Showing 156001 words to 159000 words out of 495987 words

Chapter 53 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

wallahi za'a jimu dake dariya ta sake kashewa dashi "zo ka gani zo kaga hoton nan muradi .."

Muradi ya mike daga inda yake ya duko jikin Samir yana kallon screen din wayar sai dai hoton yaki budewa kusan second biyu hoto yaki ya bude Samir ya dafe kai "kar dai data na ya kare d'azun nan nayi sub din 500 hundred fa "a'a Samir daga fara aiki an fara buge maka 500 hundred before you know it sun tsiyataka wallahi ya k'arasa maganar yana kwashewa da dariyar mugunta , mufeeda da zahra har ma da Samir suka bishi da kallon mamaki dan basu taɓa ganin yayi dariya irin haka ba, sai dai yayi murmushin gefe baki shima murmushin ba koda yaushe yake ba ."

"Nan gaba sai ka siya account five thousand zaka ga an bugeshi sannan kanka zai yi pe ya sake kwashewa da wata dariya "wannan abun fa wahalar da kai ne zalla wallahi , kasan irin abubuwan da yasir yayi lose akan wannan banza yahoo din na banza ?" duk da shima bai cika siyan account da kudinsa ba idan ya bawa mutune wayarsa suka yi loging suna wucewa zai dawo da komai kan wayarsa "kai dan Allah amman yasir shege ne Samir ya faɗa tare da mikewa zaune ."

"Ai yadda ake zamanin kenan agurinku 'yan yahoo Boy'z "gaskiya waɗan da basu da waya su aka fi cuta "kai dama wayarka ma idan baka san ta kan account ba haka za'a yi maka wayo ,kamar kai din nan da ba wani wayo ne da kai ba tsab za'a sace maka komai abarka nan ,"shi fa Yasir har neman waɗan da zai basu wayarsa yake ya mika musu wayarsa yace suyi loging zai bar su suyi free mutun na gamawa zai dawo da komai ya canza komai akan wayarsa ,shi yasa yanzu ake jin tsoron yin loging a wayar mutane ."

"Ni fa yanzu ba komai ya dameni ba kamar korota da akayi yanzu Samir yayi magana hankalinsa a matukar tashe ," in gaya maka wata magana Samir ? Samir ya gyada masa kai alamun yana jinsa tare da kallon muradi "ka damu account dinka da yawan shiga sosai ne "ban gane na damesa ba "? "Ba'a son ana yawon shiga account din da'aka canza sosai sannan ka daina bawa yasir yana maka editing, dan yana gamawa mai facebook zai bugeka maka kamar yadda kagani yanzu " saboda shi edit yana bukatar abu daya idan kasa suna yau ka bar sunan ya ɗan jima sai ka dawo kasa inda kake zaune ka bari shima yayi two days, sai ka dawo ka canza hoto to a haka zasu gane wannan bature ne yana son ya canza tsarinsa ne , amman farar daya ace za'a canza location, daga nan garin agege zuwa wani country farar daya aga ka canza suna ka canza number ka canza password kasa inda ba'a nan kake da zama ba ai dole mai facebook zai watsaka waje da gudu tun da shi dole zai gane ba'a nan kasar kake ba " mai facebook duk abinda zakayi zai gane ai dole ya watsaka waje yasan scam ne ."

" Wato shi yana zaune yana ganin komai "? zahra ta fada "Eh man yana ganin komai amman idan ka canza one by one zai barka, ko account din jahid daya bawa yasir yayi masa editing dinsa step by step yayi ,sai da yayi tsawon kwanaki a hannunsa ba'a buge ba amman yana shiga hannu yasir a ranar aka buge ,da yake bai bugu sosai ba ya amsa kayansa ya sake gyarawa sannan ya mayar masa aka cigaba da aiki , suka sa dariya gaba-dayansu "to shi Yasir editing din me yake zahra ta sake tambaya tana dariya ?"Ke ai yasir ya iya editing ya kware sosai har editing dinsa nasa a kwace facebook din mutun lokaci daya yake canza Nigeria ya koma amercan .."

"Kai baka yahoo amman kasan komai akanshi mai zai hana ka dinga yi nasan zaka samo mana kudi sosai saboda kana da brain ,ya girgiza mata kai sannan yace "bana ra'ayi zama ɗan yahoo bazan iya canza kaina daga yadda nake ba , dole idan zanyi yahoo sai tashi daga matsayin namiji na dawo mace , ko mace ta dawo namiji wanda a addinance haram ne ,duk abinda zan samu a harka yahoo zan samu ninkinsa a buga wasan kwallo daya idan nayi ,gara na cigaba da kwallo har zuwa sanda zan kare karatuna na samu club shiyasa nake ta kokarin Samir ya hakura da wannan yahoo din wallahi hasarar kudinsa kawai zatayi a banza ana samu fa ba wai ba'a samu ba amman kafin mutun ya samu ya zuba kudinsa dayawa gurin sayen katin waya da sayen hotunan matan turawa . "

"Gaskiya kayi tunani mai kyau Allah ya taimaka , ka fadawa wannan mai kan karas din ya daina wahalar da kanshi da 'yan canjinsa take Samir ya haɗe rai "idan ni mai Kan karas ne ke Kuma mai bakin kabeji kuma wallahi karki sake ce min mai kan karas ya k'arasa maganar yana kwashewa da dariya "wawiya da wani kanki agurin ya sake fada yana sake kwashewa da dariya .." ta bude baki kenan zata maka masa nata sai ga Kisna ta shigo da gudu "Oyoyo oyoyo autar mumy Kisna tayi wurgi da school bag dinta da jakar abincinta ta rungume zahra yayinda mufeeda ta mike ta shiga Kitchen "sannu da zuwa babyn mumy ta cire mata takalmi "kiyiwa yaya muradi da Samir sannu da gida "Kai tsaye ta fada jikin Samir dake zaune "gud afternoon ya samir " Afternoon autar mumy ya amsa mata yana Shafa kanta oya je kiyiwa muradi sannu da gida ya mikar daita tare da turata gaban muradi tana kokarin yin magana sai ga afra ta dawo parlour'n tana cika tana batsewa da gudu Kisna tayi gurinta afra ta dauketa cak ta rungumeta ajikinta tana sumbatarta ta nufi fridge ta sauketa ta buɗe ta dauko ruwa ta tsiyaya ta bata ta sha"ina mumy na ? ta tambayi afra tana ƙoƙarin cire uniform din jikinta "ta fita " tayi saurin sauke uniform dinta tace "to wallahi sai kin goyani kafin ki cire min uniform " tayi maganar tana dariya "shikenan cire kayanki sai na goyaki baby nah akwai shakuwa mai karfi a tsakanin afra da kisna , Kisna ta sake yin dariya tana cewa "Allah sai kin goya ni sannan in cure kayan ,nan afra ta shiga rarrashinta tana lalla'bata har dai ta yarda ta cire mata kaya sannan tayi mata wanka tayi mata shirin zuwa islamiyya nan kisna ta saka kukan bazata islamiyya ba tagaji wata razananniyar tsawa muradi ya buga mata "ki yiwa mutane shiru sannan ki tsaya a shiryaki zuwa islamiyya tsit kisna tayi tana kokarin had'iye kukanta dan tayi matukar tsorata da tsawar da muradi yayi mata mutumin da bai shiga lamarinta tsakaninsa daita ido ne "malam meye nayi mata tsawa kamar wata babba zaka gigita yarinyar mutane nan fa ba kauye bane a hankali ake bin yara , baby tunda bazaki islamiyya ba muje kici abinci na kaiki daki ki kwanta ki huta "Cikin zafin rai muradi ya karaso ya fixge hannun kisna a hannun afra ya nufi d'akin da kayanta suke daga ita sai pent batare daya kalli inda afra take ba ya bude inda kayanta suke ya dauki uniform dinta ya saka mata da hijab ya zaunar daita akan kujera "mufeeda ina abincinta ? ta mika mata plet din abinci ta makale kafada "bazan abinci ci ba ta fada tana Turi baki "kar Allah yasa ki ci ya sata gaba zuwa islamiyya , afra ta bude baki zatayi magana ganin yadda muradi ya daure fuskar fiyye da sauran lokutan baya yasa ta kasa cewa komai sai dai ta dinga cika tana batsewa ,shi kuwa niyyarsa da tayi magana sai dai taji saukan mari a fuskarta gabad'aya ya gama kudurta irin dukan mutuwar da zai mata sai Allah ya taimaka taki cewa komai ,zuwansu makarantar ke da wuya ya samu malamar ajinsu ya damka hannunta tare da cewa a kula daita karta gudo gida "inshallahu sai dai dan Allah idan ta dawo gida a sake yanke mata farcen hannunta saboda yakushin yara take yayi shiru can yace "duk wanda ta yakusa ku riketa su rama " malama tayi murmushi tana duban muradi tace "ai Kisna akwai rigima wallahi duk rabin 'yan ajin tsoronta suke ji da kayi mata abu da bakayi mata ba sai tasan yadda ta cijeka ko ta yakushi mutun kuma tafi mutu Kuka a dauka ko ita aka cuta girgiza kai kawai muradi yayi ya juyo zuwa gida ...."

Karfe hudu da rabi daidai zahra ta shiga Kitchen yayinda afra da mufeeda suka soma aikace aikace gyaran gida kafin kace me sun gyara ko'ina gidan yayi tsaf daidai wannan lokacin ne Kuma mummy ta sanyo kai cikin parlou'n gidan ta dubesu tana murmushin tace "sannuku da aiki 'yan albarka sukayi murmushi su kace "yauwa mumy sannu da zuwa "yauwa ta amsa ta shige bangarenta ta shiga wanka bata dade ba ta fito ta sauya wasu kaya ta dauki wayarta ta fito parlour "ina su muradi ne banji motsinsu ba ko sun fita sanar tasu ne ?"Eh sun fita buga kwallo inji cewar mufeeda suna zaune suna kallo a zeeworld wayar mumy dake hannun afra tana buga game ta soma ƙara alamar kira mummy ta dubeta tana fadin "waye ? "Dady ne ta mikawa mumy wayar tayi sallama suka gaisa "ya kasuwan ?"Ya amsa da "lafiya yana jin muryarki kamar babu lafiya ?",Babu komai gajiya ce kawai "okay daman na Kira naji yadda kike ne sai na dawo ya kashe wayar nan suka ci-gaba da kallo suna hira kamar ya'yan data haifa a cikinta sai tayi musu abu sau dari batayiwa ya'yan cikinta ba ,ta tarbiyarta dasu kamar yadda uwa zata bawa ya'yan data haifa a cikinta bata ga abinda zata saka ita da yaranta bata basu sun saka ba har zaginta ake cewar bata san ciwon kudinta ba ,yaran suna wahalar mata da jikinsu ko masu aiki ta dauko iyakar aikin da zasu yi mata kenan sun wahalar mata da jikinsu ,shiyasa bata bambamtasu da yaranta har unguwa wata rana dasu take zuwa duk karshen shekara mai gidan zai bari su fita zuwa Saudiya ,Dubai chaina , egypt domin su huta yaranta yan hutu ne suna samun hutu yadda ya kamata ,yaran duk abinda suke so shi ake musu tun basu kai haka suke gurinta ba gashi har sun cika shekaru shabiyar suna tare ,matsala dai daya ce ita kuma daga afra ne da muradi ta rasa dalilin da yasa ta tsane shi duk da shi baya shiga tsabgarta a duk lokacin data yunkura zata dauki mataki sai taga idan tayi magana afra zata iya daukar abun awani matsayi ,ita kuma bata son tayi mata abinda zai taba ranta ta dawo gurinta ne saboda soyayya da shakuwa tunda babu abinda ta rasa a gidansu hasalima iyayenta na mugun ji daita sai abinda ta gadama take yi zamanta tare daita ne ma yasa ta rage shagwa'ba da sangarci , zata barta da Samir tunda tasan duk sanda tayiwa muradi rashin mutunci bazai kyaleta ba .."

Akan hanyar Kisna ta dawowa daga makaranta islamiyya ita da kawarta zinnira wacce bata wuce shekarunta a haihuwa ba ,Kisna ta cire hijab dinta tana wasa dashi itama zinnira ganin haka ta cire nata suna tafiya suna wasa kamar abun arziki sai Kisna ta ja ta tsaya tare da cewa "zinnira na daure miki wuya da hijab dina na jaki kamar rago dan muyi sauri ? batare da wani tsoro ba zinnira ta gyada mata kai tana murmushi aiko Kisna ta zagaye wuya zinnira ta daure ta soma janta da karfi , take zinnira ta fashe da kuka tana ƙoƙarin kwance daurin wuyanta amman ina Kisna tayi gaba har da dan gudunta tana murna zinnira na biye daita a baya tana cigaba da kukan ta kwanceta amman taki har suka shigo layinsu tana janta har da kiran " meeeeeeeeee "... tun daga nesa muradi dake tsaye da jahid ya hangosu ya dinga juya kai cike da mamaki zuciyarsa ta jagule kamar ya daura hannu akanshi sai data karaso kofar gidan tayi masa duban tsanake sannan ta kwance hijab dinta dake wuyan zinnira tasa hannu tureta "wuce gidanku joooooo. ... " kadan ya rage zinnira bata fadi kasa muradi yayi saurin tarota yana ƙoƙarin kamo Kisna da dayan hannunsa ta kwasa da gudu ta shige karamin get din gidan da sauri muradi ya mika zinnira gurin jahid ya biyo bayanta jahid na ƙoƙarin tsaida shi amman yaki tsayawa da dan gudunsa ya karasa shiga cikin gidan yana dube dube nemanta "lafiya muradi me kake nema ? "mumy ina Kisna "yanzu ta shigo da gudu halan wani abu tayi ? "babu komai ina ta shiga ? ta nuna masa dakinsu mufeeda , hanyar dakin ya nufa direct ya shiga bai ganta ba ya tsaya a tsakiyar daki rike da kugunsa yana kallon dakin dan gano inda ta boye ita kuwa Kisna tana cikin wordrobe din kayanta ta lullube jikinta da kaya jikinta na rawa saboda tsananin tsoro, dakin ya fara dubawa bai ganta ba wani tunani yayi Kawai ya juya ya fita daga dakin ya tsaya a bakin kofa yana fita ta buɗe ta fito tana kyalkyalewa da dariya har da girgiza jiki bata ankara ba taji shigowar mutun daki ta tsure tana neman gurin buya ya damki tsintsiyar hannuta ta juyo a mutukar tsoroce cikin wani irin matsefaffen tsana ta zuba masa ido tana turo masa baki "muje ki bawa yarinyar mutane hakuri , da kika daure musu wuyan yarinya zaki kashe musu 'ya ne? yayi maganar yana d'agata sama ya fito daita aiko ta saka masa ihu "wayyo mumy

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login