Showing 495001 words to 495987 words out of 495987 words
Chapter 166 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
ta kasance ranar juma'a gbdy jikinsa kanshi yake fitarwa ta mike da hanzari suna rige rigen isa gurinsa ita da yara gbdy ya hadasu ya rungume ajikinsa sannan tajasa zuwa kan kujera cikin annashuwa yake kallonta saboda kyan da tayi "baby love kinyi kyau fa sosai kullum idan na kalleki soyayarki sake ninkuwa take a zuciyata ta kalleshi tayi murmushi "ni kaina haka nake ji kamar nafi kowace mace Sa'a da dace a rayuwa ,ina cikin rayuwar jin dadi da rayuwar nuna ma Sa'a mijin da nake da yakinin ni kadai na taba sa'ar irinsa miji mai tausayi imani taimako hakuri ,ilimi da wadatar zuci miji mai tsoron Allah hakika babu abinda zanyi sai dai na dangwama ina godiya ga buwayi gagara misali da yayi min wannan kyautar da ba kowa yayiwa irinta ba ya lumshe ido cikin jin zakin kalamanta ya bude su a hankali akanta "nima a nawa bangaren haka ne ina jin kamar nafi kowane namiji Sa'a don gani nake irinki ke kadai ce macen data tara abubuwa da dama sakina baiwar Allah mai tarin baiwa da niimomi ina tsananta godiya ga sarki Allah ina kuma rokonsa ya bamu tsawon kwana ya kuma rayamu tare da yaranmu ya karemu daga sharrin sheidanu da mahassada da aikin dana sani ya cigaba da azurtamu da yaya na gari kisna ta amsa da ameen cikin farinciki daga nan yace ta dauko masa abinci ta dauko anan suka baje kan kafe yayinda kisna ke kokarin zuba masa abinci ."bayan sun gama ya shiga d'akinsa yayi wanka ya saka gajeran wando kadai ajikinsa ya zauna a bakin gado sanyin a.c na ratsashi ta ko'ina ,ta shigo cikin shirin bacci tunda ta shigo idanunsa ke kanta bata damu ba hasalima jin dadin hakan takeyi dan yana sata farinciki ,ba macen data isa ya tsaya yana kallonta irin haka sai ita din dan haka koda wasa bata taɓa hanashi morewa kallonta ba ,dan ya fada mata sau babu adadi kallonta na qara jefashi cikin farinciki mara misaltuwa ya rungumota jikinsa tare da canza wutar dakin zuwa mara haske ya soma yawo da hannuwansa ajikinta sam baya gajiya daita jinta yake kamar farkon aurensu .."
**
Rayuwa dai tana yiwa kisna dadi sai abinda baza'a rasa ba shekarar kisna ashirin da daya kenan da aure yaranta goma cif uku maza bakwai mata uku arif aryan ,saliha ,A'isha Aliyu, Samir ,sani al'mustapha sadiq sai auta fatima arfi da aryan suna jami'a buk yayinda mother ke daf da kare secondary a rema international boarding School a yaba ,amman llum ka gansu tamkar sababbin aure duk wanda ya shigo gidansu sai sun burgsa jin dadi kuwa abun ba'a magana idan kana gidansu kuwa kayi zaton a wata kasar kake abin sai wanda ya gani a daidai wannan lokaci taje aikin hajji da Umar ita da nawal yafi sau babu adadi ,dan duk shekara sai sunje nawal dai an gaji da zama haka yanzu neman rabuwa take da auren muradi ita da danginta ganin har tsawon lokacin babu haihu sai dai tunaninta ya rabu gida biyu tana son fita tana tsoro dan tasan ba lallai idan ta fita ta haihu da wani ba, idan kuma tazo ta fita ita ba ga haihuwa ba ita bada samun miji kamar nata ba yaya zatayi kenan ".?
tsaye kisna take a gaban mirrow fitowarta kenan daga wanka ta kalli turarukanta duk na saudia ne masu dadi qamshi,daya daga cikin kayan baccin data siyo daga Saudi ta ciro ,doguwar riga ce har qasa mai hannun shimi mai shara shara me santsi ta saka ,ta feshe kanta da turaren , kana ta rage hasken fitilar dakin ta haura gadon ta kwanta tana jiran shigowar oga ,jin shiru bai shigo ba ya tabbatar mata yana can rarrashin teema dan yar rikici ce ta bugawa a jarida tana ganin ita da sani ne zasu dan dauko rigimarta ,tana nan kwance ya shigo ya kwanta a bayanta yana kokarin lullu'besu yace "I'm sorry kina ta jirana kou teema ce da kyar na samu na tayi ba....tun bai karasa ba ta juyo ta haɗe bakinsu .a kullum kisna ta daga hannu sama sai dai tayiwa Allah godiya bisa ga sauyin rayuwar daya kawo mata wuyar soyayyar data sha a baya ta zamo tarihi muradi ya gina masallaci sadakatul jariya ga kakarsa Hajiya kayi yayinda ubansa har lokacin bama a sanda inda yake ya'yansa dana sadiq mumy da dady kawai suka sani sai dai har kullum mumy na fada musu suna da kaka me suna haroon Allah Sarki hakan yaran suka kwadaitu da son ganinsa.
tun daga sama take ihun kiran danta sani kasancewar babu kowa a gidan duk suna gidan mumy shima fitinarsa tasa aka dawo dashi dan baya jin tsoron kowa sai muradi ya falala da gudu zuwa kofar gidan ta karasa bakin get sanye da hijab me gadi yace" nayi hanashi fita kodan ganin yadda ya fito da gudu amman kafin nayi wani hanzari ya fita "gara daka barshi saboda titi ta fito har wajen gidan "kazo na aike kaji dan albarka " ni gaskiya mumy na gaji wallahi yanzu fa na dawo daga wani aikin , tayi shiru tana kallonsa can sai ga wani yaron makwaftansu tace "yauwa shewu zo na aike jeactoin peju kaji , nan take sani ya waro idanunsa waje yana janye yaron dake kokarin karasawa inda take "wallahi idan ka sake kaje aiken mamana to kullum ta dinga biyoka gidanku kenan nima kaga na gaji da'akenta ne shiyasa na gudo waje aiko shewu ya falfala da gudu alamun bazashi ba ........"
anan zan dakata na godewa Allah daya bani ikon kammala wannan labari Allah ka karawa Annabi Muhammad (saw)daraja ina yiwa makaranta littafaina fatan alkhairi da godiya sai mun hadu a cigaba kuskuren baya wanda za'a cigaba da rubata shi inshaallahu..
Alhamdulillah
Mmm Sudais