Showing 420001 words to 423000 words out of 495987 words

Chapter 141 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

a germany addu'a ce a bakinsa yana fatan damuwarsa ta kau kafin kwanankin da zai yi a kasar , sai dai yana isa masaukinsa komai ya rikirkice masa ya saki kuka mai karfi yayi kuka kamar ba muradi ba wannan jajirtaccen matashin dake da karfin zuciya a komai ,sai dai akan mahaifiyarsa shi din rago ne ,shi din ba ko bane .


Tun daya bar kasar zuciyar kisna ke suya ta rasa abinda ke mata dadi ta isa bangaren aunty zee idanuwanta sunyi ja saboda damuwa sai dai tana zuwa ta rasa me zatace mata ita kenan kullum complain akan miji amman duk da haka sai da aunty zee ta gane tana cikin damuwa hakuri dai tayita bata daga nan hirar ta dawo ta muradi" aunty zee Ina tsananin son muradi , Ina son mu kasance tare dashi a matsayin miji da mata har abada bana qaunar abinda zai nisanta tsakaninmu amman shi sam bana gabansa ya ma tattara ya barni saboda baya sona kuma har yana bani umarnin na daina kuka akansa ,yaushe ne hawayena zasu tsaya aunty zee tunda yaki fahimtar irin canzawar dana yi ? "karka ce haka yana sonki mana idan kuma baya sonki har yanzu kina cikin aiwatar da aiki ne akansa , kada ki karaya inshallahu zaki ga canji kafin zuwan nawal," aunty zee idan Allah ya taimakeni ya tafi dani bikin nan ina jin bazan dawo kasar nan ba ,zan zauna a can ya taho da matarsa kawai kada na biyosu su daura min ciwon zuciya."ko dai ki daura mata ke yanzu har akwai matar da zata firgitaki ?

"kima cire wannan aranki idan ma tunaninki kenan kiyi maza ki cire , kina son mijinki Kuma yana tsananin sonki kiyi masa duk abinda zai sa yaji dadi a zuciyarsa , ladabi da biyayya kamar dai yadda kike masa a yanzu karki bar any space da zai sa wata tazo tana miki yauki a gidanki , idan ta shigo taga babu space dole ta hakura da abinda tazo dashi a karshe tabi tsarinki , idan kuma ta nace lallai sai tayi to fa bawani burgesa zatayi ba dan ya rigada ya saba gani abinda zatayi a gidansa " kusan gidan aunty zee kisna ta yini hira dai daya ce ta muradi yayi kaza ya bar zuciyata da kaza ina son muradi ."

Kwana yayi yana kuka cike da kewar mahaifiyarsa har washegari ranar sannan ya hakura dan babu laifin kukan da yayi yasa zuciyarsa tayi sanyi , ya shirya ya fita yayi musu siyayya mai yawa shi da yaransa da dan'uwansa bazai manta kalmar mahaifiyarsu na karshe garesu ba " sadiq kai ne babba ka kula da rayuwar kanneka duk abinda ka samu na Aliyu ne haka kaima Aliyu abunka na dan'uwana ne, ku jajurce duk runtsi kada ku juyawa kanku baya ina alfahari daku yarana Allah sarki rayuwa ya furta a hankali duk wani abinda yasan zasu bukata a cikin kwanaki goma da zasu yi sai da ya siyo ya dawo hotel zaman jiran karasowarsu , karfe goma sha daya daidai suka sauka cikin tsananin farinciki ya tarbesu yayi murna sosai da ganinsu suka rungume juna da sadiq ya dauki ihsan mai sunan mahaifiyarsu yana mata wasa yana son yarinyar sosai saboda kamar da take da mahaifiyarsa ,kai tsaye masaukinsa ya kai su hankalinsa ya kara kwantawa gashi ga family dinsa , tare suka ci abinci gbdynsu byn sun gama ci Aryan nata tsalle a jikinsa suna murnar ganinsa shi kuma yana fuskantar dan'uwansa "bakaga ya dace mu nemi mahaifinmu dan gano inda dangin mahaifiyarmu suke ?,sadiq ya fada a hankali yana tsaida Idanunshi akan muradin dan jin abinda zai ce "idan mun nemi inda yake meye amfaninsu su din mutanen da suka wulakanta mana uwa ? "akwai mana muradi zamu dinga kallonsu a matsayinta , muradi yayi shiru yana lilo da ihsan data hau saman kafafunsa yana girgiza kai alamun maganarsa bata da wani amfani ."ya kamata mu manta komai da dangin mahaifiyarmu suka mata suma suna da nasu dalili na ganin bata zabar mana uba irin mahaifinmu ba .." muradi ya amshe maganar yana cewa "wannan kuma haka ne wallahi da'ace ina duniya koni zance kada ta zaba mana uba irinsa domin rayuwar da suke gudar mata ita mukayi ,"kaga abinda nake son ka fahimta kenan ,na fahimceka sadiq amman yanzu ina zamu fara nemansu benue bakaramin gari ba wa zamu ce ? Shi kuma wanda yasan har gidansu bana qaunar haduwa dashi har duniya ta nade ,ka share kowa sadiq mu din nan ma mun isa mu bawa junanmu farinciki ga yarinyarka mai sunan mahaifiyarmu ga yarana biyu da Allah ya bani " ya karasa maganar yana mike wa zaune sadiq yaja numfashi yana tsura masa idanunsa rasa abinda zaice yayi saboda yadda yaga fuskar muradi ta sauya cikin yanayin daya kasa fassarawa koda gani bai ji dadin tunawa da yayi da mahaifinsu ba shima muradi zuba wa sadiq Idanunshi yayi kamar yadda yayi masa, a hankali sadiq ya saki fuska zuwa yanayi na murmushi tare da cewa " maganarka haka ne mun isa bama iya haka zamu tsaya zamu samu wasu inshallahu Allah raya manasu "ameen muradi ya furta a hankali fuskarsa na bayyanar da farinciki saɓanin dazu burinsa su hayayyafa domin ya'yansa dana dan'uwansa sune yan'uwansa .

a d'aki daya sukayi bacci cikin farinciki ,washegari farincikina ya ninku yafi na jiya, mikawa sadiq wata riga blue black mai gajeren hannu da wando baki shima ya saka irinta sukayi shiga iri daya haka ma yaransu kaya iri ɗaya suka saka bambancin na ihsan na mata ne ya kwashesu suka fita yawon shakatawa , sukayi hotuna tare , yaransu na tsakiya satinsu daya suna tare aguri ɗaya suna jin dadin rayuwarsu komai tare suke yi sosai ya samu natsuwar da yake bukata ,yanzu hankalinsa ya kwanta sosai nan kuma ya fara tunanin kisna yadda gari yayi sanyi nan gaba-daya yasan tana can kwance tana tunaninsa yasan har ya koma bazata daina zubar da hawayenta ba, zasu yi ta zuba ne zuciyarta na can cikin mummunar yanayi "ka manta komai da kisna tayi maka kai me ilimi ne bai kamata kana abubuwa irin na marasa ilimi ba laifi tayi maka kuma ta gane kurenta kayi hakuri ka yafe mata komai ya kare , matse pillow yayi gam a qirjinsa yana furta "na yafe miki kisna kuma nayiwa kaina alkwarin zan canja zan dawo miki kamar yadda kike so amman sai kin kara hakuri dani na fi kowa sanin abinda ke zuciyarki idan kina son mutun haka kike nufi har cikin zuciyarki ya mirgina tare da cire pillow ya rungume Aryan ajikinsa yana sauke numfashi ya dinga tunaninta matarsa na da tsananin kyau , bata rasa komai ba duk inda ta shiga sai ta dauki hankalin mutane maganar rohon yazo masa alokacin daya kamashi yana kallonta " ni nasan abinda nayi maka kayi hakuri dan Allah ka yafe min bada son zuciayata bane kyawun matarka ne yayi yawa kamata yayi ka sake killaceta sosai numfashi ya furzar "kai da aka yiwa kasheda shine kayi ganganci barinta ita kadai kou ? , tsaki yaja ya mike ya fito haraban hotel din yana cigaba da tunaninta duk yadda yayi kokarin cirewa aransa ya kasa abubuwan da sukayita faruwa a dawowarta suka dinga zuwan masa daya bayan daya wani yayi tsaki wani yayi dariya .
babu wanda ya tsaya masa arai kamar wanda tace "ya Aliyu idan ka isa ka biyoni da niyyar dukana kaga abinda zai faru wallahi sai na fita tsirara haihuwar uwata daga gidan tana magana tana cire kayan jikinta tana wurgi dashi ta saura daga ita sai pent ....murmushi yayi kamar a lokacin abun ya faru kwanansu takwas suka fara shirin barin kasar germany , jirginsu sadiq ne ya fara tashi zuwa naija sannan nashi."

da misali karfe biyu na dare ya sauka tana bacci a falo ya shigo ya tsira mata ido yana kallonta sanye cikin ƙananan kaya wando da riga wacce ta bayyana dukiyar fulaninta ta tufke gashin kanta a tsakiyar kanta a hankali take sauke numfashi da alamun kallo take bacci ya ɗauketa agurin dan ga tv nan a kunne ta barshi ,ya nufi sama ya ajiye jakarsa ya rage kayan jikinsa ya sauko yana tafiya a hankali kasancewarsa mara hayaniyya yasa bata ji motsin shigowarsa ba ganin tana kwance a falon yasa ya fita da kanshi ya dauko tangamemen katon frem din da'aka masa na hotunsu acikin kwali ya shigo dashi ya samu guri ya makala shi a falo sannan ya dawo inda take ya kai hannunsa jikinta ya ɗauketa ya nufi d'akin baccinsu ya shimfid'ata kan katifa ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya sanya kaya marasa nauyi ya hau kan gadon, kwanciyarsa ke da wuya yaji ta daura kanta akan damtsen hannunsa yayi shiru saboda jin qirjinsa ya amsa kafin yayi wani abu ta daura hannunta a saman faffad'an qirjinsa , lumshe Idanunshi yayi a hankali tare da fuskantarta ya daura hannunsa a goshinta yana shafa kwantaccen gashin dake kwance har zuwa fuskarta yana sauke ajiyar zuciya itama ajiyar zuciya take saukewa tana sake shigewa jikinsa har asuba suna manne da juna shine ya rigata tashi ya gyara mata kwanciya tare da saukowa daga kan gadon ya juya motsin saukar numfashinta yasa ya juyo ganin ta cigaba da baccinta ya shige bayi ."

da safe tana farkawa taga mutun zaune a gaban computer tamkar a mafarki tayi tsuru tana kallonsa zuciyarta na wani irin bugawa da sauri da sauri sarai ya fahimci mamakin ganinsa take amman ya share yaki kallon inda take ya maida Idanunshi wani gefe yana kallon agogon dake manne a bangon dakin sannan ya mike ya shiga bathroom tana ganin haka tayi saurin durowa ta dauki hijab dinta ta zira ta fita a d'akin ta shiga dayan d'akin mumy tayi alwala ta gabatar da Sallah asuba bayan ta idar ta sauko ta shiga kitchen domin daura masa abinda zai ci ".
Yayinda shi kuwa yana cikin bathtube yana having shower ya dade yana sabe jikinsa sannan ya fito ya saka boxer da black singlet ya fada kan gado zuciyarsa na matukar bugawa da karfi "inshallahu zan canza kamar yadda nayiwa kaina alkwari tunda itama ta canza kuma iya horuwa tayi a hannunsa shine abinda yayita ƙoƙarin maimaitawa kuma yana fatan hakan ya zauna cikin kwakwaluwarsa mikewa tsaye yayi tsam ya dauki system dinsa ya koma parlour'n sama ya zauna ya dauki remut ya kunna tv .


bayan ta gama hada masa breakfast cikin natsuwa ta turo kofar dakin ta shiga tare da yin sallama cikin sanyayyiyar muryarta , baya dakin tayi shiru tare da hadeye yawu tana daidaita numfashinta da natsuwarta ta fito ta nufi parlour'n sama tayi knowcking tamkar wacce kashin jikinta bashi da kwari dan kar tayi da karfi ta hassalashi sai datayi knowcking har sau biyu bai amsa ba dan haka tayi tunanin ko dai abun nashi ne ya motsa karta cigaba ya taso yaci ubanta dan haka ta juya cikin tsanani tsoro ta koma ɗakinta ta shiga gyara gidan , bayan ta gama gyara ko'ina bayi ta shiga tayi wanka tana addu'ar Allah ya cire masa komai a zuciyarsa tare da sanya masa hakuri da soyayyarta su cigaba da rayuwarsu kamar ko wasu ma'aurata ,ta fito ta shirya kanta cikin doguwar riga win colour wanda akayi mata ado da duwatsu baki yayinda hannun rigar ta kasance mai hannun roba tayi rolling kanta da mayafin doguwar rigar ta dauki turare mai dadin kamshi ta feshe ilahirin jikinta ta tsaya shiru tana tunanin abun yi tana jin tsoro kar abincin yayi sanyi batare daya ci ba a hankali ta dinga daga kafafunta har ta fito taje ta haɗa komai akan tire ta sake nufo parlour'n wannan karon bata tsaya knowcking ba ta tura kofar ta shiga tare da rufe kofar a hankali ta tsaya jikin kofar ."


a natse ya d'ago kyawawan Idanunshi masu firgitarwa ya zuba mata karaf Idanunshi suka tsarke cikin nata ya dinga mata wani irin kallo da shi kansa bai san yana yi mata shi ba tayi kyau sosai sam ba zakace tayi aure ba bare kayi tunanin tana da yara ba , take jikinta ya dauki rawa gaba-daya ta daburce saboda Idanunshi dake yawo ajikinta tiren hannunta ne ya kusan kufewa saboda rawar da jikinta keyi tayi saurin rikewa gam tana kokarin saisaita natsuwarta ganin haka yasa ya dauke kanshi a hankali batare daya furta komai ba ya cigaba da abinda yake numfashin take janyowa da kyar tana fitarwa saboda bugawar da qirjinta keyi ta dinga takowa a hankali duk da Idanunshi basa kanta amman tana jinsu a gangar jikinta ta ajiye tray akan table din dake gabansa ta tsaya tana kare masa kallo murdadden jikinsa na sake ɗaukar hankalinta kana ganinsa ba sai an fada maka ba ,zaka fahimci zai yi karfi agurin aiwatar da komai
akan aikinsa ko gurin kula da matarsa, ya d'ago ya sake kallonta Idanunshi suka sake shiga cikin nata da sauri ta dauke idanunta duk ilahirin jikinta da muryarta na rawa tace "ga ..ga ...abinci nan .."
Bai ce mata komai ba ganin yau din ma dai kamar sauran lokutan baya ne yana jin saurata yasa ta matso gabansa a natse ta bude masa komai cikin tsananin tsoron karya yarfata ta juya a natse ta fita ta dauko flaks din ruwan zafi da cup da spoon ta shigo ta haɗa masa tea ta ajiye masa komai cikin tsoro tsoro ta dinga yi sannan kuma a natse tana mai addu'ar samun nasara , bayan kamar minti biyar tana tsaye tanav kallonsa cikin Sa'a taga ya ajiye aikin da yake ya fara cin abinci naunayen ajiyar zuciya ta sauke wanda yasashi dagowa ya kalleta ita kuwa wani irin dadi ne ya rufeta saboda wannan shine karo na farko da zai ci abincinta batare da tsamgma ko fada mata bakar magana ba , dan koda yaushe tayi masa tayin abinci sai yaga dama yake ciki wata rana yaci yana zaginta wata rana yaki ci tare da watsa mata ajiki ."

juyawa tayi ta fice a falon ta shiga d'akin baccinsu ta ɗauki wayarta ta dawo falon kasa ta zauna tana neman layin mumy kira ɗaya ta ɗauka ta gaisheta cike da girmamawa tana tambayi su Aryan ,"gasu can a falo suna wasa da kyar suka barni sai labarin germany suke bani ai wannan uban naki akwai magana dan har ma na saka masa suna labari dake shakiyi ne amsawa yake mumy ta k'arasa maganar tana dariya , Kisna ta saki murmushi cikin jin dadi tace "ai bambancinsa da arif kenan surutu "gaskiya kam akwai magana ba kamar dan'uwana ba baya da magana kowannesu yaci sunansa da'aka bashi daga hirarsu aryan suka shiga wata can kuma ta juye nasih mai ratsa jiki wanda kusan duk sanda zasu yi waya hakan ce take kasancewa ,a hankali zatayita nusar daita rayuwa da yadda zata sanyawa zuciyarta hakuri zama da mijinta da nawal cikin aminci batare data nuna damuwarta , da kuma yadda zata dage da yiwa mijinta biyayya da janyo hankalinsa ," ki ci-gaba da kokarin sauke hakin daya rataya a wunyaki na sha'anin mijinki kamar koda yaushe ba'a son mace ta cutar da mijinta shima namiji ba'a son ya cutar da matarsa a cikin al'amari na zaman aure saboda shi tun ba'a je ko'ina ba Allah ke sakayya ."

cike da sanyin jiki Kisna ta dinga yiwa mumy godiya "na gode mumy ina alfahari da samun nagartaccen uwa irinki ,Allah ya qara miki lafiya ki dade kiyi nisan kwana ta karasa maganar tana goge hawayenta a daidai lokacin da muradi ya fito rike da bakar jaka cikin shigarsa ta ko yaushe suit ko kananan kaya d'ago idanunta tayi a hankali ya sauka akanshi a hankali ya kauda kanshi ya cigaba da tafiya ta yunkura ta tashi tare da cewa mumy" zan kiraki back " ta biyosa tana masa Allah ya kiyayye tare da kokarin amsar jakar hannunsa cikin kasalalliyar muryarsa yace "ki koma kiji da mumy yana gama fadar haka ya tura kofar ya fita ta tsaya shiru agurin kafin daga baya ta dawo mazauninta ta dauki wayar ta sake nemanta suka ci-gaba da wayarsu tana nan zaune gurin shabiyun rana aunty zee ta shigo can bayan kamar awa biyu sai ga safy ta shigo nan ta iske kisna da aunty zee zaune ta cire mayafinta ta ajiye ta zauna suka gaisa suka ci-gaba da hira safy tace "a she kisna haka kika yiwa muradi lallai dole idan yayi miki abu kiki jin haushinsa kuma baki son ganin lafinsa, wallahi yayi hakuri zama dake kuma muradi namijin duniya ne ."


kisna ta sauke numfashi tana kallonta "ku bakusan wani abu ba ai qarata muradi ya kai gurin nasir shi kuma ya shigo gida ya bude min wuta ta inda yake shiga bata nan yake fita ba ingaya muku har zuciya ta kwashesa ya fada min abinda na dade ina binsa ya fada min akanki yaki wallahi bakiji yadda jikina yayi sanyi ba har kuka nayi lokacin da kika cire cikin yaran nan uku , Kisna kinyi karfin hali ya'yanki fa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login