Showing 186001 words to 189000 words out of 495987 words
Chapter 63 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
"wannan gaskiya ne zan cigaba da murza zuciyar abokin rayuwata ,
"kina da matukar kyau salaha gaskiya nayi sa'ar samun kyakkyawar mace mai kyawun hali da zuciya ga tsabata da yawon ado cike da jin dadin yabon da yayi mata ta saki dariya mara sauti tace "kai kar fa kasa kaina ya kara girma "tunda dai ba rabewa gida biyu zai yi ba ai na auna arziki ta bude kular abinnsa ta zuba masa a cikin plet ta ajiye a gabansa tana dubansa ta dibo abinci "bude baki na baka abaki kaji rabin raina ya bude baki ya amshi abincin yana lumshe idanunsa "gaskiya ke macece ta gari da samun irinku ke da matukar wuya acikin gidan aure shiyasa babu babban riba a rayuwar namiji kamar ya auri kyakkywar mace ta gari mai kyawun hali Allah yayi miki albarka tayi murmushi tace "ameen sai data tabbatar da ya koshi sannan ta barshi yana sakace ta shige daki domin shirin bacci"
******
Washegari gari bayan mummy ta taya dady ya shirya kanshi ta kai shi dining area domin yaci abinci ,a lokacin Gabadaya yaran gidan suna kan table suna cin abinci ,bayan ya kammala ya mike yace "mu zamu office"Ta biyosa a baya rike da jakarsa,suna dan tautaunawa ,
"Dady sai ka dawo inji cewar mufeeda ,afra tace "Allah ya taimaka dady ya bada kasuwa mai albarka ka siyowa kisna kayan dadi yayi dariya yace "ke zan siyowa dan ko na siyo mata ai kece zaki cinye dariya ta kwashe dashi tace "ai babu komai dady kai da kaya duk mallakar wuya ne,sai da suka gama barkwancinsu sannan ya sa kai ya fice har jikin motarsa ta takashi suna barkwancinsu ya shiga direbansa yaja tana daga masa hannu..."
Mmn sudais[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 28
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602  domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096..
.....Yana shigowa unguwar yaji gabansa ya fadi daga nan yayita jin faduwar gaba har ya dafe daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da matsanancin karfin gaske , Samir ya dubesa tare da cewa "lafiya muradi ka dafe qirji ? jiki a sanyaye yace "wallahi haka nan naji zuciyata na rawa da matsanancin bugawa "kayi addu'a zaka daina ji ya gyada masa kai yana sake dafe da qirjinsa suka shigo gidan Samir ya wuce bangarensu har muradi zai bi bayansa sai ya juya ya nufi bangaren mumy tun kafin ya karaso yake jin sautin murya kasa kasa hakan ya kara masa jin faduwar gaba fiyye da wanda yake ji "Allah Akbar mumy ta fada da dan karfi Allah sarki rayuwa kenan a she duk burin da muka ci na neman rashida a she bata raye a duniya na tsawon shekaru ? Mumy tayi maganar cikin tsananin tashin hankali tana juya wasikar da mutumin dake zaune a gabanta ya bata sako ne daga haroon gabad'aya muradi ya rude sakamakon sunan daya ji mumy ta furta da kalmar mutuwa take jikinsa ya kama rawa ya tsaya a bakin kofa yana kallonsu zuciyarsa na cigaba da bugawa tamkar wanda ake bugawa guduma .
zuciyarta mumy duk a jagule ta cigaba da magana "ta ya zan sanarwa ya'yanta wannan mummunar labari daka zo min dashi ? tayi shiru hawaye na zubo mata "me yasa haroon bazai yiwa kanshi fada ba yayi rashin abubuwa dayawa a duniya mahaifi mahaifiya mata amman duk hakan bai sa zuciyarsa ta natsu ta karkato zuwa gida ba? " yanzu meye amfani wannan wasikar daya baka k kawo min sannan hakurin me yake bawa mutane ? mu bai yi mana laifin komai ba ya dawo ya rungumi rayuwar ya'yansa kada maraici yayi musu yawa wallahi naji mutuwar rashida sosai koda ban taba sanyata acikin idanuna ba ........"
tashin da ba'a sa masa rana ai muradi na gama jin maganar mumy ya saki wani gigitaccen kara wanda ya dawo da hankalinsu mumy ga kofar ya kife kasa babu numfashi mumy tayi wurgi da wasikar hannunta ta kwalla kara da ihun neman dauki tayi kan muradi tana kiran sunansa ina numfashi ya tsaya baya ko motsi kafin kace me parlour'n ya cika da jamar gidan aka daukeshi domin ceton rayuwarsa Samir da mumy da sauran yaran gidan suka dinga kuka yayinda mumy ke furta kalmar Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un muradi kuwa wuni biyu yayi a sume sannan ya farfaÉ—o cikin mayunwanci hali yana kiran sunan mahaifinsa "mamana bamuyi haka dake ba me yasa kika tafi kika barmu ?" bakice mana zaki mutu ki barmu ba cewa kikayi zaki dawo garemu mu cigaba da rayuwa na dade ina jin wani abu makamamcin haka sai dai na kasa gasgata mutuwa kikayi ," Allah sarki ya Allah kajikan mahaifiyata rashida Allah ka saka miki ga duk wanda ya zalinceki duk wanda yake da saka hannun cikin musguna rayuwarki Allah ka musguna masa tun a gidan duniya ka kaskantar dashi sosai zuciyar muradi ta girgiza da labarin jin mutuwar mahaifiyarsa sai da yayi kwana uku asibiti cikin jimami sannan aka sallamosa ya dawo gida yana kuka Samir ya rungume shi cikin tsananin tashin hankali ya nufi dakin mumy dashi ya kwantar dashi akan gadon mumy tunanin irin rayuwar da yayi da mahaifiyarsa yake ,yanzu wani rayuwa mai dadi zai yi babu ita a duniya ? mumy ce ta dinga kwantar masa da hankali da cewa "Allah na sane daku kuma shine gatan bawa zai kawowa rayuwarku tallafi Ni kuma inshallahu nayi alkwarin rikeku cikin amana da kai da d'anuwanka bari na kira number mahaifinka kuyi magana dashi ya girgiza mata kai cikin Muryar kuka yace banaso jin muryar mutumin da yayi sanadin rugujewar rayuwar nida mahaifiyata da yan'uwana wallahi na tsaneshi mumy bana ji ajikina cewar ina da wani mahaifi bayan dady ya karasa maganar yana kuka itama mumy hawaye take zubar tana cigaba da neman number haroon amman yaki dauka ta sake rushewa da wani kukan tana cewa "me ye amfani turo min da number alhalin kasan bazaka dauki kirana ba ? bata hakura ba haka tayita kiran numbersa sai daga karshe ya dauka ta dinga masa kuka tana rokonsa "haroon kayiwa girman Allah ka dawo gida muna bukatanta haka ma yayanka na bukatarka ai jin kalmar ya'ya yasa ya katse wayarsa gaba-daya ta sake kira taji number a kashe daman mutumin daya aiko mai suna shaaibu ya faÉ—a mata bai san da zaman yaran agurinsu ba a tunaninsa yaran na gurin dangin mahaifiyarsu , kowa yayi wa muradi gaisuwar mutuwar mahaifiyarsa da yake ji kamar a lokacin akayi masa amman ban da afra datake masa kallon hadarin kaza ,muradi ya rasa lafiyar jikinsa sakamakon mutuwar mahaifiyarsa ta bugesa bada wasa ba haka zai zauna a d'aki yayita kuka sosai yake jin maraicin ajikinsa ya rame sosai ya daina cin abinci gabad'aya kuzarinsa yayi kasa mumy ta dawo dashi É—akinta saboda kwana yake sambatu da kyar tasamu da taimakon Allah ya dawo daidai ya cigaba da rayuwarsa sai dai kallo daya zaka masa kaza fahimci akwai ciwo a rayuwarsa ..."
******
Bayan wata daya
Yaya badamasin ne ke saukowa daga mattatakalar benen jirgi ,jikinsa sanye da tufafi masu matukar kyau da tsada , fatar jikinsa kawai zaka kalla kasan kudi sun zauna masa ba karya ,komai na jikinsa masu matukar tsada ne, sai faman washe haƙora yake a lokacin da yake nufo inda motar mahaifinsa ke tsaye jiran karasowarsa Allah Allah yake ya k'arasa gida ya da'ura idanunsa akan kyakkyawar fuskar mummynsa da afra dinsa yaga yadda ta kara girma da kyau , da fari cewa dadynsa yayi lallai idan za azo d'aukarsa azo masa daita amman dady ya hana yace" idan tazo ai bai yiwa yan gidan suprise din da yake bukatar yi musu ba ,gara kawai su gansa daga sama ."
Motar data d'aukosa ko gama daidaita tsayuwa batai ba a haraban gidan ya bude murfin motar cike da farinciki ya fito ya nufi babban parlour'n gidan inda ya ci karo da mummy dake tsaye tana bawa muradi sako zuwa gidan hajiya Aysha , Kawai taga mutun daga sama yana washe mata baki " Mummy nah I miss you ya karaso cike da murna ya rungumeta ajikinsa ,"i Miss you too my lovely son , how was your joining ?"Shine baka faÉ—a mana cewar yau zaka sauka ba kou ?" tayi maganar tana shafa sumar kansa cikin tsananin farinciki ganinsa "sorry mummy nah suprise nake son muku amman dad yasan da dawowata yau ". "Alhamdulillah tunda Allah ya kawoka lafiya ya ka baro Australia ?"
Ya shafa sumar kansa yana kallon inda Afra da mufeeda da zahra ke tsaye hayaniyarsu ce ta fito dasu da gudu , yace "lafiya mummuy ya gida
ita kuwa Afra sai faman zuba masa murmushi take wanda yake ƙara tafiyar da imanin ya badamasi yana zare jikinsa daga rungume mummy da yayi ya karaso inda take ya rungumeta yana shafa bayanta "kin wani tsaya kina kallon mutane haka ake wa mutune sannu da zuwa ?" Mummy ta Kallesu ta girgiza kai
tare da hararasa ."
Murmushi Afra ta yi haÉ—e da rungume shi tsam tana masa sannu da zuwa sannan ta zare jikinta mufeeda da zahra suka rungumeshi atare "na same ku lafiya sister's?".
"Lafiya lau yaya ya Australia "?Murmushi yayi tare da cewa "lafiya sister's ". Muradi da Samir da madu sukayi masa sannu da zuwa sannan suka nufi waje domin shigo da kayansa shi kuma muradi ya wuce inda mummy ta aikesa ."
Kyawwan idanushi masu matukar kyau ya zubawa Afra tare da karasawa inda take tsaye rungume da hannuwanta tana sakar masa murnushi ,riko hannuwanta yayi cikin natshi wani irin zirrrrrrrrr suka ji a tare tayi saurin zare hannunta "wai ina autar mummy ne ban ji hayaniyarta ba ko bata gidan ne ?"Tana nan sarkin rigima tana daki tana bacci" mufeeda ta bashi amsa da haka "muje ka huta kafin a shirya maka abinda zaka ci kafin lokacin ma dadynka ya dawo".
" Okya mumuy bari naje na dawo ya nufi part d'insa komai kyal an gyara koina very neat tamkar yana kasar, ya cire kayan jikinsa ya fada toilet bai wani jima ba ya fito saboda jikinsa daman ba wani datti yayi ba , koda ya fito ya iske su Samir sun shigo masa da jakarsa ya goge jiki da karami towel wasu kayan ya d'auko ya saka ya fesawa jikinsa da turare mai daÉ—in kamshi ya dauki wayoyinsa ya nufi bangaren mummuy yana shiga parlou'n ya iske mufeeda da Afra suna jera abinci a dinnig table.
"sannuku yammatan mummy suka juyo a tare fuskarsu É—auke da murmushin "yauwa yaya sanunka ya gajiya ?"gajiyar nan ma idan akwaita yanzu babu ita yayi magana yana tsaida kallonsa akan Afra dake sakar masa murmushi, mummy ta fito daga Kitchen rike da plet din coslow an rufeshi da wani farin laylon ta haÉ—a ne sabida muradi na matukar so ,badamasi ya Kalli mummuy yace " sannu mummy da kokari".
tace "yauwa son ta fada tana taya su mufeeda shirya dinnig dan ko sunyi aiki indai bangare girki ne ko shirya dinnig table sai ta sake dubawa inda akwai abinda zata gyara tayi idan babu ta barshi "mummuy wai mai yasa baki son masu aiki ne sai dai ke da yara kuyita walahar aiki ?"
"Wallahi dai haka kawai bana bukata masu aiki nan nafi son nayi komai da kaina kuma nafi son kanneka su kware gurin iya kowani irin girki, alhamdullahi gashi kowane daga cikinsu ta kware ta iya kowani irin girki "yanzu mummy kina nufin waÉ—an nan yaran sun iya girki ?"
"Sosai kuwa bari kaci kaji zaka tabbatar da hakan., kamshin girki duk ya karad'e ko'ina ya karaso kusa da mummy Yana ƙoƙarin jan kujera mufeeda tayi saurin ja masa ya zauna akan kujera ya buɗe kular miya, kamshi miyar ya buge hancinsa ya lumshe ido yana fatan yadda kamshi da kyau a ido yayi dandano a baki , ya buɗe kular shimkafa basmaty ce farar sol , Afra ta matso kusa dashi tayi saving d'insa ta janye kular a gabansa ta ajiye plet din tangaran tace "bisimilla yaya ta faɗa tana sakar masa murmushi yayi mata wani irin kallo mai tsuma zuciya ," ta cika bulbul kamar ba'a yar shekara sha shida ba komai yaji ajikinta kamar yadda yayi expecting ganinta haka ya ganta ."
A natse ya soma cin abinci lomar farko ya ci yaji kunnesa yayi yummmmmm alamun dadi ya tsaida kwayar idanunsa akan mummuy kunnuwansa na motsi kadan kadan muryarsa a sanyaye yace "cikin Afra da mufeeda da zahra wacece tayi girkin nan acikinsu ?"Wayyo Allah mufeeda ta furta a cikin zuciyarta , take hantar cikinsu gabadaya ya kad'a saboda a tunaninsu ko girkin bai yi masa dadi bane yasa ya tambaya , mummy tace "to dai kusan kowace acikinsu tasa hannu saboda ayi sauri ". ya jinjina kai sannan yace "lafiya dai ko abincin bai maka dadi bane ? "Ai dadin ne ma yasa haka idan mutun yana samun yana dibar irin wannan girki ai sai dai ya tare a gidan nan gabad'ayan "ai ko Gabadaya suka saka masa dariya..
"sosai kuwa son shiyasa duk sanda zan yi tafiya zuwa wata kasa nafi tunanin girkin mummynku dana yarana dan gaskiya ba daga nan ba gurin iya girki an horasu kuma sun iya bana shayin zuwansu ko'ina , ina alfahari da wannan kyakkywar salihar matarta tawa domin itace tsanin akan rayuwarsu inji cewar dady daya shigo yanzu fuskarsa É—auke da murmushin jin dadi, "kajika kou da wani zance zaka fara zolayar naka daka saba ko "?
"zolaya ko gaskiya ".badamasi ya yunkura zai miki domin isar da gaisuwar ga mahaifinsa dady ya matso da sauri ya dafa kafad'ansa "yi zamanka son karka damu kanka "mun sameku lafiya dady ya ayyuka ?"Lafiya son muna nan muna fama har yanzu babu mataimake sai Allah, ya ka baro Australia da aikin naka fatan an samu abinda akaje nema ?"Alhamdulillah dady komai ya kammala " mummy ta Jawa dady kujera tare da cewa "banason kana doguwar tsayuwa ka zauna kusa da d'anka dan nasan yau