Showing 132001 words to 135000 words out of 495987 words
Chapter 45 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
dace da mai shi zaka zama na hannun damar oga ka saba da kowa amman ban da wannan mai fuskar birin damisa ya k'arasa maganar yana dariya yana dukan stearing mota, gama dukan stearing motar ke da wuya take stearing motar ta nemi kufce masa ,yayi ta ƙoƙarin control ta hanyar d'aura q'irjinsa dan ya rike motar amman ina tuni motar ta soma tangal tangal akan titi kafin kiftawa da bisimilla motar ta kife a gefen titi ....... ...
take suka rud'e suka shiga ihun da kururuwar neman ɗauki kowanne acikinsu na kokarin neman ceton ransa har Aliyu dan zuwa lokacin har motar ta fara fitar da hayaki ,cike da tausayawa shugaban 'yan fashin ya kalli Aliyu "yaro ina sonka ka yafe min nayi sanadin rabaka da mahaifiyarka gashi mutuwa na kusanto mu sai dai bazan juri ganin ka rasa rayuwarka a dalilina ba , zan fitar da kai kabi wannan dogon titi zai kai ka har cikin gari Allah zai kareka yana gama fadar haka yayi kokarin kwantar da Aliyu ya tura kanshi waje dan Allah yasa glass din window a bude yake sai dai bai kai kasa ba kadan ne a bude bancin haka dasu kansu zasu iya fitowa .
cikkaken minti goma ba'a yi da fitowar Aliyu ba motar ta kama da wuta aiko Aliyu na ganin haka ya kwasa da gudu ya bi hanyar da ogan 'yan fashin ya nuna masa yana kuka ,gudu yake sosai kamar ransa zai fita tun yana iya juyawa ya hango yadda motar ke ci da wuta har ya daina numfashinsa ne ya soma ƙoƙarin yin kasa ,ya tsaya yana sauke numfashi tamkar mai cutar asma , kad'an kaɗan ya dinga yi kasa har ya zube a gefen titi ,tun yana iya bude idanunshi har idanunsa suka rufe ya daina ganin duhun dare ,sanyi iskar asuba ne ya farkar dashi a lokacin da bai san a wani hali yake ciki ba ga tashin hankali ga yunwa da kishin ruwa ga firgici yana jin yadda motaci ke falla gudu akan titi suna wucewa amman nauyin da jikinsa yayi yasa ya kasa yunkurawa .
"a qalla sai da yayi kusan awa ɗaya da farfadowa sannan ya samu kwarin jikin buɗe idanunshi sosai ya shiga d'agawa motocin dake falla gudu akan titi hannunsa sai dai duk motar data zo kokarinta ta bawa tayarta iska dan gurin na da matukar hatsari , dan haka ya sake matsowa sosai bakin titi amman still babu motar datayi yunkurin tsayawa har gari ya fara haske ,cikin haka sai ga motar Alhaji Marwan ta kwaso a guje inda Aliyu ya ɗan mike zaune da kyar yana daga musu hannu tun daga nesa Alhaji marwan ya hango fuskarsa cikin matsanancin tashin hankali har direbansa ya wuce da gudu, yace "malam muhammadu mu ɗan tsaya muga ko zamu iya taimakawa yaron ce "Anya yalla'bai ma tsaya wannan hanyar fa bata da kyau ,safe dare 'yan fashi ne dankare acikinsa ,tun daga olori har zuwa nan din duk wani direba idan ya kawo nan Allah Allah yake yaga ya barta da sauri ."
"shiru Alhaji marwan yayi a lokacin da malam muhammadu ke ƙoƙarin taka mota domin falfala gudu "kai dai mu koma ban san dalilin da yasa ba amman naji zuciyata tana umartana dana taimaka masa "dady kar mu tsaya ni dai ina jin tsoro ta karasa maganar a shagwabe kamar zatayi kuka ,cikin tsananin firgita da fargaba direban yace "yauwa yar baba kisa baki gurin nan na da matukar hatsari akwai manyan yan fashi , nan fa tsoro ya sake kamata cikin rauni ta sake kallon mahaifinta tare da rike masa hannu "dady karka bari mu tsaya ,kace ma direba ya wuce dan Allah kace mu wuce ta dinga maganar cikin tsananin tashin hankali a hankali Alhaji marwan ya d'aura hannunsa akanta "me yasa mamana bayan taimako zamuyi ? "me yasa duk sanda za'a yi taimako kike nuna jin tsoro da rashin amincewa ? Saurin girgiza masa kai tayi zuciyarta na sake tsinkewa " ba haka bane dady amman dai ni yanzu banaso kayi taimakon nan tunda an ce hanyar bashi da kyau dan Allah Abba Karka bari a tsaya ni tsoro nake ji ... ...
Mmn sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
Page 23
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
....Malam Muhammad ya ɗan dubi Alhaji marwan ta cikin madubi cikin sarewa yace "Alhaji ka yiwa Allah ka saurari uzurina dana afra duniyar ce ta zama abinda ta zama taimakawa mutane yanzu ya zama abun tsoro ,sai ka taimakawa mutun ya janyo maka babbar matsala dayawa 'yan fashi suna amfani da yara ta hanyar tsaida mutane " babu yadda malam Muhammadu bai yi da alhj marwan ba amman zuciyarsa ta kekashe akan son taimakawa Aliyu ya bashi umarnin ya koma haka malam muhammad ya juya kan mota suka koma har lokacin Aliyu na nan a inda suka barshi yana daga hannu domin nemawa kanshi taimako kawai yaga mota ta tsaya a daf dashi an buɗe murfin motar cikin hanzari "kai yaro me kake yi a wannan daji haka"? sai lokacin Aliyu ya samu karfin halin yin magana yace "tare muke da mamana shine 'yan fashi suka tare motarmu a baya kaɗan nan dai ya korowa Alhaji marwan abinda ya faru cike da tausayawa Alhaji marwan ya miko masa hannu take afra dake hangosu ta runtse idanunta saboda bakinciki a hankali Aliyu ya da'ura tafin hannunsa cikin na alhj marwan ya rike gam ya shigar dashi gaban mota ya zaunar dashi ya rufe
shi kuma ya koma mazauninsa kusa da afra diyarsa ya zauna malam Muhammad ya taka motar da gudu suka bar gurin tunda Aliyu ya shigo motar afra ta toshe hancinta da hannunta daya ."
Malam Muhammad na falfala gudu akan titi Aliyu na share hawayen dake zubo masa hankalinsa ya sake tashi da al'amarin rayuwar duniya mahaifiyarsa ce tazo masa wasu kwalla suka zubo masa ina zai ga mahaifiyarsa tana raye ko ta mutu ? "Idan tana raye me yasa bata sake waiwayarsu ba ? Yayiwa kanshi tambayar yana sake zubar da hawaye ya rasa mahaifiyarsa mai tsananin son shi ya rasa kaka mai sonshi fiyye da rayuwarta yanzu kuma ya rasa anyarsa data maye masa gurbin mutane masu daraja da mahimmanci a rayuwarsa ko taya zai hadu da danginsa ? kuka yake sosai tun yana yin kukan a hankali har sautin kukansa ya soma fita afra taja tsaki tana sake kawar da fuskarta gefen titi tare da toshe kunnenta dan tun daya shigo motar kallo tayi masa ta dauke fuskarta . Alhaji marwan yace " yaro kayi hakuri rayuwa duk yadda Allah ya tsarawa mutun babu wanda ya isa ya canza masa ita qaddara tana fadawa bawa daidai yadda Allah ya hukunto masa sai dai ko addu'a ta sausauta qaddarar ka daina kuka haka inshallahu zaka ga mahaifiyarka idan da rai " afra ta fashe da kuka tana cewa "wai dady me yasa kake yin haka ka fiyye tausayin mutane ? " Allah ban so ka taimaka masa ba ni tsoronsa ma nake ji kalli fa yadda jikinsa yake duk yayi kaca kaca wayasani ma ko dan boko haram ne? take hawayen Aliyu suka tsaya saboda maganarta ta daki kunnuwansa sannan ta wuce cikin zuciyarsa sai yaji kamar ya bude murfin motar ya fita ,zuciyarsa a dake bai yi la'akari da motar na gudu akan titi ba ya kai hannunsa zai bude murfin motar yajita a kulle gam nan zuciya ya sake zuwan masa wuya ya soma kokuwa da numfashinsa saboda bai samu nasarar fita daga cikin motar ba ,
malam Muhammad ya kallesa cike da tsananin mamaki yaro Karami haka da zuciya kai ya shiga girgizawa sannan ya sake maida kanshi ga tuki yayinda Alhaji marwan ya dakatar da afra dake zuba maganar da duk tazo bakinta batare data kalli gaban motar ba , shiru tayi ba dan ranta yaso ba alhj marwan ya cigaba da kallonta zuciyarsa na tsinkewa ya lura tunda Aliyu ya shigo motar yanayinta ya sake sauyawa zuwa damuwa da tsananin ɓacin rai Allah dai ya taimakesa idan ba halin mahaifiyarta ta dauko ba , yayi shiru yana tunanin inda zai kai aliyu idan ya isa Lagos dan bai isa ya kai shi gidansa ba saboda matarsa bata son bako ko yan'uwansa ma hakurin dole take yi da zuwansu gidansa dan babu yadda ta iya , kai tsaye zuciyarsa ta umarcesa ya kai shi gurin mahaifiyarsa domin ita soyayyar mutune shine abu mafi sauki a rayuwarta d'a ko ba nata bane zata maidashi tamkar nata tare da bashi kulawar data dace sun fi karfin awa daya suna tafiya idanunsa ya sauka akan wani restaurant dan haka ya bawa malam Muhammad umarnin tsayawa a daidai bakin restaurant din yayi parking motar suka sauko har aliyu da alhj marwan yace ya fito , Afra Kam kin fitowa tayi dan haushin dauko Aliyu da mahaifinta yayi , yaro yayi kaca kaca yayi datti kamar an hakoshi a rami gashi tun daya shigo motar yanayin kamshin motar ya sauya , a hankali ta sake maida kanta gefen titi cikin yanayin na ɓacin rai tana sake jin bakinciki , alhaji marwa ya zagayo ya bude bangaren da take zaune yace "mamana fito muje kici abinci "dan turo karamin bakinta tayi alamun shagwa'ba sannan tace "bana jin yunwa dady shiru yayi kawai yana dubanta Kafin daga baya ya juyawa ya nufi cikin restaurant din babu yawon mutane kasancewar har lokacin safiya ce ,kujera yaja ya zauna tare da nunawa Aliyu gurin zama nan masu siyar da abincin suka karaso garesa suna tambayarsa abinda yake bukata ya dubi Aliyu da malam muhammad yace "me za'a kawo muku malam Muhammad yace akawo masa tuwon semoviter da miyar ugu sannan ya dubi Aliyu dake zaune zuciyarsa na tuttukin bakinciki da tsinkewar zuciya "kai fa me zaka ci yaro "? Yayi saurin girgiza masa kai "bazakaci abinci ba ? Ya gyada masa kai idanunsa na kallon table din dake tsakiyarsu babu kyamkyami Alhaji marwan ya kamo hannun Aliyu cikin nasa "ka saki jikinka dani dan ina ji ajikina bazaka cutar dani da iyalina ba , ka ɗaukeni kamar mahaifinka ni kuma zan daukeka tamkar dana abinda yarinta tayi maka kayi hakuri haka take tana da rashin sabo da mutane amman kuma idan kuka saba zakayi mamaki dan zaka ji dadin zama damu runtse Idanunshi yayi yana sauraron Alhaji marwan dake lallabashi dan ya sanyawa cikinsa wani abu da kyar ya iya bude baki yace akawo masa tuwo wani sanyayyen dadi Alhaji marwan yaji dan hakan nan yaji Aliyu ya kwanta masa take ya bawa matar dake tsaye akansu umarnin akawo masa abinda ya bukata ta juya cikin saurin ta zubo ta kawo ma Aliyu abinci da ruwa ta ajiye a gabansa Aliyu ya kalli alhj marwan yace"na gode sannan ya soma ci alhj marwan bai ce masa komai ba ya sallami matar ya bude masa ruwa , Lumshe ido Aliyu yayi a lokacin da ya kai lomar abinci bakinsa saboda dadin da abinci yayi masa rabonsa da cin abinci tun jiya da rana ,Aliyu nacin abinci alhj marwan na kallonsa yana jinjina irin kyawun da Allah yayi masa ga kyau ga kamala cin abincinsa kaɗai ya isa ka fahimci irin natsuwar dake tattare dashi ,malam muhammadu tuni ya kammala amman aliyu ko rabi bai yi ba sun kusan minti ashirin sannan ya kammala suka mike suka shiga mota.."
basu suka isa birnin iko ba sai gurin karfe biyu na rana kai tsaye gidan mahaifiyarsa Alhaji marwan ya bukaci malam Muhammad ya nufa ,tun daga haraban gida Afra ke ihun kiran sunan kakarta hajiya Aysha tana cewa "granny ki fito mun dawo har da wani yaro da dady ya tsinto akan titi ,yaron duk yayi datti har wari yake ."a falon gidan sukayi kicibis da Hajiya Aysha tana tsaye jiran shigowarsu , Afra ta kamota ta rungumeta a jikinta a daidai lokacin da Alhaji marwan ya shigo bakinsa ɗauke da sallama hannunsa rike dana Aliyu "yauwa kinga yaron ko granny a bakin titi dady ya tsintoshi ni banason shi kicewa dady ya mayar dashi inda ya dauko shi ta karasa maganar kamar zatayi kuka hajiya aysha ta kai hannu ta shafa kan afra wacce a lokacin bazata wuce sa'ar Aliyu ba idan ma ya girmemata kadan ne shima bazai fi watanni ba ."
Alhj marwan ya saki hannu Aliyu ya karaso ya kamo hannunta "kai mamana ba dai surutu ba "ai kuna fama da wannan bakin nata mai kama dana aku kuturu sannu da zuwa ya gajiyar hanya "?
"Alhamdulillah Hajiya mun sameku lafiya ya gidan fatan kowa yana lafiya? yayi maganar yana zama