Showing 285001 words to 288000 words out of 495987 words
Chapter 96 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
Musa masu yawon gaske duk abinda ta gani indai ya burgeta kuma tasan zai masa kyau sai data siya masa kusan tsarabansa yafi na yan gidansu yawa ana gobe zata wuce kuwa baccin kirki ta kasa a kagare gari ya waye washegari da misalin karfe tawas tuni ta gama shirinta wasu riga da windo ne jeans and t shirt ta saka rigar fara sai jan wando wanda ya dameta sannan ta daura gyale ta yane kanta shima ja ne gashin kanta ya matukar shan gyara ta daureshi da jan rebon ta manne idanunta da bakin glass ta janyo karamin akwatin dake cike da tsaraban musa ta dubi kausar dake kallonta tai murmushi "to ranki shi dade tashi ki jawo min dayar akwatin lokaci fa na kurewa yau dai zakiyi baccin lafiya babu wata damuwa kisna zata koma ga Musa gabad'aya kausar ta mike idanuwnta sun yi ja tana duba agogon dake daure a tsintsitar hannunta tana maseefar kaunar kisna a ranta matsalarta dai wannan soyayyar data daurawa kanta suka fice gabad'aya su suka dunguma har filin jirgi a lokacin sauran minti talatin jirgi ya tashi kisna ta mike lokacin da zata shiga jirgi suka rungume juna hawayen da kausar ke faman boyewa ya zubo tace "zanyi missing dinki yaruwa zaki tafi ki barni da kewarki itama kisna taji hawaye ya zubo mata" bancin lamarin soyayyarta da Musa babu abinda zai maida ita naija a hankali suka saki juna suna tsaye jirginsu ya tashi zuciyar kausar sai bugawa yake dan sai lokacin ta tabbatar da sun shaku da juna suna sauka a filin jirgi wani farinciki ya kamata ji take tamkar tayi shekara goma rabonta da gida bata kira kowa ba sai musa cikin kankanin lokaci sai gashi yazo cikin ƙananan kaya jajayen Idanunshi manne da glass cike farinciki ya karaso inda take bai tsaya wata wata ba ya rungumeta tsam ajikinsa yana furta "i really miss you my baby " itama ta rungumeshi cikin sansar farinciki a hankali yake shaƙar wadataccen kamshin turarenta Dior yayinda ita kuma take shaƙar kamshi turarensa mai gyaraye da warin wiwi da kyar suka saki juna suka fara hirar yaushe rabo kafin a fito mata da kayanta lokacin da kayanta suka zo hannunta lokacin ta kira dady tace a turo mata direba ko cikakken minti a shirin bata yi da gama waya da dady ba sai ga wata zankadedeyar ferari fara sol sai kyalle take ta shigo cikin mm2 ita kanta batayi tunanin ita aka zo dauka ba a cikin motar har sanda mai motar ya zuro kyawawan kafafunsa fararen tassss nasu jire da zara zaran yatsu kowane kwance da gashi a hankali ya fito cikin sanyi jiki idanun mutane dake kan motar ya koma kan mamallakin motar a natse taga ta juyo tare da ciro waya a aljihunsa muradi ta gani tsaye yana kalle lalle da alamun ita yake nema yayinda wayar hannunta ke ruri .."
"Muna saida ingantattun maganin mata masu kyau da nagarta wanda ko da kudinka sai da rabonka tsimi , zumar Mata, gunba, gari insertion,
kaza,zakara ,jigida
dadai sauransu.
1.Tsumi Yana saukarwa mace niima Kuma bazataji wuyar jimai ba.
2. Zuma Tana taimakawa wurin Jin sha'awa Kuma itama Tana taimakawa wurin jindadin jima'i.
3.insertion( Dan matsi) daban dabanne akwai Wanda ke matse mace kuma yake saukar da ruwan ni'ima sannan akwai na mallaka , idan ana bukata a tuntubi wannan number
234 815 945 0159..
Mmm Sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 42
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
.... Kisna ta tsurawa mumy idanuwanta tana jin zallar ɓacin rai mara misaltuwa gaba-daya kwakwaluwarta ta cunkushe ta shiga tunanin muhallin da zata ajiye zantuttukan mahaifiyarta masu daci tattare da sansar tsana kamar yadda take iya hango tsanarta a cikin kwayar idanuwanta , kallonta ta cigaba zuciyarta na matukar zafi tana sauraron mugayen kalaman mumy akanta da musa wanda take jin duk duniya babu wanda ya isa ya rabata dashi ko datse soyayyar dake tsakaninsu duk runtsi duk wuya ta kudurta a ranta zata jure, komai zai faru this time around sai dai ya faru amman zata jure ta jajurce duk wata azaba har ta kai su ga yin aure idan kuma ya tabbata aura mata wannan mara galihun za'a yi to cikin biyu za'a yi daya ko ta tattara ta bar musu gidan ta koma can wani bagiren dabam ita da musa su cigaba da rayuwarsu ko kuma ta aika shi makirin kinibanbi lahira idan kuma bata sanarar kudinri ba "a she kuwa za'a yi gagarumin tashin hankali dan ko sama da kasa zasu haɗe bazata zauna dashi ba akan dai tayi rayuwar aure da aliyu wallahi gara tayi daya acikin biyu , sosai taji zuciyarta na bugawa da matsananci karfi cikin kankanin lokaci jikinta ya dauki zau zazzaɓi na neman rufeta ... . "
Sautin muryar mumy ta sake ji a cikin dodon kunneta " mahaifinki ya baki wanda zai kula da rayuwarki haka nan ya daure ya amshi aurenki batare daya fallasa abinda ke karkashin zuciyarsa ba shine saboda ke dakikiya ce mara mutunci zaki watsawa mahaifinki kasa a ido ,"abinda baki sani ba shara ma ya fiki kima da daraja a idanun muradi babu dai yadda zai yi ne yasa ya amince tayin aurenki "take fargaba tayi burki a tsakiyar qirjin kisna "kenan ma har ya amince da aurenta ? Tayiwa kanta tambayar data nemi tarwatsa mata zuciya da kwamwaluwa yadda zuciyarta ta kasa sukuni haka gangar jikinta , dan wani irin kyarma jikinta yake hankalinta na sake tashi ."
" duk rashin galihun muradi shi namiji bare ma da me kika fishi ?" kuma da me ake ido bare ki muzantashi ? "Kisna taja tsaki acikin ranta zuciyarta na sake hausinewa da kalaman mumy yayinda qirjinta da jikinta ke wani irin tafarfasa a zahiri ake iya kallon yadda qirjinta yake up and down alamun ta kai kololuwar ɓacin rai "kin ɗauki soyayya wani dakiki da ko secondary school bai tsaya ya kammala ba kin maidata gabanki kina kokarin bada matan duniya saboda har yanzu kanki na cikin tukunya gaki kamar Yes sai dai banza har yanzu no kike , da kinsan mata nawa ke bibiyar rayuwar muradi da kukan ya taimaka ya sanyasu akarkashinsa da dakikiyar kwakwaluwarki bata cutar dake ba gurin kin amsar aurensa , duk inda ya shiga mata da zama hirar sa ake ana son kyakkyawar mu'amala dashi , babu wanda bai sanshi ba daga kasar nan har zuwa kasashen duniya saboda nagartashi , shi din mutumin kirki ne ga aji ta ko'ina mumy ta karasa maganar da cewa "yadda bakya son shi haka shima baya son sauran wani ....."
Wani irin luguden bugu qirjin kisna yayi ta zaro idanuwanta waje cike da matsanancin mamakin jin furucin mumy na karshe "duk abinda kike samu agurin wannan ɗan iskan yaron zaki samu fiyye dashi agurin muradi ɗan yafi shi komai bama za'a hada ba samir ya fada yana kokarin sanyo kai cikin filin parlour'n dan tun daya daso kofar yake jiyo maganar mumy kasa kasa "shi kuwa dady shiru yayi tun sanda mumy ta soma magana yana kallonta ya kasa tsaidaita saboda ya fuskanci ranta yayi koluwar tashi dan ita din macece da bata fiyye nuna damuwar ko fada akan abu sai da rayuwar da kisna ta dauka ta canzata daga mai shiru shiru zuwa mai tsanani fushi ,zai barta ta fadi son ranta amman abinda ke ransa shi dai bazai taba fasa bawa muradi auren kisna ba sai dai mumy tayi hakuri tunda har yaron ya rigada ya amince masa yasan kiyayyar mace mai sauki ne da zarar ta shiga gidan mijinta shinkenan inshallahu sai zaman lafiya mutuwar daya daga cikinsu ne kawai zai hana wannan auren ..."
"yar iskar yarinya kawai mara mutunci da tausayi ana taroki kina hauka me zakiyi da wani musa yaron da har yanzu bai dauki nauyin kansa ma ba bare har ya dauki naki ? sai lokacin hawaye ya zubo a kuncin kisna tana kallon mutanen dake parlour'n daya bayan daya Samir na surfa mata zagi cin mutunci zee kuma na bawa mumy hakuri har zuwa sanda uban gayyar ya shigo bakinsa dauke da sallama cikin shigarsa ta ko yaushe hadaddun kanana kaya ne sanye ajikinsa masu matukar kyau da tsada ganinsu tsaye cirko cirko ga kisna na zubar da hawaye yasa gabansa yayi mummunar faduwa dan yasan akwai matsala "yauwa muradi karka kuskura naji ka amshi auren nan kaji na fada maka yadda bata kaunarka kai ma ka nuna baka sonta dan......." muje uwar marayu dady ya katseta tare da riko tsintsiyar hannunta ya juya "samir ka kula da wannan yarinyar dady yayi magana yana tafiya rike da hannun mumy ...."
"Babu wani kula da za'a yi daita idan ta isa tasa kafa ta fita a gidan nan wallahi idan ban balbalaki ba kece shege nake , dan Allah ki fita ga hanya nan ,ba dai kin iya gudu ki bar gida ba bismillah this time around I will surprise you shashar banza kawai shashar wofi muradi ya kalli Samir kawai dan ba sai yayi masa karin bayani ba ya fahimci komai ita kuwa zee waskewa tayi dan bazata iya kallon tsabar idanun muradi ba saboda tausayinsa, dan duk mutumin da aka hadashi da kisna wallahi an hadashi da babban aiki
karasawa tayi gurin kisna dake kuka har lokacin "ki daina kuka ki kwantar da hankalinki nasiha sosai zee ke mata mai nuna mahimmanci iyaye da hakkinsu daya rataya a wuyan ƴaƴansu amman sam duk nasihar zee basa ratsa gangar jikin kisna hasalima ta bayan kunneta suke bi tare da daure fuskarta tamau .
cike da sanyin jiki muradi ya biyo bayan su mumy bai tsaya tura kofar dakin dady ba kasancewar a bude kofar yake ya shiga a hankali bakinsa da sallama har ya karaso tsakiyar filin daki inda ya iskesu zaune dady na rike da hannuwan mumy sai faman rarrashin yake tana botsare masa zama yayi dirshan a kasa yana sauraron maganar dady "kiyi hakuri salaha ki min wannan alfarma dan girman Allah , halin da muke ciki zaki duba sannan aurar da kisna ga Aliyu shine kwanciyar hankalinmu gaba-daya nasan bai sonta Bama su dace da juna ba amman mu zai taimakawa yanzu idan kin dage akan bai son ......"
"dad mum wai wa yace muku bana son kisna ? " a tare suka d'ago suka tsura masa ido suna kallonsa zuciyarsu na dogawa " dan Allah daga yau ku daina wannan tunanin cewar bana son kisna "kisna fa jinina ce na dade ina nema mana mafuta akanta kafin dady ya zartar da hukuncinsa ," mumy dan girman Allah ki daina damun kanki akan wannan yar matsalar dukkaninmu fa akarkashin ikon dady muke ko ban son kisna dady ya zartar da hukunci akaina dole nayi masa biyyaya bare ina sonta ya karasa maganar qirjinsa na dokawa da sauri sauri dan tabbas ba abinda ke zuciyarsa ya fada ba ya dai fada ne dan kwantar da hankalin mumy kuma duk wannan maganar da yake Idanunshi na kasa ya kasa haɗa ido da iyayen goyonsa dan karsu fahimci zahirin gaskiyarsa wanda shi kwata kwata bai taba kawowa zuciyarsa auren kisna ba a kasalance ya cigaba da magana muryarsa na rawa "inshallahu wannan auren zai kawo mana karshen matsalarmu na tsawon shekaru , har kullum mumy dady bazan gaji da godiya da alfahari daku ba kun min abinda bazan iya biyanku ba , wallahi ko auren kisna ban biyaku da abinda kuka min ba Allah qara girma ya kara muku lafiya da nisan kwana ina sonku ......." "ameen summa ameen muradi muma muna sonka Allah yayiwa rayuwarka albarka "muradi ya numfasa yana danne zuciyarsa tare da furta "ameen " mumy kam kasa cewa komai tayi illa hawaye da suka shiga turereniyar zubowa daga cikin manyan idanunta a hankali d'anuwanta haroon ya fada mata "ko yana ina yanzu ? "Har gara sadiq tana dan jin labarinsa lokaci zuwa lokaci agurin Inna jamila idan Allah yasa yaje ilo amman haroon kam yanzu ko labarinsa bata dashi tun tana kiran numbersa yana shiga har yazo baya shiga, shi kansa muradi gaba-daya ya kasa daurewa sai daya zubar da kwalla ,sai dai yayi dabaran gogewa dan kar ya sake daga hankalin mumy , dady ya mike ya shiga uwar dakansa yana zance zuci "tabbas idan mutun yayi alkhairi kanshi yayiwa haka akasinsa yau da bai amshi rikon muradi tare da kyautata masa ba wa gari ya waya ?" Zama yayi a bakin gado tare da jingina bayansa yana tunanin matakin da zai dauka akan kisna da irin tsaron da zai sake sakawa a bakin gidansa.. ."
ganin dady ya shiga ciki yasa a hankali muradi ya rarrafo ya dawo gaban mumy yana share mata hawaye "dan Allah kiyi farinciki da wannan auren , ki kuma sanya masa albarka kiyi min addu'a akan matsalolin rayuwa yayi magana cikin sauti mai sanyi "Allah ya sanya alkhairi , Allah yayi maka tsari da duk wani sharri dake tattare daita , Allah ya kara maka hakuri ,nasan baka son kisna muradi wallahi na sani ka dai amince da wannan auren ne ," Allah yasa auren ya zamo sanadiyyar daidaituwar al'amura addu'a sosai mumy ta dinga yi masa yana amsawa da "ameen a karshe yace ",mumy kin amince da auren ...?" na amince muradi ya zanyi har cikin zuciyata na yarda na amince nama zamo mutun ta farko da nake son auren nan ta karasa maganar tana shafa kansa "yauwa mumy haka nake so jin daga bakinki saboda amincewarki shine kwanciyar hankalin gaba-daya ..."
Duk wannan tashin hankali da muradi da