Showing 138001 words to 141000 words out of 495987 words
Chapter 47 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
nan ,babu abinda zai sameshi ki daina d'aga hankalinki dan Allah , Allah ya ga kinyi iyakar ƙoƙarinki akan yaron nan". "Alhaji bazan iya kwantar da hankalina ba d'a sukutun fa koda bani na haifesa ba dole naji zafin rashinsa , duk kuma ranar da mahaifiyarsa ta waiwayemu da batun yaranta me zance mata"? "Inshallahu gobe zan sa ma'aikata a cikin lamarin ayi bincike ."
"Dan Allah a taimaka a binciko min shi gara ace mutuwa yayi a hanuna akan ace yana hannun 'yan fashi azzaluman mutane ,Allah ka saka mana ka tona asirinsu a duk inda suke, Allah ka bayyana min muradina ....."ta karasa maganar tana kuka ."
Alhaji realwan na barin asibiti ofishin 'yan sanda ya nufa yayi musu bayanin komai da inda abun ya faru tashin farko suka bukaci hoton muradi sai dai babu sai kwatanta musu yayi da shekarunsa , abunka da mai arziki take labarin 'batan Aliyu ya karad'e ko'ina ,bangaren gidan tv , radio jarida da duk wani kafafen yaɗa labarai , yawan kukan da Hajiya salaha take babu dare babu rana yasa likitan dake dubata yayi mata allura saboda a samu hankalinta ya kwanta dan bp dinta ya hau sosai ."
zuwan hajiya Aysha biyu asibintin duba jikin Hajiya salaha sai dai bata taɓa zuwa da Aliyu ba ,sannan bata taɓa zuwa ta iske idanun hajiya salaha biyu ba , duk sanda zata zo tana bacci ,satin hajiya salaha ɗaya ta ɗan samu saukin rad'ad'in rashin Aliyu aka sallameta daga asibiti suka dawo gida kuma har wannan lokacin babu wani bayani akan batan Aliyu , hajiya salaha tayi baki ta rame ta fita haiyacinta, ta daina ci ta daina sha hatta magana taki yi da kowa daga sallah sai sallah ke ta da ita tsaye hatta kisna sai da tayi zazzabin rashin kulawar mahaifiya , kowa yazo kalma daya yake faɗa mata tayi hakuri Allah zai bayyana shi a karo na uku ne da Hajiya Aysha tazo tare da afra duba jikin hajiya salaha ta iske idanunta biyu "sannu salaha ya karfin jikin "? Sai data maida kanta kan pillow sannan ta buɗe baki da kyar tace "da sauki Hajiya na gode sosai hawaye na gangaro mata , kuka take sosai tana maganar zuci "wai ɗan waye ne acikin wannan yaron a cikin yanuwanki ? "Hajiya salaha bata tsaya boyewa surukarta komai ba saboda ta ɗauketa a matsayin uwa tunda itama matsayin diyarta ta ɗauketa,ta fada mata matsayin mahaifiyar Aliyu da irin rayuwar datayi da danuwanta haroon ,Sai lokacin hajiya Aysha tasan takamaiman abinda ya faru sannan sai lokacin tasan batun zuwan muradi daga ilo , haka nan hajiya Aysha taji gabanta ya fadi babu wanda yazo mata a lokacin sai Aliyu sai dai shi ai yace mata bashi da kowa a duniya sai mahaifiyarsa ..." cikin jimami tace " Allah ka shirya mana zuri'a ,shi kuma babakarami Allah ya karkato da hankalinsa gida shi ma yaron Allah ya bayyana shi a duk inda yake a hankali Hajiya salaha ta cigaba da amsawa da "ameen ameen hawaye na gangaro mata anan Hajiya aysha ta bar afra gurinsu mufida tace daga nan gidansu zata wuce daman kuma tana son zuwa gidan saboda Kisna ."
lokacin da hajiya Aysha ta koma gida tayita bin Aliyu da kallo wanda lokacin satinsa bakwai kenan a gidan, tsantsar kamaninsa da sarakuwarta ta gani sosai akan fuskarsa wanda bata lura da hakan ba a tun ranar da marwan ya kawo mata shi sai yau ,a hankali ta shiga tunanin bayanin da marwan yayi mata akanshi wanda Aliyu din ne ya fada masa da wanda shi kanshi yaron ya fada mata , shiru tayi tana kallonsa zuciyarta na tabbatar mata da lallai shi ne yaron da'ake nema dan a labarinsa akwai abinda ya shafi uwa da rashin uba haka a labarin da surukarta ta bata akwai abinda ya shafi uwa da uba sai dai uban bashi da amfani , tagumi ta rafka dan bata son rabuwa dashi ,ita dake shirin saka shi a makaranta ya cigaba da karatunsa tunda ya sheida mata ya kare primary ,duk ta daga hankalinta ta riko hannunsa cikin nata"Aliyu ta kira sunansa ya d'ago kyawawan idanunsa ya Kalleta kawai kasancewar shi din ba mai yawon hayaniya bane "idan kaga yan'uwan mahaifinka zaka koma hannunsu da zama "? Yayi saurin girgiza mata kai "ai bani da mahaifin ma bare wasu yan'uwansa yayi maganar kamar zai yi kuka ,"zaka zauna agurina kenan ka cigaba da karatunka ? tayi maganar tana fad'ad'a fuskarta da murmushi "zan zauna muddin rai agurinki sai dai idan na hadu da mahaifiyata ne to zan koma hannunta gbdy amman zan dinga zuwa ina ganinki ai ina sonki kina da kirki sosai "Allah sarki Aliyu nima ina sonka ina jinka tamkar jikana daura hannunta tayi a saman kanshi tana jin tsananin kaunar sa da tausayinta ..
Washegari
Aliyu na zaune a kusa da hajiya aysha suka ji sallama "assalamu alaikum Hajiya ta dago kanta tana duban kofar shigowa ". a'a afra ce tafe da yamma nan "?"Nice ina yini granny "? Ta gaisheta tana yatsina fuska saboda Aliyu data ganin zaune a kusa daita ga hannunsa cikin nata "Lafiya lau ya mammanki "? Shiru tayi kafin daga baya tace "wai da gaske rike wannan kazamin yaron dan tsintuwa kuma shege wanda bashi da baba zaki yi ? gaskiya ni idan yana gidan nan zan daina zuwa wallahi dan tsoro yake bani ".
"Kul na sake jin kin furta wannan kalmar hajiya ta dakatar daita tana daga mata hannu cikin ɓacin rai shi kuwa Aliyu ko ajikinsa dan bai damu ba , dama uwa tace bashi daita shine zai damu har ma ya daga hankalinsa kuma sai inda kkarfinsa ya kare amman dan wani uba bai shi da matsala da wannan azzalumi mutumin da shi kansa tuni ya kankareshi a rayuwarsa yama fi son ace masa bashi daita sai da hajiya taja kwafa tace "banason zance banza a ina ma kika ji kalmar shege ?"kin mata rana nan naji kina fadawa dady bashi da uba ? Tsam hajiya ta sha jinin jikinta tabbas sai bayan da komai ya faru ta lura daita " shikenan ki Saka ranki a inuwa ma gobe goben nan zai bar gidan zai koma gurin gidan Alhaji realwan "wani irin tsalle tayi cike da murna "dan Allah grannny kai naji dadi sosai wallahi amman can din ma ai gidan zuwana ne me zai hana ki kai shi gidan marayu kawai mu huta wallahi banason shi bana son bude idanuna na ganshi ".Aliyu ya waigo inda take tsaye ya tsura mata ido yana kallon yadda take farinciki dan zai bar gidan ,Hajiya Aysha ta Kai hannu ta shafo kanshi "manta da wannan mashiririciyar kaji ai inda zaka koma duk daya ne da nan din "Allah karki kai musu shege dan tsintuwa "?"Ke ban son hauka karamar yarinya dake sai shegen surutun tsiya wannan bakin bana marwan bane wallahi na wannan uwar taki ne maza ki bace min da gani kima tattara kayanki ki bar min gida da yake tana da wasu kayan anan gidan ida zata zo tayi kwana biyu bata zuwa da kaya ,tsimi tsimi ta shige daki tace "babu inda zata ta haye gado tayi kwanciyarta zuciyarta cike da farinciki da bakinciki farincikinta Aliyu zai bar gidan bakinciki still dai gidan yayan mahaifinta zai koma washegari Hajiya salaha ta shirya Aliyu cikin sababbin kayan data dinka masa ta rike masa hannu ,tare suka zauna a bayan mota direbanta ya jasu zuwa gidan Alhaji realwan .."
A parlou'n gidan ta iske yaran gidan gabad'aya sunyi jigun jigun ban da badamasi wanda yake karatu a Austarelia , damuwar mahaifiyarsu ta shefe kuzarin yaran gidan duk sun dawo tamkar marasa lafiya ,bakinta dauke da sallama ta karasa shigowa filin parlou'n ta samu guri ta zauna akan kujera sannan ta nunawa Aliyu gurin zama ya zauna kusa da Samir wanda ransa yake a bace saboda dammuwa ko yar sannu da zuwa da suke mata a duk sanda tazo bata samu ba daga garesu ,"Samir ina abbanku yana gida ko ya fita "?"Yana d'akin mommy ya fada muryarsa a raunane kamar zai yi kuka "maza tashi ka Kiramin shi a hankali ya mike ya nufi d'akin inda ya iske dadynsu nayi wa mummy faɗa "mai yasa kike son kashe kanki ne "? yayi maganar cikin tsananin ɓacin rai wanda yake tattare da tsantsar damuwar halin data ciki "bazaka fahimci yadda nake jin muradi acikin raina ba a yanzu in dai akwai abinda nake so bai wuce Aliyu ba kuma kai ma muddin kana sona kaso Aliyu tayi maganar tana juya masa baya juyo daita yayi suka hada ido "shikenan ki kwantar da hankalinki nima ina son shi ai sai dai bazan so wani abu ya sameki akan shi ba , yayi maganar yana goge mata hawayen daya gangaro mata ,"salaha ya kira sunanta ta d'ago idanunta dake cike da hawaye ta zuba masa "ina son kiyi hakuri ki ......"
Sallamar Samir ce ta dakatar dashi daga abinda yake son fada ya juyo yana amsa sallamar tare da bashi umarnin shigowa d'akin "dady granny tazo tana parloun tana jiranka wai kazo yanzu "Okay je kace gani nan zuwa ko cikakken minti biyu Samir bai yi ba ya dawo parloun yace "gashin nan zuwa cikin hanzari alhj realwan ya fito yana gama k'arasowa parloun ya daskare tsaye saboda ganin Aliyu zaune ,koda bai taba ganin Aliyu a rayuwarsa ba ai ya taba ganin haroon mahaifinsa sannan yasan garba yasan Bature uwa uba matarsa , tsantsar kamaninsu a bayyane yake ,bakinsa ya soma motsawa bai kai ga fadar abinda yake son fad'i ba hajiya Aysha tace "realwan wannan shine yaron da'ake nema ko "? "Gashi nan na kawoshi sunansa Aliyu ".
Bai ce mata uffan ba ya juya cikin sauri yana magana "barin na kira salaha ta tabbatar da hakan, duk dai kamaninsa ma kawai zai iya fahimtar da mutun shi din wane ne , dawo wa yayi parlou'n rike da hannun salaha ai idanunta na sauka akan Aliyu ta kwace hannunta cikin na Alhaji realwan ta nufi inda Aliyu yake zaune cikin tsananin farinciki , shima Aliyu yana ganinta ya zabura ya mike tsaye ya nufata cikin tsananin farinciki suka rungume juna bai so ya sake daura idanunsa akan wani daya danganci dangin ubansa ba amman hakan nan a yanzu ya tsinci kansa cikin farinciki haduwa da kanwar mahaifinsa ....."
"Alhamdulillah Allah na gode maka daka bayana min muradin hajiya kayi muradina , Aysha babba wacce ake kira da ummi kasancewar sunan Hajiya dataci shekarunta basu wuce sha takwas ba jin Muryar Hajiya ne ya fito daita daga kitchen inda take kokarin daura abinci a tare suka yo suka yo kan mahaifiyarsu ita da Samir da madu har ma dasu mufida cikin tsananin murna suka zube jikin Hajiya salaha suna taya murnar ganin Aliyu ,"mommy shine aliyun da kuke nema ai mun gashi a gidan granny ? suka hada baki gurin fadar haka ,Hajiya salaha ta d'ago kanta tana duban muradi tana sumbatar fuskarsa ......"
murmushi Hajiya Aysha tayi bata yi kokarin yin magana ba,tana son sai sun samu natsuwa sannan tayi magana ,hajiya salaha ta dubi surukarta cikin sansar farinciki sannan ta dubi mijinta ta karashe da sauke idanunta akan Hajiya Aysha tana neman karin bayani "yau kimanin satinsa bakwai kenan agurina marwan ne ya tsintoshi nan ta kwashe komai ta fada musu ban da godiya ga Allah babu abinda mommy take tana shafa kan muradi shima murnarsa taki boyewa sai murmushi yake yace" mummy sauran anyata ina son ganinta "anyanka na ilo itama Allah ya kubutar daita ya lumshe lumtsatsun idanunsa yana sauke ajiyar zuciya "Allah sarki shiyasa tashi farko jininsu ya haɗu da Samir a she jininsu ne Samir ya rike hannu Aliyu cike da murna shima Aliyu ya rike hannunsa ,Kafin kace me mommy ta dawo daidai sai lokacin ta bukaci abinci, ummi ta mike ta shiga Kitchen ta shirya mata abinci ,bayan sun ci har Hajiya Aysha tayi musu sallama har jikin mota suka rakata sai da suka ga tashin motarta sannan suka koma cikin gida ....
Sukusuku ta dawo gidan har washegari bata sake ba tana jin kewar Aliyu a dan kwanakin da yayi mata ,tun daya zo gidan shi ke mata shara gidan gabad'aya wankewanke har ta fara aikensa domin ya soma gane guri tana zaune afra ta shigo parlou'n sanye da wando da riga duk bakake ta tsaya a gaban Hajiya Aysha "salamu alaikum "afra
"Na'am "
"Ya'akayi "?"Lafiya qalau granny yunwa nake ji abinci nake son naci "Afra bana jin dadi shiga Kitchen akwai taliya ki dan bararka kici "
Aysha ta kwa'be baki tana dubanta kafin daga baya tace "granny na gane tunda wannan shegen dan tsintuwar ya bar gidan nan kika daina walwala, jiya ma baki yi mana abinci ba "ke bana jin dadi ne yar taliya zaki bararka kici "ni fa yarinyar ce ban iya dafa komai ba ,kawai kin wani damu akan wannan kazamin yaron ,ni gani nayi ma kamar kin fi son shi akan ni da nake jikarki "shikenan yi hakuri kiyi yau kawai gobe zan dafa miki duk abinda kike son ci amman kar na sake jin kince wa Aliyu kazami ko shege dan tsintuwar,ba tsinto sa akayi ba shi din d'an'uwansu Samir ne yanzu haka yana gidansu "
bata rai "yanzu sai da kika kai musu shege ? Hajiya Aysha ta gyada mata kai alamun "eh " kuma nace karki sake ce masa shege dan halak " amman ai shine yace bashi da uba "kin ci uwarki da wannan maganar kaji min fitannaniyar yarinya mai kwakwar tsiya ina ruwanki ma idan shegen ne ? Afra ta yi shiru tana Kallon Hajiya Aysha zuciyarta cike da haushi "dan yayan maman Samir ne uwa daya uba daya kamar yadda dadynki yake da abbansu Samir "lallai ma granny din nan ta iya girba karya ita da aka tsinci yaro a gabanta sannan yanzu tace mata wai danuwansu Samir ne ta ina take tunanin wannan maganar gaskiya ce ? ta dai maidashi can ne dan tana son yayi rayuwar jin dadi da yanci ,kafafunta ta soma d'agawa a hankali ta shiga Kitchen batare da ta sake cewa komai ba ,sai dai a cikin zuciyarta ta qudurta komawa gidan alhaji realwan dan takurawa rayuwar Aliyu sai ta raba shi da gidan ta kowane hali ,bayan sati daya da komawar Aliyu gidan Alhaji realwan afra ta matsawa iyayenta lallai tana son zuwa gidan alhaji realwan karasa sauran hutunta da yayi saura , da fari mahaifiyarta kin amincewa tayi ganin ai hutun yazo karshe kuma ita bata son tana shigewa dangin mahaifinta dan ko gidan hajiya ma dole ce kawai hakan yasa afra ta daga hankalinta kullum cikin damuwa take kwana take yini tsabar bata samu damar ciwa Aliyu zarafi ba ,ganin damuwarta yasa mahaifiyarta ta amince mata ,sai dai da sharadin hutunta na karewa ta tattaro ta dawo ba sai tayita magana ba idan tayi kwana biyu ta dawo,tayita tsalle tana murna ta nufi d'akinta ta soma shirya kayanta a cikin yar karamar akwati ,ta bude jakar ratayarwata ta kwashe kayan kaliyarta ta zuba powder ailen white lips stick duk ta zuba a cikin mahaifiyarta na siya mata kayan kawaliyata ne kasancewarta babbar diyarta sannan ita kanta tana da tsananin son kawaliya shiyasa ta koyawa diyarta