Showing 240001 words to 243000 words out of 495987 words

Chapter 81 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

ita ta lura da hakan tun dadewa har tayi mata magana sai ta tsiri gaba daita ,gani gaba tayi karfi sosai sai mumuy ta tsaresu da tambaya shine zainab ta fada mata , ranar mumy tayiwa kisna dukan mutuwa da kyar kisna ta amshi kanta da taimakon zainab da masu aikin gidan ai kisna na fitowa daga dakin mumy ta zari hijab d'inta dake shanye a igiya ta fice ta bar gidan kai tsaye unguwarsu musa ta nufa ta karo masa komai shina take yaji ya tsani Zainba a cikin ransa ya mike a fusace yana zage zage cikin harshen turanci dan shi suke yi da kisna basu fiyye yin yoroba ba ya dauki alkawarin sai yaci uban Zainba idan ya kamata da kyar abokansa suka shawo kansa ya hakura .

"to sai me idan an san muna soyayya a gidanku ke bakya son a sani ne ko me ?yayi mata tambayar yana Kallonta tayi shiru ta kasa cewa komai wata razananniyar tsawa ya buga mata wanda yasa take hantar cikinta kawada tace "ina so mana tunda ina sonka ya kamota ya mikar daita tsaye suka fita daga gidan ya nufi gidan matar yayansa adam daita ya koro matarsa karya da gaskiya tare da nuna mata jikin kisna "kiga fa irin dukan da mamanta tayi mata kamar ba ita ce ta haifeta ba ,iya arfat tace "da alamar ba itace ta haifeta ba dan uwa ba bazatayiwa yarta irin wannan dukan ba nan sukayi ta zagin mumy a gaban kisna, bata ji dadin yadda suke zagin mahaifiyarta ba amman tsananin tsoro ya hanata magana har kusan goman dare bata ji Musa yace mata ta tashi su tafi ba.
A hankali ta bude bakinta tace" zan wuce gida ya juyo yayi mata wani irin kallo sannan yace "babu inda zaki anan zaki kwana su da sake ganinki sai kinyi sati biyu ....."

Mmm Sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Page 35

~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim


"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096,.

....mumy tayi shiru kawai tana dubansa qirjinta na wani irin dokawa da matsanancin karfin gaske tana jin kamar ta cigaba da zubar da hawayen dake boye a cikin idanunta muryarta a matukar raunane tace "zauna muradina na sake fahimtar da kai halin da kisna ta jefa kanta ciki da karancin shekarunta". bai so zama ba saboda yadda zuciyarsa ke zafi da ciwon halin da kisna ke ciki amman dole tasa ya matso sosai kusa da mumy ya zauna a bakin gado saboda baya son ganinta cikin damuwa ya kamo hannunta daya cikin nashi yayinda idanunsa ke kan yatsunta masu tsananin kama danashi muryarsa a kasalance yace "mumy kada ki wahalar min da kanki gurin sake yin dogon bayani na rigada na fahimci komai sai dai addu'a zamu cigaba da yi mata da yarda Allah wannan duk mai sauki ne a gurin Allah komai zai wuce ,burina yanzu na daura kwayar idanuna akanta mumy ina son ganin kisna dan Allah karki ce a'a tayi saurin girgiza masa kai batare da tace masa uffan ba "ki fahimci muradinki wallahi ina matukar tausayawa halin da take ciki ban san yadda zan misalta miki ba amman ina jin kamar na mutu akan wannan matsalar jin furucinsa yasa babu mutsu mumy ta dauko key ta mika masa " idan ka ganta ka kulle kofar ka kawo min key karka sake ka bar kofar a buÉ—e " bai ce mata komai ba ya mike cike da sanyin jiki ya fice daga d'akin ya nufi zuwa haraban gidan qirjinsa na dokawa da sauri da sauri "..

A hankali ya tura kofar dakin ya sanyo gangar jikinsa bayan ya bude kofar , a natse ya daura idanunsa da suka sauya kala akanta zaune ta haÉ—e kafafunta guri daya ta takure jikinta tare da daura kanta akan kafafunta gabad'aya jikinta duk sashen belt ne "ya Allah ya furta a fili cikin tsananin tashin hankali ,ya dade akanta yana Kallonta itama taji motsin shigowa kuma duk da bata d'ago kanta ba tasan shi ne ya shigo saboda mayataccen kamshin turarensa na gado daya ziyarci hancinta ,a hankali ya juya ya fita tare da kulle kofar ta d'ago kanta tana jan tsaki ko cikakken minti goma bai yi ba ya sake dawowa dakin hannunsa rike da roban zuma.

Wannan karon a kwance ya ganta ta juyawa kofar baya , a hankali ya dinga daga zara zaran yatsun kafafunsa masu matukar kyau har karaso inda take kwance ya durkusa a bayanta tare da rusinowa yana leken fuskarta saurin runtse idanunta tayi saboda hucin numfasa daya sauka a gefen kuncinta , sosai ya ga ta rame fiyye da yadda ya samu labari , ya gyara tsugunonsa a bayanta ya bude roban zuman dake rike a hannunsa ya lakato ya kai daidai shashin belt din dake kwance ajikinta ya dinga bi daya bayan yana shafa mata yana jin zubar hawaye daga kwarnin idanunsa ya kasa gogewa sannan ya kasa tsaida hawayensa saboda tausayinta ,kisna mai mugun tsoron duka yau itace ke cin duka akan wani banzar jinjiri yaro , duk abinda yake mumy na tsaye a jikin window tana kallonsa itama hawayen take zubarwa, bacin wannan bala'in me zai sa ta a doketa bare har tasa a kulleta a guri daya ? ya sake kai hannunsa ya juyo daita zai duba dayan bangaren hannunta ta tashi firgice tana daga masa tsawa kamar ita da sa'anta yayinda idanunta ke runtse tace "waye ne plz zai dinga taɓa min jiki dan Allah karka sake taba min jiki banaso idan ba haka ba zan shake maka wuya ka mutu ". saurin zaro idanunsa dake tsiyayar hawaye yayi yana kare mata kallon da bai san manufarsa ba "bai damu da jin furucinta ba saboda duk a matsayin shirme ya daukesu bugu da kari yayi tunanin bata san kowaye a gabanta ba tunda har lokacin idanunta na runtse gam ya rikota sosai ta zai rungumeta ajikinta muryarsa na rawa yace "kisna ki natsu mana ni ne fa "kai wa waye ?" ban sanka ba karka sake kai hannunka jikina ta fixge jikinta tare da juya masa baya , ya tsaya yana Kallonta kawai dafe da habarsa "dama ka rabu da yar iska , shegiya mai mugun hali mai zai yi da wannan shegen jikin naki da duk wari yake ? Mumy tayi magana daga bakin window tana huci "no mumy dan Allah ki daina zaginta har yanzu kisna she's under age bata san ciwon kanta ba , dan Allah ku daina dukanta akan wannan ɗan iskan yaron "kai ne dai dan iska bashi ba " yaji sautin muryarta a sanyaye radau a cikin kunnenshi take jikinsa yayi mugun sanyi amman still bai ji haushinta ba sannan bai damu ba dan ya tafi son ya ganta cikin kwanciyar hankali akan duk wani shirme da zatayi ".

A natse ya mike ya buÉ—e kofa dakin ya fito ya kira mumy gefe "kulle kofar tukun "kai mumy babu inda zata muddin ina tsaye a gurin nan ta matso kusa dashi tana dubansa dan jin me zai ce "mumy dan girman Allah ki min alfarma budeta, kulleta bashi da wani amfani addu'a zamu taru muyi mata "addu'ar dinku banza da ikon Allah adduarku bazai yi tasiri ba indai akan ku rabani da musa ne tayi maganar acikin zuciyarta tana jan tsaki yayinda mumy tace "bafa zan yarda da zakin bakinku ba ,dady ma yayi har ya gaji ya hakura bazan budeta ba ta dai cigada da zama a nan har karshen rayuwarta babu yadda muradi bai ya da mumy ba har kuka yayi mata tace sam bata yarda ba babu yadda ya iya da rayuwarsa gashi bazai iya cigaba da mutsuwa mumy ba haka yana ji yana gani ya kulle kofar ya mika ma mumy key ya kama gabansa ai kuwa yana dawowa gida ya tattara kayansa ya koma d'akin sama dan bazai iya wuce Kisna kulle a daki bq ba tana rayuwa tamkar ta marasa galihu uwa uba fitinar afra kullum da salon iskancinta da take zuwa masa bancin shi din tsayayyen namiji da tuni tayi galaba akanshi gara ya koma sama yasan duk iskancinta bazata tsallake mumy ba ta biyosa ,tunda ya koma hankalinsa ya kwanta ganin haka yasa Samir da madu suma suka tattara suka bishi ."


wasa wasa sai da kisna tayi wata uku cif a kulle a daki sai dai a mika mata abinci ta window sannan mumy ta yarda aka budeta shima
saboda wani sati zata rubuta Junior weac dady da muradi suka ce a barta ta zana ta tsira dashi dan ko shi kansa dady bai goyi bayan tana fita da sunan karatu ba , da kyar ta shirya tana tsinewa ya badamasi da madu a ranta saboda sune silar kulleta tace "ba dai kulleni kukayi ba byn kun dokeni zaku sani wallahi bazan zauna ba kuna tauye min hakina ba kuma ina dai musa ne bazan taba rabuwa dashi ba ko zaku mutu , ko Kallonta mumy batayi ba dady da direbansa ne suka sauketa yayi mata faÉ—a sosai sai daya tabbatar da ya kaita har aji sannan ya wuce office , aiko daga school kisna bata dawo gida ba ta wuce gurin musa yana ganinta gabansa ya fadi dan shi ma zuwa lokacin ya fara gajiya da tashin hankali da'ake yi akanta a fusace yace "me ya kawoki gurina ? Ta bude bakinta zatayi magana kenan ya katse mata hanzarin ta hanyar cewa "kinga dan Allah bana son damuwa da tashin hankali ki kama hanya ki wuce tunda danginki basa sona dake " zubewa kasa tayi bisa gwiwowinta tana kuka tana rokonsa "ni haka dangina suke miki kowa na sonki amman ni kullum cikin damuwa nake akanki na gaji enough kisna kowa yaje yayi rayuwarsa ya juya zai wuce ta rungume shi ta baya tana sheshekan kuka babu yadda ya iya haka ya hakura sai dai ya rantse bazai bata masauki ba tace babu damuwa ita dai burinta su dinga haduwa shiru yayi na tsawon lokaci yana tunani inda zai samu kudin da zai sha we da kwaya a hankali ya jiyo daita suka fuskantar juna ,sosai idanunta na kanshi numfasawa tayi kana tace "tunanin fa ?" ya numfasa tare da girgiza mata kai sannan yace "ina cikin matsalar kudi ne wallahi , kudi nake so ifemi ko zan samu agurinki ? yayi maganar yana tafiya hannunsu tsarkafe cikin juna ", ban dashi sai dai ina da hanyar da zaka iya samu kudi idan zaka iya ? "me ye shi hanyar ki faÉ—a min dan ina samun kudin the next thing zan daukeki mu bar garin nan gabad'aya zuwa wani guri har sai munyi aure mun haihu sai mu dawo ya karasa maganar yana rungumota jikinsa farinciki ya kama kisna tace " me zai hana ka hadu kai da ganga dinka kuzo gidanmu akwai wata sabuwar motar da wani enemy dina da'ake rikonsa a gidanmu ya siyawa dad dina ku dauka kuje ku siyar kawai Murmushi Musa yayi yace "kema fa wasa wasa kin iya ta'adanci sata dai kike kokarin turamu gidanku "no ba sata bane cikar burinmu ne ". To shinkenan wannan ai mai sauki ne wace iri ce motar ?"kuma ta ina kike ganin za'a shiga cikin gidanku cikin sauki batare da an fuskanci wata matsala ba ? " ta daga kanta sama alamun tunanin har na tsawon minti goma sannan ta maida idanunta garesa tace *"land cruiser Prado ce "* Idan zaku shigo ku shigo ta katangar baya saboda itace bata da tsawo sosai amman kafin nan kuyi kokarin ku yanke wutar data bawa karfen dake kewaye da katangar , Murmushi Musa yayi yace " zan san yadda nayi amman ni bazani ba gaskiya saboda ina sonki sosai any single mistake ya faru zaki haramta gareni ni kuma abinda bazan so ba kenan nan dana rasaki gara na rasa rayuwata nan dai suka ci-gaba da tautaunawa daga karshe sukayi sallama da zumar zasu hadu gobe a wani lungun dake cikin kasuwa ..."

Bayan kwana biyu musa ya zauna da abokansa sun dauki dogon lokaci suna tautaunawa akan yadda zasu shiga gidansu kisna duk ta inda suka duba sai suga no way za'a iya kama su tunda basu da kayan aiki gashi su ba sana'arsu bace shiga irin wadan nan gidajen na masu kudi barsu dai da satar unguwa shima time to time ne sai sun nemi kudin shaye shaye sun rasa , duk yadda yayi dasu suka ce a'a a cikin abokansa ne wani mai suna sikiru yace zai hadasa da ganga din 'yan fashi da suke bola a munshi local government dake kusa da idiaraba dan su har bindiga suke da take musa ya amincewa sikiru washegari suka je tare akayi magana sannan aka fadi percentage din da kowa zai samu a idan an gama halkallar tare da basu full address din gidan kullum sai yan fashin sun kewaya zuwa unguwar su kisna batare da wani ido ya gansu ba kwatsam wata rana da misalin karfe 1:dot na dare suka fito zuwa unguwar su kisna cikin ikon Allah suka iske gidan babu wuta sakamakon an dauke wutar nepa basu tsaya bata lokaci ba suka hau yanke wayar wuta daya bayan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login