Showing 414001 words to 417000 words out of 495987 words
Chapter 139 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
ya bude ya dauki fury ya kafa a bakinsa bai cire ba sai daya shanye tassssss sannan ya zauna akan kujera yana sauke numfashi ya daura kafafunsa tare da yin crossing dinsu ya zubawa Samir ido shima shi din idanu ya zuba masa yana kallonsa cikin rashin sanin abinda zai ce masa?"a hankali yayita rarrashinsa amman yace sam bazai cigaba da zama Ζasar ba shi ya zauna idan ya kammala komai ya samesa .
Nan take alhj Nuhu yace tunda ya amince a mayar musu da aurensu kawai , ba'a watse ba sai da alhji nuhu ya mayar da auren kisa da muradi kuma ya kira magabatan jabir ya sheida musu suyi hakuri kisna gidan mijinta zata koma kisna ba karamin jin dadi taji ba lokacin dataji ta rungume yaranta cikin tsananin farinciki kafin kace me tuni zancen ya bazu acikin family kisna ta shirya kayanta kala biyu ta wuce gidan granny dan gujewa fushin muradi tana isa ta iske aunty afra cikin tashin hankali tana waya da jabir jikinta har rawa yake "yauwa gama kisna nan taxo na bata wayar ne?"okay to shikenan ta katse kiran kisna ta ajiye jakarta tare da rungume aunty afra "ki tayani murna yaruwa an mayar da aurena da ya Aliyu uban ya'yana wallahi ina cikin tsanani farinciki "na tayaki murna yaruwa ai gara da aka mayar hankalinki zai fi kwanciya ya akayi muradin yarda ?"tayi maganar cikin dauriya " wai jin mumy tace itama tana son mu kasance tare shine yace ya amince bai dai san an mayar da auren ba yadda naji daga sama nasan haka shima zai ji amman kina ganin babu wani matsala ?
"inshallahu babu matsala ki tayani da addu'a kawai suka saki juna kisna na kallon fuskar aunty afra dake zaune cikin tsananin faduwar gaba "yau zanyi baccin da ban taba yin irinsa ba ta karasa maganar tana kwanciya flat akan katifa , aunty afra tace "ai kuwa zakiyi ko ki bakunci barzahu ba ta fada a zuciyarta kana ta mike tsaye tana cewa " kwanciya zakiyi batare da kin sha ko ruwa bane bari na kawo miki fresh milk chocolate ki sha okay aunty afra ta fita ita kuma ta fada tunanin muradi bayan kamar minti goma aunty afra bata dawo dakin ba ta mike da niyyar shiga dakin granny nan taji sautin aunty afra a kitchen a hankali ta karasa ta kasa kunne "ai muddin ta koma gidansa nayi two zero Kena. "okya yanzu dai ki taimaka ki kawo min poison din kafin kizo zan mata amfani da maganin bacci ,okay ina jiranki da sauri kisna ta koma dakin ta zauna cikin jin faduwar gaba tare da tunanin " tabbas maganarta aunty afra take yi to dawa take wannan shawarar ?"tana nan zaune cikin tsanani tashin hankali ta dawo dakin tana murmushin ta ajiye mata fresh milk "ki sha zan fita amman yanzu zan dawo ta juya ta sake fita ta bar kisna cikin bugawar zuciya da rashin sanin madafar dafawa har bayan awa daya ta dawo dakin tana ganin kisna kwance tamkar ta mutu ta sheke da wata irin mahaukaciyar dariya tana tafa da hannuwanta duka ta dauki roban fresh milk tana kallo tana kallon kisna "jaka wawiya shasha wacce bata san meye duniya ba , wa yace miki ina daya daga cikin wadan da zasu tayaki murna komawa gidan muradi ?"never kisna bazan taba tayaki murna ba saboda ni kaina son abinda kike so nake shiyasa ma na dinga ingiza rayuwaki , nasa kika cire cikinki na farko sannan na dinga baki shawarar ki aure musa dan ki cika masa alkwarin da kika daukar masa ba dan komai ba sai dan na kara nisantaki da rayuwarsa a she dai a karshe zaki koma gidansa ina bazai yiwu ba da hannuna zan kasheki bayan nayi poison dinki zan caccaka miki wuka a zuciya ta juya da sauri sakamakon muryar granny ai tana fita kisna tayi wani irin tsalle ta duro d'aga kan gadon jikinta na wani irin kyarma bata tsaya daukar komai nata ba ta fita kofar kitchen tamkar mahaukaciya tana kuka ."
Har ta isa gida kukan maganganun aunty afra take, tayi matukar gigita Tana shiga gidan bata tsaya bin ta kan kowa ba ta shiga dakinta ta fada kan gado ta rushe da wani sabon kuka "sai data yi mai isarta sannan ta mike tsaye ta shiga zariya a filin dakin "why aunty afra ?,me ye laifina gareki da kika bada gudummawa akan ruguza rayuwata tun inda karancin shekaruna ?"wani kuka ta rushe dashi mai karfi wanda yasa mumy ta shigo dakin "kisna me yasa meke ?,batayi magana ba ta ci gaba da kuka "wai meye kike kuka haka da zariya a daki ki fada min mana ?
bata jin zata iya fitowa da wannan sirri"tabbas aunty afra ta cutar daita sai dai Allah yayi mata sakayya , Allah sarki muradi ya sha fada mata wacece aunty afra hatta yan'uwanta suna fada mata cewar tayi hattara daita , ta daina daukar zugarkata duk mai sonka bazai so kayi abinda zaka sabawa iyayenka da mijinta " wayyyohhly Allah .... ta sake rushewa da wani kuka "ko auren da'aka mayar ne bakya so bayan kice da bakinki kika zabi haka ?"mumy tayi magana cikin tsananin faduwar gaba tayi saurin durkushewa kasa tana girgizawa mumy kai "to Allah yayi miki maganin abinda ke damunki tana gama fadar haka ta juya ta fita daga dakin ta kasa runtsawa har washegari tana kan abu daya idanunsa suka kumbura
ranar a tsorace kisna tayi sa acikin daki cikin tsananin tashin hankali dan gani take tamkar aunty afra zata biyota har gida ta caccaka mata wuka kamar yadda ta fada ."
lokacin da muradi ya sheidawa nawal batun mayar da aurensa da kisan taji wani iri tashin hankali da faduwar gaba a lokaci daya ta dauke wuta amman dake ta iya bariki sai saisaita kanta tayi tace "kai norr ai babu komai wallahi naji dadi sosai ita saboda uwar yayanka ce bazan taba damuwa ba ni kawai ka Turo ayi maganar aurenmu shine damuwata wannan mai sauki ne zan turo kafin na koma suka cigaba hira har soyayya . " wajen sati biyu kisna bata cikin sukuni da walwala har sanda aka je kai kudin auren muradi tare da saka rana wata bakwai masu zuwa kamar yadda muradi ya bukata Sam kisna bata damu ba , dan hatta shi kansa muradi bata damu da lallai sai ta gansa ba dan har yanzu damuwar abinda aunty afra tayi mata bai bar zuciyarta ba , babu abinda take jin a cikin zuciyarta kamar tsanarta , bata qaunar abinda zai hadata da aunty afra .."Tana kwance a dakinta cikin damuwa aunty ummi ta shigo dakin ta tsura mata ido tana kallonta sannan ta samu guri ta zauna, kisna ta mike ta zauna tana gaisheta "kisna wai meke damunki ne ?,shin bake Kika bukaci amayar da auren nan ba amman tunda aka maidashi kike cikin damuwa ?"wallahi ba mayar da auren nan bane damuwata akwai abinda ke damuna amman inshallahu zan yi kokari na cire ,to ko dai kina fargaban bin muradi ne idan shine kiyi zamanki anan shi ya dinga zuwa idan ya samu lokaci , a'a aunty ummi ni wallahi nama fi son na bisa bin nasa zai sa zuciyata ta samu natsuwa sannan kuma wata dama ce da zan gyara kuskurena wata killa kusancin da zamu sake samu yasa ya huce abinda nayi masa "shikenan kisna amman da zan so kiyi zamanki anan dan wallahi zuciyar muradi cike take da jin haushinki ,karki bishi yayi kokarin rama abinda kika masa murmushin takaici tayi tare da cewa "Kai aunty ummi kiyi mana addu'a inshallahu babu abinda zai faru domin muradi mutumin kirki ne sannan shi din zinari ne bashi da wani aibu sannan zuciyarsa cike take da tausayi da zarar mu kasance tare zai manta komai nasiha aunty ummi tayita mata tare da fada mata tafiyarsu tun daga lokacin ta soma shirinta a hankali ita da yaran sai dai mumy tace ta cire kayan babu inda za'a dasu babu yadda ta iya haka tabi umarnin uwa ....."..
Ana gobe jirginsu zai tashi ta iske dady a falo cikin jikokinsa yayinda ya'yansa ke zaune a kusa dashi har aunty zee ya d'ago a hankali ya tsura mata ido tayi saurin durkushewa kasa taso ace yana d'akinsa amman tunda yana nan din bata da yancin da zatace suje daki ,da dai da ne lokacin da take cikin zuciyarsa tasan komai tace yayi zai yi cikin sauki , muryarta a tsarke ta soma magana tana watsa da yatsun hannunta "dady nazo ne na sake neman yafiyarka akan abubuwan da suka faru ta karasa maganar tare da yin shiru ta sunkuyar da kanta kasa kusan minti goma ya dauka batare daya ce komai ba, tausayi tabashi duk ta rame dan haka ya bude baki ya soma mgn a tsanake "na yafe miki sai dai ki zauna lafiya dan yanzu Kece kika zabi komawa gidansa a karon kanki ba dan an takura miki ba ko anyi miki dole ba , dan haka babu yaji babu rabuwa matukar ba ziyarar kirki zata kawoki gidana ba bana son ganinki da sunan matsala dan baki da masauki a gidana, kuma duk ranar da kika bari wani abu ya faru na tashin hankali a tsakanin ke da abokiyar zamanki tunda yanzu kun kusan zama ku biyu a karkashin ikonsa , karki yi abinda zaki kashe aurenki !karki yi abinda zaki kashe aurenki da Aliyu kisna !! Idan kika yi wallahi sai dai ki nemi wani uban amman bani ba...
Bazan yi ba dady dan na canza kai ne dai kaki fahimtata, haka ne ma yasa na zabi komawa ga zabinka domin na gyara kuskurena na baya, "ni dai na fada miki Ki tabbatar da alkhairi ne zai cigaba da kawoki gidana sabaninsa hk karki zo ,ki zauna lafiya a karkashin ikon muradi cikin amana da kulawa da juna muddin rai idan kika min haka kin gama min komai , inshallahu dady zanyi iyakar kokkarina ."
washegari da misalin karfe bakwai na safiyar ranar ta fito daga dakinta ta shiga na mumy ta tsugunna a gabanta zuciyarta cike da rauni "mumy ni zan wuce kiyi min addu'a " fatan nasara mamana Allah yayi miki albarka ya kade fitina kiyi hakuri da komai da zaki gani , ta mike tsaye cike da sanyi jiki ta shiga dakin dady tsaye ta sameshi goye da hannuwansa a baya bakinta na rawa tace "dady zan wuce aciki ya amsa mata da "Allah ya kiyaye batare da ya juyo ba har ta fice a dakin zuciyarta cike da rauni bancony dinsa ya koma ya tsaya yana kallonta har sanda ta shiga mota ita da mumy da yaranta yana mai jin wani iri a zuciyarsa yana tsananin qaunarta qauna mai girma sai dai laifinta ya dakushe wannan qaunar kuma shine dalilin da yasa har yanzu ya kasa sakar mata fuska .."gbdy ahlinta suka mata rakiya zuwa airport cikin tsananin farinciki hatta muradi fuskarsa a sake take bai nunawa kowa damuwarsa ba ya rungume mumy "mamana zanyi missing dinki sosai ta zaresa ajikinta tana shafa gefen fuskarsa "nima zanyi missing dinka dana inshallahu idan su aryan sun yi hutu zamu tare dasu Samir , gaban aunty ummi ya k'arasa ta janyosa gefe "dan Allah ka manta komai ku ci-gaba da rayuwaku da kisna zaka ji dadin zama da auta yanzu dan wallahi ta canza "murmushin gefen baki yayi yace bari na fara nuna miki tun daga nan kisan irin rikon da zan mata kai tsaye inda kisna ke tsaye tare da yaranta ya nufa ya duka sumbace yaransa sannan ya riko tafin hannunta cikin nashi ya soma tafiya daita wani irin zirrrrr taji a gabadaya ilahirin jikinta mai kama da shocking a hankali ta dinga binsa a baya tana mai fatan idan sun isa kasar cairo su cigaba da rayuwarsu kamar yadda ya nuna mata a farkon aurensu har suka shige ciki su aunty ummi na tsaye suna daga masu hannu tare da fatan Allah ya kai su lfy ....."
Back to the story
Idanunshi na sama yana kallon saman dakin bai san adadin lokacin daya dauka zaune agurin ba cikin tausayawa kasa tare da nadamar rayuwa duk mai ilimi baya ramuwa akan abinda akayi masa me yasa bazai zubar da komai ba ya tashi tsaye yana Zariya dakin cikin gashi dai bacci yake ji amman sam ya kasa runtsawa ,yadda bai runtsa ba haka ita ma kasa runtsawa tayi ta leko falon yake yafi sau goma sai dai har lokacin yana nan dan tuni ya ajiye diary dinsa a hankali ya koma ya zauna kasa yayi tagumi da hannunsa daya cikin zurfi a tunani , jarumta ta sanyawa jikinta ta shigo ta durkusa a gabansa ta tsurawa diary din Ido kafin daga baya ta soma kokarin budewa batare da saninsa ba dan yayi nisa a tunani ,ta fashe da wani irin kuka saboda fahimtar datayi tarihinsa ne wanda ke haΙe da abubuwan datayi masa kuka ta cigaba da rerawa tana furta kalmar " kayi hakuri ! kayi hakuri !! dan Allah kayi hakuri !!! ya sauke numfashi a hankali ta matso ta d'aura kanta a saman qirjinsa tana wani irin kuka kamar ranta zai fita ,bai motsa ba daga inda yake bare tayi tunanin yasan da zamanta har bacci ya fara figarta tana sheshekar kuka jin ya daina jin sautin sheshekan kukanta ya birkitota yana kallon kyakkwar fuskarta gbdy fuskar ta sauya tayi ja saboda kukan datayi naunayen ajiyar zuciya da numfashi ya sauke atare yana mai daura hannunsa a saman sumar kanta dake kwance a har gadon bayanta yana shafawa yana sauke numfashi ..."
Mmm Sudais
[7/19, 5:33 PM] +234 803 631 5951: ππππππ
CUTAR DA KAI
ππππ
ππππππ
Page 61
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, voil lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan Ιaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
A natse ya cigaba da kallonta yana tunanin yadda zai goge komai daya faru acikin kwakwalwarsa , yasan tayi masa laifi mai girma da tsayawa a rai wanda ita kanta ta yarda kuma ta amince da cewar ta aikata masa laifi, yayinda wasu laifikan da tayi masa tayi ne a dalilin gudumuwar da afra ta bayar a rayuwarta ,afra muguwar macece kuma azzaluma wacce ta zamo fasagurbi a cikin al'umma da yan'uwanta ya dai rasa dalilin da yasa ya kasa hakura tare da sakar mata jikinsa ne " .
" me yasa bazaka manta komai ba ku cigaba da rayuwarku tunda ta rigada ta zama qaddarar rayuwarka kuma ta gane kuskurenta ? " saboda ina jin haushinta adalilin taki fahimtata da sauran yan'uwa alokacin da muke ta kokarin fahimtar daita uwa uba tozarcin da take akan mahaifiyarka sannan da yaranka da tayi sanadiyar barinsu duniya batare da laifin komai duk zuciyarsa ta bashi amsa da hakan."
a hankali ya gangara hannunsa har suka kai kan tautausan pinky lip's dinta ya fara shafawa tare da lumshe kyawawan Idanunshi yana kokarin kawar da abubuwan da suka faru a rayuwarsa dana mahaifiyarsa amman abun na sake zama masa daram a zuciya most especially mahaifiyarsa komai daya faru daita yafi tsaya masa a zuciya yana jin ina ma tana raye bata mutu ba , da bai san adadin qaunar da zai nuna mata, shi kadai yasan irin gata da kulawar da zai mata amman mutuwa tayi musu yankin quana ta dauke musu