Showing 192001 words to 195000 words out of 495987 words
Chapter 65 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
Allah ka musguna masa tun a gidan duniya ka kaskantar dashi sosai zuciyar muradi ta girgiza da labarin jin mutuwar mahaifiyarsa sai da yayi kwana uku asibiti cikin jimami sannan aka sallamosa ya dawo gida yana kuka Samir ya rungume shi cikin tsananin tashin hankali ya nufi dakin mumy dashi ya kwantar dashi akan gadon mumy tunanin irin rayuwar da yayi da mahaifiyarsa yake ,yanzu wani rayuwa mai dadi zai yi babu ita a duniya ? mumy ce ta dinga kwantar masa da hankali da cewa "Allah na sane daku kuma shine gatan bawa zai kawowa rayuwarku tallafi Ni kuma inshallahu nayi alkwarin rikeku cikin amana da kai da d'anuwanka bari na kira number mahaifinka kuyi magana dashi ya girgiza mata kai cikin Muryar kuka yace banaso jin muryar mutumin da yayi sanadin rugujewar rayuwar nida mahaifiyata da yan'uwana wallahi na tsaneshi mumy bana ji ajikina cewar ina da wani mahaifi bayan dady ya karasa maganar yana kuka itama mumy hawaye take zubar tana cigaba da neman number haroon amman yaki dauka ta sake rushewa da wani kukan tana cewa "me ye amfani turo min da number alhalin kasan bazaka dauki kirana ba ? bata hakura ba haka tayita kiran numbersa sai daga karshe ya dauka ta dinga masa kuka tana rokonsa "haroon kayiwa girman Allah ka dawo gida muna bukatanta haka ma yayanka na bukatarka ai jin kalmar ya'ya yasa ya katse wayarsa gaba-daya ta sake kira taji number a kashe daman mutumin daya aiko mai suna shaaibu ya faɗa mata bai san da zaman yaran agurinsu ba a tunaninsa yaran na gurin dangin mahaifiyarsu , kowa yayi wa muradi gaisuwar mutuwar mahaifiyarsa da yake ji kamar a lokacin akayi masa amman ban da afra datake masa kallon hadarin kaza ,muradi ya rasa lafiyar jikinsa sakamakon mutuwar mahaifiyarsa ta bugesa bada wasa ba haka zai zauna a d'aki yayita kuka sosai yake jin maraicin ajikinsa ya rame sosai ya daina cin abinci gabad'aya kuzarinsa yayi kasa mumy ta dawo dashi ɗakinta saboda kwana yake sambatu da kyar tasamu da taimakon Allah ya dawo daidai ya cigaba da rayuwarsa sai dai kallo daya zaka masa kaza fahimci akwai ciwo a rayuwarsa ..."
******
Bayan wata daya
Yaya badamasin ne ke saukowa daga mattatakalar benen jirgi ,jikinsa sanye da tufafi masu matukar kyau da tsada , fatar jikinsa kawai zaka kalla kasan kudi sun zauna masa ba karya ,komai na jikinsa masu matukar tsada ne, sai faman washe haƙora yake a lokacin da yake nufo inda motar mahaifinsa ke tsaye jiran karasowarsa Allah Allah yake ya k'arasa gida ya da'ura idanunsa akan kyakkyawar fuskar mummynsa da afra dinsa yaga yadda ta kara girma da kyau , da fari cewa dadynsa yayi lallai idan za azo d'aukarsa azo masa daita amman dady ya hana yace" idan tazo ai bai yiwa yan gidan suprise din da yake bukatar yi musu ba ,gara kawai su gansa daga sama ."
Motar data d'aukosa ko gama daidaita tsayuwa batai ba a haraban gidan ya bude murfin motar cike da farinciki ya fito ya nufi babban parlour'n gidan inda ya ci karo da mummy dake tsaye tana bawa muradi sako zuwa gidan hajiya Aysha , Kawai taga mutun daga sama yana washe mata baki " Mummy nah I miss you ya karaso cike da murna ya rungumeta ajikinsa ,"i Miss you too my lovely son , how was your joining ?"Shine baka faɗa mana cewar yau zaka sauka ba kou ?" tayi maganar tana shafa sumar kansa cikin tsananin farinciki ganinsa "sorry mummy nah suprise nake son muku amman dad yasan da dawowata yau ". "Alhamdulillah tunda Allah ya kawoka lafiya ya ka baro Australia ?"
Ya shafa sumar kansa yana kallon inda Afra da mufeeda da zahra ke tsaye hayaniyarsu ce ta fito dasu da gudu , yace "lafiya mummuy ya gida
ita kuwa Afra sai faman zuba masa murmushi take wanda yake ƙara tafiyar da imanin ya badamasi yana zare jikinsa daga rungume mummy da yayi ya karaso inda take ya rungumeta yana shafa bayanta "kin wani tsaya kina kallon mutane haka ake wa mutune sannu da zuwa ?" Mummy ta Kallesu ta girgiza kai
tare da hararasa ."
Murmushi Afra ta yi haɗe da rungume shi tsam tana masa sannu da zuwa sannan ta zare jikinta mufeeda da zahra suka rungumeshi atare "na same ku lafiya sister's?".
"Lafiya lau yaya ya Australia "?Murmushi yayi tare da cewa "lafiya sister's ". Muradi da Samir da madu sukayi masa sannu da zuwa sannan suka nufi waje domin shigo da kayansa shi kuma muradi ya wuce inda mummy ta aikesa ."
Kyawwan idanushi masu matukar kyau ya zubawa Afra tare da karasawa inda take tsaye rungume da hannuwanta tana sakar masa murnushi ,riko hannuwanta yayi cikin natshi wani irin zirrrrrrrrr suka ji a tare tayi saurin zare hannunta "wai ina autar mummy ne ban ji hayaniyarta ba ko bata gidan ne ?"Tana nan sarkin rigima tana daki tana bacci" mufeeda ta bashi amsa da haka "muje ka huta kafin a shirya maka abinda zaka ci kafin lokacin ma dadynka ya dawo".
" Okya mumuy bari naje na dawo ya nufi part d'insa komai kyal an gyara koina very neat tamkar yana kasar, ya cire kayan jikinsa ya fada toilet bai wani jima ba ya fito saboda jikinsa daman ba wani datti yayi ba , koda ya fito ya iske su Samir sun shigo masa da jakarsa ya goge jiki da karami towel wasu kayan ya d'auko ya saka ya fesawa jikinsa da turare mai daɗin kamshi ya dauki wayoyinsa ya nufi bangaren mummuy yana shiga parlou'n ya iske mufeeda da Afra suna jera abinci a dinnig table.
"sannuku yammatan mummy suka juyo a tare fuskarsu ɗauke da murmushin "yauwa yaya sanunka ya gajiya ?"gajiyar nan ma idan akwaita yanzu babu ita yayi magana yana tsaida kallonsa akan Afra dake sakar masa murmushi, mummy ta fito daga Kitchen rike da plet din coslow an rufeshi da wani farin laylon ta haɗa ne sabida muradi na matukar so ,badamasi ya Kalli mummuy yace " sannu mummy da kokari".
tace "yauwa son ta fada tana taya su mufeeda shirya dinnig dan ko sunyi aiki indai bangare girki ne ko shirya dinnig table sai ta sake dubawa inda akwai abinda zata gyara tayi idan babu ta barshi "mummuy wai mai yasa baki son masu aiki ne sai dai ke da yara kuyita walahar aiki ?"
"Wallahi dai haka kawai bana bukata masu aiki nan nafi son nayi komai da kaina kuma nafi son kanneka su kware gurin iya kowani irin girki, alhamdullahi gashi kowane daga cikinsu ta kware ta iya kowani irin girki "yanzu mummy kina nufin waɗan nan yaran sun iya girki ?"
"Sosai kuwa bari kaci kaji zaka tabbatar da hakan., kamshin girki duk ya karad'e ko'ina ya karaso kusa da mummy Yana ƙoƙarin jan kujera mufeeda tayi saurin ja masa ya zauna akan kujera ya buɗe kular miya, kamshi miyar ya buge hancinsa ya lumshe ido yana fatan yadda kamshi da kyau a ido yayi dandano a baki , ya buɗe kular shimkafa basmaty ce farar sol , Afra ta matso kusa dashi tayi saving d'insa ta janye kular a gabansa ta ajiye plet din tangaran tace "bisimilla yaya ta faɗa tana sakar masa murmushi yayi mata wani irin kallo mai tsuma zuciya ," ta cika bulbul kamar ba'a yar shekara sha shida ba komai yaji ajikinta kamar yadda yayi expecting ganinta haka ya ganta ."
A natse ya soma cin abinci lomar farko ya ci yaji kunnesa yayi yummmmmm alamun dadi ya tsaida kwayar idanunsa akan mummuy kunnuwansa na motsi kadan kadan muryarsa a sanyaye yace "cikin Afra da mufeeda da zahra wacece tayi girkin nan acikinsu ?"Wayyo Allah mufeeda ta furta a cikin zuciyarta , take hantar cikinsu gabadaya ya kad'a saboda a tunaninsu ko girkin bai yi masa dadi bane yasa ya tambaya , mummy tace "to dai kusan kowace acikinsu tasa hannu saboda ayi sauri ". ya jinjina kai sannan yace "lafiya dai ko abincin bai maka dadi bane ? "Ai dadin ne ma yasa haka idan mutun yana samun yana dibar irin wannan girki ai sai dai ya tare a gidan nan gabad'ayan "ai ko Gabadaya suka saka masa dariya..
"sosai kuwa son shiyasa duk sanda zan yi tafiya zuwa wata kasa nafi tunanin girkin mummynku dana yarana dan gaskiya ba daga nan ba gurin iya girki an horasu kuma sun iya bana shayin zuwansu ko'ina , ina alfahari da wannan kyakkywar salihar matarta tawa domin itace tsanin akan rayuwarsu inji cewar dady daya shigo yanzu fuskarsa ɗauke da murmushin jin dadi, "kajika kou da wani zance zaka fara zolayar naka daka saba ko "?
"zolaya ko gaskiya ".badamasi ya yunkura zai miki domin isar da gaisuwar ga mahaifinsa dady ya matso da sauri ya dafa kafad'ansa "yi zamanka son karka damu kanka "mun sameku lafiya dady ya ayyuka ?"Lafiya son muna nan muna fama har yanzu babu mataimake sai Allah, ya ka baro Australia da aikin naka fatan an samu abinda akaje nema ?"Alhamdulillah dady komai ya kammala " mummy ta Jawa dady kujera tare da cewa "banason kana doguwar tsayuwa ka zauna kusa da d'anka dan nasan yau akwai labari " zama yayi kusa da ya badamasi itama ta zauna gefensa tana zolayarsa suna barkwancinsu da suka saba "eh yau din dai nasan hirar duk akan surukarki zai min suka sa dariya gbdy har dasu Afra da bata fahimcesu ba shi kam badamasi sai murmushin jin dadi yake dan rayuwar iyayensa na matukar burgeshi"
Gabad'aya hayaniyarsu ta karad'e parlour'n ya badamasi na ci abinci yana zuba santi Afra ta mike ta jingina bayanta a bayansa "ga taimakon gaugauwa dan karka rushe a kasa, ya kai hannunsa zai zuba mata dundu tayi saurin janye bayanta "yanzu ya badamasi sai ka zuba min wannan hannunka ?"Da dai kin tsaya yarinya kiga aiki da cikawa suka tuntsire dariya ...""Assalamu alaikum" sallamar abokan muradi da Samir ne ya karad'e parlour'n jahid khalifa da yasir Habib suka ƙarasa shigowa , gabadaya mutanen dake zaune a parlour'n suka amsa musu ban da afra data yatsina fuska dan sam bata qaunar masu zuwa neman muradi kusan duk wanda yake tare dashi haushi yake bata suma kuma sun san da wannan tsanar , su jahid suka k'arasa shigowa falon haɗe da gaishe da mummy sannan suka wa ya badamasi sannu da zuwa sannan suka samu guri kan doguwar kujera suka zauna kowanensu hannunsa rike da iPhone, muradi da Samir suka mike daga inda suke zaune akan kujerar dining table suka zauna kusa dasu ,nan hayaniyarsu ta karad'e parlour'n ban da hirar kwallo da yahoo babu abinda suke suna tsaka da hira jahid yace" ku tsaya na baka wani labarin ban dariya ya badamasi da yayi niyyar mikewa dan ya huta jin abinda jahid ya fada yasa ya gyara zama dan Allah yayisa da son jin labarun ban dariya musamman yake zuwa gurin hajiya kayi ta dinga bashi a lokacin da take zaune a Lagos jahid ya soma magana yana dariya "wani mahaukaci ne ya iske wata mahaukaciya a bakin rafi tana kuka sai wannan mahaukacin yace "ke mahaukaciya me yasa kike kuka ?".
Sai tace "sugar na zuba a cikin rafi kuma bai yi zaki ba ".Sai mahaukacin yace "cokali yakamata ki samu ki gauraya zai yi zaki ya karasa maganar yana kwashewa da dariya duk parlour'n babu wanda bai yi dariya ba har afra sai datai dariya ,jahid ya saida dariyarsa yana numfasawa "yanzu cikin su wa yafi wani hauka nan wata hayaniyar ta sake kaurewa wannan yace mahaukaciyar wannan yace mahaukacin ganin sun soma mutsu a tsakaninsu yasa ya badamasi ya mike ya nufi bangarensa yaso Afra ta biyosa amman mummy tayi dabara ta aiketa d'akinta dan ita dai idan tace tana qaunar hadin nan tayi karya saboda wasu daga cikin halaiyen afra din da bata so ,duk yadda ya badamadi yaso kebe wa da Afra mummy taki yarda ,hatta tsarabansu shi da kansa ya kawo musu sai dai na afra dana kisna yafi na kowa yawa, har zahra da mufeeda suka saka ayar tambaya amman ta sharesu".
Daren washegari ranar badamasi ya dade a d'akin dady suna tautaunawa akan rayuwar duniya a hankali suka gangaro kan maganarsa da Afra sun jima suna tautaunawa har sai da mummy ta shigo ta koresa tace "maza tashi ka bar min miji ya huta haka nan wai ma me kuke ta faman tautaunawa akai ?"ya Badamasin yayi murmushi ya tashi yayi musu sallama ya wuce part d'insa .
Bayan wata da dawowar ya badamasi yana tsaye a tsakiyar dakinsa yana shirya kansa cikin wasu ratsatsun kanana kaya , ya gama ya feshe ilahirin jikinsa da turare mai sanyi kamshi , kai tsaye part din mummuy ya nufa ya tsaya yayi breakfast sannan ya nufi kofar d'akinta yana isa yayi sallama ya ɗan tsaya domin ta bashi damar shigowa, mummy dake tsaye cikin wani had'ad'd'en volyal lace Mai kyau da tsada sai kamshi turaruka take ,ta waigo zuwa kofar shigowa d'akin tare da bashi umarnin shigowa, Ya badamasi ya shigo dakin fuskarsa dauke da annuri da tsantsar farinciki ,a natse ya karaso inda mahaifiyarsa take tsaye tana saka abun hannu ya amsa ya k'arasa saka mata yana yabawa da yadda mahaifiyarsa ke da tsananin tsafta da kula da kanta a zuciyarsa , ta kowani bangare baka isa kaci gyaranta ba, dan kusan dukkaninsu yanayinta suka d'auko gurin tsafta da iya tsara kwaliya son kamshi cike da girmsmawa ya durkusa har kasa ya gaisheta "ina kwana mummuy ?".
Mummy ta shafa sumar kanshi cikin farinciki tace "lafiya lau son ka tashi lafiya ya gajiyar aiki fatan komai na tafiya yadda ya dace "alhamdulillah mummuy komai na tafiya daidai sai godiyar Allah ,dan hira suka soma tabawa kafin daga baya ya yunkura ya mike "bari naga dady kafin ya fita office ."Wani dadyn mutumin da yayi sammakon fita ,ai tun bakwai ya bar gidan nan ko breakfast bai tsaya yayi ba, shiyasa yaso ace kasuwanci ka karanta amman ka nacewa wannan aiki ,gashi ka bar min miji yana faman shan wahala shi kadai ta karasa maganar tana haɗe rai tare da kawar da fuskarta gefe alamun fushi".Ya kamo hannuwanta duka cikin nashi "kiyi hakuri mummuy wallahi koni yanzu nayi nadamar za'bar aikin karatun likintanci da nayi akan kasuwanci ,sai dai babu yadda zamuyi da qaddara, inshallahu nan gaba dady zai zauna ya huta tunda ga Samir Aliyu da madu nan , mummy ta juyo a hankali ta tsura masa idanunta "naso ace kaine ka gaji mahaifinka tunda kai ne babba "ya sakar mata murmushi cikin tautausan lafazi yace "maganarki gaskiya mummuy Amman Shima wannan aikin dana yi karatu akanshi yana da nashi amfani kuma zai taimaka sosai, mummuy ta saki fuskarta "shikenna Allah ya taimaka sai ka maida hankalinka sosai akan aikinka kafin batun aureko?". ya badamasi yayi shiru na wani lokaci sannan yace "nifa mummuy nan kusa nake son ajiye iyali". mummuy ta girgiza masa kai alamun rashin yarda "bazan taɓa yarda ba duka Afra ma guda nawa take da za'a ce aure yanzu kai amatsayinka na likita kaga dacewar haka ace ka auri yarinyar yar shashida ?"ya badamasi yayi raurau