Showing 117001 words to 120000 words out of 495987 words

Chapter 40 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

fada miki gaskiya ba ,zan boye miki saboda bana son ganinki cikin damuwa, ni kaina nasan sana'ar da muke bata dace da rayuwarmu ba ko da yake ni nawa na wani lokaci ne , ina da burin barinsa a kowani lokaci domin tsiratar da rayuwata ." Tasa bayan hannunta ta goge hawayen idanunta wasu suka sake zubowa cike da sheshekar kuka tace "hakika wannan sana'ar taku akwai hatsari a cikinta, bayan haka ma kuna cutar da ya'yan al'umma ,me zaku cewa Allah "? "duk wanda kuka saidawa kun saka rayuwarsa cikin hatsari "
"wannan gaskiya ne mmn Sadiq shiyasa ma nake da niyyar barinsa saboda kazamar rayuwa ne kullum muke nan cikin fargaba da tashin hankali , yanzu idan akace miki dare yayi zaki sha mamaki yadda zaki ga manya mata da maza kala dabam dabam suna zuwa siya ,wasu allurar koken ake musu wasu kuma aininhin koken din suke siya , ya'yan masu kudi da yan film da manya mata wata a rana sai tayi allura sau uku koma fiyye da haka ni kaina ina tausaya musu wallahi nan kusa zan daina wannan business din sun dade suna tautaunawa dashi tana bashi kwarin gwiwar dainawa kafin daga baya yace tayi masa alkawarin oga bazai san da maganar ba tayi murmushin takaicin tarayyarta da haroon sannan tace "nayi maka alkawarin bazai ji komai a bakina ba suka yi sallama ya wuce .

tun bayan da esele ya bar bukkan batayi yunkurin mikewa ba ta tsurawa ya'yanta ido kawai tana Kallonsu cike da tsananin tausayawa rayuwarsu dan a halin yanzu tafi tausaya musu akan kanta ,haka tayi ta kallon haroon da aikin da yake batare da tayi masa magana ba, gabad'aya tashin hankalinta ya qara akan wanda take ciki bata runtsawa saboda kullum da abinda take gani daga garesa amman haka ta dinga hakuri har sanda Aliyu ya cika wata shida cif a duniya wanda a lokacin kusan tasan rabin mutane dake rayuwa a unguwar har shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu sai dai idan ka ganta bazaka dauka yar mai arziki bace sannan cikakkiyar
yar gata mai yawon dangi bace gaba-daya ta fita haiyacinta ita da rayanta saboda rashin natsuwar zuciya da kwamciyar hankali uwa uba yunwa dan basa samun isasshen abinci daga haroon dan sai yayi ra'ayi yake badawa wani lokacin idan ya ga dama zai bawa Sadiq amman ita ko kallo bata isheshi ba ,yadda ta kame kanta da shiru shiru acikin mutane haka zaka ga yaranta basu da yawon magana dan da wuya kagansu a waje koda yaushe zaka isketa zaune a cikin bukka ita da yaranta tana koyar da Sadiq karatun boko, tana iyakacin kokarinta na gani yasan wani abu kafin shekarunsa su karu ta kai shi makarantar boko hatta magana batayi musu da harshen hausa sai dai da turanci saboda tana son su iya sosai "cikin wannan yanayin ta yankewa kanta koyan dinki a gurin wata makwafciyarta sala saboda ta gaji da zama haka gashi yaranta na bukatar taimakonta dan tayi kokarin ta samu aiki da takardunta amman hakan bai samu ba hatta koyarwa taso ta samu amman duk inda taje ba'a daukarta duk da tana ganin tausayawa a fuskokinsu wanda ta rasa dalilin haka , shi kuwa haroon da haihuwarta da barinta duk daya ne agurinsa dan bata gabansa ita da ya'yanta rayuwarsa kawai yake yana facaka da kudi son ranshi dan har lokacin bai ji zai iya rayuwa daita , kullum magana daya ce ke shiga tsakaninsu ta bar rayuwarsa ya huta baya bukatarta ,ita kuma burinta ya barta tayi rayuwa akarkashinsa koda bazai kula daita ba saboda darajan ya'yanta tun da bata yadda zatayi ..."

*****

Karfe ɗaya daidai na daren ranar wata litinin tana zaune a tsakiyar katifa ta kwantar da Sadiq a saman cinyarta yayinda Aliyu ke kwance a kafadanta tana shafa bayansa ta kasa runtsawa saboda tashin hankali,da irin rayuwar data tsunduma kanta duk akan soyayya ,sosai tayi zurfi cikin tunani rayuwarta data yaranta halayen haroon ya dameta kwarai da gaske sai tayi kamar zata ciresa a ranta ta bar rayuwarsa kamar yadda ya bukata sai ta kasa taga gara tayi hakuri dashi wata rana zai dawo daidai ya rungumeta ita da yaranta har ma yayi alfahari dasu babu abinda zuciyarta bata kisma mata ba akan zamanta dashi ..."

a hankali taji motsin bugun kofar bukkar take gabanta ya fadi tayi shiru har sai data ji sautin muryarsa a kausashe yana bata umarnin ta bude masa , ta kwantar da Aliyu da sadiq da sauri ta mike ta bude masa kofar wani dogon tsaki yaja sannan ya raba ta gefenta yana sake jan tsaki tare da aika mata da kallon wulakanci, bayansa tabi tana kallonsa a cikin hasken da bai gama wadata dakin ba namiji har namiji amman bashi da wata nagarta , ya 'bata rayuwarsa da mugayen halaiya dabam dabam shine neman mata, shine safarar miyagun kwayoyi tana kallonsa ya kunna wuta mai haske sannan ya zare rigar jikinsa ya rataye ajikin kusa ya zare agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa tana kallonsa ya cire komai na jikinsa ya saura daga shi sai boxcer iya cinyarsa da farar vest gashin jikin nan nasa masu matukar kyau da sheki suna kwance luf dasu abin sha'awa kowace cikakkiyar mace wani miyo ta had'iye saboda sha'awarsa data tsarga mata sannan ta gyara kwanciyar yaranta tayiwa kanta gurin kwanciya daga dayan bangaren, shima ya kwanta a dayan bangaren suka saka yaransu a tsakiya babu wanda yacewa d'an'uwansa komai, tana jin kamar tayi masa magana ta nuna masa tasan aikin da yake ta lalla'bashi ya daina ya canza wata sana'ar su cigaba da rayuwarsu cikin salama sai dai tana tsoro kuma tasan maganarta bata da wani amfani agurinsa , gashi ta daukarwa esele alkwarin bazata furta masa ba .

Bangaren haroon kuwa ya dawo gida ne a dalilin tsintar kanshi da yayi da matsananciyar sha'awa gashi cikin yammatansa babu wacce ta nemeshi shine yayi tunanin ya dawo gida ko dicter zata bukacesa ya samu ya biyawa kanshi bukata , ganin ta kawar da fuskarta gefe yasa ya ciro wayarsa ya soma danne danne yayinda a hankali feeling ke sake bijero masa har ya mamaye sansar jikinsa ,ilahirin gashin dake kwance a jikinsa suka dinga mikewa daya bayan daya gabad'aya komai ya tsaya masa iya dauriya da hakuri yayi amman ya kasa ya mike ya shiga bayi ya watsa ruwa amman stil bai daina jin abinda yake ji ba sai faman juyi yake akan katifa a lokacin da tuni bacci ya ɗauketa shi kuwa babu abinda yake so da bukata a halin da yake ciki wanda ya wuce kasancewarsa da mace ,tun da yake bai taɓa tsintar kanshi cikin tsananin sha'awa irin haka ba yana da dauriya sosai dan baya son kai kanshi ga mata yafi son kullum su kawo kansu garesa gyara kwanciyarsa yayi ya koma flat yana mika haɗe da runtse idanunshi yana sake jin reaction din jikinsa na sauyawa Kamar ance ta farka idanunta suka sauka akanshi yayi pillow da hannunwansa duka yana kallon tabul din saman dakin ta mike ta kashe wutar dakin ta matsar da yaranta ta dawo kusa dashi ta riko tafin hannunsa cikin nata tana murzawa a hankali take jijiyarsa dake mike ta harba cikin shaukin da bukutuwa "meke damunka haroon "? Yayi shiru yaki cewa komai sai ciza lip's d'insa yake da karfi "ka faɗa min damuwarka ko zan iya maka maganinsa "? ta karasa maganar tana shafa qirjinshi stil shiru yayi sai dai gbdy yanayinsa ya sake ɗaukar caji ya juya ya kwanta a kan hannunsa na dama yasa hannuwansa duka ya dafe jijiyarsa , jin yaki magana yasa ta kwanta a gefensa ta shige jikinsa kamar jira yake ta kwanta ya soma yawo da hannunsa ajikinta naunayen ajiyar zuciya ta sauke karo na biyu daya kai hannunsa jikinta da kashi ,wani farinciki taji ya bakunce tsokar dake makake da kirjinta ,ta sha tunanin zuwan wannan ranar da zai bukaceta da kanshi sake mannewa tayi ajikinsa cikin kankanin lokaci komai ya gudana a tsakaninsu sannan ya kwanta yana sauke numfashi bai dade ba bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi zama tayi tana kallonsa tana addu'ar Allah yasa karshen wahalarta ne yazo tun daga wannan lokaci bai sake gangancin nemanta ba kwatsam sai ta fara laulayi tunda ta lura tana da shigar ciki hankalinta yayi mugun tashi sai dai ta dakewa zuciyarta ta cigaba da kula da yaranta da cikin jikinta, yayinda shi kuwa tsakaninsa daita ido ne idan tayi gigin shiga track d'insa zai rufeta da duka ko mari babu irin wulakanci da tozarci da bai mata, barin ma daya san tana da shigar ciki sai wulakacin ya karu ya daina basu komai hatta Sadiq dake mugun kulafucinsa ya daina bawa komai sai dai hakan bai damu Sadiq ba yana tsananin son shi
bangaren sana'arsa kuwa kullum cikin ntashin hankali yake da guje guje da boye boye domin tsira da kanshi daga ma'aikata miyagun kwayoyi , an sha kamashi sai abokan halkallarsa ne ke amso shi ..."


Tana zaune a dakin ya shigo hawayen son shi da tausayinsa da kanta dana yaranta ne ya shiga zubo mata ta rasa dalilin da yasa ya zabawa kanshi irin wannan rayuwar da bata dace dashi ba ,tasan ta cutar da kanta akan soyayyarsa dan bata cancanci rayuwa da mutun irinsa ba amman babu yadda zatayi ta dauki haka a matsayin qaddara har ya soma cire kaya jikinsa idanunta na kansa tana kallonsa tana jin yadda kauanrsa ke sake narkar mata da zuciya muryarta a raunane tace" sannu da zuwa wani irin kallon banza yayi mata " sannu da zuwa ubanki zaki min ance miki ina bukatar wani sannu da zuwanki ne ko wata kulawa daga gareki ? Abinda nake so dake ki tattara duk abinda kika san naki ne ki kama gabanki ina bukatar dakina zan saka wata acikinsa , idan kuma kinki zaki ga yadda zanyi dake wawiya jaka kawai da bata da tunani take gabanta ya fadi saboda jin abinda yace tayi tsuru tana dubansa ta kasa motsawa daga zaunen da take jikinta sai rawa yake ,saukan mari taji ta waro idanunta waje tare da dafe kuncinta "kunnenki na ciwo ne baki ji abinda nace ba da kika tsura min ido kamar mayya , ganin bata da niyyar cewa wani abu ya fixgota zuwa waje inda matan gidan ke zaune suna shan iska kasancewar yamma ce yayi wurgi daita bata taɓa tsintar kanta cikin yanayi na tsoro irin na yau ba, sosai ta soma kuka tana rokonsa ," yana da kyau ki daina wannan banzar kukan naki dan ko mutuwa zakiyi sai kin bar gidan nan yau ke har ma rayuwata gaba-daya bana son jinki kusa dani ko dole Sai mun rayu tare"? ya k'arasa maganar yana huci ..
Kuka take tana girgiza masa kai ,ya kai hannusa ya damki kafarta ya shiga ja domin fitar daita daga gidan gbdy ta turje da iyakacin karfinta tare da rike wani karfe " dan Allah kada ka min haka haroon , kada ka fitar dani daga gidan nan, ban san inda zan nufa ba , ka duba rayuwata ka duba rayuwar yaranmu ban san inda zan nufa dasu ba yanuwana bazasu amsheni ba ,kayi hakuri na rokeka kayi wa darajan Allah ka barni , wani razananniyar tsawa ya buga mata tare da jefa daita batare daya yi la'akari da cikin jikinta ba, ya tsura mata idanunsa dake cike da matsanancin kiyayyarta yana huci " ke dai anyi jaka mara hankali ,ki tashi ki ɗauke waɗan shegun ya'yan naki ki bar min gida banason ganiku , dicter taki motsawa sai kuka take tana bashi hakuri haushin naci irin nata yasa ya sauke mata wani mari guda uku ajere tare da jan hannuta a lokacin sadiq da Aliyu dake wasa hankalinsu ya dawo gurinsu suka yi kanta suna kuka da iyakacin karfinsu, tsayawa yayi tare ta ta'be baki yana kallon yadda yaran ke kuka " ki san Allah ke da wannan dakin har abada dole ki barshi ya koma jikin kofar ya rufe ya zare key bai tsaya wata wata ba ya daga ƙafarsa daya ya buga kanta da bango take ta saki ƙara tana rike gefen kanta ya ja tsaki ya wuce , ta rungume yaranta ajikinta jikinsu na rawa tana kuka mai taba zuciya suna yaran suna kuka matan gidan suka yo kanta suna bata hakuri da bata shawarar ta koma gurin danginta babu abinda take sai girgiza musu kai zuciyarta na zafi har suka gaji da rarrashita suka kama gabansu .."

"Addu'a take son yi amman ta rasa wanne zatayi a ciki ta runtse idanunta gam Aliyu dake kwance ajikinta ya kai hannu ya goge mata hawaye shima kuka yake ta daura hannunta akanshi tana tsananin kaunar yaranta , babu abinda zuciyarta ke bukatar a lokacin kamar mahaifiyarta zantuttukan mahaifiyarta ne suka shiga dawo mata "A duk halin da kika tsinci kanki ki zamo mai hakuri da juriya tare da karbanr kowace irin qaddara daga allah Kiyi hakuri ki bi ra'ayinmu ki daina naci akan wannan yaron , ina rokonki da kibarshi ki ciresa aranki ki bashi dansa ko ki kaishi gurin danginsa domin kuwa babu abinda zaki tsinta a gurinsa sai wahala , wahalar dake zai yi ina rokonki da ki dinga zuwa church kina rokon Allah zaki ga sauki a cikin lamarinki babu komai a cikin muslimci da har zakiyi sha'awarsa, karki biyewa soyayya ki koma addinin Muslunci kaf zuriarmu babu muslimi me yasa zaki gurbata mana zuri'a ? ta janyo zaninta dake jikin kofar bukkan ta shimfida ta kwantar da Sadiq da yayi bacci ta zame ta kwanta sosai tana share kwallar dake zuba a idanunta sam alokacin da mahaifiyarta take mata magana hankalinta bai taba kawo mata zata tsinci kanta cikin rayuwa mai muni haka ta ɗauka idan haroon yaga abinda ta haifar masa zai sadaukar da komai ya rungumeta "yanzu me mene mafuta gareta tunda abubuwa sun rikice mata ta ko'ina babu dadi tana bukatar taimakon Allah wani ɓangare zata kama domin kaiwa Allah kukanta ,tana da sani sosai akan addinin Christian sabanin na muslinci da bata san komai ba hawaye suka cigaba zubo mata "ina son addininka haroon amman dole na fita daga cikinsa saboda ban san komai ba Allah kagani ko haroon ne silar komai ...."
"Allah ka saka min zalunci da haroon yayi min nida ya'yana , Allah idan ka tashi sakayya Karka saka akan yarana dan basu da laifin komai ka tsaida mugun halinsa akansa haka ta kasance kwance tana maganganu tana sharar hawaye ta kasa sabawa da rashin yan'uwanta da mahaifiyarta duk yadda suka tsaneta akan haroon da ƴaƴanta zuciyarta na makale dasu wani sabon kuka ne ya kufce mata duk sai gidan ya fice mata a rai tana nan kwance sala ta kawo mata abinci da ruwa "ki tashi ga abinci na kawo miki dicter ta mike zaune da kyar tana gyara wuyan rigarta daya yage ta amsa tare da yi mata godiya "bazata taba manta sala a rayuwarta ba tana taimaka mata tana bata abinci a duk sanda ta fahimci tana tattare da yunwa haka ma ƴaƴanta duk sanda suka shiga gurinta zata basu abinci, tashin sadiq tayi ta zaunar dashi ya zauna yana gyangyadi tasa kafarta daya ta bayansa dan kar ya fadi sannan ta tayar da Aliyu shima ta soma basu abinci a baki bayan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login