Showing 48001 words to 51000 words out of 495987 words
Chapter 17 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
masa banza ya dauke masa wuta a karshe ma ya mike ya nufi kofar fita shima ya mike da sauri ya biyosa wata irin zufa na karyo masa a goshi tamkar wanda aka watsawa ruwan sanyi a daidai kofar shiga parlou'n Samir ya sha gabansa yana kallonsa yana furzar da iska ,a hankali ya kamo lip's dinsa na kasa yana cizawa yana cigaba da kallonsa ganin bashi da niyyar cewa wani abu Samir ya raba gefensa zai wuce ya sake taresa
"haba Samir mai yasa zaka min haka ? "Yanzu saboda kisna zaka juya min baya kenan kana jin zafin abinda nayi mata bayan kai sheida ne akan......"
Numfashi Samir ya sauke tare da katse masa hanzari ta hanyar cewa "Ba haka bane muradi wannan accedent din daya faru ba laifin kisna a ciki amman kaki ka daga mata kafa, karka manta hakan zai iya faruwa akanka akan kowa duk abinda zakawa kisna nawa ido ne amman akan wannan ko ba kisna kake aure ba zan ji babu dadi a raina , Aliyu ya kamo hannun Samir ya rike gam cikin nashi "to kayi hakuri kasan yadda zuciyata take idan raina ya ɓaci am really sorry ka daina fushi dani zan iya jurar komai ban da fushinka rungumeshi Samir yayi ajikinsa yana sauke numfashi "kai ma kasan bazan iya dogon fushi da kai ba, jiya zuwa yau ne gobe da kaina zan nemeka suka sake juna suka karasa cikin parlou'n suna magana kasa kasa ."
A can sama kuwa , kisna da aunty zee sun kulle kansu a daki kisna na koro mata abinda ya faru d'azu "ina tsananin jin tsoron hukuncinsa , aunty zee ki taimakeni dan Allah ki tayani addu'a Allah ya bani ikon cin jarabawa , kiyi min nasiha aunty zee ko zanji sanyi zuciyata na zafi kamar zata tarwatse ta kamo hannunta ta dauka daidai saitin zuciyarta ,a matukar fusace aunty zee tace mai yasa kisna bayan kinsan halin zuciyarsa zai iya aikata komai mai yasa kika ce ya baki takardanki gaskiya baki kyauta min ba bana son kina yin haka mahakurci mawadaci fa ki daina biye masa dan shi abinda yake so kenan ya dagaki a gindin yaranki ya bawa wata"wallahi don inji sanyi ne Kuma ai bazan sake ba "shikenan inshallahu Allah zai duba lamarin "Ameeen abinda nike so daga gareki kenan don Ina jinki aunty zee a raina don Allah ki kwantar mun da hankili bani da natsuwa kawai dauriya nake ta karasa maganar hawaye na silalo mata "Kiyi mun nasiha irin Wanda Kika saba min Ki fada mun gaskiya komai dacin ta a yanzu a shirye nake da amsar duk wata nasiharki ,
" Sannan Kiyi mun addua
Wallahi nasan duniyan nan ba matabbata bace don Allah ki gayamun gaskiyan abunda ubangiji yace Koda Raina zai baci nafison ki gayamun abunda zai sa in tsira duniya da lahira Don Allah yar'uwata karki barni a wannan lokacin Ina matukar bukatan shawaran ki na gari Wanda zai anfane ni plsssss "Kisna aunty zeey ta kirata a tsanake ta d'ago idanunta dake cike da ruwan hawaye ta zuba mata batare data amsa ba sai dai tattara hankalinta da natsuwarta gareta " Allah yace idan ya ƙaddara maka zaman aure da mijinka ka rikeshi tsakani da Allah kuma da zuciya kada ka cutar dashi kuma kada ka nufesa da mugun sharri ina miki nasiha kamar yadda kika bukata ki zauna da mijinki tsakani da Allah Karki sake ganganci cewa ya sakeki
Ki zauna dashi da zuciya domin shi kanshi furta sakin zunubi ne ki barshi shi yayita cewa zai sakeki abinda kika sani duk matar da tace mijinta ya saketa Mala'iku rahma na tsine mata dan haka ina miki nasihan ki daina
" Insha Allah na Miki wannan alkawarin na gode na gode yar'uwata " aunty zeey ta mike tsaye "ni zan wuce ki dan huta kafin lokacin fitarmu yayi "anya zan iya fitar nan kuwa da ma barshi kawai ?
"baki da hankali dan Allah ki kwanta ki huta kafin yamma tayi zan wuce dasu areef ma dan karsu dameki ".
*****"
da yamma duk suka shirya kisna ma ta shirya cikin riga da siket wanda ya ɗan kama jikinta ta d'aura abaya a saman kayan ta nad'e kanta da mayafin abayar ,tana tsaye gaban mirrow ya shigo d'akin ya bude wardrobe dinsa kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta hankalinta ya rabu gida biyu wani naga mirrow wani na garesa ya dauki kayan da zai sauya ya rufe wordrobe ya shiga bathoroom ya sauya kaya ya fito ya tsaya a bayanta ta lumshe ido saboda saukar numfashinsa da taji a daidai saitin wuyanta ,ya dauki cumb ya hau gyara sumar kanshi bayan ya gama ya zuba mata ido ta cikin mirrow batare daya ce komai ba jikinta ne ya bata ita yake kallo ta d'ago kanta a hankali idanunsu suka tsarke cikin juna sake matsota yayi sosai kamar zai hadeta da jikinsa take ta sadaukar da hakan ce zai faru sai dai abun mamaki taji yaja dogon tsaki ya zagayeta ya ajiye cumb din hannunsa ya juya wani naunauyen ajiyar zuciya ta sauke tana satar kallonsa tana karasa shirinta har ya gama ya fita yana jan tsaki , tana kokarin fitowa aunty zee ta shigo "wooooowwww gaskiya kinyi kyau sosai "? Kyan banza tunda wanda akayi dominsa ma bai san ayi ba "karki damu ko bai furta ba yaji dadi bazai dai nuna miki bane kinga muje ke kadai ake jira ta riko hannuta suka fita .."
Kai tsaye *sharma sheik* suka nufa had'ad'd'en guri ne daya fi ko wani gurin shakatawa a kasar misra tsari da kyau ,guri ne wanda ko turawa idan sun kawo wa kasar ziyara nan suka fi hallarta saboda tsaruwansa ,duk wani abu na shakatawa akwai shi a gurin ,tunda suka shiga gurin aryan ya makale mata yayinda areef ke rungume a kafad'an Aliyu suka nufi wani bangare dabam dan shi babu inda bai sani ba aguri, yawon zuwan da yake ne ma suka haɗu da nawal .."
A hankali take rausaya wanda daman haka tafiyarta take aryan na rike da hannunta tana kallon yanayi gurin ,
mutane kala dabam dabam ne gurin kowa rayuwarsa yake babu ruwan wani dani har ta karaso inda aka kilance domin wasan yara ta shiga aryan na rike da hannuta gam yana ganin inda suka shigo murnarsa ta k'aru uwa uba hango lilo da yayi ,ya fixge hannunsa dake rike cikin nata ya kwasa aguje taku biyu tayi ta damko shi ta daga shi sama "zaka hau lilo ne babana "? Ya gyada mata kai alamun "eh .
"okay kabi a hankali zan kai ka da kaina kaji babana ya sake gyada mata kai sai dai jikinsa har rawa yake ya matsu basu karasa gurin lilon ba ,a natse ta karasa ta d'aurasa ya saki murmushin jin dadi wanda har fararen hakoransa da dumple dinsa suka bayyana, ya tafi suuuuuu ya sauka ya sake dawowa da gudu "mommy sake d'aurani " ta sake daukarsa ta d'aurashi tana sakar masa murmushi "mommy ina areef kije ki amso shi guri papa shi shima ya hau lilo "papa zai kawo shi karka damu yarona tana cikin magana ta jiyo kamshin turarensa ko bata d'ago kanta ba tasan mammalakin kamshin dan haka taki d'agowa ta kamo hannu aryan tana jin sautin muryar areef yana kiran aryan amman taki tsayawa dan bata son tashin hankali tunda duk suka kasance sai yayi abinda ya bata mata rai suka nufi wani guri ta tsaya hannunta daya dafe da kafad'an aryan suna kallon larabawa ."
A hankali wani mutumi ya zo ya tsaya kusa da kafad'anta wanda sauran kaɗan kafadunsu ya hadu da juna ta waigo a hankali suka hada ido ya kashe mata idonsa daya "sannu ko " yayi magana cikin harshen larabci saboda siffarta gabad'aya ta nuna masa balarabiya ce , cikin sanyayyiyar muryarta tace " ban fahimci abinda kace ba cikin harshen Ingilishi tana matsawa daga kusa dashi , jin abinda tace ya sake motsata sosai kamar zai rungumota "Masha Allah a she yar kasar ku ce "ko zan iya sanin sunan malamar tun da kika shigo gurin nan naji kin kwanta min a rai ko zaki iya bani dama na mallaki zuciyarki "?a matukar frigice ta waiga bayanta ganin Aliyu bai gurin ta sake maida idanunta kanshi tare da cewa "no.." sannan ta bar gurin da sauri tana tafiya tana waigen bayanta kawai ta ji tayi karo da mutun a matukar firgice ta furkanci mutumin da suka yi karo ba kowa bane illa Aliyu gabanta yayi wani mahaukacin bugu ganin har wayar hannunsa ta subuce kasa tayi saurin dukuwa shima ya duka tana daura hannunta akan wayar hannunsa na sauka akan nata a tare suka d'ago suna kallon juna , qirjinsu ne ya buga a tare kusan second goma suna kallon juna kafin daga baya yayi saurin mikewa kamar wanda yaga mugun abu ,"bashi wayarsa muje ki bani minti biyu kacal ma ya isheni ,damuwata nasan inda kike a matukar tsorace ta mike tsaye jikinsa na rawa ta mikawa aliyu wayarsa batare data yiwa mutumin magana ba, sai dai yanayin bugawar zuciyarta sai ya baka tsoro saboda da karfi yake bugawa jikinta sai rawa yake , kasa amsar wayar yayi ya kamo gefen lip's dinsa ya ciza da karfi yana kallon zara zaran yatsun kafafunsa sai areef ne yasa hannu ya amsa wayar ,kana ya kai dayan hannunsa ya yaja kumatun aryan yana masa murmushi ."
Aryan ya sakar masa murnushin shima "na hau lilo kace pa........Tun bai kai ga karasa maganar ba ta soma tafiya dashi , mutumin ya kasa biyota saboda ganin kamar Aliyu muradi ne tsaye a gabansa dan wasan kwallon daya fi so a rayuwarsa kuma wanda duniya take ji dashi siyansa ma sai kasa ta shirya yana ƙoƙarin masa magana Aliyu ya bar gurin babu shiri ya biyo kisna yana mata magana jikinta da zuciyarta dake rawa yasa ta kasa saidashi sannan ta kasa tsayawa bare ta sheida masa matsayinta , bata tsaya a ko'ina ba sai a haraban gurin inda ta hango aunty zee da ya Samir jingine ajikinsa mota suna shan ice cream ta karasa gurinsu da sauri tana sauke numfashi "ke lafiyarki"? Aunty ta fada tana dubanta ta janyo hannunta aunty zee suka koma gefe "Kalli bayana zaki ga wani mutumi sanye da kaya ash colour"
"Eh na ganshi lafiya me ye hadinki dashi "?"Bina yake wai na bashi address din inda nake ko na bashi number wayata kuma wallahi ya Aliyu ya ganshi ni tsoro nake ji Kar ya nuna min halinsa da rashin mutuncinsa a cikin mutane aunty zee dan Allah muyi mu bar gurin nan tsoro nake ji ."
aunty zee tayi dariya " ya Aliyu yayi masa magana ne daya ganku"?
"Bai ce mana komai ba hasalima bai nuna ya damu ba "sharesa kawai ki kwantar da hankalinki ki cigaba da lamuran gabanki kema ki nuna ko ajikinki shi dake aurenki ma bai damu ba saboda me ke zaki damu ?" Dan Allah aunty zee wallahi tsoro nake ji "Common saki jikinki dan daga nan ma shopping zamu ina bukatar ƙananan kaya "dawowa sukayi gurin Samir "gulmar me kuka je kuka yi dan bakwai rabowa da gulma "? "kai kuma baka rabo da saka wa mutane ido ba suka yi dariya banda kisna data rasa natsuwarta Aliyu bai karaso gurin ba sai bayan minti goma ya fito yana taku kamar baya son taka kasa ya shiga mota batare da yayi musu magana ba yayiwa motar key "kai kai malam meye haka tafiya zakayi ka bar mu anan ko me kake nufi "?
Samir yayi magana tare da lekowa cikin motar "idan baku shigo ba zan wuce wallahi sanin halinsa yasa ya buɗe motar da sauri yana cewa" ku shigo muje wannan sarkin zuciyar ya hau sama ko wa ya kunnosa oho?.
jiki kisna a sanyaye ta shiga gidan baya idan aunty zee ke zaune hira Samir yake masa amman yayi masa banza aunty zeey tace "ranka shi dade dan allah ina son siyan wasu dogayen riguna .Aliyu bai ce mata komai ba sai gani tayi ya faka a bakin *kaafor mall* batare da yace uffan ba .
"muje kisna bani da abinda zan siya aunty " tayi magana muryarta can kasa "Ke dai muje ta bude bangaren da take ta fito suka shiga rike da hannun aryan ."
Samir yace Aliyu tun d'azu ina maka magana amman ka shareni me yasa kake takurawa rayuwarka ne kana son kisna me yasa bazaka manta komai kuyi rayuwarku ba tsaki yaja "dan Allah karka daga min hankali banason damuwa " malam ka bada kai bori ya hau kaima ka dinga shiga sawun ........
"Please Samir mai yasa har yanzu ka kasa fahimtata ne ?sanin kanka ne soyayya bata gabana ko nawal daka ga zan aura tausayi ne yasa zan aureta ba wai soyayya ba, idan kuma soyayyar zanyi kisna bata cikin jerin matan da zan iya so kayi hakuri idan maganata ta maka ciwo "
Tsaki Samir ya ja "dadina da kai wallahi taurin kai kamar mutanen farko yarinya tana sonka yanzu ka bata dama kaki " takaici ya rufewa Aliyu zuciya ya bude murfin kofa da karfi ya fito a kufule tare da saba areef a kafad'ansa Samir ya biyo bayansa yana cewa "gaskiya lamarinka akwai gyara ana gabas kana yamma kana bukatar addu'a Allah zan fadawa momy ta mike tsaye a samu ka soma soyayya "dan Allah ka rabani da batun soyayyar nan bani da lokacinta ...."
Cikin mall din suka shiga kai tsaye Aliyu yayi layin takalman yara suna tafiya suna hira da Samir har suka karaso kusa dasu aunty zee, muryarsa tasa ta jujowa idanunta ya sauka akan Samir "baby ta kira sunansa ya waigo da hannu tayi masa alamar yazo ya karaso ya tsaya a bayanta tare da daura kanshi a kafadanta "ta yani zabar kanana kaya kema kisna Ki zabi wanda kike so yayanki ya biya ,kananan kaya masu yawan gaske da dogayen riguna masu kyau ta dinga ɗauka ,duk abinda ta gani indai ya burgeta sai ta ɗauka ganin kisna ta ki ɗaukar komai ,yasa ta dinga zabar mata bom short da riguna masu kyau wanda zasu dauki hankalin mijinta sannan suka kara gaba suka bar kisna dake tsaye rike da hannun aryan kamar ance ta juya bayanta idanunta ya sauka akan mutumin d'azu yana tsaye rungume da hannuwansa duka a qirji ,tsura masa ido tayi tana kallonsa mutun kamar aljani har zata bar gurin taga gara kawai ta tsaya ta fada masa gaskiyar ita din matar aure ce ya daina binta a hankali ya karaso ya tsaya a gabanta yana kare mata Kallon tsab irin typing din matar da yake so ce ya dade yana neman irinta bai samu ba sai yau sautin muryarsa taji ta doki kunneta "tunda nake arayuwata ban taba ganin halittar data ɗauki hankali ba irinki dan Allah kibani dama na zamo abokin rayuwarki, farinciki da bakinciki ne suka hade mata a lokaci daya ,ga mijinta na tsananin nuna mata kiyayya ,ga wani na mata naci ta so shi wanda a yan sakonin da suka gabata ya daura idonsa akanta batare da yasan ko ita din wacece ba ."
Ta tsuke karamin bakinta gashi dai magana take son yi amman ta kasa sarrafa harshenta kawai ta juya zata wuce yayi saurin shan gabanta " ki tsaya ki faɗa min sunanki da address din inda kike kafin ki wuce dan bazan bari ki subuce min ba saboda na dade ina nema irinki ...."😳
Mmn sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: .💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Free page 11
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...🥰🥰
A matukar harzuke ta shiga dakin zuciyarta kamar ta kama da wuta , tana k'arasa shiga cikin filin d'akin idanunta ya sauka akanshi tsaye a tsakiyar d'akin ya zuba hannunwansa duka a cikin aljihun wandonsa yayinda idanunshi ke runtse yana ciza gefen lip's dinsa na kasa a hankali , duk da bai bude idanunsa ba yasan itace ta shigo dakin duba ga yanayin da yaji bugun zuciyarsa ya qaru."
kallon second biyu tayi masa ta ɗauke idanunta akan shi ta k'arasa da sauri ta bude wardrobe ta dauko akwatin kayanta data zo dashi kasar ta ajiye akan gado ta bude ta soma dibo kayanta ɗaya bayan ɗaya tana zuba aciki ,still bai bude idanunshi ya kalleta ba bare ya dakatar daita daga abinda take ƙoƙarin yi ya cigaba da ciza lip's dinsa , hakan yasa taji sabon ɓacin rai ya mamaye zuciyarta taji muddin bata bar masa gidan a lokacin ba zata iya mutuwa.."
Aunty zee ta shigo dakin cikin tsananin tashin hankali ta k'arasa gareta ta rike hannuta batare da ta kalli inda Aliyu ke tsaye ba hankalinta a matukar tashe ta soma magana "mai kike ƙoƙarin yin saboda Allah ? "Kiyi hakuri mana
duk fa abun bai kai haka ba, idan fa rai ya ɓaci hankali baya bata kisna , ki dawo hankali ki natsu dan girman Allah Karki yi abinda zai janyo bacin rai fiyye da wanda muke ciki yanzu ".Tun da aunty zee ta soma magana kisan bata furta komai ba ta cigaba da zuba kayanta cikin akwati zuciyar na wani irin zafi da ciwo , haka shima Aliyu bai ce komai ba sai sake juya musu bayansa yayi yana furzar da iska mai