Showing 141001 words to 144000 words out of 495987 words
Chapter 48 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
dan haka a shekarun afra ta iya tsara kwakiya sosai ga iya tafiya da rausaya kamar bishiya ,kullum fuskarta cikin kwaliya take an sha dukanta a school akan kwaliya sosai tayi kyau tayiwa mumnynta sallama tare suka jero da mummynta har jikin motar ta rakota tana mata fada" afra ban da rawan kai ki natsu dan Allah kinji ki zauna da kowa lafiya karkiyi tashin hankali da kowa ."naji umma karki damu kinji zan zauna da kowa lafiya Amman ban da wannan kazamin yaron sam bazan raga masa ba tayi murmushi tare da bude mata gidan baya ta shiga ta zauna ta maida murfin ta rufe direbansu ya ja suka bar gidan sai data ga mai gadi ya kulle get din gidan sannan ta juya ta koma cikin gida kai tsaye hanyar gidan Alhaji realwan suka ɗauka tana zaune a bayan mota zuciyarta na shirya mata abinda zata yiwa Aliyu idan taje gida ."
dareban ya sauketa a had'ad'd'en haraban gidan Alhaji realwan tana hakince a bayan mota kamar wata babbar yarinya cikin wani irin yanayi ta lumshe idanunta tana sake zurfafa tunaninta ,turare ta cire a cikin yar karama jakarta ta fesawa a jikinta ta bude murfin mota ta fito a hankali gabanta kawai take kallo tana taku kamar bata son taka kasa tana shiga parloun da Aliyu idanunta suka soma cin karo yana sanye cikin bakaken kaya wonda three quarter da rigar yan kwallo long selve kallo ɗaya suka yiwa juna kowane ya dauke kanshi ,yar farar dake fuskarsa ta ɗauke yana jin babu dadi a ransa dan bai mata da halinta ba ,tabe baki tayi ta samu guri ta hakinance akan daya daga cikin kujerun gidan a daidai lokacin direban ya shigo parlou'n hannunsa rike da akwatin kayanta ya ajiye a gefenta yana kallonta "sai yaushe zan dawo na daukeki '?
"Zan fadawa umma ta fada fuskarta a haɗe ."
tun sanda Afra ta dawo gidan Alhaji realwan Aliyu bai sake samun kwanciyar hankali ba saboda takurawarta bashi da ikon sakewa acikin gidan ,idan kuwa tana guri dole ne ya hakura da gurin ya killace kanshi a daki ko a lambun gidan saboda kallon wulakanci da aibantashi da take a cikin yaran gidan babu wanda bata fadawa a unguwar shi din dan tsintuwa ne kuma shege ne , a duk sanda Samir yaji ta fadi haka sai sunyi rigima daita , wani lokacin ma har da dambe suke yi da Samir yayi mata duka amman hakan baya hana gobe idan taga Aliyu ta furta masa bakar magana wanda shi ko kallon inda take bayayi sannan baya nuna alamun yasan da zamanta ,wani safiyar Lahadi wanda ya kasance weekend ce kuma bai fi sauran kwana uku ta koma gidansu ba ya badamasi daya dawo hutu daga kasar Austaraliya yace su shirya zai kai su shan ice cream Wanda shi saboda Afra ya shirya tafiya dan Allah ya jarabeshi da qaunarta tun haihuwarta ,ta shirya cikin hadaddiyar doguwar riga mai shegen kyau haka ma ummi ta shirya kisna cikin kanana kaya riga pinky da wando baki ta sanya mata takalmin pinky mai kalar kayan ta kama mata gashinta gida shida ta mika wa Aliyu ita "rike min ita muradi naje daki na dawo ya kai hannu ya amshi kisna wacce zuwanta hannunsa ke da wuya ta saka kuka tunda yazo gidan bata yarda dashi daman kuma shegen kiyuwa gareta bata yarda da kowa bayan mamanta sai yan'uwanta shima kuma baya son d'aukarta tunda ta fesa masa zawo ajiki "kinga aunty ummi dake haka yaji suke kiranta dashi bisa koyarwa mummy "Dan Allah amshi yarinyar nan bata son ina d'aukarta "kai dai muradi ka fadi gaskiya na lura dai tun randa aka yi maka wanka zawo kake gudun ɗaukar kisna ". Yatsina fuska yayi yana mika mata ita tana amsarta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya shi kuma ya juya zai bar parloun "wai kai bazaka fita bane naga baka shirya ba? tsaki yaja yace "gaskiya babu inda zani Sai kun dawo bata kawo wa ranta komai ba ta nufi daki ,Koda afra taga kowa acikin motar bata ga Aliyu ba sai taji babu dadi haka nan taji ranta ya ɓaci kamar tace ta fasa zuwa
A daidai haraban shoppright ya badamasi yayi parking motarsa kiran pijo ,daya bayan daya suka sauko ya badamasi , ummi ,Samir Muhammadu wanda suke kira da madu kisna duk ya'yan Hajiya salaha ne sai Zahra da mufeda ya'yan da mumuy ke riko .
a hankali afra ke taku wanda yake kara sa badamasi jin wani iri akanta yarinya ce sai dai Allah yayita da maseefar iyayi da yangar bala'in ,bata tsaya bin ta kan kowa ba ta samu guri ta zauna tana jiran karasowarsu ,sai dai hakan bai faru ba dan shigewa sukayi ciki ,batayi minti goma da zama ba sai ga ya badamasi ya dawo da yar fararsa yace "yar tsohuwar nan tunanin me kike yi haka "?
Yayi maganar yana mika mata abinda tafi so ice cream ta amsa tare da cewa "babu komai a shagwa'be kamar zatayi kuka "hannu ta kai kan itacen tsinke dake ciki ta dibi ice cream ta kai bakinta kamshinsa da gardinsa ya kaiwa kwakwaluwarta lumshe idanunta tayi tana buɗe idanunta suka faɗa cikin na ya badamasi daya tsura mata ido yana kallon kyawawar fuskarta .... "
Mmn sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 27
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
"Mummy ta dawo parlour'n ta iske afra ta cire uniform d'inta tana jujjuya kai ta bita da kallon mamaki sannan tace "ya naga kin cire kayan makaranta ?" cikin marairaicewar muryar tace "kaina ke ciwo mummy "karya take wallahi babu wani kanta dake ciwo , ba tayi assignment d'inta bane ai naji Sanda kike fad'awa mufeeda cewar kin tuna bakiyi assignment d'inki ba Kuma malamin Chemistry bai da mutunci dukan tsiya zai miki shine dan tsabar karya zaki ce kanki ke ciwo " ? inji cewar samir ya fada yana zabga mata harara "wallahi karya yake min mumy da gaske kaina ke ciwo wai ma ina ruwanka dani ne ? " ke mufeeda yaushe na faɗa miki haka ?" Allah mumy ki rabani da Samir idan ba haka ba zamu yiwa junanmu rashin mutunci . "to muyi mana yau muka fara rashin mutunci kece zaki sha wahala mai kan karas kawai ki dai tuba da karya dan Allah ya tsinewa mai karya".
mumy tayi murmushi sannan tace " kai Samir banason jan magana tunda tace kainta na ciwo babu inda zata ku kama hanya ku wuce Allah ya tsare "Mufeeda Zahra da suka wa mumy sallama dan tuni muradi yayi fita mufeeda ta riko hannun kisna nan fa ta fara zillewa itama bazata ba tunda aunty afra bazata ba , mumy tayi rarrashi ta lalla'bata amman taki ,cike da jin haushi Samir ya zuba mata rankwashi a tsakiyar kanta tare da ɗauketa ya rungumeta ajikinsa ya nufi hanyar waje daita ihu ta dinga yi tana kokarin saukowa amman ta kasa ya shiga gidan gaba daita tana rungume a jikinsa yana mintsini gefen cikinta , sauran kuma suka shiga gidan baya direba ya tada mota suka wuce, kisna aka fara saukewa sannan aka wuce dasu .."
Bayan tafiyarsu mummy ta shiga daki ta dauko wa afra maganin ciwon kai ta bata ta sha sannan ta kama sauran aikin gidan da ba'a karasa ba ,daman kuma haka take yi a duk sanda suka wuce school haka zata bi gidan ta sake gyara inda basu yi ba , bayan ta gama ta koma d'akinta tayi wanka ba ita da dawo parlour'n sai karfe ɗaya dan sai datayi sallah inda ta iske afra kwance akan doguwar kujera tayi mata sannu da jiki sannan ta samu guri ta zauna " cikin haka wayar mumy ta ɗauki kara batare data duba ba ta dauki wayar ta kara a kunnenta dan tasan mai kiran duk yanayin da mumy take ciki tana magana dady zai gane , hakan ce ta kasance ma yanzu yana jin muryarta sai daya tunhumeta tace "wallahi gajiya ce kawai , yayi murmushi yace" ko babu gajiya bakya gajiya da washhhhh , gashi kin hana a ɗaukar miki masu aiki ."karka damu aikin gidan nan guda nawa ne , ga yara mata kuma suna iyakacin kokarinsu ,bugu da kari nafi son su iya komai da kansu karsu je gidan miji basu iya komai ba ".
"wannan kuma gaskiya ne ranki shi dade Allah ya saka miki da alkhairi ,daman na kira naji muryarki ne naga shiru baki nemeni ba har yanzu ga aiki ya sani gaba ga rashin jin muryarki ,wannan sabon tayi masa ne tun suna ganinyar quruciyarsu har bisa yanzu da suka dan manyanta ,da zarar ya fita aiki wayarta bata yankewa gurin kiransa ,wani lokacin ma tana aiki waya na nanne da kunneta sun dade suna waya sannan sukayi sallama ta ajiye wayar .afra ta dube mummy tace "Allah sarki mummy dady na ji dake "mummy tace "idan bai ji dani ba da wa zai ji afra? "Biyayya da soyayya ta haifar da haka kema kiyi kokarin idan kinyi aure ki haifar da haka a gidan aurenki , kulawa mai kyau ina yiwa dady, ina kwantar masa da hankali bana damunsa da bani bani ,idan kudi zai bani bana amsa sai idan ya zama dole ke sawa na amsa , shiyasa banga abinda zance yayi min ba yaki yi min , sai dai idan bai dashi , Allah dai yaja da ranshi "
afra tace "ameen ".
Suna zaune suna ta hira har uku da minti hasim " bari na tashi ga la'asar har ta kusa ya kamata a soma haramar abinci dare ". afra tace" mai za'a daura mummy ?" Ke da kanki ke ciwo ki bari idan su mufeeda sun dawo sai su d'aura ko da yake ga islamiyya zaku jiya baku je ba lallai su shirya yau suje ke kuma zuwa gobe kya je nayi aikin da kaina ."
"ai tunda na sha magani naji sauki zan yi aikin islamiyya dai naje gobe idan Allah ya kai mu " Mummy tace " afra na lura baki son karatu gashi nan Kisna ma ta dauko halinki na rashin son karatu mace babu karatu akwai matsala kar fa a cireki cikin 'yan walima "Allah mumy ba haka bane walima kuma dole ayi dani bayan dayawa ma yan ajin basu san komai ba kudi zasu biya ayi musu walimar "to ke dai ki maida hankali karki yi walimar zuku azo ana tambayarki karatu ki kasa "zan kokarta "okay ki duba frizer kiga akwai raguwar kaya a ciki a yiwa dady farfesu cat fish yace ai masa " Afra ta mike cikin sanyi jiki ta nufi kitchen ta duba taga akwai saura har yayi kankara ta debo ta samu yar madaidaiciyar rabo , ta bude famfo ta tara ruwa jim kaɗan ta kashe famfo ta ajiye ta saka kifin a ciki roban domin kankarar ta narke , ta fito parlour ta zauna tana kallon tv".
mummy ta Mike tace bari naje nayi sallah na dawo muyi aikin tare ganin afra na kallon tv yasa mummy ta dan tsaya tace "kije kiyi sallah kou " afra tace "to haɗe da mikewa ta nufi dakinsu ,karfe hudu da minti goma gabad'aya yaran gida suka dawo daga school , suna cire kayan school mumy ta umarce su da saka kayan islamiyya tare da daura alwala dan gabatar da sallah , mufeeda ta yiwa kisna wanka bayan tayi sallah taci abinci , tana ƙoƙarin saka wa kisna kayan islamiyya kisna ta tubure tana kuka "wallahi aunty mufeeda bazani islamiyya ba ki kyaleni kullum sai malama tayi min bulala ni banason bulala tana kuka tana zame wandon makarantar da mufeeda ta saka mata ta fito parlour da gudu tana ihu bazata islamiyya ba har da birgima a kasa mummy daga cikin d'aki ta kwallawa mufeeda Kira tace "kyaleta zata zo daga baya ,dungure mata Kai mufeeda tayi sannan ta dubi afra data dauki Kisna ta rungume ajikina tace "afra bazaki bane kema "?"Ke sai gobe zani suka fito tare da zahra suka wuce dan tuni Aliyu da madu da samir sun kama gabansu dan dama basa jiransu zuwa islamiyya .."
Mummy ta fito tana kokarin zama kisna ta boye a bayan kofa dan kar mummy tace akaita islamiyya ,
mummy tace "har kin gama komai Afra tace" na kusa dai "yaran duk sun wuce islamiyya ?"Eh duk sun tafi sai kisna ,rabu da jairar yarinyar nan so take ta dinga kin zuwa islamiyya kamar ke kuma bazai yiwa ba karatu dole kuyi . "ai mummy duk kece da wannan mai kan karas din ke shagwa'bata inji cewar samir daya dawo ɗaukar hula "ai dole na shagwa'bata Samir uwa guda ai ba'a bar sawa bace amman akan islamiyya kowa zai jimu suka sa dariya banda Afra data haɗe rai kamar wacce aka aikowa sakon mutuwa ta zabga masa harara tana cewa " naga alamun suna kake son saka min to wallahi yau ya zamo karo na karshe da zaka Kirani da mai kan karas ".ya dauki hularsa yana tafiya yana cewa "baki isa ki sani dole ba sai nayi ra'ayi yar rainin hankali kawai ,kisna dake la'be a bayan kofa jin fitar samir ta rarrafo ta fito ta matso kan kafe ta zauna tana dariya sai ganin samir sukai ya dawo a lokacin da yake daf da ficewa daga parloun , aiko yana gama tsayawa ya zuba ma kisna rankwashi a tsakiyar kanta "ba dai kina biyewa wannan mai kan karas din ba tana gudun karatu kema kina gudun karatu zaki sani ne "?"Maza tashi mu wuce Ina kayanta mummy daita zan wuce Kisna na jin haka ta sake bare baki tana kuka har da birgima , "kai Samir zan bata maka rai fa ,rabun min da yarinya ta fada tare da janyo kisna jikinta tana rarrashi ya fita yana murmushi. "
"Mummy mai za'a dafa idan an sauke parfesun?" Mummy ta yatsina fuska tana fadin "ni yau na rasa me za'a d'aura kije store ki dauko doya Afra ta shiga ta kwaso guda biyu ta fito tana nunawa mummy ,"mummy guda biyu ya isa ? "Eh sun yi kawo na fere".
"haba mummy gani meye amfanina kije ki kwanta ki huta ".Mummy tace "kwanciya yanzu da