba, mikowa areef hannu yayi alamun suje parlou'n kasa babu mutsu areef ya mika masa hannu suka fice daga dakin da kayan wasansu .

Suna saka da hira kisna taji gabanta yayi wan irin mumnunar faduwa sakamakon tunowa datayi ta daura ruwan zafi kafin ta hawo sama qara ta saki tare da durowa daga saman gadon ta sauko da sauri "lafiya kisna "?Safiyya ta tambayeta cikin tsananin tashin hankali "wallahi ruwan zafi na daura tun dazu na manta sai yanzu na tuna tayi maganar tana karasa barin dakin da sauri ,tana taka step taji qara areef da gudu ta karasa saukowa jikinta na wani irin rawa kamar mazari ,ganinsa jikin hot plet jikinsa na rawa yasa ta saki qara ta fito da gudu dan ta kashe wutan gidan gbdy sai dai rudewar datayi yasa ta kasa hada kujera , ta dawo zata rungumeshi ajikinta adaidai lokacin da safiyya da aunty zee suka shigo kitchen sakamakon ihunta da suka jiyo safiyya tayi sauri riketa cikin tashin hankali tana furta " inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Samir da nasir ne suka shigo atare ban da Aliyu dake amsa wayar wani abokin harkallarsa hankalin samir a matukar tashe ya kai hannu ya kashe meter gidan gbdy yana kashe meter arif ya zube kasa a sume kisna ta fixge jikinta ta karasa rungumeshi tana kuka da kiran ta shiga uku.."

samir ya dawo kitchen din da hanzari ya amshe areef a hannuta yana tambayarta yadda abun ya kasance ta biyosa tana yi masa bayani tana kuka ,Gaba-daya Samir ya gigice ya rasa inda zai nufa dashi kawai ya nufi sama dashi gabad'aya suka biyo bayansa hankalinsu a matukar tashe kofar dakin mommy dake bude ya shiga ya kwantar da yaron yana kiran sunansa tare da taɓa kumatunsa cikin tashin hankali "areef! areef!! dukkaninsu babu abinda suke faɗa sai sunan areef bude idanunka.
aunty zee tace "areef my boy open your eye', amman Shiru ...
kisna data karasa shigowa dakin ta tsaya daga bakin kofa ta kasa k'arasowa inda suke hannuwanta duka dafe da qirjinta dake wani irin mahaukacin buguwa da karfi ,jira kawai taji abinda zasu ce mata ya mutu ko yana raye ....

a guje Aliyu ya shigo dakin sakamakon faɗa masa da nasir yayi yana k'arasowa bai san sanda ya matsar da samir gefe ba ya cicccibi d'ansa ya rungume ajikinsa yana kiran sunansa "areef !arerf !! aunty zee ta d'auko ruwan roba dake ajiye ta mikawa Samir sannan ta amshi yaron daga hannun Aliyu ta kwantar dashi ta amshi ruwa ta shafa masa a fuska ya ɗan sauke ajiyar zuciya da kyar yana ƙoƙarin bude idanunsa amman ya kasa Samir ya fita da gudu tunawa da yayi idan mutun ya samu shock na electric ruwan gishiri ake fara bashi ko cikkaken second biyu bai yi ba ya dawo dakin ya mikawa aunty zee ruwan rige rige safiyya da aunty zee sukayi gurin amsa ruwan aunty zee ce tayi nasarar amsar ruwan ta bashi ya sha tana kiran sunansa "areef plz my dear open your eyes say something to aunty zee ..."

" Nasir Kira doctor plz inji cewar Samir , Nasir ya mike ya fita da sauri, gaba-daya sun rude sun gigice , a mutukar fusace aliyu yace " wai ya'akayi wannan accident din ya faru dashi "?Cikin rawar jiki samir ya sheida masa kamar yadda kisna ta fada masa ta daura ruwan zafi ta manta amman tana tunanin areef yayi wasa da ruwa kafin ya taɓa hot plet din , saurin dafe goshinsa yayi yana furta "ya Salam yaji kamar ya kamota ya rufeta da dukan mutuwa ,
jin yadda suke kiran sunan areef har lokacin ta sadaukarwa ranta cewar ta rasa d'anta wasu zafafan hawaye suka soma turereniyar zubowa daga idanunta ta sake makalewa a jikin bango tana furta kalmar data ji ta fito daga bakin aunty zee wato "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, shi kawai take furtawa tana maimaitawa cikin haka nasir ya shigo tare da doctor rike da briefcase a hannunsa gabad'aya suka matsa suka bashi guri ya cire abun awon daga wuyansa ya auna shi yaga yana numfashi sai dai ba sosai ba Aliyu ya daga kafafunsa daga inda yake tsaye ya fuskanci inda kisna take tsaye "kuka munafurcin me kike wa mutane bayan sakacinki ne duk ya janyo zan rasa d'ana "? Gabanta ya shiga dokawa da karfi ta
Hannuwanta duka ta haɗe guri daya alamun yayi mata afuwa "ki daina nuna kamar kin damu da halin da areef yake ciki kowa yasan baki damu dasu ba saboda tsanar da kike min yayi maganar a fusace yana nuna qirjinsa ..."

"Aliyu dan Allah ka natsu areef zai dawo daidai bai kamata kayi bleming d'inta ba kasan bazata bari wani abu ya samesa da ganga ba inji cewar nasir .. "furzar da iska mai zafi yayi haɗe da rike kugunsa da hannunsa daya "bata sona komai zata iya yi dan ta dakushe farincikina bayan waɗan nan yaran sune rayuwata, sune dangina ,sune komai nawa ya karasa maganar cikin tsananin fushi yana nunata da yatsansa "wannan muguwar babu abinda bazata iya yi akaina ba tun da bata sona ..."...

Doctor ya kai hannu yana ƙoƙarin bude idanun areef "open your eyes da kyar yaron ya iya dan bude idanunshi da taimakon doctor , haka ma bakinsa ya buɗe ya duba sannan yace "karku damu zai dawo daidai Aliyu yace doctor "kana ganin zai rayu ? "Zai rayu sai dai jikinsa yayi week sosai saboda shock din daya samu me kuka bashi kafin na karaso ?" An bashi ruwan gishiri suka hada baki gurin fadar haka "Yes wannan abu ne mai kyau, abinda ake son abawa duk wanda ya samu shock daga wutar lantarki kenan garin yaya ma karamin yaro kamar wannan akayi careles dashi haka "?"Wannan mahaukaciyar uwar tashi ce tayi sakacin dashi yanzu kalli abinda ya faru dashi bancin yana da sauran yawanci rai da ba abinda za'a fada kenan ba "gaskiya ta dinga kula dashi idan ba haka ba zata iya rasa shi wata rana ,yanzu dai ku bar shi ya huta zuwa wani lokaci duk suka fito daga dakin suka bar aunty zee tana shafa masa kai ....."

Nasir ya dubi Aliyu yace "muradi abinda kayi sam bai dace ba ban ji dadin abinda ka faɗa a daki ba , tun bakasan da zaman yaran nan ba ita ke kula da yaranta dan me zaka yi bleming d'inta without any reason for god sake"dan Allah karka faɗa min babu dadi kulawar banza kulawar wofi ,wacce irin kulawa ce wannan da har za'a yi careless da rayuwar yaro ? idan har tana kulawa dasu bazata bari abinda ya faru yanzu ya faru dashi ba "."karfa ɓacin rai ya sa ka furta sabo itafa yar adam ce "ai komai za'a fada akanta ba yarda zaka yi ba kana bayanta ".

"ba haka bane wallahi nasan tayi kuskure tunda tasan yaran suna gidan kuma suna da kiriniyya bai kamata ta barsu a parloun kasa su kadai ba alhalin kofar Kitchen a bude yake sannan kuma bata gurin sai dai ya zamu yi da qaddara "? "Allah ya qaddara haka dole sai hakan ya faru babu tsumi babu dabara kisna ta matso kusa dashi saboda ganin yadda ɓacin ransa ya fito fili muryarta na rawa tace "dan Allah kayi hakuri wallahi ba da ganga nayi ba ai jin maganarta yayi kamar garwashin wuta a zuciyarsa ya juyo a fusace yana dakatar daita da hannunsa " baki da abinda zaki kare kanki agurina bare wani hakurinki din banza ,me zanyi da hakuri ?
" kima san wani abu wallahi bazan barki haka ba sai na hukataki bisa gangancin da ki ka min akan yarona ......"


zaro ido waje tayi hawayen dake makale a cikin kwarnin idanunta suka gangaro ya kai hannu zai cafki wuyanta nasir yayi saurin rike masa hannu "haba aliyu meye haka kake kokarin yi "? ya fixge hannunsa da nasir ya rike yana damko tsintsiyar hannunta yayi hanyar waje daita tana biye dashi tana kuka tana kallon bayansa jikinta na wani irin rawa gabad'aya suka biyosa har Samir daya zuba masa ido suna masa magana yayi musu banza bai kula kowa ba sannan bai tsaya a ko'ina ba sai a haraban gidan yana gama k'arasowa yayi cilli da hannunta ta tafi luuuuuuuu zata fadi "ki bar min gidana sannan ki fita a rayuwata bana bukatarki ,Aliyu baya bukatarki arayuwarsa"shiru tayi tana kallonsa zuciyarta na dokawa da karfi kamar zai fasa qirjinta ya fito waje ,"bana sonki bana bukatarki arayuwata da ki kashe min ya'ya gara tun wuri na zareki acikin rayuwarta ya karashe maganar jijiyoyin kansa na mikewa alamun ya kai kololuwa gurin ɓacin rai ".

" Aliyu dan girman Allah ka tsaya ka dawo hankalinka idan rai ya ɓaci hankali ke dawo dashi abinda kake yi sam bai dace ba haniyarsu ta fito da aunt zee haraban gidansu "kasan Allah bazan saurari duk abinda zaku faɗa min akan wannan ba kawai ta bar rayuwata kafin nima ta kasheni dan babu imani a zuciyarta "no aliyu wannan ba daidai bane aunty zee ta fada tana kallon samir dake tsaye rungume da hannuwansa duka a qirji ya bala'i tsurawa Aliyu ido yana kallonsa yana mamakinsa yana jin wani irin d'aci acikin ransa wanda bai taba tunanin zai ji akan Aliyu ba mutumin da suka taso tare, gurin baccinsu daya komai nasu tare sutura iri daya suke sakawa hatta karatu iri daya suka yi babu abinda ya bambamta su sai karfin zuciya cikin fushi aunty zee tace "ka tsaya kana kallanmu ka masa magana mana nasan idan ka masa magana zai fahimka akan tamu maganar "numfashi ya sauke yayi mata alamar tayi shiru tare da cewa "bana bukatar ki sake cewa komai..."

"Na tsaneki fiyye da tsanar da kika min , duk kalamanki basa shiga zuciyata bare su samu matsuguni sannan karki sawa ranki ni Aliyu zan dawo na soki a wannan duniyar never hakan ba zai taɓa faruwa ba ,bani da lokacin da zan fahimci kowa daga cikinku akan wannan yarinyar ya nuna kisna kinga zamanki acikin gidan bashi da wani amfani dan dake da babu duk daya ne agurin Aliyu gara ki kama gabanki ."
Cike da tsananin tashin hankali tace "dan Allah ka tsaya ka fahimceni ta kai hannuta zata kamosa ya buge mata hannu da sauri "don't don't ever touch me ,karki ga na dawo dake cikin rayuwata ki ɗauka ko tsoro ne a'a hallaci na duba if not ke da Aliyu har abada dan ko alahira bana qaunar na hadu dake ,wallahi akan wannan gangancin da kika min zan iya sakinki ......."

kanta ne ya soma juyawa saboda jin kalmar daya fito daga bakinsa take ta soma ganin juya jikinta ya kama rawa sosai fiyye da d'azu gabad'aya tsayuwa ya gagareta jikinta ya kasa ɗaukar kafafunta ta soma yin kasa zata fadi aunty zee tai saurin matsowa kusa daita ta rikota jikinta tana girgiza mata kai "aunty zee kina jin abinda yake faɗa akan ya'yan da ni kadai nasan irin azabar dana sha akansu , nasan nayi masa kuskure amman ya kamata zuwa yanzu ya yafe min ko da yake na fuskantarshi so yake ya koreni ya rabani da ya'yana suyi rayuwa tare da wata "exactly abinda nake nufi kenan kuma na gode da kika fahimci haka saboda bani da abinda zanyi dake , jin haka yasa ta sanyawa jikinta jarumta ta mike bisa kafafunta da suke rawa ta goge hawayen idanunta "to ya kake tunanin zan iya rayuwa babu ya'yana"? "Ka barni na rayu tare da yarana karka nisantani dasu , dan Allah kayi hakuri bazan sake ba nasan nayi kuskure bazaka sake kamani da makamancin irin wannan laifin ba, kayi hakuri nayi kuskure bazan sake ba ". tana kuka tana rokonsa ..."

"baki da hankali ki rike hakurinki dan babu abinda zanyi dashi rayuwa dake ne dai bai zai me min dole sai nayi ba dan haka ki kama kanki da kyau dan at any time zan iya rabuwa dake wallahi coz you are nothing to me ya karasa maganar yana huci kamar zakin daya ga abincinsa ya rasa har zai juya ,ya tsinkayi muryarta cikin kuka "yadda baka damu dani ba nima bazan sake damuwa da kai ba ......"

"daya fiyye miki Kinga kin hutar da bakar zuciyarki son Wanda baya sonki yana gama fadar haka ya juya ya shige gidan , kuka take sosai kamar ranta zai fita haka aryan shima kuka yake yana rike da hannunta duk ta fita haiyacinta da kyar aunty zee da safiyya suka kamota suka shigo daita suna rarrashinta "har sai yaushe Aliyu zai ga farina aunty zee "?
"Na kaskantar da kaina na bashi hakuri yaki hakura ,na bishi na bishi yaki saukowa me zan masa aunty zee ki faɗa min abinda zanyi masa ya huce "? ta karasa maganar tana sake rushewa da wani sabon kuka "aunty zee ko hakura zanyi dashi ne na hutawa rayuwa tunda baya sona ya furta min ni dashi ya furta agabanku "wani irin tsana ce haka ? aunty zee ta girgiza mata kai" maganar hakura dashi ma bata taso ba " kai aunty zee wallahi na hakura da Aliyu koda kuwa shine karshen namiji a duniya zan barshi ta mike cikin rawar jiki ta hau sama tana taka step biyu biyu aunty zee ta biyo bayanta da sauri tana kiran sunanta ....."

Mmn sudais[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

~TRUE LIFE STORY~

Free page 12

*PAID

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login