Showing 351001 words to 354000 words out of 495987 words

Chapter 118 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

daban dabanne akwai Wanda ke matse mace kuma yake saukar da ruwan ni'ima sannan akwai na mallaka , idan ana bukata a tuntubi wannan number
234 815 945 0159..

Mmm Sudais[7/19, 5:33 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Page 52

~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, voil lace Swiss lace   duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096.


....."Take habib yabi umarninsa ya shiga neman layin samir kira biyu ya É—auka a lokacin yana asibiti tare da zee "ya'akayi habib ? "kazo yanzu gidan muradi akwai matsala mai girma dan .. " ai bai tsaya gama jin sauran bayanin ba ya katse wayar , bai tsaya amsar result din pregnant test din da'aka wa zee ba ya riko tsintsiyar hannunta sai inda yayi parking motarsa ya bude mata tashiga shima ya zagaya ya shiga ya fige motar da matsanancin gudu , zee ta waigo inda yake cike da fargaba tace "lafiya kuwa me ya faru ne naga duk yanayinka ya canza ?"I don't know habib ne ya kirani wai akwai matsala a gidan muradi " shiru zee tayi tana addu'ar Allah yasa ba wani matsalar bace ta taso tsakanin kisna da muradi ..."

Habib na gama wayar ya kalli muradi wanda idanushi ke runtse sai dai har lokacin baya numfashi ya dawo tamkar matacce cikin zuciyar muradi kuwa sake sake yake ya so ya mutu ya huta kafin zuwan wannan bak'ar ranar mai tattare da tashin hankali "me yayiwa kisna ta tsaneshi har haka ?"me ya'yansa suka mata ta kashe su tun basu zo duniya ba "? Habib ya dafa shi kana yace "kayi hakuri ka kwantar da hankalinka inshallahu muna tare da kai duk runtsi muddin muna raye bazamu bari ka wulakanta ba ,"ko su dady basu É—auki mataki akan wannan matsalar ba wallahi mu zamu dauka dan bazamu yarda muna ji muna gani mu rasaka ba".
"sannu ubansa " kisna ta fada tana yatsina fuska bama wannan ba ,daka kira ya samir a waya me yasa ba kace idan yazo ya kasheni ba? Habib ya mike a fusace ya daga hannu zai sauke mata mari komai ya tuna sai kuma ya sauke hannunsa yana huci ya dungule hannunsa ya naushi iska sannan ya dinga kai kawo acikin falon" bai yi mamakin halaiyenta ba dan ba tun yau yasan kisna ba hatsabibiyar yarinya ce mara jin magana , ta kallesu daya bayan daya a wulakance sannan ta cigaba "dama kun tattara kun kama gabanku dan kun wani zo kun tare a gidan mutane akan abinda bai shafeku ba ". naunayen ajiyar zuciya jahid ya sauke dan lamarinta gabadaya tsoro yake bashi gaskiya shi da bai da hakurin nan ba zai iya zaman kwana É—aya daita ba , tuni ya farfasa mata baki ya hadata da takarda sakinta ".


shigowarsu samir yayi daidai da lokacin da kisna ta gama rashin mutunci ta shige É—akinta cikin matsanancin tashin hankali da bugawar zuciya samir ya k'araso kusa da muradi ya dan duka a gabansa yana girgiza yana shafa qirjinsa ganin baya breth , fuskarshi cike da sarewa Samir ya kalli Habib da jahid yace "ya naganshi haka kamar baya numfashi ? "me ya sameshi habib ? yayi musu tambaya a jere cikin tsananin tashin hankali habib da jahid suka shiga koro masa bayani zufa ne ya shiga tsatsafowa samir ,cikin matsanancin tashin hankali ya kai Idanunshi inda yaran suke wani irin kuka ya barke dashi yana fadi "sai kinga karshenki kisna sai kin girba abinda kika shuka wannan karon ni ne da kaina zan miki hukunci daidai da abinda kika aikata mana kai tsaye dakinta ya nufa yana sunce belt din Jikinsa hawaye na zubo masa daga idanu , babu wanda yayi kokarin hanashi har sanda ya banka d'akin a lokacin da take kokarin zama a bakin gado aiko yana gama shiga yayi kanta gadan gadan tana ganinsa ta kwalla qara mai karfi wanda yasa zuciyar muradi motsawa ya sake runtse idanuwansa gam , kokarin magana kisna take sai dai kafin tace wani abu samir ya shiga lafta mata belt ta ko'ina wani irin ihu ta saki da iyakacin karfinta tana neman hanyar gudu ya fixgota ya dinga lafta mata "ban taba sanin baki da imani ba sai yau har ki iya daukan halakin rayuka har uku kisna ?"Cikin yanayi na tashin hankali ya cigaba da dukanta yana furta me muradi ya tsare miki ?"wa ya kashe miki shi da ya'yansa?" me wadan nan bayin Allah da basu ba basu gani ba suka miki ?"me yasa baki da imani wallahi ban taba jin na tsaneki ba irin yau na tsanaki kisna! na tsanake !! yana magana hawaye na zubo masa "tukunna ma uban wa ya kaiki inda ake cire ciki ? " babu kowa ta fada cikin murya kuka tana tsusa inda belt ke sauka ajikinta "babu kowa fa kika ce ? ya maimaita yana cigaba da dukanta " na rantse da girman Allah baki fada min wanda ya kaiki ba sai na kashe yau kamar yadda kika kashe min yaran yana magana yana lafta mata belt ."..

dukanta kawai yake yana kwallo daita a dakin har sai daya ga bata motsi sannan ya barta ya ɗauketa ya saba a kafad'ansa ya fito daita yayi hanyar waje inda motar take dan bai shigo daita cikin haraban gidan ba ya bude bayan mota ya sakata ya shiga mazaunin direba ya nufi gida daita tun kafin ya karasa gida labarin abinda ta aikata ya samu mumy dasu aunty Ummi Samir kuwa tuki kawai yake yana kuka tamkar karamin yaro idanunsa gaba-daya sun fito waje ko cikakken minti goma Samir bai yi da fita ba su habib suka biyo bayansa har muradi bayan sun kulle ko'ina ."zaune kawai muradi yake a cikin mota hawaye na bin kuncinsa zee dake zaune kusa dashi tana bashi hakuri babu abinda yake tunani sai rayuwar kuncin da sukayi agurin ubansu gashi har yanzu bai fita ba kullum daga wannan sai wannan shi yaya zai da qaddararsa ? "idanushi na runtse amman tunanin mafuta yake akan zamansa da kisna zai cigaba da zama daita ne ko kuwa zai sawwake mata kamar yadda take buƙata .."

Hauka ne kawai mumy batayi ba , a sanda taga gawar yaran tayita surutai tana kuka tana zagin kisna dake kwance a sume kamar wata mahaukaciya sabuwar kamu , fadar irin tashin hankali da suka shiga bata baki ne gabadaya ahlin mumy sun cika a gida har afra cikin tsananin tashin hankali babu abinda suke sai jajanta wa juna yayinda qirjin afra sai faman luguden bugu yake wanda kallo daya zaka mata ka fahimci rashin gaskiyarta a fili , gefe guda kuma su jahid ne ke kara kwantarwa muradi hankali dan har lokacin ya rasa abinda zai ce dan ko ma yace zai yi magana maganar bazata fito ba saboda tashin hankali da yake ciki ya wuce misali numfashi ma da kyar yake janyo yana fitarwa , ruwa mai sanyi Samir ya dibo ya kwarawa kisna dake sume taki motsawa ya shiga girgiza ta "ki tashi ki fada mana uban wa ya kaiki inda ake zubar da ciki ? ya karashe maganar yana sake diban wani ruwa ya watsa mata sai gashi ta sauke numfashi tare da atishawa ,byn second biyu ta bude idanunta a gigice tana kallon mutanen dake zaune fuskarta cike da matsanancin tashin hankali "ubanwa ya kaiki inda aka cire miki ciki ? "Ɗan rashin imani kisna har ya'yan cikinki ma bazaki bari ba ,sai da kika kashesu to na rantse da girman Allah yau baki fada mana wanda ya kaiki inda ake zubar da ciki ba sai na kasheki da hannu "ya karasa maganar yana ƙoƙarin damko makoshinta ganin Samir zai yi kisan kai yasa aunty zee ta rikeshi da hannuwanta duka cikin rawar jiki tace "ka barta abi lamarin a hankali zata fada ai tunda kisna bata karya zata fadi wanda ya kai ta".

"ki fada mata tayi magana tun wuri dan wallahi banga wanda ya isa yasa na daga mata kafa ba "kisna kiyiwa girman Allah ki fada masa wanda ya kaiki kika wulakanta ya'yanki , cikin Muryar kuka tace "zan fada kice masa ya koma can zan fada miki tayi maganar tana ƙoƙarin gudu Samir yasa mata kafa nan ta zube kasa tana wani irin kuka "ina zaki gudu kije munafukar Allah wallahi sai kin gane baki da imani ana cikin haka dady ya shigo a firgice kasancewar madu ya kira shi a waya ya masa bayanin komai da kyar yake daga kafafunsa yana karanto duk addu'ar data zo bakinsa sannan ya samu guri ya zauna dady ya kalli inda yaran suke masu tsananin kama da muradinsa hawaye ya fara zubo masa yana jinjina girman rashin imanin kisna wai yarsa ta cikinsa ce ta mayar da rayuwarta haka ?" wani sabo duka Samir ya rufeta dashi duk ya canza mata kammani sai kalmar zan faɗa take furtawa kuma taki fadan shi kuma yaki daina dukanta "babu abinda ya dace dake sai azaba mai radadi nan ya cigaba da dukanta da iyakacin karfinsa har sai da jahid da habib suka rikeshi " ku barni na kashe wannan yarinyar wallahi rashin imaninta yayi yawa .."Ka barta haka karka yi kisan kai suka fada atare yayinda suke jin zuciyarsu fesa dan sun ji dadin dukan da Samir yayi mata wallahi ko babu komai ya wanke musu zuciya ."

dady bai ce komai ba har lokacin illa ya mike tsaye ya dauki bakar laida da yaran ke ciki ya nufi d'akinsa domin suturtasu ganin haka yasa muradi ya mike da kyar yana layi ya bi bayansa batare daya kalli inda kisna ke tsugunne tana kuka da neman dauki ba , koda ya shiga dakin bai iske dady ba jin motsin ruwa ya fahimci yana cikin bayi dan haka ya karasa bakin kofar bayin ya tsaya dake kofar a bude take yana kallon ciki nan yaga dady yana wanke yaran duk sun lanbabe alamun sun sha wahala Hakan yasa hankakinsa ya sake dagawa qirjinsa ya shiga bugawa da matsanancin karfin gaske , numfashinsa ya soma sama da kasa a hankali ya fara ganin jiri, yayi saurin dafe goshinsa da hannunsa daya , wani duhu ya gilma cikin Idanunshi nan take jiri ya dibeshi sai dim dady yaji alamun faduwar mutun ya bar abinda yake ya fito a daidai lokacin da madu ya shigo dakin yana ganin muradi kwance ya karasa shigowa da sauri nan suka kwshesa sai asibiti ya badamasi da kyar da taimakon likitoci da taimakon ya badamasi aka samu ya dawo haiyacinsa sai dai tunda ya farka bai ce uhm ba bare uhmm sai mutane yake bi da idanu suna zaune su duka a gaban muradi har afra wacce tafi kowa shiga tashin hankali addu'a take Allah yasa kar wahala yasa kisna ta fallasa cewar da saka hannunta dady yace "sannu muradi ya jikin ? " kai kawai muradi ya gyada masa yana sauke numfashi da kyar tamkar mai cutar asma dady ya cigaba da magana yana cewa " wannan tashin hankali yayi yawa wai garin yaya ma har tasa kafa ta fita daga gidan bayan kace ka hana mai gadi barinta fita koina ,muradi bai ce komai ba sai Habib ne yace "ai yau kwanan mai gadi uku a asibiti bai dai fada muku bane , ai maganin bacci ta bawa mai gadi ta kama gabanta a she cikin taje zubarwa sai fa jiya mai gadi ya dawo haiyacinsa babu wanda bai yi salati ba muradi ya tsaida kallonsa kan dady nan take ya fahimci akwai abinda yake so fada dan haka ya matso kusa dashi tare darakwafowa "ya'akayi dana ko akwai abinda kake bukata ?"bana bukatar komai dady ina yaran suke ?"ya tambaye dady yana kukan zuci "na binnesu dan bazan iya zubar dasu ba "ya fada cike da tausayawa masa runtse idanuwansa yayi gam yana cigaba da kukan zuci ."

a daren ranar aka sallami muradi daga asibiti dukkaninsu suna zaune a falo har afra suna jiran kisna ta fada musu wanda ya kaita asibiti zubar da ciki kamar yadda tayiwa aunty ummi alkwari idan sun dawo gida zata fada dan haka yanzu ita suke jira gabadaya zuba mata ido sukayi ta fada musu gaskiya ,mutsu mutsu ta fara yi ita kaÉ—ai zuciyarta na rawa yayinda gaba-daya zuciyar afra ta tsinke ta tsurawa kisna ido tana gargadinta , idanun kisna ya fara cika da ruwan hawaye bata son fada wanda yasata saboda gudun saka rayuwar afra cikin tashin hankali Samir ya mike tsaye nan take jikinta ya kama rawa "wallahi idan bakiyi magana ba sai na miki abinda zaki gwamaci mutuwa da rayuwa hakuri take bashi amman yaki sauraronta gabadaya yanayinsa ya daga mata hankali zuciyarta ta kasa samun natsuwa sai faman rera kuka take kai kace da gaske har cikin zuciyarta tayi nadama ..."


gyaran murya ya badamasi yayi kana yace "duk ku daina wahalar da kanku dan bazata fada muku wanda ya kaita ba amman ni nasan wanda ya kaita " nan take qirjin afra dana kisna ya buga alokacin daya zufa ta shiga karyo musu suka maida idanunsu kanshi suna kallonsa shima su din yake kallo cike da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login