Showing 105001 words to 108000 words out of 495987 words

Chapter 36 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

haroon  sake  fitowa saboda tsadaddun  kayan da yake  sakawa jikinsa  ya famtama  gari  gurin abokai ,  duk  sanda uncle garba  yayi  masa maganar  aiki  kuwa  ranar babu zaman lafiya a gidan ya  dinga  nunkurfici kenan  yana  cewa "shifa  ba zai iya  harkan  canji ba  ci baya ne agurinsa    dan  ba zai iya tsayuwa  a bakin titi yana kiran  mutane suna masa wulakanci   ba su da sukaji  zasu  iya  su cigaba   da  tsayuwa akan   titi  bai  zai hanasu ba  amman shi bazai iya  ba , iya gata hajiya kayi ta  nunawa haroon  , duk abinda  yake so tana masa  saboda kasancewarsa  mai sunan kanin mahaifinta  kuma shi ya riketa har aure tana ji dashi sosai   .."

"  Mahaifina   kuwa  asalin  iyayensa   yan kano  ne a karamar hukumar  kiru  , sai dai shima  zama ne ya kawo iyayensa  lagos ,  anan  cikin  garin lagos aka haifeshi  a unguwar agege shi  da sauran yan'uwansa  ,kakana na gurin  uba  alhaji lukman shararraren   mai  arziki ne   wanda  sunansa ya shahara  a  jahar  lagos sannan  ya karad'e   sauran  garuruwan dake cikin  nigeria kasancewarsa  ɗan siyasa , Alhaji  lukman   yana  da  tarin ya'ya da yawa   wajen su a shirin da  shida  ya haifa , ya mallaki  maza da mata  ,maza  shabiyar mata  goma  amman gabad'ayansu  kansu a haɗe  yake duk da wasu daga  cikinsu  sun mutu sauran  ashirin a raye  , mahaifina  yana  da yawon  yan'uwa  sai dai yawansu  bai sa kansu ya  rabu ba ,  hakan  kuma  ya  samo asalin ne agurin  mahaifinsu  shi ya  haɗa  kan ya'yansa  ,hakan  yasa  yaran suka taso  kansu  a  haɗe cikin tsananin son juna babu   ruwansu da wannan  uwarsu  ɗaya ubansu  ɗaya,  wannan uba  daya ne , suma  haka  zalika  iyayen ma  kansu  a  haɗe  yake  haka  ma  jikoki  muna matukar  qaunar junanmu   .."

" mahaifiyata  salaha da mahaifina Alhaji  realwan sun   haɗu ne a wani zuwa bikin abokinsa idiaraba soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu ,sunyi aure bayan gwagwarmayar  rayuwa da  mahaifina  ya   sha kafin  mahaifin mahaifiyata  Alhaji sani  ya  yarda da aurensu  a cewarsa  ba zai ɗauki tilon  diyarsa mace ya bawa    bare   kuma  yare  da ban  ba zarma d'an'uwansa ba , dan asalin  zarma  basa bada auren  ƴaƴansu ga wani yare  baya  ga yarensu bisa  nasu ra'ayin ,dan har  yanzu  ba kowane bazabarme  ke  daukan ya'yansa  mata  ya aurawa   bahaushe ba , sai dai zabarmawan dake   zaune  a garin lagos suna  kokarin su bawa bahaushe   idan sun san asalin   daga  ina yake  kuma  sun san halinsa amman  yawancin na kauye  basa bada yaransu  saboda suna ganin  hausawa basa rike aure  ga saurin saki , har yanzu  har kwana gobe ba  kowani  zarma ke daukan  d'ansa ya bawa bahaushe  ba  sai dai su kan  yarda ƴaƴansu maza  su auro  ya'yan hausawa  mata  ."
 

   Tun  bayan da'akayi auren  iyayena  Allah bai nufesu  da  samun haihuwa  ba  sai da suka kai  kimanin  shekaru goma  da aurensu sannan  Allah ya basu haihuwar ya badamasi , yayinda  a wannan lokacin  tuni   uncle  garba  da uncle bature sun yi aure kuma a rana daya  kuma  duk yaren  zarma  suka  aura  mazauna  Idiaraba .
   bayan  bikinsu  bada jimawa  ba  hajiya kayi ta koma  ilo  da zama ita da mijinta  kasancewar girma  ya  soma zuwan musu  wanda  kusan al'adar  zamar ne basa karashe  rayuwarsu a wani  guri sa'banin garinsu  na haihuwa , duk yadda suka kai ga neman kudi  aguri  da zarar girma  yazo musu zasu tattara  su koma jaharsu su  cigaba da rayuwa  ..."

  A  wannan  lokacin kamar  yadda muka samu  labari  uncle haroon  bai bi bayan iyayensa  zuwa ilo ba acewarsa  mai zai yi a kauye  babu  wuta  babu network   babu jin dadin rayuwa  tsakaninsa da kauye  sai  dai kallo ya tattara  ya bi wani abokinsa  farhan zuwa  jos ,duk sanda  mommy  taje ilo  gurin   mahaifiyarta  dan kai mata  ziyara ta dinga mata  kuka kenan akan uncle haroon  tare da bar mata wasiyya  iri iri akanshi  ,  "Idan  garba da bature sun  juya masa baya  salaha  karki  juyawa d'anuwanki  baya " ina son  babakarami tamkar raina ,dan Allah  kema ki so shi kamar yadda nake son shi  ki  janyosa  jikinki  ko bayan  raina  idan Allah yasa  ya  dawo kuka hajiya  kayi  keyi sosai wanda  har  yasa mommy  kuka  suka rungume  juna gam  suna  kuka yayinda Alhaji sani yayi  shiru yana Kallonsu  cike da takaici da bakinciki  dan duk  tautaunawarsu yana shiga  kunnuwansa , kuka  suke kamar ransu zai  fita  ,   cike da zafin zuciya    alhj sani  ya    tako  zuwa inda  suke rungume da juna ya  fara  magana cikin zafin  zuciya  yana cewa" momy    karki  kuskura  ki ɗauki maganar  mahaifiyarki  da  mahimmancin da zai sai  ki damu rayuwarki akan   takwaran Alhaji   dan ko ya dawo garemu   bashi da muhalli acikin  gidan nan, ban ciresa a cikin ya'yana ba amman na ciresa a cikin zuciyata dan bazan amshesa ba ,ba dai yana gudun zama damu bane saboda bamu da arziki yaje duniya ce gashi nan gata wanda bai zo ma tana jiransa "hajiya  kayi  ta zabura ta mike  tsaye  tana fuskantar shi cike da mamakin  jin furucinsa sannan   tace  "saboda me  zaka fadi  haka alhalin  d'anmu ne babakarami bashi da iyayen da suka fimu ",ana ki tunanin  ba ai shi bai daukemu  a matsayin iyaye ba , kafin kace me gurin ya hargitse da magana  da rudani tsakanin hajiya kayi da Alhaji sani zuciyar hajiya  kayi ta tsinci  kanta cikin  rashin natsuwa  da jin hukuncin mijinta  , ranar tamkar mutuwa  akayiwa a gidan  mommy  da hajiya  kayi babu  abinda suke sai aikin zubar da hawaye yayinda  shi kuwa a lokacin  haroon  yana can  yawon duniya bashi wannan  gari bashi wancan  gari duk garin da yasan zai ji dadi zashi ,kullum kuma  cikin  samun sabbin  abokai da yammata  yake  kuma har  wannan lokaci mata basu  daina kashe masa kudi ba  , a hankali har ya shiga  harkan neman mata  da smoking kamar yadda  momy   ta  samu labari   mata na biyansa  kudi dan  ya  kwana dasu , ranar  kuwa momy  tayi kuka  tamkar ranta zai bar  gangar jikinta bata fadawa kowa ba ranar da  zazzaɓi ta kwana a jikinta ta aika masa sako ya dawo gida  ya bar harakar da yake duk abinda  yake so zata masa  amman yaki yace shi yanzu bazai iya rayuwar gida ba   ..."

Numfashi  kisna ta sauke a lokacin data zo nan  sannan  ta fuskanci safy fuskarta  cike  da tsananin damuwa tace   "a  iya  nan zan dakata  bazan  iya cigaba  da bakin labarin ba  saboda akwai  wani  boyayyen sirri  akan ya aliyu ba kuma zan  so wannan sirrin ya fito  daga bakina ba  ta karasa maganar wasu hawaye na gangaro mata  safy ta numfasa  tace ,"to ai baki  faɗa  min yadda kuka  yi aure da Aliyu  ba dangantakanku kawai kika fada min ni rayuwar aurenku nake son ji " "Muddin  zan faɗa miki  yadda muka yi aure dashi dole  zan bayyana wannan  sirri  " .

murmushi safy  tayi sannan tace" kisna  kenan  ba dai zurfin  ciki  ba  sai naji kin  sake  shiga raina ina matuƙa  son mutun mai rike  sirri wanda samun irinku  yanzu kuke da matukar  wuya, kisna  ta gyada mata kai  kwayar idanunta na kallon sama dan ita  kaɗai  tasan  yadda take  jin zuciyarta a  hankali  ta mayar da idanunta  zuwa ga safy ta cigaba da magana "ciki   ba'a yisa  dan abinci kawai  ba duk mutumin daya  kasa rike sirrinsa karka  yi  tunanin zai iya rike na  waninsa ta karasa  maganar hawaye na  sake  gangarowa daga cikin kwarnin idanunta  "wannan  magana   taki haka take amman   naso  naji yadda  kuka yi aure da Aliyu gaskiya " parlou'n  ya d'auki shiru  babu  wanda ya sake  yin magana har aunty  zee wacce ke aikin mayar  da  kayan lefe cikin  jakunkuna, " Kisna  kiyi hakuri ki daina kuka  bana son  ganin hawayenki yana sani jin wani iri wallahi  "ai  indai kisna  ce yanzu  haka take  abu kankani ke sata  kuka  saɓanin da  ta mike ta karaso kusa da kisna ta rungumeta suna kukan tare wani abu ya tokare makoshin Kisna dan komai daya faru ya shiga dawo mata daki daki suna cikin kukan muradi ya shigo parlou'n ya iske su
cikin  wannan  halin suna kuka safy na basu hakuri   saurin katse sallamar yayi  daidai  lokacin da aunty zee ke magana murya can kasa  tana gogewa Kisna  hawayen " .

kyawawan idanunshi masu  matukar kyau da haske  ya sauka akan kisna  dake zaune tana matso ruwan hawaye tamkar wacce aka yiwa mutuwa   tare da  kare mata kallon tsab  idanunta sun canza daga  fari zuwa kore , a hankali ta d'ago idanunta suka  hade da nashi wani irin mummunar faduwar gaba  taji  ,take  gaba-daya ilahirin jikinta ya dauki rawa  lokacin da kwayar idanunta ya haɗe da  nashi kallonsa kaɗai nasata jin  abu biyu a lokaci  daya, faduwar gaba  tare da alfahari   kasancewarsa uban ya'yanta .

kusan minti biyar ya dauka tsaye a bakin kofar dakin  yana Kallonta sannan ya soma takowa a hankali yana mata kallon kasan ido ,nazarin yanayinta  yake, wannan yanayin daya gani a tattare daita yanayi ne na damuwa dan kuwa idanunta sun tabbatar masa da haka guri ya samu ya zauna akan kujera  yana kallon safy dake faman zuba sannan yana kallon kisna ta gefen idanu muryarsa a kasalance ya soma magana cikin tsigar tsokanar safy   "ya kika ga kayan  amaryarta sun bugeki  ko "?"Sosai  kuwa duk  sun   burgeni   sai dai gabad'aya kayan sunfi dacewa  da kisna ba wannan  mai kama da busashen bishiya ba, ko ka taba ganinta da irin wannan waɗan kaya"?ta karashe maganar cikin tsigar wasa tare da yunkurawa ta tashi "wannan kuma son ranki kika faɗa saboda kina da wata manufar munafurci a ranki ai sai na zuga mijinki ya qara aure " kalmar munafurcin daya dangantata dashi ya mugun bata rai murmushin takaici tayi tana rataya jakarta  "kai ma daka hakura mai mata kamar kisna mai zai yi da wata nawal din banza mai siffar munafuka "? Ta fada tare da nufi kofar fita tun kafin ya antayo mata bakar magana data fi na farko tana cewa "sai anjimanku " aunty zee ce  ta mike tayi mata rakiya  har haraban gidan kalmar ta bala'in bata masa rai zuciya tazo wuya a hankali ya dinga girgiza ƙafarsa daya ...."

Kisna   ta mike  tsaye ta karasa inda yake ta durkusa  muryarta cike da rauni tace "sannu da zuwa " ta'be baki yayi batare daya amsa mata ba , bata damu  da rashin amsawarsa ba tunda idan da sabo ta saba da halinsa .
  ta soma cire masa canves din dake sanye da kafafunsa hawaye na ziraro mata sanda ta karasa cire masa kafafunsa ya saura da  safa kawai , ita kanta aunty zee data dawo parlou'n ta ganta durkushe a gabansa kasa daurewa tayi sai da wasu suka qwalla zubo mata  ta kawar   da kanta tare da danne abinda taji bawai shishige masa da kisna  take bane yafi damunta irin banzatar da rayuwarta da yake kai tsaye  juyawa tayi ta nufi kofar fita tana goge hawaye "zainab ya kira sunanta  muryarsa a dake cike da ɓacin rai tsayawa tayi cak batare data juyo ba   "kowa  murna   yake  akan  auren  nan da zanyi  banda ke   da wannan yar iskar me  yasa kika   manta abinda yar iskar nan ta  aikata  ga rayuwata kunnuwan Kisna   suka jiyo mata sautin muryarsa  yana fadar haka a can kasan makoshi , kamar ta cigaba  da durkuso a gabansa ta cigaba da sauraronsa tare da  rarrashinsa da bashi hakuri sai zuciyarta ta haneta dan haka ta mike hannuta  rike  ta canves dinsa  tana kokarin hawa  sama kamar zai mata magana sai kuma ya fasa  ya cigaba da magana "wallahi kina biyewa son zuciyarki dana wannan abar sai dai bata isa bakincikinta ya kasheni ni kadai ba kamar  yadda taso faruwar hakan  kafin taga mutuwata  ina tabbatar miki ni ne zan soma ganin nata duk da nima nasan  bazan cigaba da zama ba amman wallahi tallahi ba zan barta tayi rayuwa mai dadi ba ina nan akan bakana har sai nayi magani iskancin data min numfashin Kisna ya soma fita da sauri da sauri , ta kasa cigaba da daga kafafunta aunty zee ta gigice ta juyo tana kallonsa cikin tsananin damuwa itama Kisna ta juyo tare da tsura masa ido canves din hannunta ya subuce shima kallonta yake cikin tsana muryar a zafafe Kisna ta soma magana cikin kunar rai "kai cika mutun mara imani   hakika na soma danasanin kasamcewa mata kuma uwar yayanka a rayuwata ,alfaharin da nake na kkasancewarka ubansu Aryan reef da janye domin sun yi hasarar uba wallahi ,kasani wani  bakincikin ne dabam  zai kasheni ba sanadin   ciwon zuciyar da kake kokarin haifa min ba kuma duk abinda kake yi Allah yana kallonka zai saka min sannan auren nawal da kake ganin yana cikin bakinciki da zaka kunsa min wallahi  ko  ajikina  saboda banga abinda zai sa na daga hankalina akan matar da tsinannu kadangarun bariki suka gama da rayuwarta yar iska da kowa yasan ba yar mutunci bace kawai bakar zuciyarka ce ta hanaka ka fuskanci komai ni kuma da kake kira da yar iska duk iskancina ban bari yan iskan kadangaru bariki sun .........."
shiru tayi sakamakon toshe mata baki da aunty zee tayi tana girgiza mata alamun tayi shiru saurin cire hannu aunty zee tayi a bakinta "ki bari na fadi abinda ke raina ta yaya zai dinga dangantani da kalmar iskanci wallahi duk matakin da kake shirin dauka akaina ka dauka amman ka kwana da sanin cewa Allah bazai barka ba saboda ina da hakki akanka kuma babu inda Allah yace dan nayi maka  laifi ka tauye hakina daya rataya a wuyanka ya mike a zuciye yayi kanta yana huci ya daga hannunsa zai doketa yana auna mata zagi aunty zee ta kare "haka zaki kare cikin tsananin bakin ciki a gida nan rayuwar farinciki sai dai kiga ana yinsa a wani gida .."

  "da ikon Allah sai Allah ya kunyataka,   karewa cikin bakinciki tana gurinka mutumin da baya yafiya tunda har nadamata bata sanya kaji zaka iya hakura da abinda nayi ba hakika zaka ga yadda rayuwa zatayi da kai hakina dana yayana bazai barka ka zauna lafiya ba aunty da zee ta rikesa gam da hannuwanta duka tabashi hakuri   saboda jikinsa dake tsuma  da kyar ta samu ya zauna yana huci duk cikin maganganun ta babu wanda ya taba zuciyarsa da tsaya masa arai kamar kalmar data danganta nawal daita take gumi ya rufeshi gabadaya ya nemi natsuwarsa ya rasa ji yake kamar zuciyarsa zata buga a yanzu da ya soma  jin soyayyar  nawal na dan  shigarsa shine zata fadi mummunar kalma akanta yasan tayi haka ne dan kawai ta bakanta masa amman bazai yi sakacin da zuciyarsa zata amince da kalamanta ba,cikin tsananin zafin rai Kisna ta  juya  cikin sauri   ta hayewarta  sama zuciyarta kamar zata  buga ,itama aunty zee  ta fita ko  dan  rarrashin data saba yi  masa  a duk sanda ya hau sama bakinciki yasa ta kasa sannan taki masa magana akan yadda za'a yi da kayan lefe dan nan ta barsu yasan yadda zai yi dasu ai ta gama mai wuyar , duk yadda zuciyarsa taso ya yarda da kalaman Kisna akan nawal kin yarda yayi domin ganinsa yana yin nasara akan komai dan tun daya taso yake samun nasara arayuwarsa yana da tabbacin zai yi nasarar samun nawal cikakkiyar mace a gidansa kamar yadda ya saba nasara dogon   tsaki  yaja  wayarsa dake qara ya ciro yanayin yadda ya soma magana kasan shi da mommy ne.."

Tana  tsaye a dakin tana datasanin abinda tayi ya shigo dakin   yana  cire yar saman   rigarsa  ya ajiye akan gado ta karasa zata tayashi cire sauran ya dakatar daita yana zabga mata harara taja ta tsaya tana kallonsa ta madubi gabanta na cigaba da faduwa ",sannu tantiriya Kinga ma ci min mutunci ke da wancan yar rainin hankalin yanzu  shine ɗan iskanci zaki wani nuna ke mutuniyar arziki ce  yayi maganar yana  ajiye rigar akan  wanda ya cire ya ɓalle agogon diamon din  dake daure a tsintsiyar hannunsa ya ajiye "bai kamata kaji ciwo ba , babu inda  maganata ta shafi ta safy data biyayyar aurena da kai ,magana ka fada na baka amsa daidai da maganarka meye abun

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login