Showing 255001 words to 258000 words out of 495987 words

Chapter 86 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

rungume belt din na sauka ajikinsu  "kunga  bala'in da musa ya jawo min kou  ina zaman zamana ?   dole  ne ya rabu musu da yarinya  mana nifa na gaji da wannan wahalar  ta karasa maganar tana rushewa da  kuka tana kokarin kamo Aliyu kafafuwan Aliyu amman ina sake tureta yayi yana haci tamkar kumurcin  maciji  .."

mumy  kuwa  tuni numfashinta  ya soma  barazanar  daukewa  ya badamasi dake kanta ya dinga   kokarin     numfashinta   ya daidaita  sai  dai har lokacin numfashin  yaki daidai  sai haki take tana huci  kwayar  idanunta  nayin sama a matukar fusace muradi yace  "waye  stupid goat  din  dake  damun rayuwar  sister dina  who's that animal  ?  ya tambaya a tsawace  yana   kaiwa bango nashi   dan  shi  ko a hanya ya ga musa zai wuce  ya  wuce  dan  bai sanshi ba  Zainab tace  "ga dan iskan can kaci  ubansa ya Ali  "what wannan dan yaron    ? Zainab  ta gyada masa  kai "wannan   snal  din  take so ?  yayi magana  yana kallon Musa  tare da nuna shi da yatsa ..."
Take   Musa  ya shiga  girgiza masa  dan  ya bala'in tsorata da ganin yanayin  Aliyu dan a yadda yake kallonsa zai iya kashe  mutun har lahira    sosai  Aliyu  ya daura idanunshi  akan  Musa dake rike da hannunsa daya  karye , ganin irin kallon da  Aliyu ke masa yasa musa  soma ja da baya  domin guduwa shi kuwa baban musa tuni ya lalla'ba ya shige daki ya kulle  kofarsa tun  kafin Aliyu ya gama da musa  ya dawo kanshi dan ya  lura babu wanda  Aliyu bai doka ba a gidan ."

Aliyu  na  gama  kallon Musa  yasa ƙafarsa daya yayi wani irin  kwallo dashi  Musa  yayi sama ya  zube kasa yana haki kamar ransa zai fita "kai ! kai !! kai!!!  ne   kake dagulawa iyayenmu  lisafi  ?"  ya  dinga kwallo da musa yana takashi   take   gidan ya  kaure  da  ihu neman taimakon za'a yi kisan kai   kusan   yoroba da  ihun akan faɗa idan abu  yayi  bala'in , gida ya sake  cika  makil  da mutane yan bada hakuri yayinda wasu  daga cikin mutanen dake tsaye agurin  suka fara magana "amman wannan soja ne dai  ko kalli yadda yaki dukansu kamar ya samu dabbobi ,wanda ke tsaye kusa dashi yace "wallahi yayi min daidai Allah yasa yayi masa laga laga shegen yaro mai nacin  tsiya  yana neman bata rayuwar yarinya   .

kisna  kuwa da  iyakacin karfinta take buga kofar tana kiran sunan musa hawaye na bin kuncinta ,cikin dacin rai haɗe da bakinciki  Aliyu ya kai kafarshi ya daki   kofar dakin  duka daya sai ga kofar ta balle kisna ta fito a gigice  idanunta  bai kai ga kowa ba sai kan  musa Wanda ke kwance  baya motsi , da gudu ta karasa gurinsa ta zube  bisa gwiwowinta ta kife kanta a jikinsa taji baya motsi nan   ta soma jijiga  shi tana kuka tana kiran sunansa  kuka take sosai mai matukar cin rai  "waye  ya masa haka ?
"Bolaji tace wannan yayan naki ne "ta bata amsa tana  kukan  zugin belt din Aliyu ,   kisna  ta d'ago idanunta  ta kalli  wanda aka nuna mata Aliyu ta gani  idanunta na tsiyayar da ruwan  hawaye sam idanunta sun rufe ko inda mumy take bata kalla ba ta mike da  sauri  ta ɗauke Aliyu da mari Wanda yasa take numfashin mumy ya dauke  ta daina numfashi gabadaya , yayinda zuciyar Samir da madu da ya badamasi suka tsaya cak suka daina aiki na wani lokaci kafin daga baya zuciyoyinsu ya soma bugawa da karfi hatta zuciyar afra ta  kusan  tarwatsewa   saboda tsananin tashin hankali da firgici abinda kisna tayi , abu  kamar a mafarki  wai kisna ta mari Aliyu akan Musa ?  sam firgicin marin da kisna tayiwa  Aliyu bai sa sun lura da daukewar numfashin mumy ba . "me yasa ka dokesa har ya daina motsi  zaka kashesa ne ?  " ni ya kamata  Ku kashe   tunda bakwa soma bashi ba , "me  ya maka da zaka kashesa ? ta sake daga hannu zata sauke masa wani marin Samir yayi saurin mikewa ya  rike hannunta ya soma gaugaura  mata mari hagu da dama , ta fixge hannuwanta tana kuka "wallahi  kun  damu rayuwata ku kyaleni  mana dole  sai kun hanani soyayya da Musa   ,ni musa nake so bazan  taba rayuwa babu shi ba  kuma babu wanda zan aura sai Musa  ......"

Tunda  kisna  ta mari aliyu  yayi mutuwar  tsaye yana dubanta q'irjinsa na wani irin bugawa da  matsanancin karfin gaske , a zahiri ake iya  kallon yadda zuciyarsa ke tafasa , jijiyon kasa gabad'aya sun  yi rudu rudu , Kallonta  kawai yake zuciyarsa na  mamakinta , bai bata  expecting zata iya kai hannuta jikinsa ba ,duka  guda nawa kisna take  yarinyar  da loma daya zai yi daita ya gama  da ita  amman  ta Iya karfin halin marin mutun irinsa ?
gabad'aya jikinsa yayi sanyi karfinsa yayi kasa yaji kamar zuciyarsa zata buga wani irin bakinciki ne daskare da zuciyarsa yana jin kamar ya zube kasa saboda sanyi da kafafunsa sukayi  , yan uwan musa kuwa  babu Wanda bai ji dadin marin da kisna  tayi wa Aliyu ba Samir ya sake dauketa da wani marin sannan  ya  shiga dukanta yana kwallo daita  madu ya samu sanda ya  dinga maka mata  tana ihu "zasu kasheni wayyo zasu kasheni  shi kam Aliyu ya  kasa hanasu dukanta   yayi shiru kawai  saboda  zuciyar dake zafi .
zainba ce ta lura da mumy bata numfashi tasa ihu   "mumy bata nufashi fa ku rabu da kisna take suka yo Kan mumy suna rige rige  har Aliyu shi kadai ya dauki mumy ya fito waje  daita sai lokacin hawaye ya zubo masa har akan fuskar mumy  kai tsaye  gurin mota  ya nufa ya badamasi da Samir  suka sa  hannu suka   saka mumy a bayan mota Zainab da afra suka   zagaya suka shiga   Aliyu ya shiga mazaunin direba  cikin zafin nama hawaye na gangaro masa ya juya  motar madu da samir  na rike da hannu kisna dake kuka  suka bar unguwar    ,Aliyu  ya  kalli ya badamasi  ta mirrow ina muka nufa da mumy ?"Muje gida a kofar gida suka iske dady  goye da hannuwansa duka a baya  zuciyarsa na zafi dan  mai gadi ya sheida masa abinda ya faru kamar yadda ya sheidawa Aliyu  ganin ana ƙoƙarin fito da mumy  gabansa yayi mummunar  faduwa  ya saki hannunsa yayi gurin motar yana tambayarsa "me ya faru babu wanda ya yi bashi amsa saboda gabad'aya a rud'e suke suka shiga cikin gida ya badamasi ya nufi bangaren sa cikin sauri domin dauko kayan aikinsa tare da Afra suka dawo ya shiga bawa mumy taimakon gaugauwa cikin haka Samir suka shigo da kisna ai kuwa dady yayi kukan kura yayi kanta ya dinga dukanta "zaki kashe uwarki ko ? "Kina son ta mutu ko ?
"A'a dady ku kyaleni karku kasheni wallahi bazan sake fita ba na tuba ku kyaleni "karya kike kullum haka kike faɗa kai madu dauko min sansar can na karya kafar fita da sauri madu ya dauko dady ya dinga makasa kakafuwanta sanda Afra ta dinga bawa dady hakuri tana kuka Zainab t cikin kuka ta karaso ta dungure mata kai "bakya jin magana kisna kina son kashe mumy daga zubar da shafa kika sa kafa kika fita wallahi dady ko Musa nada laifi laifin kisna yafi yawo tunda ita na waya gareta ba idan bataje gurinsa ba bashi da hanyar da zai nemeta "ai yau sai na balla kafar fita nemansa tun kisna na ihu ana iya jinta har aka zo ba'a jin muryarta yayinda Aliyu ke zaune yana Kallonsu ya kasa dakatar dady gashi kukan da yake yasa ya  badamasi dake dakin mumy domin   ƙoƙarin dawo da numfashinta yace fito  da kyar ya samu ya dawo daidai sai dai bata buɗe idanunta ba ya daura mata drip ya fito tana kallon kisna dake nad'e shi ya ma rasa abinda zai mata dan idan yace zai taba kasheta zai yi bayan dady da Samir sun mata lilis sun tabbatar da bazata iya daga kafafunta ba suka kyaleta "kwanto min igiyar shan madu da sauri ya yaje ya kwanto ya dawo "ku daure mata ita kafin gobe na daba mari wallahi dana rasa salaha akanki gara ki damgwama a kulle shasha dabba damsulbasee ,ban da ke kidahumace ma zaki yi da wannan da bai da mutunci yaron da ko ganina yayi sai dai ta daga min kafada saboda kin bashi damar ta raina mu yana tsaye aka daureta yayinda Aliyu da Afra har da zainab ke kuka "dan Allah karku daureta dady ku bata last chance bazata sake ba inji cewar Afra ko saurararta bai ba ana gama daure kisna aka jefe ta bq aka kulle ranar kwana suka yi akan mumy sai cikin dare ta farka da sunan kisna Aliyu ya rikota yana mata sannu dady ya talla'bo Kanta ya bata ruwa tasha tana cewa "kisna ?
"Ki kwantar da hankali mumy bamu barta tana gida "muje ku kaini na ganta "salaha kinsan ba baza yi miki karya ba tana bq daga yau matsalarmu ta kare  ki kwantar da hankali gobe da yarda Allah mari zan sa mata wasu hawaye masu zafi suka zubo mata Aliyu ya tare "kiyi hakuri mumy ki daina zubar mata da hawaye maseefa ne a gareta kiyi mata addu'a zata daina ta jijina masa kawai zainab ta shigo da plet din abinci Samir ya amsa ,shima ya Aliyu ya amsa a hannusa ya soma ƙoƙarin bawa mumy "bazan iya cin komai ba muradi yau ni aka watsawa kalanzir har ana neman a shana irin wannan zaka dauki d'anka ka bashi takarashe maganar tana kuka har washegari kuma mumy take wanda hakan yasa jinita ya hau ya wuce ka'ida yayinda zuciyarta ta dinga mata ciwo ko mikewa bata iyayi gabad'aya ciwon mumy yasa aka manta da kisna har bayan kwana biyu mumy  dubesu gabad'ayansu harssu zahra da mufeeda da aunty ummi  suna zaune a gabanta banda  kisna ,tace "kun manta  da kisna  ko ?
Sukayi shiru cike da takaici a"kuyi hakuri ku duota karta ,kuyi hakuri nasan zan mutu na barku da aiki kuyi iya yinku ko bayan raina ban yarda ku bar kisna ta auri wannan yaron ba duk suka gyada mata "inshallahu mumy ai idan muka bari sunyi galaba akanki ki kwantar da hankalinki bazamu taba yarda ba inji cewar madu duk hirar da'ake hankalin mumy na gurin kisna lura da hakan da Aliyu yayi ya tashi ya shiga Kitchen ya zuba abinci a plet ya dauko goron ruwan ya nufi   dakin tana nan a daure,duk  kafafuwanta sun kunbura haka fuskantar duk sun kun bura ya durkusa a gabanta ya ajiye plet din abinci ya  soma ƙoƙarin kwance ta, ta zuba masa ido tana kallonsa har ya gama batace masa kalla ba haka shima bai ce mata ba ya kai spoon din abinci bakinta saboda yasan bazata iya daga hannunta ba sai dai juyin duniya taki ci ta soma motsi da bakinta yayi kokarin fuskantarta domin jin abinda zata ce a hankali ya fahimci abinda take fada "me yasa  ka kwanceni gara ku barni na mutu nafi son mutuwa da rayuwar duniya ".
Ya kura mata ido yana kallon karamin bakinta "lallai wannan yarinyar tana da mugun taurin kai ga kafuwar zuciya kamar ta arna tunda ta fadi abinda ke ranta ta kife kanta
Hannunshi daya ya kai kan suman kanta dake zube har gadon bayanta yana shafawa a hankali yana tunanin kalar rarrashin da zai mata wanda zai natsar da zuciya , wani irin tausayinta yake ji yana ratsa jinin jikinsa , zuciyarsa ke kwabarsa akanta sai dai har lokacin matsayinta na nan na diyar mumynsa shi yasan da wata ce tayi masa abinda tayi masa da ya kulle daita har duniya ta nade amman ita din dabam ce hannunsa ya cigaba da yawo dashi akanta kafin daga baya ya fara magana cikin sanyi murya "ya kamata zuwa yanzu kiyi tunani mai kyau duk dai har yanzu akwai kuruciya acikin lamarinki ,wannan yaron mai kama da tana sam bai dace da mace irinki ba me yasa bazai canza tunaninki ba ya dawo irin namu dan ...."A fusace ta katseshi tana buge masa hannunsa dake kanta sannan ta zuba masa idanunta muryata a shake tace " tunanina ba irin naku bane kuma bazai taɓa dawowa irin naku ba saboda haka har abada bazan taba daina son Musa ba " ya tsareta da kyawawan idanunsa da suka dawo jajayen tsabar damuwa "ka fita a dakina bana kaunar ganinka saboda na tsaneka na tsaneka i really hate you tayi maganar tana kuka " ya watsa mata wani kallo wanda ya tabbatar masa da wasu abubuwa tsakaninta da Allah ta tsaneshi kamar yadda ta fada tsana kuma bata wasa amman shi bai taba jin zai tsaneta ba ko dan darajan mumy ita din uwa ce ta dabam a zuciyarsa komai yana yi ne darajan mumy da sunan Hajiya kayi if not ko kallon arziki bai kamata yayi mata ba bare tausayawa, a hankali ya mike ya bar daki zuciyarsa cike da wasi wasi tunda ya fita ta kife kanta take kuka bata d'ago ba har bacci yayi awon gaba daita...


Mumy da Aliyu  sai da suka kai  ruwa rana da dady aka sakawa kisna mari kuka suke suna  rokonsa karya sa mata mari maganar har gurin hajiya Aysha sai data tako da kanta sannan dady ya hakura sai dai yace bata sake fita babu zuwa boko babu zuwa islamiyya ta zauna anan muddin rai Hajiya Aysha tace "hukuncinka yayi daidai jairar yarinyar so take taga bayanku da ikon Allah sai Allah ya kunyatata bari  naje  na ga mara jin magana  suka tashi tare da aunty  Afra  dady ya basu key tana zaune ta d'aura  kanta akan gwiwowinta kamar koda yaushe ta bushe ta rami tayi wani irin baki tamkar ba kisna ba saboda rashin cin abinci da kulawa dan yadda aka kawo mata abinci haka ake zuwa a tadashi ,aunty  Afra na  d'aura idanunta akanta ta k'arasa da sauri ta durkusa a gabanta ta  rungumeta "baby  nah ......"
Kisna  ta runtse idanunta gam  dan bata qaunar ganin kowa daga cikin ahlinta hajiya Aysha tace" sannu shugaban marasa jin magana Allah dai yasa kiji magana yarinya kamar mai kunne kashi ,ina ke ina jikan oduduwa masu fitsari a tsaye ? " duk da cikin yoroba muka taso amman me zamuyi  dasu  wallahi kikayi kuskuren da kika gurbata min zuri'a bazan taba yafe miki ba ,ke yanzu rayuwar yayyenki da kika taso kika gani a gidan nan bai isheki misali ba ? "gabadayansu babu wanda yayi saurayin kansa sai wanda aka zaba musu amman ke dan rashin jin kece sai dan  gurguwa  aunty afra ta d'ago tana duban hajiya Aysha fuskarta da alamar tambaya "daman mahaifiyar yaron gurguwa ce ? "Ke da kukaje gidan baki ga alama ba "Ai bata da maraba da gurguwa baki ga kafafunta ba hagu a dama ba ai sai da aka kwantata min ita sosai sannan na ganeta na san kakar yaron wacce ta haifi ubansa gabad'aya daginsu marasa mutunci ne acikin yoroba , Allah dai ya shiiryeki sakina yasa ki gane daga faɗa Hajiya ta dawo yi  mata addu'a akan Allah yaye mata abinda ke damunta anan  ta tafi ta bar aunty  Afra  rungume da kisna dake kuka a tun sanda Hajiya ta soma zaginta ..."

Aunty afra ta kira sunanta cikin sanyi murya  "kisna ina son tambayarki wani abu kuma ina bukatar ki faɗa min gaskiya  kun taɓa  zuwa wani guri  da musa kunyi  imole ne ma'ana (cin maganin soyayya ) ?Ta girgiza mata kai alamun a'a " ki  faɗa min gskiya idan kun taba zuwa sai an san yadda za'a yi a karya  kin san  dai babu wanda zan fadawa wannan maganar   "Allah aunty  Afra bamu taɓa yi ba mun dai taba zuwa gurin wani malami amman shi cewa yayi zamuyi aure amman sai mumy ta mutu "ya rabbi yanzu ke zaki auri wanda sai mahaifiyarki ta mutu "? Kisna tayi shiru taki cewa komai ba "ki daina wannan tunanin duk abinda zaki mallaka muddin zaki rasa wani naki ba mahafiyarki ba na banza kema har da kuruciya bancin haka ko fada wani yace kiyi baza kiyi ba ni dai ki faɗa min gaskiya bayan bayanin malamin bai baku wani abu kunci ba "? "babu idan mun taba yi kinsan zan faɗa miki  ",to kun taba  shan jinin juna  ? Kisna tayi shiru tana tunani  dan tasan sun taɓa sha  "kun taba sha ko ? Kisna ta gyada mata alamun" eh "subuhanallahi  shiyasa kuka kasa rabuwa da juna wallahi " dan Allah  aunty afra ki taimaka min na auri musa sannan ki taimaka kije min gidansu ki duba min shi wannan azalumin  yayi masa dukan mutuwa ko  ina ruwansa da rayuwata ?

"Abinda Aliyu yayi masa daidai ne baki ga har kalazir musa ya watsawa mumy ba ke yanzu zaki  iya auran  mutumin da ya iya watsawa mahaifiyarki kalanzir har yana cewa a bashi a shana suka jiyo Muryar mufeeda  a bayansu ."Wallahi ban taba jin na tsani wani halitta a rayuwata ba kamar yadda na tsani ke da wannan yaron ,ke ko mu da ba mumy ce ta kawo mu duniya ba bazamu iya ganinta cikin damuwa ba bare ke wallahi ki guji fushin mahaifiyarki idan nan gaba duniya ta juya miki baya Allah yasa muna raye mu karar da abinda kika shuka da karanshin shekarunki yar banza yarinya kawai mara imani ta k'arasa maganar tana barin dakin ...

Kisna ta rushe da kuka "kowa ya tsaneni a gidan nan ,me yasa bazu fahimceni ba?  "Karki  damu ki kwantar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login