Showing 6001 words to 9000 words out of 495987 words

Chapter 3 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

sanye  ajikinsa .."

Take  Jikinta  ya  sake  ɗaukar  rawa  sakamakon  irin  kallon iskan  da  yake  jifanta dashi  , yayinda  zuciyarta  ke dokawa da matsanancin karfin gaske ,  da  sauri  ta durkushe  a gabansa tare da haɗe hannuwanta duka  "dan   girman Allah kayi  hakuri  nasan nayi kuskure ,  karka dakeni nayi  maka  alkawarin  bazan sake ba  "..
  ya   zuba  mata kyawawan  idanunshi kawai  yana  kallonta "kayi  hakuri  nasan cutar da  kai  na sakaka cikin damuwa  nasan wannan kadai  zai ......."
"Shiiiii........" ya  d'aura  yatsansa   ɗaya  akan lip's  d'insa " karki  sake na  sake  jin  sound d'inki anan  "kin  jawowa kanki dan babu ruwana da wani  banzar  hakurinki   dan  sai  jikinki  ya gaya miki  ya  ajiye  rigar hannunsa  a kan  kujera ya  soma  ƙoƙarin  sunce belt  din jikinsa " shegiya har  da  wani cewa kar  dakeki   gaki  yar gwal ko ?"  zaki yadda   zanyi  dake   gobe  idan  nace  ga  yadda nake  son tsarin  gidana  haka zaki bi  ,tana  ganin  ya kusan gama  sunce  belt din kugunsa  ta  kwasa aguje ta  haye  sama  tana ihu  dan tasan mai kwatarta a hannunsa  sai  Allah bayanta  ya  biyo  taku uku  yayi  ya samu nasarar  hard'e  kafarta ɗaya  ta  fadi  akan step , yasa  kafarsa  ya take mata  kafafu  ya  shiga zuba  mata  belt tana ihun  Kiran sunan iyayenta  "wayyo Allah na shiga  uku  wallahi bazan sake  ba ! bazan sake ba!!  kayi  hakuri bazan sake  ba  karka kasheni dan  girman Allah ka maidani  gida  wallahi na hakura  da aurenka  jin haka  yasa ya sake daddagewa  ya lafta mata belt  a tsakiyar bayanta  wani  gigitaccen qara ta  saki  tana dafe gadon bayanta   tare da furta  wallahi  zan bi umarninka  bazan sake ba "....

     "kima  sake  an  faɗa miki  wannan  aliyu  irin wanda  kika sani  ,wanda  kika  raina  , wannan Aliyu  ya  wuce  da tunanin  dakikiya sakariya  irinki  , yana magana  yana  lafta mata  belt  tana  ihu tana  tarewa  da hannunta sai daya  lilis  sannan ya barta  yana haki  " Useless  girl Kawai , idan   kika  sake  min irin wannan   ganganci zaki  ga  aikin  ganganci dan  daidai   sisin   kwabo bazan  raga miki .."

yayi kwallo da kafafunta ya  nufi  d'akinsa  ya buɗe ya  shiga  ya soma balballe  botiran  gaban rigarsa  ya  cire  ya saura daga  shi  sai dogon wando  da  farin singlet ya  rike  kugunsa  yana fifita  da  hannunsa  kafin daga  baya  ya ɗauki remut  ya  kunna ac  d'akin ,  karasa cire kayansa  yayi  ya  shiga bayi  yayi  wanka  ya fito ya  sauya  wasu  kayan ligth  blue  jeans   da riga dark  blue  ya  fito yana takowa  a  hankali kamshin daddad'an  turarensa  na  tashi,  rakube  ya  ganta a gefen kujera  ta  mike  kafafunta  tana  kallon jikinta  daya  shashin  belt  abinda tafi tsana kenan duka sam bata qaunar ganin shashin bulala ajikinta bare belt .

"ki  ɗauke min  waɗan nan  banzayen kafafun naki masu kama dana aljanu ,da  sauri  ta janye kafafunta jikinta na rawa  "na  ɗauke  " ta fada bakinta na rawa .
"karki  ɗauke  kiga yadda zanyi  kwallo   dake , ya samu guri ya zauna akan kujera  ,yana  zama    ana murd'a  handle  din kofar parlou'n  tare da turo kofar   ,nasir  ne  ya  shigo  tare  da  matarsa , d'agowa yayi ya  kalli  kofar , gani  nasir   ya gyara   zama , yayinda matar  nasir  data shigo karshe  ta maida kofar ta rufe  ta k'arasa  shigowa bakinta dauke da sallama  .

Fuskar  nasir  ɗauke  da murmushi  ya  mikawa Aliyu  hannu shima ya mika  masa   hannu  suka gaisa "har  kun karaso  ?" nima ban ɗauka  zamu  karaso da wuri haka  ba nasir ya kai bakinsa  kunne Aliyu yayi masa  rad'a  yatsina fuska  Aliyu yayi tare da cewa" Madam   ki zauna mana  kin   tsaya  tayi murmushi   "ina  yini uncle aliyu  an dawo lafiya  ya ka baro mutanen gida ?"

"alhamdullahi  kowa  yana  lafiya  a tare suka zauna bayan kamar second  biyu   tace "ina  amarya  ayi  min kiranta na  ganta  dan wannan  zuwan nata  ne    sam hankalinta  bai  ga kisna dake  ruku'be  ba , shi kuwa  aliyu  wata uwar  harara  ya  sakar  mata yana  cewa  ",ke  baki iya gaisuwa  bane  kina wani kallon mutane da wasu idanunki can ?"
"am sorry ,  sannuku da zuwa  Ina yinku ?"  ta faɗa  muryarta  na rawa a  hankali  Aliyu  yaja tsaki  daga  nasir har matarsa    safiyya    da ido  suka  bi  kisna   dashi  ,shi kuma Aliyu yayi  kwafa  yana girgiza kai  dan  bai so suka isketa  a  parlou'n  ba ,ɓacin ran abinda tayi masa yasa ya manta da batun zuwansu , mikewa Safiyya  tayi  ta k'arasa inda  take  zaune , ta durkusa a  gabanta  tana sake  binta  da kallo, gaba-daya sumar kanta ta  hargitse  fuskata kwance  da ruwan hawaye  sha'be Sha'be , ga  jikinta  duk  ya tashi da  alamun  duka taci .
ta kamo  hannuta ta mikar  daita tsaye  ta nufi gun  doguwar  kujerar daita  tana  cewa  "uncle aliyu ...    "
shiru  yayi  mata kamar ba  dashi  take  ba , ya shareta  "mai  ya samu kisna  haka  duk jikinta yayi  rudu  rudu  kar dai laifi  tayi  maka ka  mata duka irin  haka  ta fad'i haka  ne  saboda hirarsu  data  ji suna yi da mijinta "zan   taho  daita  amman  bazan d'aga mata  kafa  daidai dana second  ɗaya  ba kurkusre kaɗan  duka ne da izaya kala dabam dabam"
"   ita  kuwa  kisna shiru tayi  qirjinta  na  dukan uku uku  a hankali ta d'ago  kanta shima ya d'ago  kyawawan idanunsa   idanunsu ya tsarke cikin juna  ido cikin ido  suke kallon juna , itace  tayi saurin janye  idanunta cikin nashi  "haba uncle aliyu duk  abinda  kisna zata maka  bai  dace ka mata irin  wannan dukan ba kalli  jikinta  fa  tayi maganar  kamar zata yi kuka  tana nuna masa hannun kisna  ,"  ko karen gidanka banyi  expecting zaka iya yiwa irin wannan hukuncin ba bare kisna da take da matsayi biyu a gurinka matakar kuma  yar'uwarka  , gaskiya  banji dadi ba ".

sake waigowa Aliyu yayi ya  kalli  kisna a daidai lokacin  data  sake d'ago kanta , kura  masa  ido tayi  na  zuwa wani lokaci  sannan  ta  mike ta soma tafiya , da kyar take d'aga kafafunta   ta  shiga  bayi tayi  wanka  tayi alwala dan  la'asar  ta kusa gashi  ko azahar bata yi ba bayan  tayi  sallah kwanciya   tayi  akan gado  ta lullu'be jikinta saboda zazzabin da jikinta ya ɗauka, gabad'aya  hankalin Safiyya ya tashi zaman parlou'n  ya gundireta kamar  ta  mike ta bi bayan kisna  daki take ji , amman  ta  kasa,  dan bata son  yiwa  rayuwarsa  shishigi "

"Uncle  aliyu  ....."
Safiya  ta sake kiran sunansa  ,a  natse ya d'ago  yana  kallonta batare  da  yace  komai ba  "dan girman Allah uncle aliyu zan nemi alfarma  agurinka , karka sake  dukan  kisna  zai fi kyau  kayi  mata wani punishment  dabam idan tayi maka laifi  ,amman tsarin  duka sam bai yi ba ga macen aurenka ".
"Dan baki  san  halin  wannan makirar yarinyar   bane  shiyasa  kike tausaya  mata  ,ki tambayi  mijinki shi ai yasan  komai  wannan  yarinyar da kike gani  matsala  ce  arayuwa ta ,ta  haifar min da matsaloli  bila'adadi ".
Safiyya ta  kalli mijinta domin  jin ƙarin  bayani ganin  yaki  cewa komai  ta  sauke ajiyar zuciya "kina  kallona  dan kiji wani  abu  ,ba  sai kinji komai ba  , friend ka ƙara hakuri  idan  baka manta abinda  ya faru  a baya ba bazaka taɓa  samun kwanciyar  hankali ba, rayuwa  duk  yadda Allah ya  rubuta  babu wanda ya  isa  ya canza rayuwarku kaddara ce ,  a hankali  ya  dinga  masa nasiha mai ratsa jiki  sai kusan  shida  na yamma suka  bar  gidan zuciyar Safiyya  cunkushe da bakinciki  duk   abinda mijinta   ya  faɗa  bata dauki komai  ba , ita dai tasan  Aliyu  ya taho da diyar  mutane  ne ɗan kawai  ya cutar  daita ".a mota  tsokano maganar  ta  dinga yi dan nasir  ya faɗa  mata abinda ya faru tsakanin kisna da Aliyu  amman yaki  ,dan  baya son tasan  komai  dangane da rayuwar Aliyu , ganin haka  ta  kudurta  a ranta zata  dawo musamman  domin  taji  komai  abakin kisna"

Ranar  haka kisna  ta kasance  da  zazzaɓi , ko falon  bata sake fitowa ba , ya  shigo d'akin kallo ɗaya  yayi  mata ya fahimci  zazzaɓi ne ke d'awainiyya daita "kin shigo  daki  dan bakin munafurci  kin boye  ,to ki buɗe  kunnuwanki da kyau , duk abinda kika san  nawa ne acikin gidan  karki yi ganganci ta'bawa idan ba haka ba wallahi  wallahi  ......"
qarar  wayarsa ce ta katseshi  ya ɗauka  ya  juya  ya  fita daga d'akin  kunneshi  manne da wayar  har  ya  fita  bata san  ya  fita ba wani sabon  tashin hankali da faduwar  gaba  da wani irin  tsoronsa ne suka d'arsu a zuciyarta "yanzu irin  rayuwar da zata yi kenan  "?
"a she Aliyu bai san darajan  dan adam ba kamar yadda tai tsammanin   ? " mutumin  da kullum take  wa kallon yafi kowani  ɗan  adam kirki da nagarta a duniya  shine yau  yake kokarin kasheta  da ranta  ta share  hawayen daya wanke  mata fuska ta tashi  ta soma haɗa kayanta  a jaka  tana cikin  zubawa cikin jakarta  ya  shigo sai da gabanta yayi  wani mumnunar faduwa  da ganinsa ,  da sauri tayi  jefa da  kayan da  yake hannunta  sakamakon kallon  da yayi mata ta matsa  baya  da sauri  "kashina ya bushe ta furta hakan  a kasan ranta " cikin matsananci mamaki  yake kallonta "a kwana  biyu kacal har ta gaji dashi  ya furta a ransa  dariyar  mugunta na  kokarin  subuce masa  yayi saurin had'iyewa  yana watsa mata  harara, tausayin kanta ya ka mata "a kwana  biyu  kacal har kin  gaji  da aliyunki kin  soma  nemanwa  kanki mafuta ba ?"

"haba  yarinya har yaushe daren yayi?  "ai yanzu  aka  fara  buga wasan  ,ina  irin naki wasan  yake ?"yayi  magana  yana  tsareta da idanushi  tare da tsuke ƙaramin  bakinsa  "Okay a she  fa yanzu son Aliyu ake  baza'a  iya aikata komai  ba , amman zan so  ki fito da salon  iskanci  da kika iya kala kala  sai  mu buga wasan mugani  cikin ni dake waye  zai yi nasara ".

"babu abinda zanyi  har kullum  hakuri   zan cigaba da  baka saboda nasan ...... " yi  min shiru  munafukar Allah kawai  hakurin  ubanki zaki cigada da bani  ? tayi saurin  girgiza masa kai jikinta  na rawa  wallahi kika sake bude wannan rubabben bakin naki da zumar bani hakuri sai Kin  dawo ball a gidan nan , dan na dinga kwallo da kanki kenan har sai kin mutu  .."Tsit tayi tare da sunkuyar da  kanta kasa  tana sauke numfashi ,"mai mugun hali kawai ya fada yana fad'awa saman gadon ya talla'be kanshi da hannunwansa duka  ya runtse idanunshi gam yana jan dogon  tsaki ..."

Tun   daga   rana  bata sake  samun  canji rayuwa daga Aliyu   ba, tsananin  yafi  na wanda take  ciki , kuskure kaɗan duka  da  zagi  ga azabar yunwar  da yake mata, sai ya  fita tun  safe ya barta  babu abinci , sai idan ta roki mai  gadi  ya taimaka  mata dashi  a rana sau daya take cin abinci ,  kafin   kace  me ta  zabge  tayi wata ƙatuwar  rama sai dogon hanci da wuya  ,a qalla sai  datayi  sati  biyu a kasar , sannan wata ranar lahadi  yace ta shirya  dan   shiga  kasuwa shima  darajan  nasir taci if not  haka  zai barta tayi rayuwar yunwa   daga karshe ta mutu ya huta  ..

yana  zaune  cikin motarsa  kiran  beaz  330   hannuwansa   akan  stearing , ganinsa cikin mota ya hana escout dinsa harama biyosa dan duk sanda yayi haka baya nufin yana da bukatar rakiyarsu , ta fito jikinta  sanye cikin doguwar riga marun colour  har kasa mai zanen  fulawa  milk colour tun   daga wuyar rigar har zuwa shashin dukiyar fulaninta ,rigar tayi mata kyau sosai ,kafafunta sanye cikin flat shoe masu matukar kyau , babu  kwalliya a fuskarta sai  powder data dan shafa, ta shafawa lip's d'inta  Whit lipstick
duk da ta rame sai dai hakan bai hana kyawun da Allah yayi mata fitowa ba ,ta fito haraban gidan tana taku  a natse kamar koda yaushe  ta  bude murfin mota ta  shiga cikin dari dari ta  zauna  batare da ta sa seatbelt  ba , ya murza stearing  din motar  ,  take mai gadi ya bude musu makeken get din gidan  suka  fita .

a hankali motar ke gudu akan titi  ta ɗan juyo inda yake   ta kallesa yayi kyau  sosai , komai nashi irin  nasu  aryan ne babu abinda  suka bari nasa , ya ɗan  juyo ya kalleta ya ɗauke  idanunshi  yana jan  tsaki "mayya kawai ji yadda  ta kurawa mutu ido kamar zata cinye mutu  ,burki  yaja  aiko gabad'aya  ta gigice ta zubo   jikinsa dole yasa ya tsaya ba dan ya shiryawa hakan ba  yana kallonta , a fusace yace  "kina hauka ne  ,ki sanya seatbelt  mana "am sorry ta  fada tare da janyo seatbelt  ta sanya tana kallon  wani bangare "komai  yayi kyau yake masa  zan cigaba da hakuri  da  kai nasan wata rana zaka sauko ka  soni ?"
  Duk  wani  abun bukata a gida  bangaren abinci babu  wanda  bai siyo ba sai  daya  cika bayan  Boot d'insa  sannan suka ɗauki  hanyar dawowa gida , akan hanyarsu   tace "ina bukatar waya da  sabon layi  ina son nayi waya  da mummy ".
banza  yayi mata cikin haka  taga wani guri da'ake  siyar da  waya da layin  waya tace "yauwa dan Allah ka tsaya ka  siya  min , ya tsayar da motar  kamar abun arziki yana  gama tsayar da motar  ya sauke mata  yatsunsa biyar  a fuskarta "shiga hankalinki  baki isa kisani yin  abinda banyi niyya ba, duk abinda kika ga nayi  na gadama ne wawiya  mara  kamun kai kawai , kina wani hauka kamar tinkiya  , ke din da bakowa bace , ba matsayi  gareki  a zuciyata ba ,dake da jaka  daya  kuke  agurina , ya kai  hannunsa ya murza stearing  ya cigaba da tuki  har suka karaso gida kuka  take  kamar wacce akace uwarta da ubanta  sun mutu yana gama  daidai tsayuwar motarsa  ya bude boot  ya  fito ya shige ciki abunsa ya barta ..

yana zaune a parlou'n ta shigo  fuskarta tayi jajur  kwayar idanunta sunyi luhu  luhu sun kod'e har ta  kusan gifta shi ya hard'e  kafarta tayi kasa  luuuuuuuu  zata faɗo   jikinsa  , bai san yadda  akayi  ya   tarota  ba aikuwa  hannuwansa duka suka  sauka akan  dukiyar fulaninta  wani irin shock yaji a gabad'aya jikinsa  , idanuwanta ta tsura masa tana kallonsa a tsorace ,  hakan yasa yayi saurin cire hannunsa "ya'akayi hannuna ya kai jikinki "? 
yayi maganar cikin ɓacin rai  zuciyarsa  na wani iri  zafi ,mikewa  tsaye yayi  jikinsa na rawa  yana mata  wani  irin  kaskantacce kallo mai razana  duk wanda aka yiwa shi   "ba  tambayarki nayi  ba kika min shiru" ya'akayi  hanuna ya kai wannan banzar jikin naki  "wallahi  ban bansani ba nasan dai san  zaka taimaka min ne  hakan ta faru "

"meye shi hakan ya faru yanzu  ?  tayi saurin girgiza masa kai idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye ta samu guri zata zauna" uban wa zai  kwaso miki kayan ?" ta kalleshi da sauri hawaye na zubo mata . "oh kina tunanin ni ne zan shigo miki da kayan  bayan naje nayi wahala na siyo da kudina ?"
"bance   ka  shigo dashi  ba amman dan Allah ka bawa  mai gadi umarni ya  shigo dashi jikina ciwo yake "ubanki da ciwon jiki  dan Allah malama tashi kije ki kwaso  ,"  sai na maidake kaskantacciyar baiwa a gidan nan  , duk wata babbudewa da cikar iskar  da kike takama  dashi sai na sauke  miki shi  ,ya  zira hannunsa   cikin aljihun wandonsa  ya zaro  wayarsa ya soma danne  danne .... ...."

   Juyawa  tayi  jiki a matukar sanyaye  ta  koma  haraban  gidan ta k'arasa bayan  motar ta buɗe  ta soma fito da caton din monster  fury  energy, lamunsa ne  yana bala'in son  shi  ya kusan carton goma , ta fito dashi ta kai kitchen  ta  dawo ta  ɗauki  carton din ruwa  shima  guda goma ,sai kayayyakin  amfani shikafa  manja mangyada   da dai sauransu , gabad'aya ta haɗa  gumi  tana cikin aikin  Safiyya  ta shigo gidan da sauri ta karaso gareta , ta dafa kafad'unta a tsorace ta juyo  ganin Safiyya  ta sauke naunauyen ajiyar zuciya  tana fad'ad'a fuskarta da murmushi "
a she kice ?" ta gyada mata  kai ",abinda zaki saka  mai gadi ya  shigar miki  dashi shine kike yi da kanki  ,"kai  ai babu komai zan iya ai ne shiyasa  "zaki iya ko wannan  mugun mijin naki  ya sakaki , kalli idanunki kamar ma  duka yayi miki , kai bama kamar bane marinki yayi ko? "
"Karki damu dani plz mu shiga ciki ta ɗauki  wani kwali  guda biyu muje ko "bari  na tayaki safiya  ta ɗauki wani  kwali  tare suka shiga parlou'n basu iske  Aliyu ba ya hau sama  tare suka kwashe kaya  sannan ta tayata ajiye  komai a mazauninsa  ,suna aikin Safiyya  na zargin Aliyu"Allah yana sama yana  kallon abinda Aliyu yake miki shi zai kwatar miki  hakinki   ,kuma inshallahu  nan ba dadewa  ba sai ya girbi abinda  ya shuka  ,mugu azalumi  kawai ,kisna tayi dariya tace ayya Safiyya ki daina fadar haka babu abinda zai sameshi inshallahu , mijina mutumin kirki ne wallahi wannan abinda  ya faru a tsakaninmu ki ɗauka qaddarata  ce haka , tayi  tsaki  "lallai yanzu har wani yabonsa kike ? "To ai bashi da laifi wallahi, bana ganin laifinsa hasalima zuciyata sake qaunarsa take "tab gaskiya zuciyarki bata miki adalci ba " ......

Har kusan shida Aliyu bai sauko ba, tare da  Safiyya  suka da dafa soyayyiyar taliya wacce taji salad garbage da carote da soyayyen nama kaza sai dataci sannan  tayi mata sallama ta wuce.

bayan   safiyya ta wuce ya sauko yana mika haɗe da  salati ,ko kallon inda take  bai yi ba , ya zauna ya dauki remut ya kunna tv  ya janyo jakarsa ya fito da  computer  d'insa ya kunna  ya soma duba sakonnin mutanen dake kaunarsa  wasu yayi maida martani wasu kuma ya wuce , ganin haka  yasa  ta mike ta shiga kitchen ta dauko kular   data  zuba  masa abincinsa , ta daura a tire da ruwa da fury  ta  dauko  ta  fito , ta ajiye akan  table din da computer  dinsa ke kai.

ya d'ago  kyawawan idanunshi ya zuba mata yana  kallonta, murumushi tayi masa mai narkar da zuciya tamkar ba ita ce ta gama cin azaba a hannunsa ba  dumple d'inta ya lotsa hakan yasa ta ƙara kyau  "kaci  abinci  sannan ka cigaba da aikin "baza'a ci ba , ki  ɗauke  abincinki  yanzu  kafin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login