Showing 402001 words to 405000 words out of 495987 words

Chapter 135 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

ya sha kanta taja ɗan karamin table din glas dake tsakiyar falon ta d'aura kular abinci akai ta zuba masa abinci cikin plet tasa spoon murya a sanyaye tace " ga abinci nan inji mumy ta fadi haka ne dan yaci amman ya shareta ya cigaba da wayarsa ta dawo ta bayansa tana son yi masa magana akan ya yafe mata abinda tayi masa sai dai tana jin tsoron yadda zai bata amsa a hankali ya janyo computer dinsa ya kunna gabanta ne yayi mummunar faduwa sakamakon ganin hoton wata da bata san ko wacece ba a fuskar screen dinsa ta sha make up idanuta manne da space , shiru tayi na minti goma tana kallonta sannan tace "bari na shiga na gyara maka d'aki shima banza yayi mata ta shiga ta gyara ko'ina ta fito har lokacin bai kalli inda plet din abinci yake ba "baka ci abinci ba " tayi magana gabanta na faduwa "wani irin dagowa yayi ya zuba mata Idanunshi masu firgitata yanzu ,sannan yayi mata wani kallon rainin hankali wanda yasa jikinta ya kama rawa sannan ya fara magana a dake cikin zafin zuciya " ni ne zanci wani abu daga hannunki?,haka kawai kije ki zuba min shinkafar bera idan kina tunanin akwai ranar da hakan zai faru ki daina dan har abada bazan ci abincin hannunki ba , ke wai ma me yasa kika min magana ne ?" baki ga alamun bana bukatar komai daga gareki ba, to be your first and last da zaki sake min magana ko yi min tayin wani banzan abincinki "yana gama fadar haka ya mike ya shige bedroom dinsa ya barta tsaye cike da tausayawa kanta kusan min goma tana tsaye tana sauke numfashi sannan ta fita kai tsaye dakinta ta nufa ta shiga zariya a dakin kwakwaluwarta na neman mafita ita ko bazai cigaba da rayuwa daita ba ya bata dama ta rokeshi gafara ."

Bayan kwana biyu
da yamma yana zaune yayiwa yan'uwansa maza da mata alert din kudi maza 2 million mata 1million yace kowacce tayi tsaraba dashi kasancewar bai yo musu tsaraba cikin farinciki aunty ummi ta kira shi tana masa godiya"haba aunty ummi ki daina min godiya a duk sanda nayi miki wani abu "to Allah ya raya su Aryan dan nasan zuwa yanzu kasan komai "numfashi ya sauke yace " kasa hakuri nayi na tambayi dady dan kamarmu da yaran ta ɓaci ,ai kinyi forcub aunty ummi da kin kirani kin min albishir samunsu wallahi da sai abinda kika zaba zan baki tukuici "umarnin dady muka bi, yanzu ma nasan idan rabona ya rantse zan samu "okay ki fara tunanin irin business din da zaku kedasu zahra ina son kafin na koma zan baku jari kedasu "Masha Allah ai kuwa mun gode suma ina tayasu godiya kafin su kira . " Kuyi tunani mai kyau dan da zarar an gama bikin madu zan wuce "to kai fa sai yaushe naka auren naji mumy tace ka samu wata ? "eh to na samu amman gaskiya ba yanzu ba sai nan da shekara biyu "karka ce haka rayuwar babu tabbas muradi nan suka ci-gaba da tautaunawa daga karshe sukayi sallama
Bayan sati daya ya tattara ta koma westwood hotel da zama saboda baya qaunar ganin kisna dan ya lura bakinta akwai magana shi kuma baya son abinda zai sake hadasu, bancin daranjan su mumy da yaransa da ma daina zuwa gidan har abada ."

da misalin karfe shida sai ga jabir abokin madu yazo gurinsa dan yana son su tautauna akan biki kasancewar shine babban abokinsa sai dai bai samesa a gida ba hasalima falon babu kowa daga kisna sai twins ya kamo twins yana wasa dasu suka gaisa da kisna bayan sun gaisa yace tazo waje yana son ganinta babu mutsu ta mike ta fito twins na biye daita har inda yake tsaye jikin motarsa ya kalleta sama da kasa ya kalli yaranta yana murmushi yace "gaskiya kisna kin iya haihuwa , yaran nan nada matukar kyau ga shiga rai ,"na gode sosai "ko zaki bani su ?tayi murmushi wanda yake bayyana ainihin kyawunta sannan tace "babu matsala an baka ,ina godiya kuwa "Malama kisna ya shirye shiryen bikin ? "alhamdulillah nan dai ya fara janta da hira har ya fito mata da manufarsa "babu zancen boye boye kisna ina matukar sonki kuma da aure ina fatan zan samu karɓuwa suna cikin magana taga kamar an dauki daya daga cikin yaranta an wulgasu ,ta d'ago kanta da sauri dan ganin me wucewar, muradi ta gani cikin shigarsa ta ko yaushe wato kananan kaya har ya gota su rike da hannun Aryan arfi na kafadansa qare wa bayansa kallo tayi sannan ta sauke numfashinta a ranta tace "wadan nan yaran zasu iya zamo min makamin komawata gareka nan kusa dan ta lura da yadda yake bala'in son su duk da bai san matsayinsu ba ."


ta cigaba da sauranro jabir kafin daga bisani tace "zatayi tunani akansa ya amshi wayarta yayi dialling numbersa har sai data shiga sannan ya mika wayar yace "ga numbeta nan kiyi saving duk abinda kika yi tunani akai ki fada min amman zan so ace kinyi tunani mai kyau akaina tace "to ta shige cikin gida cikin jin wani irin faduwa gaba wanda ya sanyata rufe idonta dan muradi na zaune a falo aryan zagaye da wuyansa yayinda arif ke kwance ajikinsa suna zuba masa shirme nan ta wuce su ta haye sama dan lokacin sallah magrib ya kusa ..Shiru shiru jabir na jiran amsa daga kisna amman shiru kira kam kullum sai ya kirata sama da sau ashirin amman bata dauka daya gaji ya fito ya fadawa madu "kaje kasamu uwar dakinta zata shawo maka kanta cikin kankanin lokaci "wacece kenan ka fada min inda take zani nan take ya fada masa "dan wannan ai mai sauki ne afra ai tamu ce muna goodtime daita bai yi sanya ba yaje gidan granny ya samu aunty afra bayan tayi masa tarba mai kyau suka gaisa ya bayyana mata abinda yake ciki tayi murmushi tace" karkaji komai kamar anyi angama ai kayi sa'ar mata wallahi bazakayi danasani ba dan kisna na da kirki nan tashiga zuba masa abinda bai tambayeta ba ,a ranar ta kira kisna a waya tayi mata bayanin sakon jabir "wallahi aunty afra Ina jin kunyar jabir tayi shiru tana zance zuci dan ita yanzu yadda zata koma gidan muradi take "munyi shiru daga kina jin kunyarsa shi surukinki ne da zaki ce kina jin kunyarsa ?" Shikenan amman dai ya bani lokaci kadan "dan Allah karki wulakatanshi Saboda yana tsananin sonki gashi na yabeki sosai kar yaga sabanin rashin tarbiyya Ki kwantar da hankalinki ki fita harka muradi dan na lura so kike ki koma gidansa kuma abinda kika san bazai yiwu bane kinsan yayi miki nisa ki saurari jabir ko bai zama mijinki ba dan Allah dan Annabi ki soshi yasan duk abinda daya faru dake a baya amman yace yaji ya gani so dan Allah karki wulakanta mutumin nan kisna yana sonki na rokeki karki wulakanta shi "kinyi shiru kina jina baki ce komai ba "zan dai yi tunani ki bani wani sati to shikenan Allah yasa muji alkhairi suka yi sallama wajen kwana hudu da zuwan jabir ya sake lalubo aunty afra tana dauka yace " Afra ya Kwana biyu wai ya alkwarina ? , yakamata kiyi mata magana Idan kin mata bata amince ba dan Allah kar ma a ja doguwar magana , kuma ba sai kin fada min ba tace "ka dan kara hakuri tace a bata sati sauran kwana uku muji me ta yanke "okay na baki wuka da nama "kayi addu'a jabir Allah yasa ta soka musha biki a kai maka amaryarka Kaduna murmushi yayi cike da jin dadi yace "kamar kin sani gaskiya Kaduna za'a fara kaita ta zauna da hajiyata daga baya sai ta dawo Lagos mu cigaba da zamammu ai hakan yayi daidai ko?"taje sai ta dawo logas Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi a tsakanina daita wallahi serious nake magana ina son kisna sosai ina son naji ta amince wallahi babu maganar wasa shiyasa nake ta addu'a na dade ina son aureta amman Ina ta addua Allah ya zaba min abinda yafi alkhairi atsakanina daita wallahi afra bansan meye goronki ba idan maganar nan ya tabbata ,ban san wani irin kyauta zan miki ba kyautanki sai nayi nazari naga me ya dace dake ya karasa maganar yana dariya "zanyi komai akan shawo maka kanta ni ba sai kabani komai ba ka aureta ma ka gama min komai wallahi, ai duk randa ta amince sai nayi karamar walima cikin satin aunty afra ta damu kisna da batun jabir ba dan ranta yaso ba tace ta amince dan haka cikin sauri ta dauki waya tana ihun murna ta soma kiran layinsa yana dauka "tace jabir ta amince ta amince
"Allah sarki afra dan Allah karki sani a kwando karki sani a ciki ki ratayani ,karki sa na kasa bacci da daddare nan " to alhamdulillah indai Allah yasa da gaske ne wannan albishir "wallahi da gaske ne ta amince "alhamdulillah afra gaskiya kinyi jahadi Allah yasa ki gama duniya lafiya ina godiya sosai sai nayi nazarin kyatan da zan miki na shiga na fita na zagaya gari inga wani kyauta ne ya dace dake saboda haka Allah yasa har acikin zuciyarta ta amince da wannan karbuwar ".

"Ba dai kin cikata dadin baki ne yasa tayi sauri amincewa ba"to koma dai menene na gode sosai har yanzu dai amanar na hannunki na gode Allah ya tabbatar da alkhairi Allah ya zaba miki miji na gari mai amana ,mai gaskiya ,mai tausayi mai ilimi wanda yasan ya kamata wanda bazaki sha wahala ba wanda bazai ci mutuncinki ba wanda zai rike amanarki na gode yana gama fara haka ya katse kiran yana shafa qirjinsa cikin tsanani jin dadi afra ta kwabe baki "wahalallen banza ai ni ko kudin auren nata ma sai na biyaka muddin auren zai tabbata ni burina bai wuce naga kisna a gidan wani ba .." kisna na zaune da yammacin ranar asabar jabir ya kira wayarta ta dauka naunayen ajiyar zuciya ya sauke ya fada mata gashi a haraban gidansu ,jiki a sanyaye ta gyara shirinta ta fita aiko yana ganinta ya sakar mata murmushi "sannu da fitowa sauraniyar mata ,ina yini ?"lafiya lau sauraniyar mata matar da bata da kishiya a duniya , tayi shiru tana jinsa yana zuba surutu ta kai dubanta ga agogon hannunta taga har tayi minti talatin a tsaye ta yatsina fuska tace "zan shiga gida "tun yanzu gimbiyar mata ki dan qara min minti talatin mana kinga kinyi awa daya kenan ,akwai abinda zanyi ne ta fada cikin damuwa , shikenan na ma gode da wannan minti talatin din sai yaushe kenan ?"ya tambayeta yana tsareta da ido "ka bari ko zuwa bayan bikin madu ne , zaro ido yayi waje yana cewa" bikin da sauran wata daya nan gaba yanzu adalci ne na zauna har sai byn wata daya sannan zan ganki ?" gaskiya baxan iya ba zanzo wani sati bata masa mutsu ba tayi masa sallama ta shiga cikin ranta babu dadi kallon fuskarta kadai ya isa mutun ya fahimci tana cikin damuwa "lafiya ?" mumy ta tambayeta cikin kulawa tace "babu komai mumy "to daga ina kike ?,ya jabir ne ya yazo tana gama fadar haka ta shige ɗakinta iya tashin hankali ta shiga tana son tambayar mumy me yasa basu fadawa muradi cewar su Aryan yayansa bane ko ta samu sausauci daga garesa amman tana jin tsoro ." washegari ko break fast batayi ba taga kiran jabir tayi shiru tana kallon wayar a dalilin muradi dake zaune akan dinnig area yana karyawa tare dasu Aryan har sai daya kira sama da sau a shirin bata dauka ba mumy tace "wai wake kiranki ne ki dauka mana ?"mumy jabir ne wai sona yake ni kuma bansan me zance masa ba wallahi, tayi maganar tana satar kallon muradi taga ya reation dinsa zai yi sai dai babu abinda ta gani akan fuskarsa sai zallar ɓacin rai dan nuna wa yayi ko ajikinsa tamkar bai ji abinda tace ba , mumy tace "jabir din ?"kisna ta gyada mata kai alamun "eh! "kar dai ki wulakantashi Allah dai ya tabbatar da alkhairi ai mutumin kirki ne jabir ga kamewa mumy na cikin magana kiransa ya sake shigowa tana dauka ya sauke naunauyen ajiyar zuciya tayi saurin "cewa sorry kayi hakuri " wani irin abu muradi yaji ya tsaya masa a kahon zuciya ,da kyar ya hadiye wani miyo daya tsaya masa a makoshi can yaja tsaki acikin ransa ya cigaba da abinda yake yana jin haushi dan bai san dalilinsa najin wani abu ba , jabir dake zaune ya koma ya kwanta "yace shinkenan na hakura sarauniya amman anjima zanzo dan Allah koda wasa karki bata lokaci kafin ki fito dan a matse nake na ganki ,wallahi ina tsananin sonki kisna ,idan na rasaki mutuwa zanyi "ta mike tayi hanyar kitchen tana cewa "inshallahu bazaka mutu ba karaf sai cikin kunnen muradi "na gode my wife to be inshallahu nan , suka bude shafin hira magana take amman gabanta da jikinta rawa yake ,sai dai koda ta juyo tana kallon cikin falon bata ga alamun muradi ita yake kallo ba ta cigaba da waya dashi kafin suyi sallama ,ta fito tayi breakfast ta koma daki ta cigaba da tunanin daya ysarkafi zuciyarta wallahi bayan zazzafar soyayyar har sha'awarsa take ji ita bata ma san tana da tsananin sha'awa ba sai a wannan lokaci komai daya gabata daya mata yake ."

Da daddare kisna tayi kwaliyya ta shirya cikin atamfar ja mai yellow flowers ta d'auko mayafi yellow ta yafa bawani kwaliya tayi ba Iya power ne sai white lip's ta feshe ilahirin jikinta da turare ta shiga dakin mumy ta isketa tare da muradi yana kwance flat akan gadonta yayinda aryan da arif ke kwance ajikinsa kunnensa manne da waya wanda yake nuna alamun shi da budurwarsa ce " mumy zan fita gurin jabir "to shinkenan ki gaishesa ,to mumy sai na dawo
tana juyawa twins suka sauko suka biyota ta rike hannusu suka fita muradi kamar ya tsaidaita ya kwace yaransa amman ya share a daidai wannan lokacin aka fara shiye shirye bikin madu domin sauran sati biyu kacal ya rage, tun safe jabir yazo gurin madu ya kawo masa invitations Dan shine ya buga suna dade a dakin madu suna rubuce rubuce cikin wannan satin nawal ta dira a kasar saboda bikin madu har gida tazo gaishe da mumy tare da muradi kuma lokacin taga twins lallai kam sunyi kama kamar yadda ya fada mata babu wanda zai ce ba yaransa bane da zata wuce ta bawa mumy check na Naira million biyar matsayin gudumuwarta sannan ga akwati guda biyu na tsarabarta mumy taji dadi sosai har ta ba gidan basu hadu da kisna ba ."


ranar dinner jabir da kanshi ya nemi mai makeup ya kawowa kisna ta tsarata sosai tayi kyau cikin wata hadaddiyar doguwar riga black mai tsone yellow Tayi kyau sosai da kanshi yazo ya ɗauketa zuwa gurin dinner bata tsaya daukar yaranta ba dan tasan suna gurin muradi suna tafe ita da jabir suna hira har suka shigo hall ya yadu sosai a hankali ta hango muradi cikin mutane shima cikin shadda baka ta sake kallon jikinta ta kalleshi anko dai sukayi gefensa wata da bata san ko wacece ba ta soma taku a hankali nan idanu mutane yayi caaaa akanta shi kansa muradi sai daya d'ago ya kalli inda take saboda ganin hankalin mutane ya raja'a akai gbdy ya raina shigar jikin nawal dake kusa dashi twins na hango uwarsu sukayo gurinta suna kiranta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login