Showing 348001 words to 351000 words out of 495987 words
Chapter 117 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
bazaki iya haihuwa da kanki ba dan wannan allurar da zarar anyiwa mutun zata taimaka masa gurin sauƙin nakuda ,wannan cire cikin ya zamanto karo na karshe da zakiyi idan ba haka ba zaki iya rasa ranki " "Kisna dai na jinta bata amsa mata ba dan babu tsautsayin zai kaita sake ɗaukar wani cikin ,Allah Allah ta dinga yi a sallamesu su wuce gida ta kaiwa muradi sakamakon taurin kansa ya gani bed rest aka bata na wasu awani ."
karfe bakwai daidai na safiyar ranar suka dauki hanyar komawa gida "kina jina Kisna karki kai masa gangar jikin yaran nan mu samu wani guri mu yardasu mu ƙara gaba "Kisna ta girgiza mata kai alamun a'a "zan kai masa abunsa ya gani zuciyarsa ta tarwatse ai muddin bai ga yaran nan ba wallahi ruhina bazai samu salama ba "suna zaune acikin taxi suna tautaunawa inda afra tafi jan ra'ayin Kisna akan su yar da yaran ita kuma ta rantse sai ta kai masa ya gani babu kalar rarrashin da bata mata ba dan ita gabadaya tsoro ya shigeta bata ma San me zata fadawa mijinta ba a ina zata ce masa ta kwana ?" har suka karaso isolo inda suka dauketa afra tana can duniyar tunani har sai da kisna ta tabota tayi firgigib ta dawo haiyacinta "mun fa zo inda zaki sauka " numfashi ta sauke da ajiyar zuciya atare sannan ta yunkura ta fito suka qara gaba jikin afra a sanyaye ta bi bayan motar da kallo tana jinjina taurin kai irin na Kisna bata taɓa nadama da danasani aikatawa muradi mugunta ba a rayuwarta irin na yau ,sosai taji abun ajikinta da zuciyarta ,gangar jikinta da zuciyarta suka shiga matsanancin damuwa banda rawa babu abinda suke da kyar ta sanyawa jikinta jarumta ta shiga mota zuwa unguwarsu .."
*****
Karfe tara daidai Kisna ta karaso bakin get din gidanta ta iske shi kamar yadda ta barshi ta shiga ciki tana daga kafafunta da kyar ,
A hankali ta leka d'akin mai gadi bata gansa ba ta kada kafadunta ta kara gaba zuwa bakin kofar shiga falo ta ciro key ta bude tana shiga cikin parlour ta zare key tana kallon falon nan ta fahimci muradi na gida sai dai bai falo dan haka ta ajiye masa bakar laidar dake rike a hannunta akan table ta yadda zai gani da kyau daman kuma ga jakar office dinsa nan da system dinsa ta shiga kitchen ta daura ruwan zafi ta sha haɗe maganin da likita ta bata sannan ta shige ɗakinta , kai tsaye ta shiga bathroom ta haɗa ruwan zafi tayi wanka da tsarki ta dawo ta canza kaya zuwa na bacci ta kashe duk wutan d'akin ta kwanta akan gado tana sauke numfashi dan har lokacin safiya ce gashi wani irin baccin take ji dan da kyar take bude idanunta ."
A hankali ta soma gyangyadi daga karshe bacci ya d'auketa muradi ya shigo dakin a matukar zuciye ya kunna wutar dakin haske ya gauraye d'akin sannan ya tasheta yana kiran sunanta , idanuwanta ta bude da kyar taga yana zaro mata ido" tashi Malama kiyi min bayani inda kike je wato iskancinki ya samu promotion har kinsan kisa kafa ki fita da aurenki ki kwana a wani guri kuma ɗan rashin mutunci ki dawo min gida.
"ta d'ago kanta ta dubeshi sama da kasa a wulakancinki sai dai babu fuskar yi masa mutsu , inda agogo yake ta kalla karfe shadaya saura sannan ta duro daga saman gadon ta dauki after dress dinta ta d'aura akan kayan bacci dake sanye ajikinta ta sake kallon fuskarsa babu wasa yace "gidan ubanwa kika je kika kwana jiya ? "tayi masa banza tana hura masa hanci tare da cika tana batsewa ya buga mata tsawa "ina wasa dake ne ina magana kina jina ?" Tayi hanyar waje tana cewa "ka daina tada jijiyar wuya kamar wani ubana" tuni ya cimmata a tsakiyar falon tana tafiya da kyar kai tsaye kitchen ta shigewarta ta soma hada ruwan tea ya biyota yace "wato gurin wancan katon jakin kikaje kika kwana kou saboda ke dakikiya ce da baki san hakin aure ba ? Kaga malam bana son damuwa kasan irin abinda zaka dinga fada min idan ma dakikiyar ce an daure maka ita ne ? "Sannan kuma idan gurin musa naje na kwana kai tsaye zan fada maka dan babu abinda zaka iya tunda na iya fadawa ubana daya kawo duniya naje gurin Musa na kwana babu uban da zan tsaya ina wa karya ".
muryarsa a sanyaye kamar zai yi kuka yace"to ina kika je kika kwanta ? "Kaga dan Allah ka sarara min dan yanzu haka bana jin dadin jikina ban son yawon magana "ta karashe maganar tana cigaba da abinda take hankalinta kwance tana gamawa ta raba ta gefensa ta wuce ta shige ɗakinta ta cire after dress ta zauna tana sauke numfashi a hankali ya shigo d'akin ya zauna a gabanta yana kamo hannuwanta cikin nashi ta soma ƙoƙarin cirewa sai dai ta kasa "ya jikinki naki yanzu ko zamu hospital ne ?kanta kawai ta girgiza masa tana sake janye hannunta tana furzar da iska amman Sam yaki saki ya rike gam yana murzawa a hankali yana kallonta gabansa na wani irin faduwa wanda ya rasa dalili kusan minti biyar yana zaune a gabanta yana kallonta kafin daga baya ya mike tsaye ya rankwafo yayi kising dinta sannan yace "ki kula da kanki plz zane asibiti naga sanusi akan ta'asar da kika masa ya fice yana duba agogon hannunsa ,bayansa tabi da kallo tana ta'be baki hade da zabga masa harara , ranar yuni tayi a daki kwance dan tashi yin sallah ma ba'a magana har dare tana kwance tana Allah Allah ya dawo yaga sakonsa .."
Tana nan kwance ta fara jin faduwar gaba mai tsanani sai dai ta dinga sharewa gashi dai bacci take son yi amman tsananin tsoro ya hanata runtsawa duk yadda taso ta manta abinda ta aikata hakan ya garara dare yayi ta kasa runtsawa gbdy sai kusan asuba bacci ya saceta koda ya leko yaga bacci take bai tasheta ba ya juya ya fita zuwa parlour shiru yayi yana kallon falon saboda sauyin yanayi daya samu tun daya fita zuwa Masallaci yake jin wani cent, shi ba warin bera ba shi bai san da me zai kira warin ba ya shiga kitchen dan samar mata abinda zata ci ."wajen guraren karfe shadaya ya dawo ya tarar daita still kwance sai dai idanunta biyu a sukwane yace "sannu ya jikin naki ? Ki tashi ga abinci can kici "bazan ci ba ko dole sai naci nifa banason damuwa kana daga min hankali wallahi gyara zama yayi ya fuskanceta sosai "ni ne ma nake daga miki hankali ? Tace "sosai kuwa kana damuna wallahi ta fada tana durowa ta fito ta shige kitchen ya biyota yana cewa " shi wancan bakar laidar meye ciki ne da kika ajiyewa mutane har ya fara wari ? yayi maganar kamar ya kamota ya rufeta da duka saboda takaicin rashin kula da gidan da batayi "oh ! baka bude kaga abinda yake ciki bane tun jiya ? Ya kalleta qirjinsa na dokawa da sauri "gaskiya ya kamata kaje ka bude kaga jarababbun yaranka dake ciki ,ai su naje cirewa shekaranjiya shiyasa ban kwana a gida ba ta karashe maganar tana cigaba da abinda take shiru yayi yana dubanta cikin tsananin tsoro da firgici kafin daga baya ya karaso inda take tsaye tana kurba ruwan tea bai tsaya wata wata ba ya dage rigar jikinta sama aiko yaga wayam babu dan tudun da cikinta yayi ya d'ago a gigice ya kalleta , zuciyarsa cike da tsoro ya kama hanyar komawa falo inda bakar laida take ajiye jikinsa na wani irin rawa ya dauki laidar ya bude sosai yana sake dubawa tun awanin da suka gabata yaji cent din falon ya canza ya leka cikin laidar sai dai bai fahimci komai ba shiyasa ma ya tambayeta dan yasan itace ta shigo da laidar dan ko daya bar gurin jiya kafin dawowarta babu laidar , abinda ya gani ya bala'in bugar masa da zuciya cikin matsanancin ɓacin rai yake kallon halittar Allah da ba'a gama karasa halitta su ba cikin jini ,ya dinga jin kamar ya suma a gurin ya farfaɗo yaga karya ne ba ya'yansa bane aka wulakanta masa su , hanyar fita ya nufa saboda rasa abinda zai yi sai dai hanyar ta hade masa take ya fara ganin biyu biyu dan haka sulalewa yayi a kasa ya daura gwiwowar hannunsa akan gwiwar ƙafarsa daya tare da dafe goshinsa yana furta kalmar Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un allahumma ajirni fi musibatihi waklifni khairan minha sai faman juya girman abinda tayi masa yake yana sake maimaita kalmar Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un kamar ya daura hannuwansa duka saman kansa ya kurma ihu ko yaji sauƙin zafin da zuciyarsa ke masa ,nan take kansa yayi mummunar sarawa gabadaya ya rasa abunyi ........."
Yana zaune tsananin cikin jimamin abinda ta aika masa ta fito tana tafiya daya bayan daya ta tsaya a gabansa "Sarkin naci kenan kaga karshen inda nacinka ya kai ka ko ?" Kadan kagani a cikin tsanar dana yi maka , dan wallahi kai kanka baka fi karfin na kasheka har lahira ba na huta da rayuwa da kai "a sukwane ya d'ago kanshi ya zuba mata idanushi da suka rikide suka koma ja tsabar damuwa da tashin hankali daya tsinci kanshi Kallonta kawai yake numfashinsa na neman daukewa daga gangar jikinsa yana jin ina ma kashe shi din tayi da wannan aika aikan data masa, a hankali yasa duka hannuwansa ya toshe kunnuwansa saboda baya qaunar cigaba da jin sautin muryarta ana cikin wannan halin sai ga jahid da habib sun iso bakin kofa tare da rafka sallama shi dai muradi bai ko ji sallamarsu ba domin kuwa ya dawo tamkar matacce agurin toshe da kunnnewansa ga wani irin zufa dake tsatsafo masa a gabadaya ilahirin jikinsa kamar an watsa masa ruwa da kyar ta bude baki ta amsa sallamar tana cewa "waye ? "Mune suka bata amsa daga waje gane ko su waye yasa tace "yauwa ku shigo kuga yadda karshen dan nacin nan ya dawo ".
suka sanyo kai bakinsu dauke da wata sallamar sai dai ganin halin da muradi yake ciki yasa basu bi ta kan kisna ba suka yo kansa suna tambayarsa abinda ya sameshi ,shi kuwa kasa magana yayi ya kamo lip's dinsa na kasa yana taunawa da karfin gaske fuskarsa dake cikin rudani da tashin hankali suka zubawa ido dan son gano abinda ke faruwa dashi ,sai da sukayi magana ya kai sau goma sannan ya iya kokarin nuna musu bakar laida ai take hankalinsu ya tashi jikinsu ya kama rawa dan tsab suka fahimci ya'ya ne aciki nan take suka zuzuge labulen falon suna cewa "garin yaya haka ta faru"garin shegen nacinsa kisna ta basu amsa daga inda take tsaye a bayansu rungume da hannuwanta su jahid basu kalli inda take bare ta fahimci sunji ko kuwa basu ji abinda tace ba suka kamo muradi zuwa kan kujera suka zaunar dashi wanda zuwa lokacin tuni Idanunshi sun fara fitar da kwalla rige rigen kai hannu saman goshinsa suke dan goge masa gumin dake tsatsafo da hawaye idanushi ya zuba musu ido yana furta "me yasa abubuwa suke zuwan min haka ? "meye laifina dana cancanci wannan sakamakon "?
"Wani laifi na yiwa Allah daya jarabeni da auren kisna a rayuwata ?" baka yiwa Allah komai ba haka qaddararka tazo kayi hakuri Habib ya karashen maganar yana tayashi zubar da hawaye muradi ya runtse Idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ta kasa sukuni sai zafi take masa ya motsa bakinsa a hankali "me ya kama nayi habib "..
Cikin kulawa habib yace "ka saketa ka hutawa rayuwarka dan wannan yarinyar azzaluma ce kuma muguwa sam babu digon imani a zuciyarta cigaba da zama daita bashi wani amfani dan wallahi zata iya kasheka" . a hankali muradi ya sake kamo lip's dinsa ya ciza da karfi alamun komai ya tsaya masa duniyar ma gaba-daya ta cukude masa guri daya duk ac dake aiki a falon hakan bai hana gumi cigaba da tsatsafo masa ba "wayyyohhly Allah ya furta a makoshi "ya'yan......" ya sake furtawa hawaye na zubo masa "ya'yan da zai fara samu a rayuwarsa kenan kuma sune a gabansa a wulakanta aka kawo masa idan ma mutuwa zai yi ya mutu me zai cewa wannan ranar ? " yau ta zo masa da abubuwan sai dai cike take da rudani da bakinciki "dan girman Allah muradi ka saki yarinyar nan dan ... "
"An so idan ha sake ni ? "ya sakeni mana ai nafi son haka tunda ba dole sai yayi rayuwa dani ba ,ko dole sai yayi rayuwa dani ne ? ta fada jahid haka tana fuskantar shi tana masa kallon banza " Me ma zanyi dashi a rayuwata ? " ai wallahi Dady ya gama cutata tunda ya rasa Wanda zai hadani aure dashi sai wannan abun , bari na fada muku abinda baku sani ba , shi din fa bakowa bane face mara galihu wanda tamkar me aikin gidanmu yake ,dan tsintuwa wanda aka tsinta akan titi Wanda babu da rashi na talauci yasa kanin mahaifina ya taimakawa rayuwarsa ya yantosa daga bauta zuwa yan'ci kai "ku yanzu ji kunyar jin haka ba shi kasan yasan abun kunya ne kasancewarsa miji gareni "..
" Kalleni sama da kasa Ka gani Aliyu nafi karfinka nafi karfin aurenka, ni ba kalar matar mara galihu irinka bace . "wallahi yau ko duniya zasu taru ko sama da kasa zasu hade ko zaayi ruwan jini sai ka sakeni domin babu ta yadda zan cigaba da rayuwar aure da kai " a mutukar zuciye jahid yace " wallahi babu abinda ke damunki sai tsabar jahilci da rashin cikakken ilmin addani, karancin ilimin addini shi yasa kikewa mijin aurenki hk ,wallahi da kina da cikakken ilimin addini da bazaki taba yiwa mijinki na sunnah haka ba ......."
"kai ne jahili dan talakawa kawai , danging matsiyata waye Kai ? Waye ubanka a garin nan da zaka shiga hurumin da bai shafeka ba ? "me ye ma matsalarka da matsalar gidanmu ?"okay wuyanka ya isa yanka tunda anzo cikin arziki da bana ubale aba ana birgima ana ci ana sha ba ai dole zaka zake dayawa , "shima wannan daya janyoku cikin arzikin da bana ubansa ba har ya nemi yafi ya'yan masu gida karfi bai isa bare kai karan kada miya shiga hankalinka babu ruwanka da matsalar gidana ......."
Ya Salam muradi ya furta kamar ya mike sai dai yasan yana mikewa kafadunsa bazasu iya d'aukarwa ba dan haka ya fara motsa bakinsa a hankali "habib kira min Samir ......."iya abinda ya iya furtawa kenan ya runtse Idanunshi tare da dauke numfashi "...
****"
Muna saida ingantattun maganin mata masu kyau da nagarta wanda ko da kudinka sai da rabonka tsimi , zumar Mata, gunba, gari insertion,kaza,zakara ,
jigida dadai sauransu.
1.Tsumi Yana saukarwa mace niima Kuma bazataji wuyar jimai ba.
2. Zuma Tana taimakawa wurin Jin sha'awa Kuma itama Tana taimakawa wurin jindadin jima'i.
3.insertion( Dan matsi)