Showing 78001 words to 81000 words out of 495987 words
Chapter 27 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
auntynka ta fad'a min gaskiya kada ta wahalar da zuciyata idan kuma bazata amince min ba ta bari mu zama friend's daita ..... "."wayyo Allah na shiga uku shikenan kasani a matsala ta furta a matukar tsorace sakamakon idanunta daya haɗu dana Aliyu dake tsaye "dan Allah ka rufa min asiri ka sauke min yaro kuma ka bar gurin nan yanzu tayi maganar kamar zatayi kuka a hankali mutumin ya sauke aryan domin ganin wanda ta kira da sunan mijinta ...."
A natse idanunshi ya sauka akan Aliyu daya soma takowa da kyawawan zara zaran yatsun kafafunsa masu matukar kyau cike da jarumta irin na karfaffan namiji mai tattare da natsuwa da haiba zuwa inda suke tsaye ,yayinda kisna dake tsaye qirjinta ya cigaba da bugawa da matsanancin karfin gaske hankalinta yayi mugun tashi take gumi ya shiga tsatsafo mata a goshinta da sansar jikinta ,ta tsura masa narkakkun idanunta da suke a matukar tsorace domin son tabbatar da yanayinsa ,
Irin na d'azu zai yi musu ya sharesu ya basar kamar bai ga komai ba ko kuwa zai yi magana ne a matsayinsa na mijinta "?yana daf da k'arasowa inda suke wayarsa ta soma ringing kafin ya d'auka kiran ya katse a hankali ya ciro wayar daga gaban aljihunsa ya duba ganin mai kiran ya soma neman layin yana cigaba da daga kafafunsa yana ciza gefen lip's dinsa yayinda hannunsa daga ke cikin aljihun wandonsa dan tunanin maganar da zai fadawa mr birsat dake bukatar zantawa dashi ta musamman a gobe .."
Ta daura laulausan tafin hannunta akan goshinta ta goge gumin dake tsatsafo mata zuciyarta na rawa yayinda har wannan lokacin tana cigaba da kallonsa jikinta na wani irin rawa , tana kallonsa ya soma wayar bata ji yace komai ba illa "to shikenan naji zamu yi magana later cikin tsadaddan turancinsa ya cire hannusa cikin aljihunsa ya riko hannu areef dake tsartsarfa yana biye dashi ,bakinta na rawa ta dinga furta kalmar " ka wuce ! Ka wuce dan Allah !! Allah ya gani bata so Aliyu ya ganta ba saboda gudun tozarcinsa da wulakancinsa dan tasan duk abinda zai yi dan tozartata yana so saboda baya kaunar ganinta cikin farinciki sai dai babu yadda zatayi yanzu aikin gama ya gama sai ta jira taga sakamakonta , mutumin ya kallesa ya ganesa sarai realwan Aliyu muradi ne da suka haɗu d'azu nan take ya shiga wasi wasi acikin ranshi anya kuwa gaskiya ta faɗa masa? tunda ganin idanunshi suka yi karo dashi babu wanda yayiwa d'an'uwansa magana ko nuna alamun sun san juna idan kuwa har mijinta ne ta yaya zasu haɗu da juna batare da sun nuna alamun su din ma'aurata bane ? "ganin Aliyu yana ƙoƙarin nufo inda suke yasa jikinta ya sake ɗaukar kyarma gumi ya sake wanke mata jiki wani irin tashin hankali ne ke sake kawowa gangar jikinta ziyara a hankali ta cigaba da maimaitawa mutumin kalmar "ka rufa min asiri ka tafi dan girman Allah, amman ko gezai yaki tafiya ya tsaya kyam kamar mashi yana jiran karasowarsa yaga mai zai yi ," dan tabbas idan matar aurensa ce dole ne ya dauki mataki ......"
Sunkuyar da kanta kasa tayi tana kallonsa ta kasan idanunta , yana takowa qirjinta na luguden bugawa da matsanancin karfin gaske, saurin fixge hannu aryan tayi ta rike gam a hannunta ganin yana cigaba da karasowa "momy look at papa ......sororo mutumin yayi kar dai gaskiya ta faɗa masa ita din matar aure ce ,matar ma ta Aliyu muradi ,gaskiya ta cancanci ta kasance matarsa sun dace matuka, tana da kyau sosai kamar yadda shima yake da tsananin kyau na bugawa a jarida daman irinsu sai irin wadan nan matan masu tsananin kyau kamar su sukayi kansu ..."
yana gama k'arasowa ya fixge hannu aryan a hannunta ta d'ago idanunta a gigice ta kalleshi ,hanunusa ya mika baya tunaninta marin mutumin zai yi dan haka tayi saurin durkushewa kafin ya gama dashi ya dawo kanta ga mamakinta sai gani tayi ya riko hannu samir ya zagaye kanta dashi tare da mika masa hannu aryan suka juya suka soma ƙoƙarin barin gurin ,wani wahalallen numfashi ta sauke ta mike tsaye a firgice "da alamun kina matukar son wannan dan wasan kallon ba dai mijin aurenki ba ? " ki duba kiga yadda ya nuna ko in kula akanki babu mutumin da zai ga matarsa ta sunah tsaye da wani reaction d'insa bai canza ba kina son maso wani wannan da shafukan sadarwarsa hotonsa dana wata buduwar ne wanda ake rade raden zai aureta me yasa zaki 'batawa kanki lokaci akan mutumin da bai sonki kuma bai damu dake ba ki bawa yusif modibo dama ya zamo abokin rayuwarki zan kula dake da duk abinda na mallaka a duniya zan baki .. .."
"Enough dan Allah ka dameni da surutunka na banza shasha kawai sai wani zuba kake kamar fanfo babu class babu aji babu mannes ," kasani koda ni din ba matar aure bace bazan taba kula ka ba saboda baka daga cikin tsarina tana gama fadar haka taja tsaki ta barshi tsaye ...."
Bayanta yabi da kallo a ransa yace duk abinda zakiyi sai dai kiyi amman bazan hakura ba sai na mallakawa zuciyata ke "..
Jiki a sanyaye ta k'arasa inda suke wanda zuwa lokacin numfashi ma da kyar take fitarwa "lafiya me ne ne ka wani fixge hannu yarona a hannuna ai ba kai kadai ka haifeshi ba tayi maganar cike da dakiyar zuciya Aliyu ya buɗe baki zai fara magana cikin sanyayiyyar murya Samir ya dakatar dashi dan haka ya juya a fusace ya tsaya nesa kaɗan dasu "wato daman kina da wata manufa a cikin ranki shiyasa kika ce a fito dan ki samu damar kula maza ko "? tsayawa tayi kawai tana masa wani irin kallon ,ya kalleta kamar zai ɗauketa da mari saboda kallon raunin hankalin da tayi masa "wuce muje gida "kayi hakuri dan Allah yanzu fa muka fito inji cewar aunty zee "lafiya kisna mai ya faru yayanki ya dauki zafi haka "?"Babu komai tayi magana muryarta can kasa hawaye na zubo mata ita ba fadan da yayi mata ne yafi damunta ba kamar yadda Aliyu ya wulakanta aurensa dake kanta "tabbas yanzu ta sake fahimtar Aliyu bazai sota ba "me ye babu komai ki faɗa mata wani kato kika kula da aurenki saboda bakinsa darajar kanki ba yana faɗa yana kara d'aure fuska nan take kisna ta sake tsoronta motar da suka zo daita ya nuna mata duk abinda Samir yake faɗa mata yana shiga kunnen Aliyu amman ko ajikinsa bai nuna ya damu ba dan shi ko yawo zatayi tsirara tayi ba zai damu ba bare kula wani kato ..."
A hankali su aunty zee suka karaso gurinsa tun daga nesa take kallon Aliyu so take ta fahimci reaction d'insa akan kisna amman taga babu alamar haka hasalima wasa da yaransa yake ya daga ariyan sama ya daga areef"Hannu areef ya rike aryan na saman fad'ansa ya nufi inda ya paka mota ya shiga ya sanya aryan a gabansa ,su aunty zeey suka shiga mota ya ja , gabad'aya hankalin kisan yana kan Aliyu dake zaune yana tuki "ya Allah ka taimakeni ka nuna min hanyar da zan shawo hankalin mijina gareni ...
Gudu yake sosai akan titi duk maganar da Samir yake masa yana bashi hakuri akan abinda kisna tayi bai ce uffan ba haka zalika bai waigo inda yake zaune ba yana karaasowa get din gidan ya danna hon da karfi mai gadi ya taso da sauri ya bude masa get ya sanya hancin motarsa cikin haraban gidan madadin ya karasa inda aka tanada domin ajiye motoci sai ya tsaya a tsakiyar gidan ya fito ya nufi kofar parlou'n gidan Samir ma ya fito da sauri ya biyo bayansa Aliyu na kokarin hawa step samir ya shigo yana masa magana "ina son na kasance ni kaɗai i will see you later samir , samir ya gyada kai ya zauna akan doguwar kujerar parlou'n yana furzar da iska mommy dake zaune tace "wani abu ya faru ne da kuka fita "?
Girgiza mata kai yayi "babu komai momy ya fada mata haka dan kwantar mata da hankali "karka min karya fa samir ? babu komai mommy idan akwai ai zan faɗa miki "Allah yasa ta fada hk tana jiran shigowar jikokinta a guje suka shigo suna kiran sunanta "granny ta ware musu hannuwanta "oyayo sannuku da dawowa me kuka kawo min my dear"? "Ni yunwa nake ji inji cewar aryan yayi magana yana yatsuna fuska tare da shafa ciki Samir ya kalleshi "babana ban da karya fa duk cire ciye da kuka yi amman kace yunwa kake ? Turo masa karamin bakinsa yayi yana sake kwabe fuska mumy tayi murmushi Tace "karku damu yarana I have oredy cook delicious for you ta fada tare rungumesu ajikinta "really granny ? "sure my grandchildren's babu abinda ban muku ba "yeeeeeeee suka soma tsalle suna sake rungumeta a daidai lokacin da kisna da aunty zee suka shigo hannunsu rike da kaya "iyeeee kunga yan gatan granny areef ya mike ya amshi farar ledar da Aliyu ya siyo musu takalma ya dawo gurin mommy "granny I want to show you something ya bude ledar takalma suka zubo masu yawa "papa ne ya siya mana nida aryan "iye lallai papa na ji daku ,aryan ya cire takalmin dake sanye da ƙafarsa ya matso ya dauki guda daya acikin wanda aka siyo "ki samin granny ina son nasa sabon takalmi " ka bari zuwa gobe kaji my sweet heart ya kwasa takalman da gudu ya hau sama shima areef ya kwashi wasu ya bishi a baya "sannu da gida mommy aunty zee da kisna suka hada baki ."
"sannuku kun sha yawo "wallahi ai kasar akwai tsari gasu da dogayen riguna da kananan kaya ai ina ganin sai na sake komawa tayi maganar tana nuna samir da baki ya juyo ya kalleta "aikuwa sai dai ki nemi mai kai ki dan duk kwananki nan zamuyi busy "haka zaka daure ka kaita "Allah mommy kina shagwa'ba yaran nan da yawa ya fadi haka tare da mikewa ya fita domin gabatar da sallah , Kisna ta mike" bari nayi sallah nima nazo na daura mana girki "huta abunki mamana na dafa muku had'ad'd'en girki kala dabam dabam "thats why I love you mommy ta kai mata pick a kumatu ita kuma mumy ta shafa kanta .."
Sama ta hau zuciyarta cunkushe da bakincikin nuna ko in kulan da Aliyu ya nuna mata lokacin daya gatan da wani kato wannan abu ya bala'i taba mata zuciya tana kan step ya sauko sanye cikin wasu kayan kunnensa manne da waya yana magana kasa kasa ",okay ka fito da marcende kawai yana ganinta yayi saurin ɗauke kanshi , idanunta ta lumshe tare da sake bashi hanya qirjinta na bugawa cikin natsuwa ya raba ta gefenta yana sake janye jikinsa dan kar jikinsu ya haɗu kamshin turarensa dake tashi ne ya cika mata hanci da zuciya hakan yasa ta ɗan ji sanyi acikin ranta har taji kashi dari na ɓacin ran daya haddasa mata kashi goma ya kau a cikin zuciyata , ta gefen idanunta take kallonsa har ya gotata sannan ta cigaba da tafiya , kofar fita ya nufa muryarsa a ƙausashe yace " mommy zan ɗan fita amman ba jima zanyi ba zan dawo "
"Muradi ......"Mommy ta kira sunansa ya juyo tare da tsurawa momy idanunsa da suke a rikici sun yi jawur tamkar garwashin wuta bama zaka taɓa cewa farare bane sannan cike suke da matsanancin maseefa ya kasa amsawa mumy illa tsura mata ido "amman naji kacewa Samir zaka huta ina kuma zaka yanzu da alamun ma akwai abinda ke damunka , murmushin gefe baki yayi mata wanda yafi kuka ciwo yana girgiza mata kai alamun babu komai, bata fuska tayi "karkawa mommynka karya mana zaka iya k'arasowa ka faɗa min damuwarka koni na taso na sameka"?murmushi ya sake yi yasan komai zai yi mommy Sai taso tasan abinda ke damunsa ko abinda zai fitar dashi a daidai wannan lokacin yasan yadda mommy take matukar sonshi bata haɗa shi da komai ba a rayuwarta , uwa ce data amsa sunanta shi kuma yana tsananin sonta zai iya mallaka mata komai daya mallaka a duniya koda kuwa rayuwarsa ce koda kuwa ba itace sila inganta rayuwarsa ba ,bashi da wata uwa kaf duniya data wuce ta, itace uwarsa itace ubansa itace komai nasa k'arasowa yayi ya zauna kusa daita ya kamo hannuwanta duka cikin nashi aunty zee na ganin haka ta mike tsaye "uhmmm bari na bawa uwa da d'a guri ta nufi sama mommy tayi murmushi "gara ki tashi kam .
bakinsa ya kai daidai kunnen mommy yayi mata magana a hankali , murmushi ne ya sake bayyana akan fuskarta ta ja kunnensa ya ɗan saki qara mara sauti yana kai hannunsa kan na mommy "ashhh mommy akwai zafi fa "kabi a hankali muradi bana son kana damun kanka dayawa Allah ya tsare min kai sai ka dawo amman karka dade sannan karka yi abinda zai ....." Hannunsa ya d'aura a saman bakinta "mommy babu abinda zai faru kin rigada kin min addu'a ya mike ya fito zuwa haraban gidan yana waya "okay na gane unguwar ,no karka damu zani ni kaɗai ya katse kiran ya karasa inda direbansa ke jiransa har ya bude masa murfin gidan baya amman yaga ya bude gaban mota ya shiga direban ya karaso da hanzari ya bude mazaunin direba ya shiga ya tada motar mai gadi ya wangale musu get din gida...
Jingina bayansa yayi da kujerar motar da yake zaune , zuciyarsa na wani irin zafi da tuttukin bakincikin mara misaltuwa ,shi kadai yasan yadda yake jin kanshi da zuciyarsa da yake jin kamar zata kama da wuta, runtse sexy eye's d'insa yayi yana dukan cinyarsa da hannunsa daya "ina muka nufa ne boos"? direba ya tambayesa yana dubansa *"madinaty* ya bashi amsa a takaice ...."
Zaune a bakin gado aunty zee ta iske kisna ta rafka tagumi yayinda aryan da areef ke guje guje a dakin ta karaso ta zauna a gefenta tana dafa kafad'anta "me yayi zafi kisna komai yayi zafi fa maganinsa addu'a ".
Naunauyen ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe idanunta "zuciyata aunty zee ina jin ajikina bazan dade a duniya ba na kusan mutuwa dan Allah ko bayan raina ga ....
"dan damuwar datayi miki yawa ne yasa kika fadi haka bai zama lallai damuwar tayi sanadin barinki duniya ba ,idan Allah ya ga dama kina cikin damuwa zai rayaki na tsawon shekaru abinda zakiyi shine addu'a Karki gaji da kaiwa Allah kukanki "ina addu'a sosai aunty har na fara ga..." "Karki gaji ,ba'a gajiya da addu'a kisna , Allah na amsa addu'armu sai dai ana jinkirtawa bawa ne amman kisawa ranki duk abinda kika roki Allah ya amsa wai ma meye abun damuwa yanzu "?
"Damuwata da bakincikina aunty zeey Bai wuce yadda ya Aliyu ya nunawa mutumin nan ni din bawata tsiya bace agurinsa alhalin na sheida masa ni din matarsa ce wallahi dana san wannan wulakanci zai min dana ce masa ni din ba matar aure ba kai dana ma bishi mun wuce gidansa ..........
Aunty zee ta kwashe da dariya har da rike ciki "ai kuwa da kin haukata ya Aliyu kinsa wani abu ?Kisna ta girgiza mata kai "sai kin fada min " wallahil azim yaji mugun haushin ganinku tare da wannan mutumin Samir ma yaji haushi bare shi mai mata "karki faɗa min haka aunty zee dan ba yarda zanyi ba " kinsan Allah ko ki yarda ko Karki yarda Aliyu yaji haushi ya dai ki nunawa ne dan karki ɗauka ya damu dake "yaushe ne zai damu dani aunty wallahi na gaji dashi zama dashi ya fita raina banki ya sakeni ba ......"? Tayi maganar hawaye na gangaro mata "karki fidda sautin kukanki kinga yara suna gurin nan shiru sukayi gabad'aya yayinda kisna ke kokarin maida kukanta "nasan yadda kike jin wannan situation din da kike ciki sai dai bani da abinda zan faɗa miki daya wuce ki zauna da mijinki lafiya ki ci-gaba da ƙoƙarin janyo hankalinsa shiyasa ma na siyo miki kananan kaya domin ki dinga sakawa kina daga masa hankali" .
"Wannan mai zuciyar dutsen ai ina fada miki ko tsirara zanyi yawo a gabansa bazai taba nuna ya ji wani abu ba bare wasu kaya , na dai sawa jikina naji dadi "karki gaji kisa tun bai damuwa zai zo ya fara nuna sha'awarsa tunda shi ba dutse ba "kai aunty bazan iya ba fa Kuma bazan cigaba da miki alkwari ba at any time zan iya barin rayuwarsa dan wallahi na gaji dana mutu nayiwa yayana hasara wallahi gara na bar rayuwarsa ,na dawo rayuwarsa ne dan na gyara kuskurena amman yaki bani dama sai faman wwulakantani yake , me ye amfani dawowata ?
" da amfani sosai bazaki gane ba sai nan gaba abinda nake so da Ke ki kara hakuri ki bar maganar rabuwa wai bana ce miki ma'aikun rahma na tsinewa matar dake neman saki daga mijinta ba kema fa kinsa furta hakan haramun ne shiru Kisna tayi kirjinta na buga ita fa ta kudurcewa ranta zata sanarwa mumy tana bukatar rabuwa dashi gara ta rungume rayuwar ƴaƴanta " bari naje na bar yayanki shi kadai gashi banyi sallah ba Kisna ta sauke ajiyar zuciya "Okya shikenan nima bari nayi sallah na sauko an bar mommy ita kadai ..."
Sai wurin karfe goma da minti goma shabiyar Aliyu ya shigo gidan yana haki kamar wani zaki ,suna zaune gabadayansu akan dinnig table suna cin abinci kallo ɗaya yayi musu ya dauke kanshi ya haye step momy na ganin yadda ya shigo ta biyo bayansa da sauri kallon kallo suka bi juna dashi batare da sunce wa juna komai ba kisna kuwa kasa cigaba da cin abinci tayi duk taji komai ya fita akanta kawai ta cigaba da bawa areef zuciyarta na tsinkewa saboda hukunci zuciyarta yayinda aunty zee ke