Showing 45001 words to 48000 words out of 495987 words
Chapter 16 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number08059623096,
yauwa har ma da agwalumar cotonou mai dan Karan zaki muna turawa kowani gari ...🥰🥰
Shiru yayi yana kallonsu suna kuka zuciyarsa cike da matsanancin takaici , haka kawai tana neman d'agawa yaransa hankali a karon banza da kukanta ,qirjinsa sai faman tafasa yake , babu abinda ya tsana a rayuwarsa kamar yaga uwa da ya'yanta suna kuka rungume da juna wannan abu na bala'in d'aga masa hankali .. "wannan wacce irin tarbiyya ce yayi maganar a zafafe zuciyarsa na kuna "? "kin wani rungume yara kina ƙoƙarin gur'bata musu tunanin da wannan dakikancin naki "kina son nuna musu zalintarki nake saboda su tsane kou me "? yayi maganar a tsawa ce gaba-daya yaran suka sake makalewa jikinta suna kyarma
"kiyi kokarin yin duk abinda zai sa su tsane a cikin zuciyarsu wallahi kece zaki kwana a ciki dan nan kusa zan samu wasu ya'yan da zasu maye min gurbinsu aikin banza kawai komai kuka kamar wata matar mamaci ,da yarda Allah sai Allah ya maida miki mugun nufinki akanki ni bazan ga kuka a rayuwata ba ". ya k'arasa maganar tare d'aura hannunsa ɗaya akan sumar kansa dake kwance luf luf gwanin ban sha'awa kamar irin na areef da aryan ."
D'akin ya dauki shiru bata sake yunkurin yin kuka ba bare yaranta su tayata ,shima kuma bai sake cewa komai ba sai aikin jan tsakin da yake aika aika zuciyarsa na bugawa da karfi , a hankali ya runtse idanunshi da sukai jawur yana Allah wadai da irin halayyar wasu matan , ya furzar da iska sannan ya gyara kwanciyarsa cike da takaicinta yayi rigingine yana ƙara jin tsanarta a cikin zuciyarsa , ai muddin bai nika abinda tayi masa ba to bai kyautawa rayuwarsa ba, tamkar ya rako maza duniya ne , gara ya rama itama ta d'and'ani irin abinda yaji ."
Har goshin asuba kisna bata runtsa ba tana tsaye bisa kafafunta ta dukufa gurin kaiwa Allah kukanta , tasan abinda tayi masa yayi muni da yawa ,amman abinda yake mata a yanzu har duniya ta nad'e bazata taɓa mantawa ba, ta d'aga hannuwanta duka sama tana rokan Allah akan ya sanyaya zuciyarsa ,"Allah Kasanyawa Aliyu hakuri a cikin zuciyarsa , Allah kasan ina cikin tsananin damuwa akanshi , kasan yadda nake sonsa a halin yanzu karka bari zafin zuciyarsa ya rabamu alhalin ina tsananin son shi , Allah na tuba bazan sake aikata abinda nayi masa ba , Allah ka yafe min bisa kuskuren dana aikata ya Allah Aliyu bawanka ne kai kake da karfin ikon akansa ka gaugauta sanyaya zuciyarsa akaina ,Allah na rokeka da sunayenka tsarkaka ka sanyaya zuciyar aliyu yayi min afuwa Allah kasan ina son aliyu saboda kai ,Allah ka tausaya min saboda darajan fiyyayen halitta ,Allah kafi kowa sanin zuciyata nada rauni a kan bawanka Aliyu , Allah idan soyayyar da nake wa Aliyu alkhairi ne a rayuwata da addinina kasa Aliyu ya hakura ya dauki al'amarinmu da sauki idan babu alkhairi Allah ka cire min son ka raba tsakaninmu cikin sauki batare da tashin hankali ba sannan ka k'arawa mahaifiyata lafiya dan tayi namijin kokari akaina dan ganin rayuwarta ta inganta ba kowace uwa ce zatayi irin abinda mahaifiyata tayi min ba a ganiyar kuruciyata ta karashe addurta tare da haɗawa da yiwa yaranta akan Allah ya albarkaci rayuwar su sannan ta shafa addu'ar tare da shafawa akan yaranta da bacci yayi awon gaba dasu tuni ,bata tashi ba har sai data ji ana ƙoƙarin gabatar da sallar asuba sannan ta mike ta shiga bayi ta d'auro sabon alwala ta fito ta gabatar da sallah tayi azkar din safe sannan ta kwanta a kasa kusa da yaranta ta rungumesu ajikinta ..."
Washegari sai gurin karfe tara na safe ta tashi shima sautin zazzakar muryarsa ce ta dinga shiga kunnuwanta yana waya da coch dinsu , ta yunkura da kyar ta mike cikin sanyin jiki tana kallonsa suka hada ido shine yayi saurin janye kwayar idanunsa akanta yana yatsina fuska kamar yaga mugun abu , yaranta ta kamo ta soma yiwa wanka ta shiryasu cikin kananan kaya ta kai su dakin mumy sannan ta faɗa wanka ta jima acikin bayi tana saɓa jikinta da turarukan wanka masu kamshi sannan ta fito ta shirya cikin wata had'add'iyar doguwar riga wacce take da adon fulawa tun daga kasa har sama cikin kayan da mommy ta siyo mata ne jiya tayi tunanin ta saka ta gani kafin su bar kasar , ƙaramin gyale tasa ta nad'e kanta dashi kafarta na sanye da takalmi kalar kayan tayi matukar kyau kwarai babu wanda zai ganta bai sake Kallonta ba, gashi daman jikinta akwai shi da daukar kaya ,babu kayan da zata saka basu amshi jikinta ba , ta shafa hoda kadai a fuskarta dan bata damu da yin fente fenten a fuskarta ba sannan ta feshe duk ilahirin jikinta da ruwan turare .."
Aliyu dake tsaye sanye da kananan kaya wanda daka Kallesu kaga kalar kudi bama sai an faɗa maka adadin kudin kayan ba zaka fahimci iya tsadarsu ,ga tsabar kyau da kwarjini sai kace shi yayi kanshi ga siffarsa kamar dan larabawa , Allah dai yayi a kasar Nigeria za'a haifosa kuma acikin jinsin *zarma* amman idan ba faɗa maka aka yi ba bazakace asalinsa dan nigeria bane ."
kallon kasa da sama yayi mata hakan yasa tayi saurin durkushewa kasa a gabansa dan tasan ma'anar kallon cikin rawar murya tace "ina..ina kwana"? yaja dogon tsaki yana kawar da fuskarshi a ranshi yace "mai zan yi da ina kwananki "? jiki a sanyaye ta mike tana ƙoƙarin barin d'akin ba dai ta gaishesa ba kar ya amsa ita dai tayi , dan gaisuwar na cikin dokokin daya kafa mata ko ta sha mahaukacin mari , tana daf da barin d'akin tana rausaya taji sautin muryarsa mai shegen dadi da tsuma zuciya wanda tsautsayi yasa ya faɗa kunnuwansa koda kuwa bakar magana zai faɗa sai mutun yaji tasirinsa ajikinsa "tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin mace mai tsananin muni irin ki ba ......"
cak ta ja ta tsaya ta kasa cigaba da tafiya sannan ta kasa juyowa , sai dai take jikinta ya ɗauki rawa kamar mazari ta dinga bin jikinta da kallo gabanta na faduwa "ban taba ganin mace mara kyan fasali irinki ba yanzu ke nan har wani kyau kika yi da kike wani tafiya kina rausaya kamar wata gurguwa ..... "?
wannan karon da hanzarinta ta juyo gaba-daya ta zuba masa narkakkun idanunta tana kallonsa, ido cikin ido suke kallon juna zuciyarta na rawa cike da tsananin mamaki jin furucinsa " ya rabbi mai kuma nayi masa da safiyar nan yake aibantani haka ? ta yiwa kanta tambayar har lokacin idanunta na cikin nashi , take idanunta suka kad'a suka yi ja tsabar ɓacin rai da yake son haddasa mata . "me ke laifinna da sassafen nan da zai muzani haka wato dai Aliyu ba zai bar rayuwarta ta huta ba duk yadda zai yi ya dagula mata lissafi sai yayi daga wannan balain sai wannan
Allah ma yasa daga ita sai shi ne a dakin dan tasan ko agaban mutane haka zai mata dan ya kuntatawa rayuwarta ,bafa tsoronsa take ji ba kawai dai tana son gyara kuskurenta ne yasa take had'iye abubuwansa "
Ranta yayi bala'in 'bace akan abinda yayi mata yanzu a cikin ranta tace "lokaci ya kusa da zan taka maka burki akan abubuwan da yake mata ,a zahiri kuwa cewa tayi "wannan shine lokacin da zangargadeka matukar kana son zaman lafiya a gidan nan to ka fita hanyata kamar yadda kace na fita naka , idan ba haka ba zan rikeka a matsayin gawurtaccen makiyina da yake son kassara min rayuwa ,wai dole ne sai ka min magana ma tunda kace baka bukatar hakan a tsakaninmu " ai kace baka bukatar zama dani to ka sawwake min saboda nima yanzu ba bukatar zama nake da kai ba ka bani takardata dan Allah kaga aiki da cikawa ta k'arasa maganar tana sakar masa harara gabanta na faduwa dan karfin hali tayi kawai amman zuciyarta a matukar tsorace take da kalmar ya bata takardanta cikin sanyi jiki ta dinga daga kafafunta zuciyarta na zafi tana data sanin furta masa haka dan tasan halin zuciyarsa kadan da halinsa ya maka saki .."
Murmushin mugunta yayi dan abinda yafi bukatar gani kenan akan fuskarta damuwa da tashin hankali sannan ta bukaci rabuwa dashi da kanta kuma duk yayi nasarar haifar mata ,bai barta iya haka ba yace "ayi gaba dai zuciyata ta huta da tashi saboda ganin wannan mumnunar banzar fuskartaki mai mugun hali kawai ai nasan duk abinda kike faɗa akan kin canza karya ne dan ba zaki taɓa canzawa ba maganar zaki rikeni a matsayin gawurtaccen makiyinki ai nafi son haka , ke na ma fi makiyinki tasiri a rayuwarki idan baki manta ba ni dake makiyan juna ne baza mu taɓa sauyawa daga matakin da muke ba saki kuma tunda kin bukata sha kuruminki sa ido kiyi kallo kina zaune zai sameki saboda zama dake bashi da wani amfani dan bana sonki i really hate you ..........." abinda kunnuwanta suka jiyo mata kenan a lokacin da zata karasa ficewa daga d'akin kafafunta kawai take dagawa zuciyarta na zafi da rad'ad'i idan shi bai sonta ai ita tana son shi , dole ne sai ya furta baya sonta ko sai ya saketa ya barwa zuciyarsa mana har sanda zai aiwatar da niyyarsa akanta, Allah kaga bawanka Aliyu ko allah ka kawo min ɗauki ,kasa min dauriya amsar duk abinda zai zo daga garesa zama dashi ko rabuwa dashi "
Tsayawa tayi ta daidai natsuwarta tare da goge hawayenta sannan ta cigaba da tafiya a kan step ta hango aryan da areef suna rige rigen Isa gurin mommy gabad'aya suka faɗa kan cinyar mommy dake zaune saman doguwar kujera tana ware musu hannuwanta alamun su taho gareta Hajiya mommy ta dubi jikokinta cike da farincikin ganinsu cikin koshin lafiya, yayinda qaunarsu ke cigaba da ratsa kowani sashi na zuciyarta ,ta shafi kansu daya bayan daya tana yiwa Allah godiya daya azurta Aliyu da kisna da samun kyawawan ya'ya wanda take qauna fiyye da komai a duniya , mikewa tayi tare dasu suka isa dining table inda Samir da aunty zee ke zaune suna murmushin jin dadi ganin areef ya tashi lafiya babu wata matsala kisna ta karaso jikinta a matukar sanyaye ta durkusa har kasa tana gaishe da mommy "Ina kwana mommy .."? "Lafiya lau mamana kin tashi lafiya ya karfin jikin"?"Alhamdulillah naji sauki sosai ta sake fad'ad'a fuskarta da murmushi dan kwantar da hankalin mahaifiyarta , ta juya inda samir yake ta gaishe dashi da aunty zee.
aliyu ya sauko yana ciccin magani kamar wanda aka yiwa wani laifi ya gaishe da mommy cike da girmamawa ta amsa masa cikin sakin fuska ita dai tana son Aliyu arayuwarta a natse yaja kujera ya zauna kusa da Samir aunty zee ta kalleshi fuskata dauke da murmushi tace "Aliyu gadanga kusar yaki an tashi lafiya "? " Lafiya ya amsa mata a takaice yana danne danne a wayarsa ita kam kisna bata ce masa komai ba illa matsawa daga gefensa da tayi ta samu guri kusa da mahaifiyarta ta tsaya dan bazata iya da balainsa ba, shi kuwa Samir ko kallon inda yake bai yi ba hakan kuwa yayi mugun dagawa Aliyu hankali ya dan saci kallon inda yake yaga ya balain hade rai kuma hankalinsa baya kansa yana wani guri zuciyarsa yaji yana rawa zai iya daukar fushin kowa a duniya amman banda samir shi din ajin farko ne a zuciyarsa da rayuwarsa ."
Abinci sun kai kala uku dake kan dinning table din duk aunty zee ce ta dafa , kisna ta zubawa kowa har uban gayya , babu Wanda mommy bata bawa aryan da areef kadan kadan sun ci ba , suna ci suna hira duk sanda aryan yayi kokarin bawa mommy labarin abinda ya faru jiya sai kisna tayi saurin kai lomar abinci bakinsa "ya fa koshi amman naga sai tura masa abinci kike kamar jira aryan yake mommy tayi magana ya kwa'be fuska tare da buɗe baki yana nunawa mommy abinci "ka koshi kou .."?ya gyada mata kanshi mommy ta janyo tissue ta tara a daidai bakinsa "zubar a ciki karki sake bashi komai cikinsa ya koshi "okay mommy ta cigaba da tsakurar abinci, ta kai spoon bakinta kenan taji aryan ya soma magana granny "yesterday when you not a round areef was shocked and papa ....
"Shut up wa tambayeka mai shegen surutun tsiya tayi maganar tare da kai hannunta zata buge masa baki zaraf taji an rike tsintsiyar hannunta tunda taji saukar hannu tasan shine take qirjinta ya shiga dokawa dan bata san abinda hakan zai janyo ba tsoro da matsanancin firgici ne ya ziyarce gaba-daya ilahirin jikinta,ta d'ago kyawawan idanunta ta zuba masa tana kallonsa fuskarshi babu walwala gashi ya haɗe rai kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa a hankali tayi kasa da kanta dan bazata iya jura kallon kwayar idanunshi ba yayinda har lokacin yake rike da tsintsitar hannunta yana hukuntata da idanunshi gabad'aya ta rikice saboda idanunsa dake yawo ajikinta cikin ƙasaitacciyar muryarsa yace "don't ever try kisna Karki kuskura hannunki ya taɓa lafiyar jikin d'ana karya ya fada da kike ƙoƙarin dukansa "? A natse ta d'ago idanunta suna kallon juna ido cikin ido zuciyarsu na bugawa da karfi hankalinta yayi bala'in tashi bata son mommy ta san wani abu ya faru gashi yana ƙoƙarin fallasa komai tasan yayi haka ne dan mommy tayi mata faɗa yaji dadi "kana nufin shocking ne ya kama areef ta yaya hakan ya kasance "? mommy tayi magana hankalinta a matukar tashi tare da kamo areef din tana duba jikinsa take jikin kisna ya fara rawa ", Allah ne ya kikaye da tun jiya areef ya mutu bisa sakaci irin nata yanzu kuma aryan yayi magana tana ƙoƙarin dukansa nan ya kwashe komai ya fada momy ya karasa maganar yana numfasawa .."
Samir yace "ki kwantar da hankalinki mommy babu abinda ya samesa tun jiya ya ga doctor ayi masa duk abinda ya dace yayi maganar yana zabgawa Aliyu harara karaf idanun mommy ya sauka akan Samir "dan me zaka hararesa dan yayi magana idan kaine hakan ta faru killa sai kayi abinda ya fi nashi nan mommy ta dingawa kisna faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba ,momy ta kai hannunta ɗaya ta daura akan hannun areef tana shafa tsintsiyar hannunsa , cikin rawar murya kisna tace "am sorry mumy banza sake ba dan Allah ku bar maganar nan haka wallahi ina jin kamar na mutu ta karasa maganar hawaye na wanke mata fuska ta mike da sauri zata bar gurin Samir yayi saurin kamo hannunta cikin nashi "ina kuma zaki koma kiyi zamanki babu mai sake miki fada akan yaranki wasu hawaye masu zafi suka zubo mata bazan iya cigaba da zama a nan ba gara kawai na kama kaina nice fa na haifi areef ta yaya zan yi abinda zai cutar dashi ko mahaukaciyar kan bola ce ni bazan cutar da d'ana ba ... ..'
Nan kuma jikin mommy yayi sanyi tayi shiru tare da daura hannunta akan dinnig table tayi tagumi tana Kallonta ganin yadda take kuka tun daga kasan zuciyarta yasa momy tace "shikenan kiyi hakuri amman kinsan kiyi kuskure ko "?"Nasani kuma na bada hakuri me kuma zanyi masa saboda Allah idan dai ba kasheni zai yi ba .... aryan ya matso kusa da momy ya rike hannuta gam kamar zai yi kuka saboda ganin kisna na zubar da hawaye "Am sorry mommy bazan sake ba stop crying I don't want to see your tears mommy please Ki daina kuka kinji granny kice ta daina kuka "zaki sha ice cream zan sa papa ya kai mu Ki sha ice cream kinji".
"kinga aryan ma hakuri yake baki yaranki suna matukar sonki sosai kiyi hakuri saboda su duk rarrashin da Samir da aryan ke faman mata , haɗe rai tayi taki yin dariya "me kike son ayi miki ki huce autar momy dan gaskiya bazamu barki haka cikin fushi ba , idan kika ki hakura nasan yau bamu ba ganin farar momy an tabo mata auta gabad'aya suka sa dariya har momy banda Aliyu da yayi bala'in bata rai jin furucin wai ya'yanta suna sonta shi kuma fa ko oho kenan "?
Fuskarta shimfide da murmushin jin dadi tace "zaku kaini gurin shakatawa "dan wannan ai mai sauki ne saki ranki yau ba sai gobe ba za'a kai ki duk inda kike so , dariya tayi Jin tautaunawarsu yasa aliyu ya mike ya koma kan doguwar kujera ya kwanta kasancewar weekend ne babu inda zashi samir yace "ranka shi dade sarkin zuciya kaji abinda uwar gida take buƙata ya kamata ayi mata abinda take so yau tunda weekend ne " yayi maganar yana haɗe rai haɗe da harararsa kamar yace baza shi ba saboda kisna ce ta bukaci fitar amman bazai iya ba saboda Samir zai iya yin komai ga kuma uwar gayya mommy dake gurin ya kasa fadar haka yace "babu matsala idan kun shirya ka min magana kisna ta kwashe kwanuka da suka ci abinci ta shiga Kitchen ta dawo ta gyara dinning table ta sake komawa dan wanke kwanuka .."
Kowa ya watse parloun ya saura daga Aliyu sai Samir duk yadda Aliyu yayi kokarin son magana Samir yayi