Showing 294001 words to 297000 words out of 495987 words
Chapter 99 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
zama cikakkiyar budurwa komai yaji ajikinta suna tsaye lawan ya shigo da akwatinta ta yatsina fuska kamar tayi magana sai kuma ta fasa tunawa datayi a gaban sahebarsa take ."
Jan akwatinta tayi ta nufi dakinsu ta shiga sai dai bata iske zee ba ,dan haka ta fada toilet ta watsa ruwa sannan ta sanya wata doguwar riga mara nauyi ta nufi shashin mumy tana tambayarta zee "tana makaranta zuwa anjima zaki ga "kisns ta yatsina fuska wanda ya rigada ya zame mata jiki sannan tace "gaskiya naija akwai ci baya mumy yanzu har na kare karatu na bar aunty zee ?" tayi fa kusan 2 year's kafin na bar kasar nan koda yake da taso da kun turata wata kasar itama ". haka ne zee ce akwai kulafin gida "kulafucin gida ko kulafucin son ya samir ? "Ban sani ba muje kici abinci, abinci kusan kala hudu taci suna hira da mumy sai bayan la'asar zee ta shigo da murnarta tun daga haraban gidan ta samu labarin dadowarta ta tsaya bayanta ta rufe mata idanuwa tana fadar "canki ?" Kai tsaye kisna ta kira sunanta cike da doki tayi dariya ta bude mata ido suna cikin haka sai ga aunty afra wata irin Kara ta saki sannan ta rungume kisna itama ta rungumeta "kisna kice haka ? "Kin ganki kuwa ? Kamar wata balarabiya ko ?"inji cewar zee "wallahi babu wani bambanci suka sa dariya gaba-daya har kisna afra ta ja hannun kisna zuwa ainihin parlour'n gidan yayinda zee ta shiga daki dan watsawa jikinta ruwa hira ta balle tsakanin aunty afra da kisna suna cikin hira kisna ta kalli afra tace "aunty afra ya naga kin Kara lalacewa fiyye da lokacin da nake kasar nan"? "wai meke damunki ne haka "? " Ko dai kina da matsala da yaya badamasi ne kika barwa cikinki kina azabtar da kanki a banza ?".. tayi mata tambayar ajere tana sake kafeta da idanunta domin jin abinda zata ce ganin tayi shiru ga yanayinta gbdy ya sauya alamun dai tana cikin damuwa yasa kisna kamo hannunta "plz tell aunty afra ki fada min damuwarki dan Allah ban ji dadin yadda naganki ba" "damuwata tana girman da bazan iya fada miki ba amman karki damu da sannu zan shawo kan komai ai dai kinsan auntynki babu sanya gurin dabaru "? Kisna ta gyada tana murmushi .."
Bayan aunty afra ta koma bangarenta zee ta fito ta shiga kitchen ita kuma ta koma daki ta kwanta ta soma tunani musa tsawon wasu awannni ta dauka tana tunaninsa ita kanta wani lokaci tana mamakin yadda girman son shi yake a zuciyarta ta yadda bata ita hadashi da kowa dan tana jinshi kmr rayuwarta ne a haka har bacci ya dauketa mai cike da mafarkinsa kala kala hayaniyar jamar gidan ne da suka dawo aiki ne ta tayarda ita daga naunauyen baccin daya sureta tun byn sallahr la'asar ga shi yanzu har an idar da magrib, madu ya shigo yana cewa "mutanen London kenan an dawo lafiya ?dariya tayi tace "lafiya ya madu na sameku lafiya ""
"Alhamdullahi kije inji mumy ta mike "ina zuwa" Toilet ta nufa ta dauro alwala tai sallar magarib da isha'i sannan ta fito zuciyarta na wani irin tsinkewa a lokacin data hango muradi a saman dining yana cin abinci qirjinta yayita bugawa kujerar da mumy ke zaune ta raba ta zauna ayangance tana fadar "mumy yauwa na manta daman ina son nace mai yasa ba'a turo ya Samir ko madu ko direba daukata ba sai wannan sauran kadan fa yau da gawata za'a kawo miki "
"na sha fada miki muradi ya wuce wannan agurinki yayanki ne fa "nifa yayyayena guda hudu ne fa ki daina sakashi a sahun yayyayena sannan shi ai yasan matsayinsa kece dai kike kai shi inda Allah bai kai shi ba "karki fara da bani ciwon kai kisna daga dawowarki ,yanzu ke ba yarinya bace "bari na sake tuna miki matsayin muradi ɗan yayana ne da muke ciki daya kamar yadda na sha fada miki "yaakayi har tsawon lokacin nan bamu taɓa ganin yayan naki ba wanda ya kasance mahaifinsa ? Wata tsawa mumy ta daka mata " kinsan banason tambaya ko maza tashi ki bar gurin nan tsorace ta mike ta nufi hanyar shiga dakinsu "ina zaki hajiya kayi ? yayi dauriya fadar haka dan kar mumy ta fahimci damuwarsa ta galla masa wata ƙatuwar harara . "dawo ki ci abincinki " yatsina fuska tayi a ranta tace baza'a dawo ba uban yan iyayi kawai ta koma ta zauna kan kujera kasa cigaba da cin abinci yayi ya tsura mata ido zuciyarsa na raya masa al'amura da dama sai da ya mike ya dawo kan kujera sannan ta dawo taci abinci..
Dady yayi matukar murna da dawo war kisna ,ganinta zaune akan kujera ga alamun natsuwa a tattare daita yasa zuciyarsa samun natsuwa "auta ya furta a hankali jin muryar dady ya sakata tsalle ta nufo inda yake a guje tana kiran "dady nah !dady na!! Ta fada jikinsa tana faman kyalkyala masa dariya yace "mamana sannu dawowa fatan an kare karatu lafiya ? A shagwabe "tace lafiya lau dady tun dazu nake jiran dadowarka "to yanzu gani na dawo bari naje na watsa ruwa maza ki fito min da tsarabata kafin na dawo tayi murmushin jin dadi tana gyada masa kai ,daki ta koma cike da doki ta fito da akwatin data zo dashi a lokacin Samir madu muradi har ma da zee suna zaune ana chapter ta zauna ta bude ta soma raba tsaraba ta bawa Kowa nashi ta cire wa masu aikin gidan ta kirasu ta basu hatta baba mai gadi ta cire masa nashi amman banda muradi duk suka tsura mata ido har ta gama sannan samir yace "ina tsaraban muradi naga kin bawa Kowa ban dashi ta dube shi sosai fuskarta a hade "wane ne haka kuma ya Samir ? "Kina hauka ne ni zaki tambaya waye shi ? Yayi mata tambayar a kufule kamar zai wanka mata mari "ni ban san shi ba dan haka banyo tsarabata dashi ba kamar jira suke ta fadi haka gaba-daya suka dawo mata da tsarabanta suka mike tsaye suka barta daga ita sai muradi wanda ko kallon inda take bai yi ba, harkokinsa yake akan system dan kallonta ma na sashi jin matsanancin faduwar gaba tsaki taja ta mike "aikin banza sai me idan kun dawo min dashi me zai dameni ? "Babu abinda zai dameni sai ma wasu da zasu mora ta kwashi na dady ta nufi bangarensa a daidai lokacin daya gama shirinsa yana ganinta ya fadada fuskarshi da murmushi "duk tsarabata ce wannan mamana ?kisna ta gyada masa kai sannan ta zube kayan akan kujera "gaskiya mamana na gode nima kuwa zan miki kyakkyawan tukuici tare da neman alfarma agurinki ya kamota ya zaunar daita shima ya zauna "maman kin kara girma kinyi kyau tayi murmushi tace "haka kowa yake cewa "wannan gaskiya ne idan na natsa akwai magana mai mahimmanci da zan yi dake nasan zaki fahimceni da kunnen baseera tunda ga dukkanin alamun mamana tasan ciwon kanta yanzu "ta sake gyada masa kai kusan minti goma suna magana su Samir kuwa suna dakin mumy babu wanda bai zage kisna ba ",wallahi mumy har yanzu kisna na nan da mugun halinta sam zuciyarta bai da kyau na rasa abinda muradi yayi mata data dauki karan tsana ta daura masa inji cewar madu "babu abinda ya mata da ikon Allah mugun halinta akan zai kare duk ku fita harkar shegiya ta karasa maganar tana fitowa .
a nan dakin dady mumy ta biyosa da abincinsa tana zabgawa kisna harara take tasha jinin jikinta "ya da hararar min uwa kuma daga dawowarta ? "ai tasan abinda tayi kuma wallahi idan bata canza manufarta akan muradi ba kowa zai ji mu daita a gidan nan "ta fadi haka tana sake zabga mata harara ",wani abu ne ya faru ? "Gaskiya nima akan Aliyu zamu samu matsala mamana ganin sun hade mata kai sai fadar yadda suke qaunar muradi suke yasa simi simi ta bar musu dakin suje su karata bata masa tsaraba kuma babu wanda ya isa yasa ta bashi .."
Yau kwana uku da dawowar kisna amman babu mai shiga lamarinta duk wanda tayiwa magana baya kulata kowa ya dauke mata wuta akan abinda tayi itama ta sharesu amman samun kiran musa da tayi yana son ganinta a waya itama kuma tana son ganinsa wannan dalili yasa ta saki fuskarta sosai da kowa amman still babu wanda ya waiwayeta ta bawa zee hakuri "kiyi hakuri aunty zee daga fushin da kuke yi dani "to ke din ce baki da kirki ai ba'a yin haka ya Aliyu na matukar kula da rayuwarki tun kafin ki bar kasar nan har zuwa sanda kika dawo duk kudin da za'a aika miki London daga aljihunsa yake fita shine mutumin daya tsaya bisa lamuranki ta ya zaki bawa Kowa abu ki hanashi muji dadi bayan har masu aiki kin bawa?" "naji nayi kuskure ni yanzu bana son na samu matsala da kowa a gidan nan muje ki rakani na bawa ya Samir hakuri da kyar ta lallaba zee ta tajata dakinsu ta bashi hakuri yace "muddin kina son na hakura sai kin bawa muradi hakuri "muryarta a raunane tace "kayu hakuri "yayi kamar bada shi take magana ba har sai da ta sake maimaitawa "wuce " ya fada atakaice batare daya kalleta ba kai tsaye daga dakinsu na mumy suka shiga dan bata hakuri itama fada tayi mata sosai sannan tace ya wuce amman ki canza "naji mumy .."
******
Washegari gidan ya hargitse da farinciki kowa ya saki ranshi sai chapter suke a tsakaninsu har dady dake kokarin fita office tare dasu Samir kisna ta mike bari naje na shirya zanje gidan granny ta shirya ta fito cikin wata hadaddiyar doguwar riga bata ga dady ba da su ya Samir da alamun sun fita zuwa office "mumy bani mukulin motarki zanje gidan granny na dawo " mumy ta girgiza mata kai "ban yarda ba kuma kice zakiyi diraving da kanki sai dai ki bari direba ya kaiki idan kina so kenan cikin jin haushi tace "na yarda mumy ta kira lawan ta bashi umarnin ya kai kisna gidan Hajiya aysha kuma ya tsaya har ta gama ya dawo daita ya amsa mata da "to" yayi gaba ta biyo bayansa har haraban gidan ya bude mata baya a natse yake yin komai saboda yana da labarinta agurin mai baba gadi daya zama kamar dan'uwa yanzu a gurin Alhaji realwan .
suna fita daga gidan tace "dauki hanyar agege ogba yayi mamakin jin abinda tace Idanunshi ya dago ta glass din cikin motar ya kalleta sosai domin jin karin bayani "kallon me kake min ko bazayi abinda nace bane ? Muryarsa a sanyaye yace "zanyi sai dai Hajiya ......"shiiiiiii muje kawai inda nace kwarjininta ya hanashi musamata ya cigaba da tuki yana mamakinta ta ciro wayarta ta kira number musa tace su hadu dashi a ogba garding , basu dade da zuwa ba ya karaso akan mashin ta mike tsaye daga zaunen da take suka rungume juna har da manna mata kiss a baki rayuwar yoroba dai sak kisna keyi da musa tana biye masa ga abinda yake bukata sannan suka zauna tsuru lawan direba yayi yana kallon daga inda yake lamarinta yafi karfin tunaninsa yar muslima daita take irin wannan rayuwar "?
cikin wata irin kasala Musa ya riko laulausan tafin hannuta cikin nashi yana murzawa a hankali tare da tsura mata Idanunshi itama tsura masa ido tayi har bata son kiftawa wani Murmushin jin dadi ya sakar mata itama bata san sanda ta sakar masa ba " yaushe zamuyi aure ifemi ?" ina son muyi aure saboda bana son wani ya kwace min ke dan jikina ya soma bani saboda wannan kyaun da kikayi da wuya ace tun dawowarki wani bai ce yana sonki da aure ba, kinyi kyau sosai kamar wacce ta fado daga sama ya karasa maganar yana shafa saman kirjinta kuma duk akan idanun direba daya dawo tamkar wawa a inda yake labe yana lekansu wani irin yanayi ta tsinci kanta gaba-daya tsigar jikinta suka mike ta Lumshe masa ido tana sake jin kaunarsa "naji dadi sosai ifemi da kai yi nasarar hasashen abinda ke zuciyata ina son muyi aure very soon "ya numfasa sannan yace "to da farko dai a shirye ni yanzu nake damin abinda zan rikeki Allah ya hore min aikina na bogilari zai ishemu idan bai ishemu ba ga karatunki wanda nasan saboda ni da yaranmu kika yi shi " ta gyada masa kai alamun haka ne maganarsa. sun dade suna tautaunawa akan yadda zasu yi aure daga karshe ta ciro dalolin kudi masu yawa ta bashi "gashi kaje ka siya mota domin nan gaba kadan zamu daina haduwa a waje zaka dinga zuwa gidanmu kamar zai hadiyeta dan murna sai da batun zuwa gidansu ya dan razanashi tare suka jero suna magana "ifemi ina jin tsoron nufar kofar gidanku "be a mana ifemi nima na tattara tsoro na watsar bare kai boye boye bazai kai mu ba gara asan muna tare "wannan kuma haka "dan haka ka sanyawa jikinki jarumta ka kuma cire tsoro muddin kana son aurena "angama ifemi ina alfahari dake har jikin mota ya rakata tare da bude mata ta shiga ya sanyo jikinsa ya kamo bakinta ya tsotsa son ranshi sannan ya fito ya rufe mata murfin motar ya hau machin ya wuce tana jiran lawan direba bayan yazo suka dauki hanyar gida akan hanyarsu tace su wuce gidan hajiya aysha da sallama ta shigo parlourn Hajiya aysha " a'a sakina ce ? Kisna tayi murmushi tana fadar "nice tunda baki zo min sannu da zuwa ba gashi ni nazo nuratu jika ce ga granny diyar mace ce ta fito daga daki a guje tana ihu murna suka rungume juna da kisna hjy tayi murmushi "yar nema anki anzo din " nuratu ta jata suka shige daki saman gado suka haye nan fa hira ta balle ta yaushe gano nuratu ta dinga bin kisan da kallo har ta tsargu ta zungureta tana cewa "ya dai mutuniyar na canza miki ne da kike kallona "allahumarzukuni fi miji na gari wallahi sakina kinyi kyau kin kuwa ga yadda kika hadu ?" Kisna taja tsaki in dai irin wannan maganar ce har tagaji da jinta a bakin mutane har ta dawo bata jin dadinta nuratu tace "ai kinyi ne wallahi ina ma namiji ce ni da wallahi sai na aure ki wata irin dariya kisna tasa suka tafa tace "gaskiya nuratu baki dama ana ta bata lokaci sosai sannan suka wuce gida haka duk bayan kwana biyu zata shirya tace zata gidan hajiya aysha alhalin ba gidan take zuwa kai tsaye ba sai ta gama da musa zuwa guraren shakatawa sai su dauki awanin kafin su rabu sannan ta nufi gidan granny .
A wata safiyar monday tafiya ta kama muradi zuwa Abuja kwananshi biyu ya dawo da misalin karfe goma na dare yana sanyo hancin motarsa unguwarsu idanunsa suka ci karo da mugun abu domin kuwa wata kyakkyawar fuska ya hango cikin mota Camry tana manne da fuskar namiji da bai san kowaye ba suna tsotsan bakin juna da fari har zai rage hasken motarsa sai ya fasa ya sake kara haske sai da yayi kusa dasu sosai sannan ya fahimci kisna ce da Musa suke makake da juna suna shan bakin juna ,hasken fitilar motarsa yasa suka dawo haiyacinsu ta gefen motarsu ya wuce gabansa na faduwa sannan yana jin babu dadi tare da tausayin iyayenta sai dai ya kudurta bazaa ji komai a bakinsa ba yayi mata addu'a yayi hon aka bude masa ya shiga babu kowa a parlour'n ya shiga ɗakinta mumy bai ganta ba da alamun tana dakin dady ya leka dakin su zee tana kwance itama bacci take ya fito ya haura sama nan ma madu da Samir suna cikin kowane yana lamarin gabansa nan take ya fahimci rashin su a parlour'n ya bawa kisna damar fita a lokacin ya shiga wanka ya fito ya sauya kaya ya fito yana bawa mai gadi umarnin kar ta sake barin kisna ta fita da zarar isha'i ta wuce yace "an gama dan albarka "
kisna na zaune dady yayi mata kyautar mukulin mota yace idan zataje gidan hajiya ba sai an kaita data mumy ba tayi farinciki tare da yi masa godiya ta fito haraban gidan ta duba motar taga irin wacce take so ce 4mart ta dawo parlour'n da sauri "dady gaskiya ka burgeni yaakayi kasan irin motar da nake so ? "nifa babanki ne duk abinda zai min nasan zaiwa mamana ta rungumeshi ajikinta "thank you my dad Allah ya Kara budi "ameen kisna fatana ki zauna lafiya har zuwa sanda zee zata karasa karatunta a saida maganar aurenku ta sake rungumeshi saboda jin dadi ga dama ta samu da zarar an tambayeta miji Musa zata kawo ta sausata rungumar da tayi masa "dady kace akwai magana mai mahimmanci da zamuyi har yanzu ka min shiru "kaiki damu nan kusa zan yi miki fatan bazaki zuba min kasa a ido ba ? ta girgiza masa kai ya shafa fuskarta tare da nufar hanyar step ..."
A cikin wannan satin direba ya tuka kisna zuwa gurin musa sun dauki lokaci sosai basu dawo ba har dady ya dawo gida ya kira direba a waya ya tambayesa inda suke yace "suna wani guri a ogba yayi shiru ya kasa cewa komai sai wajen karfe takwas da wasu mintuna suka dawo gidan tayiwa mumy sannu da gida ta shige daki ta afka toilet mumy ta mike ta fito dady dake tsaye a bancoly dinsa ya mike ya sauko kai tsaye haraban gidan ya nufa ya kira direba "karka boye min komai ina ka kai kisna yau ?"direba bai boye masa komai ya fada masa gaskiyar inda yake kaita a duk sanda suka fita da zumar zuwa gidan hajiya aysha dady ya zuba masa ido kawai yana kallonsa yana jin wani zallar ɓacin rai na ratsashi hawaye na bin kuncinsa ji