Showing 288001 words to 291000 words out of 495987 words

Chapter 97 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

kisna suke ciki na afra ya ninka nasu dan tamkar zatayi hauka lokacin da ya badamasi yake sanar daita hukunci dady ,dawowa tayi tamkar mahaukaciya sabuwar kamu nan ta hau sambatu da surutai "aure kuma ?" "wani irin aure kuma auren ma da kisna ?" kisna tawa kai dan Allah ka natsu ka fada min abinda kwakwaluwata zata dauka "ke yanzu meye damuwarki da wannan matter din da zaki wani daga hankalinki ? "A'a babu komai kawai dai sai kuma ai ....." sai kuma tayi shiru ta nufi ɗakinta da gudu ya tsurawa bayanta ido yana dubanta zuciyarsa cike da tunani iri iri ".

****
Daren ranar muradi tunani da fargaban auren kisna bai bar kanshi ba duk inda ya juya yanayin zamansu yake gani duk Samir na hankalce dashi har sanda ya mike ya zira silipas ya fita daga dakin kai tsaye saman gidan gaba-daya ya nufa ya shiga shawagi rungume da hannunsa a qirji yana sake tunanin yadda zai yi rayuwar aure da kisna tafiya yake a hankali yana kallon gabas ,a hankali yaga mutun a gabansa sauran kadan suyi karo da sauri suka ja baya da sauri suna sauke naunauyen numfashi shiru dukkaninsu sukayi kowannensu babu wanda numfashinsa bai fita da sauri ba saboda ganin dan'uwansa a daidai wannan lokacin kisna ce ta soma juyawa tana jan dogon tsaki saboda ciwo da radadin da ta ji a zuciyarta data fahimci ko waye , tafiya take tana rausaya kunneta manne da waya tana magana kasa kasa , shi kuma kokarin fincikota yayi dan ya tsani tsakin da take masa a duk sanda suka haɗu amman saboda kar ya zubar da aji da kimarsa yasa ya danne zuciyarsa dan damuwa da tsakinta zai sa ta dauka da gaske ya damu daita alhalin taimakawa rayuwar kawai zai yi ..."

"Yanzu me kake ganin za'a yi ifemi nifa bazan iya wannan biyayyar ba ka nemo mana abun yi sati daya ne kawai ? "Okay yanzu naji bayani tana waya muradi yazo ya raba ta gefenta yana matse jikinsa dan kar jikinsu ya hadu , itama matse jikinta tayi ta manne da step amman hakan bai hana hancinta zuko daddadan kamshin turarensa ba tsaki ta sake ja tare da cewa " wallahi mutun zai gwammace mutuwarsa da rayuwa dani ,dan gara mutun ya je ya rungumi transformer da rungumar aurena da yayi me ma yasa nake wannan hasashen abinda bazai taba faruwa ba ? "Dan Iya church kawai masu galihu ma ba'a aauresu ba sai marasa galihu wanda ubansa ya nuna baya qaunar ganinsa " duk ganganunta suna shiga kunnensa daya bayan daya sai dai duk cikin kalmarta kalma daya ce ta sotsa masa rai wato "dan iya church dan ta mahaifinsa wannan baya gabansa dan har mancewa yake yana da wani uba a raye , bai juyo ba ya cigaba da tafiya haka zalika bata daina zaginsa ba tana rike da waya har ya sauka akan step .."..

Zaune afra take a tsakiyar gadonta ta rafka uban tagumi a daidai wannan lokaci da take jin tana gaf da rasa ranta gaba-daya ta hargitse cikin damuwa da zullumi da rashin sanin madafar tunaninta abu daya tasani shine tana tsananin qaunar muradi da dukkanin rayuwarta fiyye da son da kisna take wa Musa dan da za'a daura soyayyar kowannensu akan sikili lallai wanda takewa muradi zai ninka wanda kisna takewa musa," wayyo Allah na shiga uku " ta furta da matsanancin karfi tare da daura hannuwanta duka a saman kanta qirjinta na mata wani irin azababben zafi , a firgice ya badamasi ya farka daga baccinsa ya tashi zaune lokacin qarfe biyu daidai ya nufi ɗakinta da sauri inda ya isketa tana kuka tana ihu ya tattara jallabiyarsa sannan ya hau gadon ya rungumota jikinsa yana tattara gashin kanta daya baje ya rufe mata fuska "menene baby love ?
Da wani irin karfe ta fixge jikinta tana kuka ""Ka sakeni bana sonka bana qaunarka kuma bazan taba sonka ba har duniya ta nade ,ka cuceni ka tauye min zuciya ka tauye min rayuwa mai yasa ka aureni ? tayi maganar a firgice tamkar mahaukaciya "bana yin auren wallahi yau sai ka sakeni idan ba haka ba zan kasheka na kashe kaina kowa ya huta "me ya kawo waɗan nan maganganu "? yasan afra bata son sa amman bai dauka zata iya furta masa a zahiri ba wasu abubuwa yaga tana yi kamar mai aljanu har dasu sadarewa kunfa na fitowa a bakinta yayi tunanin lallai kodai aljanu sun shigeta ne ya kamkameta yana kiran layin dady kafin kace me tuni dady ya hallara kallo daya yayi mata yace "iska ne dan haka ya shiga yi mata addu'ar nan kuwa afra tana jinsu radau fahimtar dady tayi ne yasa ta ɗan dawo daidai sai gurin uku da wani abu bacci ya dauketa . washegari gidan ya cika makil da yan'uwa har mahaifiyarta tana ganinta ta rungumeta ajikinta tana kuka "shinkenan mumy na rasa shi kisna zai aura wallahi mutuwa zanyi mom ki taimakeni ..."mahaifiyarta ta dinga shafa bayanta "hakuri zakiyi afra wa yace miki kisna zai aura ?"ya badamasi kuma ya tabbatar da wannan hukuncin dady ne ni dai kiyi duk yadda za'a yi na rabu da wannan auren na aureshi "bazan iya ba afra bazan iya kashe miki aure ba saboda wani banza can ki natsu ki sanyawa zuciyarki natsuwa me kika nema rasa me mijinki ya rasa da zaki dauki son wani namiji ki sawa ranki ?
"bari kiji na fada miki bai zama lallai idan kin kashe aurenki wannan yaron ya au...... saurin katse maganar mumy tayi sakamakon inuwar ya badamasi da mumy ta hango a jikin labulen kofa take ta soma gogewa afra hawayenta jin sun yi shiru ya juya cikin tsananin tunani da tashin hankali "me maganar mum din afra yake nufi ?"waye idan wannan yaron da idan ta kashe aurenta bazai aureta ba ?iya abinda yaji kenan daga bakin mahaifiyarta kenan afra akwai wanda take so ne bai sani ba ya aureta ? idan kuma akwai waye shi wannan yaron ?"yayi wa kanshi tambayar da bashi da mai bashi amsar tambayoyinsa sai afra ko ita mahaifiyarta gidan ya bari gaba-daya ya koma office saboda zuciyarsa dake tafarfasa .."

*****
Bayan kwana ɗaya da faruwar lamarin dady ya canza mai gadi sai dai ya bar tsohon mai gadinsa, ya bawa sabon mai gadin umarni kuma a gaban kowa a gidan" kada ya kuskura ya bar kisna ta karaso ko bakin get din gidan bare fita idan tayi masa mutsu ko taurinka yayi mata duka idan ya dawo ya ganta kwance a sume zai ninka masa albashinsa yayi murmushi kawai yana girgiza kai shi dai muradi bai ce uhmmmm bare uhmmmm sai idanu daya zuba kisna ta rushe da kuka har da cewa "an tsaneta , zuciyarta haushin kowa take ji a cikin gidan hatta mum dad su kansu haushinsu take ji ta mike tsaye sai dai tarasa inda zata taji sanyi duk da suna waya da musa amman hankalinta baya jikinta ta rame sosai saboda damuwa idanunta sun yi ja saboda bakinciki ta fito kamar wata zautacciya tana isa falon daidai lokacin da suka dawo daga masallaci kowannensu rike da casbaha har muradi dake sanye cikin jallabiya ta gabanta suka gifta babu wanda yayi mata magana jikinta yayi sanyi komai ya sake kwance mata kai tsaye sama suka nufa bayan kamar minti goma suka sauko sai dai batare da muradi ba , kan table suka nufa kowa yaja plet din abinci yana zuba kansa abinda zai ci ita kuwa tsura musu ido kawai tayi zuciyarta kamar zata buga ...."

Zee ta fito daga dakin mumy ta karasa inda kisna take "tashi muje kici abinci kinji yar kanwata "bazan iya cin komai ba tayi maganar a sanyaye kamar zatayi kuka dan bata jin dadin zuciyarta da bakinta hatta miyon baki daci yake mata "Ki koyi hakuri kisna karki bari ki samu matsala da iyayenki akan namiji namijin da bashi da tabbas yanzu ka auri wanda iyayenka ma suka saka albarka a auren ma ya aka kare bare wanda suka ce basa so ?"ya Aliyu mutumin kirki kema kin sani sai dai idan zaki ki fadar gaskiya mutun ne da mata suke bala'in sonshi baya sauraransu" Allah wadan mata da tarin mutanen dake son sa ," ayi mutun ba fara'a ba annushuwa banza mara galihu dashi amman ku zauna kuna yaba masa ta fada a fili tana gyara zamanta dan bata ki duk su dady suji ba " sam bana kaunar ganinsa tuntuni bare yanzu da tsanar ke da dalili "na tsaneshi bana son ganinsa ta fada kamar zatayi kuka idanunta na kan su dady dake zaune a dining ya madu ya zuba ferfesun hanta da koda bayan ya gama cin tuwon shimkafa ya shiga aikawa cikinsa dan shi bashi lokacin wani rarrashin kisna dan gata ta samu ..."


Babu yadda ta iya haka zee ta takura mata suka karasa dining table gabadaya ta kalli abinci dake kan table duk bata ji shawar komai ba dan haka ta shiga bin plet din mutane da kallo sautin Muryar dady taji yana cewa "wai ina Ali ya shige ne ?yayi maganar yana kallon Samir "yana daki nace ya taso muje muyi dinner amman yace ya gaji bazai iya tasowa ba dady ya girgiza kai dan yasan abinda ke damunsa ya maida kansa ga kallon kisna "tashi maza kije ki kai masa nasa abinci take ta zunburo baki ",'dady ai ni bansan abinda yake son ci ba " eh nasani ai ki zuba masa abinda ya dace tunda ba abinci kala daya bane agurin .
ranta a bace ta soma kokarin zuba masa "kirki zuba masa soyayyen masa saboda bai fiyye son cin abinci mara nauyi ba Samir ya fadi haka ganin masa take kokarin zuba masa a ranta tace " giwa kenan komai sai mai karfi babu yadda ta iya ta juye wanda ta fara zuba masa ta zuba masa tuwan shinkafa da miyar wake abinda tasani ne tun tasowarta baya gajiya dashi da wake da shinkafa amman dangin taliya da tsurar shinkafa duk basa gabansa saboda basa rike masa ciki ta jera akan ture ta nufi hanyar sama" ina ma zan samu shinkafar bera wallahi da barba masa zanyi ya ci ya mutu kawai na huta babu sallama ta shiga dakin dan a ganinta yin sallama a dakin bai zama dole ba saboda mutumin dake dakin ,dakin tsit baka jin sautin komai sai na ac yana kwance a saman carpet daga shi sai dogon wando babu riga ajikinsa yana ganinta ya zabura ya mike yaja bargo ya lullube jikinsa dashi yana kallonta dariya ta kusan kufce mata duk da ɓacin ran da take tattare dashi "kai wannan akwai dolo ,wannan irin gidadanci fa ?
"to meye ma abun boyewa anan ?tayi maganar tana jan tsaki amman kuma ilahirin qirjin nasa suna da kyau daga kwantaccen bakin gashin dake kwance a qirjinsa zasu yi laushi sai dai ko daya basu burgeta ba ta ta'be baki ta dungura masa abincin ta juya abinta tana sake jan tsaki .."

"Ke zo nan ya fada a harzuke da sauri ta juyo saboda bakinciki kalmar ke din da ya fada "kwashe kayan ki bana bukatar komai daga gareki wani tsaki taja masa ta duka ta dauki tire tayi gaba "ji mana ya fada a kasalance ta tsaya cak batare data juyo ba sai dai idanunwanta a warwaje suke "daga yau karki kuma shigo mana daki batare da izinin ko sallama ba " a hanzarce ta juyo idanunwanta akanshi "kai kuma a suwa kenan kare da gudun layya ? "Ka tsaya matsayinka kai ma kasan baka isa ba kuma baka kai matsayin dani kisna zan maka sallama ko neman izininka ba saboda nan gidan ubana ne ko yau dady ya mutu dole a raba gado dani kai fa "..
"Abu na gaba mutun nawa ne muslimai acikin dangin iya church ?" "Mutun shi ba kowan kowa ba sai kutirin kinibibi da dagawa da nuna kai Allah yasa an hasali balbela ta taalbaleshi da bala'i da harara "banza mai kwadayi yaga fresh body shine har da wani saurin amsar aure kolelenka wallahi nan gani nan bari tayi gaba tana zaginsa "da kinsan yadda matsayinki yake a zuciyata da kin sausaurawa kanki yayi maganar a zuciyarsa tana dawowa ta dire abincin tana cewa yace"kar a dame sa baya ci " da sauri dady ya mike "dauko abincin ki biyoni dashi "a'a ya fa ce baya ci "a'a din kaniyarki ki dauko ki biyoni nace " babu yadda ta iya ta dauka ta biyosa haka suka samesa sai dai yanzu idanunwansa sun kada sunyi ja dady ya duka ya shafo wuyansa da bayan hannunsa yana cewa "meke damunka dana ? Ya yunkura ya tashi zaune yana fadar "babu komai dady kawai gajiya ce "ai na lura , na sanka da rashin son hayani nasan duk hayaniyar maganar auren nan ce ta maida kai hk ka daure ka tashi kaci wani abu ka sha magani "ban iya cin komai dady dady ya dubi kisna ",meye a cikin nan ? "Abincin gado ne ?"ban gane abincin gado ba ke wai wasa ake dake ne da kike wa mutane magana a tsaye haka ?

Dady da kanshi ya bude yaga abinda ke ciki ya dubeshi "zaka iya cin abincinka ne ko kuma a dafa maka wani ? Ya girgiza kai alamun "a'a dan iya gaskiyarsa ya fada baya bukatar cin komai dan baya jin dadin bakinsa "me kake so ci ? Idan zan samu coslow da rice and beans"
Dady ya juyo ya kalli kisna maza tashi ki samo masa abinda ya bukata ta zaro ido waje "dady a ina kenan za'a samu ya dan kura mata ido yana kallonta kafin daga baya yace "yi hakuri kije kiyi masa kinga bashi da lafiya " to ni ina ruwana da rashin lafiyarsa ya ma mutu na hutu "? ta fada a ranta a zahiri kuwa idanuwanta ne suka yi raurau tace "dady ai bamu da komai na hadin coslow muradi yace "akwai a kitchen dinmu ki shiga baza'a rasa komai ba ya fada yana runtse idanunsa "dady yace "yauwa maza tashi ki hado masa ki kuma zauna ki tsareshi yaci sosai kinji "wallahi nifa ban iya ba "tayi maganar kamar zatayi kuka "nasani ai baki iya amman ki daure kiyi masa ta mike ta baro dakin tana tsinewa muradi karo sukayi da madu "ya Aliyun kike tsinewa haka ?tayi saurin girgiza masa kai "shi kike tsinewa mana bayan na jiki "Allah bashi bane " tayi maganar tana hawaye "Okay na dauka shine yanzu na soma kutubal dake da Allah bar gurin wawiya kawai ..."
ta haɗa coslow da abinci ta kai masa karshe dai ƙasa yaci yayi daman kuma yasan ba wani abun kirki zatayi ba saboda kwanciyar hankalin dady dan yasan muddin bai ci wani abu hankalinsa bazai kwanta ba "
Dady na zaune aunty ummi ta samesa akan Samir yace a hada bikinsa zee dady yace "babu damuwa zai nemi mahaifinta , koda ya samu mahaifin zee cewa yayi "ai diyarsa ce dan me zai samesa da maganar ,ai ya taimaka masa da yanzu tana hannunsa shi zai yi komai yanzu da yake fama da kanshi na abinci ma sai mumy ta taimaka masa dan kamar ya sani ya turo rabi ta nemi alfarma dawowar zainab ..."

*****


Ana sauran kwana biyar daurin aure dady ya buga iv ya fara aikawa yan'uwa da abokan arziki ciki har da alhj tijjani muhamud adam da Abubakar tafida sun sha mamakin ganin wanda kisna zata aura ,yini muradi na tare da dady su shiga nan su fita nan abinci ma basu samu damar ci ba sai bayan la'asar suka dawo gidan da kyar muradi yake hadiye abinci saboda azabar damuwar da take zuciyarsa yana iya kokarinsa dan kar su fahimcesa saboda yasan basa son damuwarsa yana zaune shiru a dakinsu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login