Showing 357001 words to 360000 words out of 495987 words
Chapter 120 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
idan rayuwa da kisna alkhairi ne a rayuwarka da addininka Allah ya karkato da hankalinta gareka idan ba alkhairi bane Allah ya rabuku cikin sauki ya haɗaka da rabonka mafi alkhairi"ameen mumy Allah ya qara miki lafiya "ameen ta amsa cike da farinciki "bari naje na sameta mu wuce kawai jiki a sanyaye mumy tace "to".
Kai tsaye dakin daya san take ya nufa tana kwance a lokacin bacci ya dade da ɗaukarta ya zauna a gefen gadon yana kallonta da kyakkyawar fuskarta ta rame sosai sai dai kyanta na nan bai je ko'ina ba yaji kamar ya kwanta a gefenta ya rungumeta ajikkinsa amman ya kasa dan babu wannan damar a tsakaninsu yanzu wannan damar ta wuceta har abada a hankali ya fara tashinta "kisna !kisna !! ta motsa batare data bude idanunta ba ta sauke numfashi tare da daura hannunta daya akan cinyarsa ta cigaba da baccinta "ke ki tashi mana yayi magana yana dan marin kumatunta firgigib ta farka cikin mayen bacci tana mutsuka idanunta kafin daga baya ta bude su fesa akansa "yaushe rabon data sanyashi a cikin kwayar idanuta?"ki tashi muje gida "nayi me ai na dauka na dawo nan kenan zaka aiko min da takardata ..."
Mmm Sudais
[7/19, 5:33 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 54
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, voil lace Swiss lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
"Sakina ! Sakina !!! dady ya shiga kiran sunanta a mutukar fusace, ta fito da sauri qirjinta na wani irin dokawar da bata jin irinsa ba , ta tsaya can nesa dashi ya cilla mata takardar sakinta " burinki ya cika yau muradi ya sakeki bisa umarnina kamar yadda na roki alfarma agurinsa a farko ya aureki bayan wulakacin da yan'uwa da abokan arziki suka min na kin amsar auren " . gabanta ne ya yanke yayi wani irin faduwa gabadaya ta rude sai zufa ya shiga tsatsafo mata , gashi dai abinda ta dauki lokaci tana nema kenan amman sai da taji wani qulli ya tsaya mata akan kahon zuciya ,qirjinta ya cigaba da bugawa da wani irin karfi kamar ana buga mata guduma , jiki a sabule ta durkusa ta ɗauki takarda tana dubawa jikinta na kyarma ,shi kuwa dady zuba mata ido yayi kawai yana jin wani zallar ɓacin rai na ratsa shi a hankali hawaye ya fara cika Idanunshi bai kai ga zubar dashi ba ya fara magana cikin ɓacin rai "na gode sakina da sakayyar da kika min "kin manta ni ne ubanki ,na ɗauki dawainiyarki tun daga haihuwarki har zuwa sanda na aurar dake ga mutumin da nake ganin zaki yi farinciki ko bayan raina , alfarma daya na nema agurinki ki zauna da muradi lafiya ki kwantar masa da hankali kiyi masa biyayya amman kika nuna bamu isa ba bamu daraja a rayuwarki ya tsakaninta yana sauke numfashi sannan ya cigaba " yanzu na sake tabbatar da cewar bakya qaunarmu nida mahaifiyarki duk yadda muke son d'auraki akan hanyar tsira kince karyamu tasha karya bamu isa kibi umarninmu ba 'bata bakinmu kawai muke to mun gode mun gode amman kisan wani abu daga yau babu ni babu ke har abada na cireki a cikin ya'yanna ki nemi wani uban bani ba ,Kuma karki sake naga wadan nan kafafun naki cikin gidan ki san inda zaki dan bazan sake zama dake ba yana gama fadar haka ya juya fuuuuuuu sauran kadan ya tuntsira ..."
ta rushe da wani irin gigitaccen kuka tamkar wacce aka zane ta cigaba da duba takardar sakinta adadin data karanta bazai misaltu ba , yau dai ta tabbata sakakka abinda tafi komai bukata fiyye da komai sai dai ta rasa me yasa abun ya tsaya mata a kahon zuciya kuma ya d'aga mata hankali uwa uba hukuncin mahaifinta akanta shine abinda yafi dagula mata lissafi a halin yanzu "na cireki acikin ya'yana ki nemi wani uban kuma kar naga wadan nan kafafun naki a gida lallai wannan hukunci ya tabbatar mata data fada motar wahala batasan mintunan data ɗauka agurin rike da takardar saki tana juyawa tana tunani maganar mahaifinta wata irin zabura tayi a matukar rude tamkar mahaukaciya ta nufi d'akinta ta fada kan gado ranta duk babu dadi ta damke takardar sakin gam a hannunta tana kuka tana furta kalmar " na shiga uku dady karka min haka karka cireni acikin ya'yanka ina sonka dady wallahi nayi ƙoƙarin na juya zuciyata ta amshi muradi amman na kasa kuka take sosai har da shesheka .."
tunda dady ya shiga mota ya zauna a bayan mota direbansa yaja zuciyarsa ke tafasa suna isa gida bai jira direba ya fito ya bude masa ba ya fito ya shiga cikin gidan mumy dake tare da sadiq suna hira tana ganinsa ta mike tsaye cikin tashin hankali dan bata taɓa ganinsa cikin yanayin daya shigo ba, ya fada dakin ya zube akan gado ya rushe da kuka ta rufa masa baya tana shiga dakin ta gansa yana kuka jikinsa na bari nan ta shiga tambayarsa "lafiya meke faruwa ?" Salaha sakina ta cutar da kanta da rayuwarta ta cutar damu da duk wasu masoyanmu duk tarbiyar da mukayi dakon yi da tattalinta ya tashi a banza sakina ta rusa komai ta bata komai yau dai nabawa muradi ya sawwake mata aurensa dake kanta karta kashe dan mutane azo ana kuka damu "jikin mumy na rawa tace "yan .. yanzu ya saketa kenan ? ta fada a kidime " Eh "iyakar abinda mumy taji kenan ta tafi ta kifa cike da daukewar numfashi ya shiga jijigata cikin. kururuwa "salaha salaha karki min haka "wayyyohhly Allah kisna kin kashe uwarki na shiga uku kin kashe min mata , ganin kukan bazai fishshe ba sai kawai ya kwaso da gudu ya fito falo yana neman layin ya badamasi cikin tsananin tashin hankali yake fada masa abinda ya faru cikin sauri ya karaso cikin gidan dan daman shigowarsa kenan daga aiki shine ya sukunci mumy gabadaya ya fito masu aiki sadiq da dady suka biyo bayansa ya sanyata acikin mota yana kuka dady na kuka ya shiga gidan baya ya rungume mumy ya badamasi soma juya kan mota suka fice ."
Suna isa asibitin ya badamasi aka sanya mumy a gadon daukar marasa lafiya aka wuce daita dan a lokacin ta farfaɗo sai dai wata irin jijiga take kamar mai iskokai badamasi kamar ya zare ya kasa duba mahaifiyarsa ya tsays yana kuka a tunaninsa mutuwa zatayi sai likitoci abokan aikinsa ne suka rufa akan mumy suka shiga aikin ceton rai , cikin kankanin lokaci asibiti ya cika makil da ya'yan mumy Samir ne yazo daga karshe yana zuwa ya isa gaban aunty ummi dake kuka ya riko hannuwanta "lafiya aunty meke faruwa ne ? cikin kuka take ce masa " babu lafiya Samir al'amura sun rikice mumy dai tana cikin wani hali a dalilin kisna batasan wanda ke kanta ba". ta karasa maganar tana rushewa da wani kuka yadda aunty ummi ta sheidawa samir haka ta kira number muradi Wanda ta samu da kyar ya ɗauka , ta koro masa halin da ake ciki cike da tashin hankali yace "gani nan zuwa shap shap ya wuntsulo daga gado ya shiga bayi yayi wankan janaba ya sauya kaya ya shiga dakin kisna dake kwance har lokacin rike da takarda a hannunta "ki tashi muje mumy babu lafiya wata irin zabura tayi tana masa wani irin kallo shima sai lokacin idanunsa ya kai ga hannunta bai ce komai ba ya sauko ta nufi hanyar waje tana sake damke takardata suna isa taga halin da mumy take ciki zubewa a kasa tayi tana kuka cikin wani irin tashin hankali wanda bata taɓa riskar kanta ba aciki ba, a yanzu halin da take ciki bai dameta ba illa lafiyar mahaifiyarta dake tsakanin mutuwa da rayuwa shima muradi a rikice yake Idanunshi tap da kwalla ya durkusa a gaban kisna "Kinga abinda kika jawo ko ?" ta d'ago idanunta da suka canza kala tana masa wani irin kallo na tausayin kanta , muryarsa a dakushe yake cewa "hakika kin cutar min da uwa adalilin mugun halinki kalli kiga yadda zalincinki da rashin tausayi da rashin imaninki ya janyo zamu rasa mumy" . yasa hannu yana share hawayen da shine karo na farko data ga yana kuka akan idanunta wasu hawayen na sake zubo masa " .
"Ban taba jin tsanar wani mahaluki ba irinki sakina ban taba jin kinyi min abinda nake jin bazan yafe miki ba sai yau bazamu iya karasa rayuwa dake ba kamar yadda dady ya fada dan bamu da abinda zamuyi dake". inji cewar ya badamasi wani sabon hawaye ya sake gangaro masa "kin cucemu wallahi kin cucemu Allah ya saka mana abinda kika mana ki tashi ki bar asibitin nan bama son ganinki har duniya ta nade babu mu babu ke ki tashi ki bar nan ya karasa maganar yana janta bai tsaya a ko'ina daita ba sai a haraban asibiti ki bar rayuwarmu ". kisna ta tsaya bisa kafafunta tana wani irin ajiyar zuciya da addu'ar Allah ya tashi kafadan mahaifiyarta ta kai hannu ta share hawayenta "tabbas ta barwar kanta tabon da bazai taba gogewa ba idan ta rasa mahaifiyarta bata san tsayin rayuwar da zatayi cikin kunci da bala'in abinda ta haifarwa ahlinta ."
bayan ya badamasi tabi a hankali a daidai lokacin da wani likita ya fito daga dakin da mumy ke ciki muradi ya biyosa yana hawaye sai faman cewa yake "likita ya mahaifiyata ?
"wani hali take ciki abinda yake iya furtawa kenan cikin ruwan murya da jiki , gabadaya likitan ya daidaita natsuwarsa a lokacin da Samir ya karaso a rude Shima yana cewa "likita ta mutu ne ?ya girgiza musu kai alamun a'a "gaskiya tana raye muna kan iyakacin kokarinmu akan ta dawo daidai ku dai yi mata addu'a ya karasa maganar yana shiga office dinsa ya badamasi ya jingina bayansa da bango gurin dan rasa abinda zai ce wannan bayanin ya dan kwantar da hankalin kisna ta shigo cikinsu tamkar mara laka tana zazzare idanu inda aunty ummi ke cewa "mufeeda Allah ka bamu ya'ya masu albarka wadan da zasu ji maganarmu Allah ka rabamu da haihuwar ya'ya irin kisna "tana kuka tana magana kafin a hankali ta dinga ja da baya dan matsawa daga inda kisna ke tsaye tana zubar da hawaye gabadayansu suka dare suka barta tsaye muradi ne kaɗai ya cigaba da tsayuwa yana kallon kasa zuciyarsa na wani irin zafi gbdy ya rasa natsuwarsa tana nan tsaye Samir ya karaso ya kai mata mari ",tsayuwar me kike yi anan ko bakiji abinda ya badamasi yace ba Bama bukatarki bama son ganinki ki kama gabanki cikin kuka tace "nima mahaifiyata ce fa kuma ina damar da zan tsaya tare daita ". hannuta ya rike gam cikin nashi ya shiga tafiya daita tana kuka bai tsaya akoina ba sai a bakin titi ya tsaya yana dubanta wallahi kika sake shigowa asibitin nan zan mugun baki mamaki kisna bata d'ago ta kalleshi ba illa ta fashe da kuka shi kuma ya juya ya koma cikin asibiti a hankali ta dinga tafiya tana kuka "yanzu akan muradi suka juya mata baya ?" tunda take a rayuwarta ba'a taba mata irin wulakacin da ahlinta suka mata ba ,sun wulakanta ta sun tozartata akan bare amman ta rantse da Allah zata bar rayuwarsu kamar yadda suka bukata zatayi nisa da rayuwarsu ta cigaba rayuwarta tafiya mai nesa tayi har ta iso unguwarsu musa anan ma wani sabon tashin hankali ta iske domin kuwa abdulfatai abokinsa ne yake mata bayani musa na jail tun wata uku da suka wuce batare da yasan laifin daya aikata ba "
durkyshewa tayi agurin tana rusa wani sabon kuka "na shiga uku ni sakina meke shirin faruwa da rayuwata ?" Shikenan bani da wanda zai taimaka min "fatai dake tsaye a gabanta ya zuba mata ido kawai yayinda wata irin zufa ke tsatsafo mata a gbdy ilahirin jikinta a hankali ta juya tana tunani kanta ya daure tunanin inda zata take babu wacce tazo mata sai afra dan haka soma tunanin nemanta sai dai tunawa da tayi babu waya a hannunta yasa ta juya da sauri ta koma gurin fatai da kyar ta saita kanta tace "dan Allah ara min wayarka zanyi kira dashi " nan da nan ya bata da yake ta haddace number afra sai ta hau kira tana jin ta dauka ta sakar mata kuka "aunty afra na shiga uku afra na jin kukanta ta saki murmushin jin dadi dan tasan dole ta nemeta dan tun awa biyu da suka gabata suka ji batun mutuwar aurenta da halin da mumy take ciki har ma da hukunci dady, dad dinta ma bai jima da fita zuwa asibitin ba sai dai cike da makirci afra tace "kisna lafiya ?"me yake faruwa ?"cikin kuka take cewa ba lafiya ba aunty afra komai ya kwabe min muradi ya bani takarda sakina sai dai adalin haka mumy na kan gadon asibiti gashi dady ya sallamani in fact ya cireni acikin ya'yansa ga musa a jail ta karasa maganar tana rushewa da kuka "yanzu ya za'a yi kenan ? "wallahi ban sani ba ,ban san inda zani ba "Ya kamata kiyi tunanin inda zaki Kinga. tunda dady ne yace ya koreki duk wanda ya amsheki a cikin dangi zai iya haifar da gagarumin matsala ki samu inda kika laba ko acikin family musa ne kafin abubuwa suyi sauki". "Bari nazo gidan Hajiya mu hadu mu zauna tare tunda bata koreki ba ai bazata koreni ba "kiyiwa Allah kiyi hakurin kin san daman can ni mai laifi ce idan kuma zaki zo na tattara nasan inda dare yayi min "jiki a sanyaye kisna ta zame wayar a kunneta ta mikawa fatai ta soma tafiya ."
bayan kisna ta kashe wayar aunty afra tayi wani irin juyi acikin dakin da granny ta bata tana cewa "kadan mumy ta gani ba dai ta iya danne laifin ƴaƴanta ba ta hangi nasu tare muka aikata laifi da kisna amman dan zalinci sai tayi murna da sakin da badamasi yayi min yau kema ga naki sakamakon nan an saki kisna kuma muddin ina raye kisna ta bar rayuwar Aliyu kenan yadda banyi rayuwa dashi ba itama bazata koma garesa ba da sannu zan cigaba da dauraki akan hanyar da bazata bulle miki ba bazaki fargaba har sai lokaci ya kure miki ".muradi kuwa tunda Samir ya fitar da kisna hankalinsa ke tashe yayi tunani iri iri akan inda zata bai hango ba kawai yayi tunanin ya kira habib da hanzari ya kira shi a waya yace" maza ya taimaka ya taho ta gurin asibitin ya badamasi ko zai hadu da kisna ka ɗauketa kaje ka kama mata hotel ko nawane zan biya "friend lafiya kuwa meke faruwa ?" muradi ya runtse idanuwansa ya bude muryarsa dake a dakushe ya shiga yiwa Habib bayanin duk abinda ke faruwa har da kwalla, nan Habib ya haɗe rai tamkar yana gaban muradi yace"yanzu akan wannan mara mutunci yarinyar ka shiga damuwa har kake kokarin taimakonta ? Muradi yace darajan iyayenta ne " .
"to gaskiya ni bazan wani iya taimakawa ba Allah ya bawa mumy lafiya sai nazo ya katse wayarsa , muradi ya sauke naunauyen ajiyar zuciya yana furta "ya Allah ya kira jahid shi kam babu yadda zai yi yace "to Shikenan Allah yasa na ganta "na gode jahid "babu komai muradi yiwa kaine nan da nan jahid ya shiga motarsa ya biyo hanya sai dai babu inda bai duba ba bai ga kisna ba ya kira muradi nan fa hankalinsa ya qara tashi ya shiga tunanin ina ta nufa ya dai nasan musa baya nan to ina zata ?"Zariya ya shiga yi zuciyarsa na wani irin zafi shi kansa zazzafan zazzaɓi yake ji amman ina bazai iya kwanciya ba har sai yaga makomar mumy cikin ikon Allah awa uku da shigar da mumy aka turota a gadon marasa lafiya tana baccin da aka
nemammta dan hutu gbdy suka rufa mata a baya cikin farinciki saboda ganin tana numfashi aka shigar da mumy daki na musamman aka daura mata ruwa a jijiyar hannunta gbdy suka zagayeta suna mata addu'ar samun sauki ".
Kusa awa hudu kisna na tafiyar kafa batasan inda zata dosa ba a cikin gidajen yan'uwa kawai ta yanke shawarar komawa gidan muradi shi zai fi mata sauki kafin ta samu gurin ra'bawa ta kwankwasa kofar karamin get mai gadi ya leko ta karamin huji ganin itace yayi saurin bude mata ta shiga jikinta a sabule kai tsaye dakinta ta nufa ta kwanta ta rasa yadda zatayi ,ta rasa abinda ke mata dadi komai na duniya ya tsaya mata me ya kamata tayi ?" Zuciyata ki fada min abinda ya kamata nayi ....?" Har dare ya fara yi tana kwance tana tunani mafuta tana son dole kafin wayewar gari ta samowa kanta mafutar abun yi domin cigaba da sabuwar rayuwarta sai dai har asuba bata runtsa ba haka zalika bata samawar kanta mafuta ba .."Karfe bakwai daidai na safiyar ranar muradi ya shigo gidan direct d'akinsa ya shiga sai dai ya tsaya yana kallon dakin tun daga inda sa'insarsu ta jiya ta fara har zuwa sanda ya makata akan gadonsa ya kai idanunsa kan gadon nan take komai ya shiga