Showing 144001 words to 147000 words out of 495987 words

Chapter 49 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

yamma nan kafin tace wani abu Afra har ta gama fere doya ta shiga Kitchen domin wankewa , mummy na zaune rungume da kisna tana Kallonta tana tofa mata addu'a a zuciyarta kuma take yabawa da afra duk wanda ya aureta zai yi alfahari daita matsalarta dai kyamar talaka wannan kuma halin uwarta ta dauko , sam bata son talaka ya rabeta sai masu arziki idan kaga tana haba haba da mutun to mai arziki ne talakawa kuwa banza ne agurinta ."

Jim kaɗan Afra ta gama da farfesu tazo ta fadawa mummy sannan ta d'aura doya ta shirya ferfesun acikin kula mai daukar zafi mummy tace" sannu Afra Allah yayi albarka ya baki miji na gari Afra batayi magana ba saboda kunya, ta koma Kitchen tana buɗe tukunya dan gani ko doyar ta nuna taga da saura kisna ta taho da gudu tana kiran yunwa naje ji aunty Afra "sorry my baby yi hakuri na kusan gamawa yanzu zan kammala ".
Nan kisna tasa shagwa'bar data saba tana bubbuga kafa a kasa "to ki goyani kafin abinci yayi tayi dariya tace "ke dai babu abinda kike so arayuwarki kamar goyi . "Ai kece kika saba min dan haka Allah sai kin goya ni tayi tsalle zata hau bayanta ,Afra tayi murmushi tana cewa "autan mummy daga ke babu wata ".Ita kuwa kisna sai dariya take tana ƙoƙarin hayewa bayan Afra "har doki zaki min "kince yunwa, kince goyo yanzu kuma doki bari kici abinci duk zan yi miki my baby Kisna tace "to my mumy "mummy'? afra ta fada tana zaro ido waje tare da kamo kisna jikinta " ni ba mominki bace ni sister ɗinkin ce tace to "muje kici abinci "ki samin da nama ."Ba nama bane kifi ne autan mummy ta duba taga abincin ya karasa ta kashe gas ta samu faranti ta zuba mata suka fito "amman ni kadai zan ciye abinci na ko" ."Sosai babu wanda zaki bawa ".Tace "sai ke da mummy nah kawai zan bawa ,Afra na dariya tace "to autan mummy mun gode ta zaunar daita ,a lokacin da yaran gidan suka fara shigowa daya bayan daya suna yiwa mummy sannu da gida mata suka wuce bangarensu maza ma suka wuce part dinsu suka yi shirin zuwa massalaci dan lokacin sallah yayi ,Afra ta dubi mufeeda da zahra tace "tunda kun dawo ku raba abinci suka amsa mata da" to " bata koma Kitchen din ba sai mufeeda ce ta shiga ta rarraba abinci ta zuba a kula ta kai dinnig table tana kammalawa ta nufi daki dan yin Sallah bayan sun yi Sallah mufeeda ta fito ta danna kararrawar dake bayyanar da kammala shirya dining sannan ta ɗauki abinci baba mai gadi da direba ta kai musu ...."

Mummuy kuwa tuni ta fada wanka saboda tasan dady ana yin isha'i yake shigowa kafin ya shigo tayi wanka da sallah, data idar ta samu humura da kulacca mai kyau ta shafa da mai me kamshi, duk tabi lungu da sako na jikinta ta murza ta dauko rigar bacci mai kyau mara shara shara ta saka ta dauko turaren wuta irin wanda ake haɗawa amare tayi amfani dashi , idan kaga mummy bazaka CE itace ta haifi badamasi ummi da Samir madu da kisna ba har ma kayi tunanin tana da siriki saboda yanayin tsarin jikin da Allah yayi mata komai cassss cassss daidai jikinta tamkar yarinya yar talatin duk lokacin data yi irin wannan shirin dady kamar ya cinyeta saboda kauna uwa uba ga kamshi ta ko'ina dady na matukar son kamshi shiyasa Bata rabo da turaruka kala dabam dabam tsab ta gama shirinta ta daura after dress akan kayan ta fito a lokacin yaran basu shigo ba tukunan ,ta zauna akan kafet tana jiran shigowar dady can sai gashi ya shigo ta mike ta karbi jakarsa da laidar daya shigo dashi tana yi masa sannu da zuwa ,ya rungumeta tsam ajikinsa yana shinshina kamshinta " ina son kamshin nan ranki shi dade gaki nan kullum kamar yarinya mutun ko yayi niyyar kara aure dole ya hakura ". tayi murmushi "dady baka rabo da tsokana ,"idan zakayi aurenka kayi mana menene na salaha acikin zai yi magana tace "muje ka huta karka tsaya tsokanar faɗa ya wuce ciki tana biye dashi zuwa falonsa sai data bishi har uwar dakansa ta cire masa hula "duk kayi zuru zuru yau kamar kayi ciwo yana dariya yace "akwai ki da kallon kurulla ya akayi kika gane haka "?
"Yanzu bani da kowa sama da kai a duniya gaba-daya tunanina da komai nawa yana kanka , idan ban kula da kai ba wa zan kula da? "kai ma kasan dole na dinga lura da yanayinka ta karasa maganar tana shiga bayi ta haɗa masa ruwa ta fito "na haɗa maka ruwan wanka ka shiga kayi ko kaji dadin jikinka"Yace "ina bukatar hutu sosai Amman nasan ba yanzu ba , karshen shekaran nan badamasi zai dawo gida , Kinga da kasuwanci yaron nan ya karanta da gabad'aya ayyukan zasu dawo garesa ni kuma na huta , shiyasa na kwallafa raina akan waɗan nan yaran suma gashi kowannensu yace buga kwallo zai yi"gaskiya ne kana bukatar hutu amman dole su Aliyu su hada aiki biyu buga kwallo da kasuwanci idan sun yarda idan kuma basu yarda ba su hakura da kasuwanci dan ina bukatar na ga kana samun hutu yayi murmushi ya shige bayi ."

A can parlour kuwa gabad'ayansu suna zaune akan dinnig table kowane gabansa plet din abinci ne ,kowa ya ci abinsa ya rage ban da muradi daya cinye tas saboda shi mutun ne mai tsananin son doya da tuwon shimkafa sam shinkafa zalla da kayan kwalama basu damesa ba shi dai ya samu abu mai tauri baya son Mai ruwa shiyasa idan tuwo za'a yi tukawar farko mumy take dibar masa ,afra ta kalleshi tace "su bamburu bawan ciki ko yaushe za'a koyi cin abinci a rage ,mutun kamar dan abinci aka halittosa ta karasa maganar tana kwashewa da dariya ,duk suka bita da ido babu wanda ya tayata dariya Samir ya bude baki zai mata magana muradi ya da dakatar dashi tare da d'ago kyawawan idanunshi ya zuba mata take ta daburce ta kasa kallonsa ta ɗauke idanunta tana jan tsaki "ko kallon uwar me yakewa mutane ? shiru yayi yana jin yadda tsanartab ke sake samu mazauni acikin zuciyarsa sau tari daman shi tsanarta mutun shine abu mafi sauki da zuciyarsa ta iya bare ita da yake jin kamar kaya yafi minti biyar yana hukuntata da idanunsa babu shiri ta dauki kisna ta bar parloun tana gunguni "wai me yasa bazaka bude baki ka ciwa wannan yar rainin hankalin mutunci ba ganin fa kana kyaleta ne yasa iskancita ke gaba ? "bari naje na fito maka da shegiya "no barta kawai a kwai lokacin nadama zai zo mata har ma ya aureta iya abinda ya faɗa kenan ya mike ya bar gurin zuciyarsa na tuttukin bakinciki daya bayan suka mike suka bar parloun gabad'aya.."

Dady na fitowa daga bayi idanunsa akan mummy yayi mata murmushi yace "hmmmmm " Ta dubesa da murmushi akan fuskarta itama tace "hmmmmm din nan ban yarda dashi ba akwai magana a bakinka yace "sosai kuwa gani nayi bakya tsufa salaha daga shigata bayi har naga kin sake canzawa ki dai bi a hankali kin kusan ɗaukar wata suruka ....."
tasa dariya tana kallonsa "Allah idanunka ne ke ganin haka Amman kowa ya kalleni yasan na tsufa 50 something fa ".Cikin barkwanci da yake mata ya fada mata batun auren afra da badamasi mummy ta sha mamaki jin abinda ya faɗa tace "daman suna soyayya ne ko kuwa dai kune kuka ga dacewar haka zaku hadasu?"

"Shine da kansa ya fadawa marwan tun da dadewa to sai yau marwan din yake sheida min sai na kira badamasin dan na sake jin ta bakinsa ,shine ya tabbatar min da gaske ne da zarar ya dawo yake son ayi aure mummy ta zaro ido waje "bashi da lafiya guda nawa Afra take duka shibiyar gareta ko shashida fa ? "To ma ya fada mata ne da zai wani ce yana dawowa za'a yi aure idan kuma bata son shi fa......"? Murmushi kawai dady yayi " d'ana ne fa badamasi ta yaya kike tunani Afra zata ce bata son shi kiyi addu'a ki kuma masa fatan samun nasara ".
"Shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi yasa muna raye za'a yi yace ameen "amman dai ku bari ta gama karatunta na gaba da secondary "aa suna gama karatun secondary gaba-daya zan aure dasu wace ta kawo miji shikenan wace bata kawo ba zan samo mata tace "Allah ya taimaka muje kaci abinci ".
Ya dan harareta ta gefen ido yana fadin "ke kinci abinci ne ?" ta masa wani kallo da su kadai suka san manufarsa "ai kasan bana cin abinci sai da kai sai dai idan baka nan shima kaɗan nake ci". Suka fito daga dakin zuwa dining table ta zuba masu suka fara ci suna hira dady yace "wai ina mutuniyata kisna ne najita shiru ?" Dariya mumy tayi tace "yar shagwa'ba da rigima kenan tana gurin mutuniyarta killa ma tayi bacci dady yace "ai wannan mammartamu bata da matsalar rayuwa gashi tana son Afra za'a Sha daga idan zatayi aure ,"wannan gaskiya ne idan kace Afra to ka gama da zuciyar kisna "yau rigima tayi sosai ita bazata makaranta islamiyya tunda nake haihuwa ban taba haifar yar da bata son zuwa karatun addini ba irin kisna har gara ma idan afra zata ba'a fiyye samu matsala ba ko da yake tace malamar islamiyya ke dukanta ko za'a yi mata magana tayi hakuri ta daina saboda a samu tayi karatun "idan bata son zuwa ki rabu daita sai samo mai koya mata a gida kamar ina ganin zai fi "karatu cikin mutane yafi gaskiya zan so tayi cikin yara y'an'uwanta "to shikenan zan sa ayi min kiran shugaban makarantan nasu ya karasa maganar yana canzawa da wata "yau fa na sha wuya a office kuma ga baki kala kala gashi yawanci duk mata ne kinsan kasuwanci da mata sai hakuri naga wata kamar nayi miki kanwa daita , kawar da maganarsa tayi ta hanyar cewa "dady dan Allah na tambayeka wata magana mana ".?
ya gyada mata kai "wai irin son da nake maka kana yi min kwatankwacinsa iri sa kuwa ?"
ya zabga mata harara sannan yace "bana miki kwantakwacinsa zan aureki har mu kai tsawon wannan shekaru ko kin mata irin wahalar dana sha kafin na samu aurenki? " ko dan kinga ina cewa zan miki kishiya shine zaki yi wani tunani ?"
"Ina dai zance kishiya ne a cikin barkwanci ,duk da an san aure nufi ne na Allah idan Allah yayi dake kadai zan zauna har kashen rayuwata haka zan mutu da mata daya, idan kuma da rabon zan kara zan kara
ke irin wannan kwalisan da kike min da kulawar da kike bani ina zai bar ni na ga wata nace ina so ? idan na shigo bani da damar sake lekawa ko'ina, amman dai zaki sani ne allah dai ya kai damo ga harawa yarinyar karama sa'ar su mufeeda zan dauko nayi wasan sallah daita ".mummy ta kasa cewa komai sai murmushi take dan tasan wasa yake a ranta take aiyana irin soyayyar da dady yake mata ita tasan biyayyar da take masa ko yayi aure bai zama lalle ya samu ba ,cikin kwantar da murya tace "wallahi irin son da nake maka araina ko nace a zuciyata ya wuce misaltuwa, ina mai alfahari da kai a rayuwata ," nima ina alfahari dake kuma babu wata mace da zata sha gabanki, kina da kyau uwar marayu ga ladabi da biyayya kwaliya da kamshi dukan ba kya tsallakesu, shi yasa nake kara sonki Allah ya dangwamar damu cikin farinciki har karshen rayuwarmu a natse take bashi abinci har ta gama ta janyo kular farfesu kifi daya sha kayan hadi ta zuba a farantin tangaran yaci suna ta hira har ya gama can ya d'ago ya kalli agogon bango dake manne da parlour'n karfe goma daidai ya mike ya fita zuwa gurin baba Mai gadi ."bayan wasu mintina ya dawo parlour'n ya isketa tayi shiru tana jiran dawowarsa cikin kwantacciyar murya tace "ka dawo nima na gaji muje mu kwanta nan suka tashi suka nufi daki suka kwanta cikin aminci da nuna kulawa ga junansu .."

Daren ranar kasa runtsawa muradi yayi duk inda ya juya tunani kashi da kashi ya addabeshi , tashi yayi ya mike yaje ya dauko kundin tarihin mahaifiyarsa ya dawo ya zauna akan kujera mai zaman mutun daya karo na farko da yayi tunanin dubawa a tun sanda ya dawo hannunsa ya soma buɗe shafin farko mai dauke da kyakkyawan rubutun mahaifiyarsa a hankali ya dinga bin rubutun yana karanta rayuwar jin dadin da mahaifiyarsa ta gudanar tare da ahlinta har zuwa kan had'uwarta da mahaifinsu da irin rayuwar da sukayi cikin kankanin lokaci kwakwaluwarsa ta soma yamutsewa babu abinda yake ambata a cikin ranshi sai kalmar" Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un gumi ya haɗa sharkaf manya lamura guda biyu suka shiga yawo a cikin kwakwaluwarsa kuma kowanne yana bukatar nazari sosai yana matukar bukatar sake ganin mahaifiyarsa da bukatar sanin yadda zai yi da afra wacce take kokarin zame masa karfe kafa da yiwa rayuwarsa karan tsaye ,gaba-daya ta gama yad'awa kowa a school da unguwa matsayin rayuwarsa a gidan duk hanyar da zata aibantashi tasani wanda ya rasa dalinta na yin haka amman duk laifin waye ? Sannan kuma aikin waye ? ya shiga tambayar brain dinsa "duk laifin azzalumi mahaifinsa ne daya tsaya ya rungumi rayuwarsu da wata killa yanzu suna tare da mahaifiyarsu cikin soyayya da farinciki da shi kansa bai danganta kanshi da kalmar shege ba bare ta samu damar musguna masa cikin kankanin lokaci idanunsa suka kada suka yi ja ya dinga huci kamar kumurcin maciji wani bala'in tausayin mahaifiyarsa ya mamayeshi "me ye laifinta da yan'uwanta suka mata haka ? "Ko yanzu a wani hali take ciki ? "me yasa suka aikata mata abinda suka mata ? Yana son sani inda take da halin da take ciki Muradi ya rushe da wani irin kuka dan a ganinsa shine ya kamacesa " Allah sarki mamana ya furta a fili "kin tsinci kanki cikin matsalar rayuwa ne a dalilin azzalumi mahaifinmu "shi kuwa me zai yi dashi a rayuwa har kullum adduarsa Allah ya haɗa shi da mummunar bala'in da zai kawo kanshi garesu shi kuma a lokacin ne zai tabbatar masa da bashi da wasu ya'ya a duniya, sosai yayi nisa cikin kuka yana tunani "me yasa kake masa mugun fatan ? wani ɓangare na zuciyarsa ya tambayesa "shine mutumin da zai sadaka da inda mahaifiyarka take domin shi yasan inda suka dauko rayuwarsu "no no bazan bukaci komai daga garesa ba zan nemeta da kaina idan lokaci yayi bana neman taimakonsa ya mike a fusace yana yarfe hannu tamkar wanda yaji ciwo kafin daga baya ya soma Zariya a dakin duk runtsi duk wuya bazan bukaceka ba nasan duk inda mahaifiyata take hankalinta na kanmu ba karamin dalili ne ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login