Showing 306001 words to 309000 words out of 495987 words

Chapter 103 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

tsayuwa glass ba kofar ya bude ya fita cikin sauri qirjinsa na bugawa fiyye da qaida ,Allah Allah yake Samir ya fito yaji meke faruwa cikin haka Samir ya fito cikin sauri ya riko hannun muradi ya nufi inda motarsa take "shiga muje gida ana nemanmmu" "lafiya ?" Kai dai muje "
"No ka fada min abinda ya faru ? "kai dai muje gida nace "idan baka fada min ba babu inda zani suna cikin magana kiran mumy ya shigo ya dauka gabansa na tsananta fad'uwa jin muryar mumy na kuka yasa hankalinsa sake tashi bai san sanda ya fada cikin motar ba Samir ya shiga ya tayar suka fice , tunda suka shiga mota babu wanda yayiwa dan'uwansa magana har suka karaso gida ya fito da sauri ya nufi cikin gida batare daya tsaya rufe murfin motar ba , burinsa kawai ya isa gaban mumy yaji meye matsalarta ?"

Ya shiga parlour'n bakinsa dauke sallama a lokacin da aunty ummi dasu zahra da mufeeda suna goge wa mumy hawaye suna bata hakuri suna ganin shi duk suka dare ya karaso ya durkusa a gabanta zuciyarsa na tsinkewa dan zuwa lokaci ko ba'a fada masa abinda ya faru ba jikinsa ya bashi matsalar Kisna ce "menene kuma mumy ?
"kinsan yadda kukanki yake daga min hankali kuwa ? Yayi magana yana goge mata hawaye da hannunsa "duk abun bana kuka bane duk abinda kika ga ya samu bawa nayi imani da sanin Allah Kiyi hakuri mumy komai mai wucewa ne "muradi Kisna na son ganin bayana ta karashe maganar tana kuka tamkar ranta zai fita gaba-daya kana ganinsu zaka fahimci suna cikin tsanani damuwa da tashin hankali mara misaltuwa especially muradi wanda idan ka kalleshi bazaka sake marmarin kallonsa ba saboda yanayin jikinsa yayi sanyi kamar ba Aliyu ba , a hankali ya mike tsaye ya koma kan kujera kusa da mumy ya zauna ya daura kafafunsa akan center table har lokacin an rasa wanda zai fada masa Kisna ta gudu a qalla ya kusan minti talatin zaune cikin tashin hankali yana girgiza kafafunshi batare da yayi magana yana tunani jikinsa sai tsatsafo da zufa yake ,a hankali ya d'ago Idanunshi ya dubi agogon dake daure da tsintsiyar hannunsa yaga takwas da wasu yan mintina sun wuce yaja tsaki a lokacin sako ya shigo wayarsa da kamar bazai duba ba sai kuma ya fito da wayar daga gaban aljihunsa ya duba ga abinda sakon ya kunsa .."

_aliyu haroon dan bazan taba hada sunanka dana mahaifina ba saboda baka cancanci haka ba a matsayinka na wanda ba kowa ba sai banza dan iya chuch mara galihu , ka daina murna da zakewa zaka tare da Kisna a daren farkon ka , wannan daren na musa ne dan yanzu haka muna tare dashi ,bana sonka aliyu kuma har abada bazan soka ba idan kaganni agidanka to wallahi gawata ce ,sannan bazan hanaka fadawa uwarka wannan sakon nawa ba , ka fada mata dan tuni na yafe maka ita_

Naunayen ajiyar zuciya ya sauke a lokacin daya gama karanta sakon ,a hankali ya dinga juya wayar hannunsa yana sake karanta sakon take kansa yayi wani irin mugun sara ya ajiye wayar yasa akan center table tare da cire hullarsa ya ajiye yasa hannuwansa gaba-daya
ya dafe kanshi dashi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa madu dake tsaye a bayansa ya zagayo ya dauki wayar yana karanta sakon bayan ya gama ya mikawa Samir ,shi kuma Samir ya mikawa mumy cike da mamakin sakon Kisna mumy ta rushe da wani sabon kuka "daman na dade da yafeki Kisna a cikin Ya'yana ke ba 'yata bace saboda dan dana haifa bazai taba min haka ba," wallahi ke ba 'yata bace ku sheida na yafe Kisna acikin ya'yana aunty ummi da mufeeda da zahra har ma da afra da zee suka rungumota suna Kuka suna bata hakuri " dady kan dan tsabar bakinciki ya rasa me zai ce.
"ya ma a kayi Kisna ta gudu ta bar gidan nan wallahi duk yadda akayi na tabbatar da hadin bakin wani a cikin gidan da taimakon wani ta samu ta gudu kuma duk wanda yake da saka hannu cikin gudunta alhalin yasan zan shiga tashin hankali na barshi da Allah , Allah shi kawai zai min sakayya akansa ita kuma duk inda taje Allah kasa gurin yayi mata zafi , Allah idan mota ta shiga Allah kasa motar ta kife daita ta mutu a can na hutu da bakincikinta dukkaninsu sukayi kokarin rufewa mumy baki suna bata hakuri amman ina ran mumy yayi kololuwar tashi maganganu kawai take fada marasa daddi akan Kisna ".

"tabbas da sanyawa hannun wani a fitar Kisna to waye shi?" Dady yayiwa kanshi tambayar yana tsaye rungume da hannuwansa a qirji zuciyarsa na tafarfasa tamkar zai fasa qirjinsa ya fito bai taba danasanin haihuwar Kisna ba a rayuwarsa sai a lokacin , kafin kace me har zance gudun Kisna ya bazu acikin kunnen yan'uwa da abokan arziki nasir dake tsaye a haraban gidan shi da jahid wadan da zuwansu kenan a dalilin jin abinda ya faru yace "shi ma muradi dana shi matsalar me ya kai shi amsar auren yarinyar nan ?" ni fa daman nasan za'a rina wallahi bazata zauna ba , idan ma ta zauna bazata taba kwantar masa da hankali ba tunda wancan yaron ya gama kwakuleta taji dadinsa yaushe zata kwantar da hankalinta tayi zaman aure ?"ai nima abinda na dinga hango masa kenan amman ya kasa fahimtata mutun kamar maye idan an yi magana yace bai sonta kawai ya amsa aurenta ne darajan iyayenta inji cewar jahid haka dai sukayita tautaunawa a tsananinsu suna jiran suga fitowarsu ."

a hankali madu ya dauki number da Kisna ta turawa muradi sako ya soma tracking number cikin kankanin lokaci aka nuna masa number a royal hotel dake kusa da express din ladipo jection oshodi road cikin tsananin tashin hankali yace "ya Ali Kisna na royal hotel fa " gabadaya suka tsura masa ido suna nema karin bayanin "yanzu nayi tracking number data turo sako kuma abinda tracking ya nuna min kenan tana royat hotel tsabar rudewa tasa muradi manta ina ne ma royal hotel ,kuma a ina yake ? mumy kuwa wani sabon kuka ta rushe dashi tsawon minti goma muradi yana nazarin inda royal hotel yake can kwakwaluwarsa ta hasko masa bai san zaman me zai cigaba da yi ba dan haka ya zabura ya mike tsaye tare da surar mukullin motar Samir ya fito da sauri tamkar wani iska hakan yasa Samir ya biyo bayansa da sauri yana kiransa , dady ya badamasi mumy ma cikin saurin suka biyo bayansa kai har mufeeda da zahra da afra da zee duk suka fita aguje mumy na ihun kiran sunansa amman ina muradi bai tsaya jin mai zata ce masa ba haka ko ta kansu nasir bai bi ba ya shiga mota ya fige aguje ya bar gidan kasancewar get din gidan a bude yake dan tun safe ake shiga da fita mota suka shishiga suka bi bayansa har su nasir . "

gaba-daya muradi ya nemi duk wani natsuwarsa ya rasa ji yake kamar zuciyarsa zata buga hakan ne ma yasa baya ganin irin gudun da yake akan titi motoci kuwa sai kauce masa suke yayinda wasu ke zaginsa sakamakon mugun gudun da yake, a bangarensa kuwa gani yake tamkar ba gudu yake ba har gara ma ya fito ya tafi a kafa watakila gudun kafa zai fiyye masa akan na mota tsaki kuwa yaja yafi sau babu adadi ,duk ilahirin jikinsa tsuma yake yayinda kwakwaluwarsa ke sake hargitsewa kamar wanda sabon hauka ya kama "matata a hotel kuma karshenta ma tana tare da wannan yaron ya Allah have macy on me "wannan wacce irin mummunar qaddara ce ta afkami ? "Allah wani laifi nayi daka jarabeni da auren Kisna a rayuwata ? sambatu iri iri yake cikin fita hankali a haka har ya karaso bakin get din royal hotel yayi parking yana huci tamkar mayunwanci zaki sai dai ya kasa fitowa daga cikin motar kuma sai lokacin nadama zuwansa tazo masa "me ya kawoni ?"yayi wa kanshi tambayar sannan yaja zazzafan numfashi ya fesar yana gyara zamansa tare dasa tafukan hannunsa ya share hawayen daya biyo gefen Idanunshi bai dade da yin parking ba motocin su mumy dana nasir suka iso gaba-daya duk sukayi parking suka firfito sai dai har lokacin muradi ya kasa fitowa ,
baya yayi da kujera da yake zaune ya kwantar da bayansa tare da runtse idanuwansa yana addu'ar "Allah yasa Kisna bata cikin hotel din dan muddin aka ganta zuciyarsa zata buga " Samir da madu da ya badamasi da dady ne suka yi kokarin shiga cikin hotel din, kai tsaye reciption suka nufa inda suka nemi ganin manager batare da bata lokaci ba suka gansa sai dai yana gama jin bayaninsu yace "bazai yiwu a duba daki daki ba saboda sunyi baki Kano pilas ne da wasu tsirarrun mutane kuma hakan bai dace ba , ya badamasi ya janyo hannun manager suka kebe gefe da zumar zai bashi wani abu muddin ya taimaka musu da kyar ya shawo kanshi ya amince amman yace sai dai suje suzo da police da report din ana suspect din barayi ne , jiki a sanyaye suka fito cikin tashin hankali inda su mumy ke tsaye cirko cirko suna tautauna yadda zasu station bayan kamar minti biyar sako ya shigo wayar mumy ta dauka ta mikawa zahra dan bazata iya duba kowani irin sako ba, zahra na dubawa da sauri ta mikawa aunty ummi take aunty ummi tayi forwoding din sakon zuwa wayarta ta goge sakon a wayar mumy dan ganin sakon zai iya bugar mata da zuciya tayi nesa kadan dasu ta fara sakon tana kukan zuci ."

_Duk abinda kike faɗa a gidan ina nan inaji komai ,kince Ni sakina ba yarki bace naji na yarda ni ba yarki bace zaki ma manta da kin haifi 'ya Kisna a rayuwa kuma kince idan na dawo gida sai kin kasheni bama zan dawo gidan ba bare ku kasheni , gida kam na barshi kenan har abada dan babu gidan da zan dawo bijahidi rasulillahi ni bazan dawo ku kasheni ba kuma addu'ar mutuwar da kima min na mutu akan titi inshallahu mumy bazaki kasheni keda yayanki ba tunda raina ba'a hanunki yake ba sai kwanana ya kare kuma bazan yi mutuwar titi ba duk inda naga damar zuwa nan zani amman ni da gida har abada wallahi ko cewa kikayi na dawo wallahi bazan dawo gida ba dan babu abinda zai dawo dani Amman inshallahu yadda kika ce ni ba yarki bace na yarda! na yarda !! na yarda !!! ta maimaita har sau uku kince zaki manta cewar kin haifi ya kinsa na yarda amman daga nan inda nake duk inda nake so sai naje ko nan da birnin sin ne sai naje naga gari da dai na zauna tare da wannan mara galihun, sai abu na karshe karku bata lokacinku gurin nemana dan baza ku gani ba dan yanzu haka nayi nisa igiyar aurensa kuwa idan yaga dama ya saki idan bai ga dama ya cigaba da rikewa yama cinye idan zai iya ..."_

Aunty ummi na gama karanta sakon a wayarta hawaye ya zubo mata ta tsurawa mumy dake tsaye ido tana kallonta cike da tausayawa gaba-daya ta kasa samun natsuwa hatta zama ta kasa hawaye kawai take gogewa"abun bakinciki ma yadda Kisna tasan komai dake faruwa a gida ta juya ta kalli afra sannan ta kalli mufeeda da zahra sannan ta maida kallonta ga zee cikinsu babu wanda zai kira Kisna ya fada mata halin da ake ciki "to kodai cikin bakinsu ne wani ya fada mata ?"kai babu ta yadda hakan zai faru "ya rabbi kamana tsari da mugayen mutane da abinda mumy ta fada da wanda bata fada ba duk an kwashe an fadawa Kisna "

Dady dake jingine ajikin motar nasir kamar an tsikaresa ya kamo hannun madu ya nufi gurin motarsa dashi "shiga muje "babu mutsu ya shiga ya tayar da mota ya fito daga kan titin royal hotel xuwa kan express sannan yace "ina muka nufa dady ?"gidansu wannan ɗan iskan yaron zamu "madu bai sake cewa komai ba ya taka mota basu zame ko'ina ba sai unguwarsu Musa suna isa dady bai tsaya aika yaro ba ya shiga cikin gidan yana kwarara kiran sunan mai gidan da karfi kamar zai tsaga gidan alhj abdulganiyya ya fito da kyar yana dingisawa da tunanin kowaye wannan daya shigo masa gida babu ko sallama yana fitowa yayi harba da mahaifin Kisna yana huci da zaro masa ido duk bala'in irin na jinin olegele sai daya ji jikinsa yayi sanyi da ganin alhj realwan saboda ya gane fuska sosai dan yawon zuwansu ma ya isa ya kware gurin saninsa sannu da zuwa alhaji ya fada da kyar yana nuna masa dogon banci dake fasaje din gidan ,dady ya daga masa hannunsa cikin daga murya wanda wannan shine karo na farko da sautin muryarsa ya fito haka "ba zama nazo yi ba nazo ne in gargadiku sannan kujawa sheidanin danku kunne tunda shi ɗan iska ne wanda bai samu tarbiyya ba wallahi na kama shi tare da diyata yau wallahi wallahi kaji na rantse shariace zata rabamu dashi alhj abdulganiyya ya firgita sosai yana kallon dady cikin rashin fahimta dan shi a tunaninsa Tuni an gama wannan film din "Wai wani yaro kake magana akai ....?"

Dady yayi saurin katseshi "wani yaro kake dashi dan iska da wuce musa yazo har cikin gidana ya dauke min yarinya sannan yaki bari tarbiyar dana bawa yata ya zauna acikin kunneta kullum yana hure mata kunne yau aka daura mata aure kuma yau aka nema ta aka rasa wallahi bazan daga kafa ba ",na shiga uku ni abdulganiyya gaskiya bai kyauta ba amman kayi hakuri ...".Dady Ya katseshi cikin tashin hankali "ai banzo dan abani hakuri ba nazo ne dan a shiga daki a fito min daita tun da ba da ubansa mukayiwav uwarta ciki ta haifeta ba na rantse da Allah bashi ba har kai ubansa sai ka gwamace baka haifesa ba koda yake da gani gado yayi dan iskan yaro dan akuya dan matsiyata kaji na gaya maka mintuna kadan na bayar a fito min da yarinya ko mu hadu a kotu gobe da safe jagwab alhj abdul ganiyya ya zube akan hanci sororo da idanu taf kwalla tunda yake bai taɓa haduwa da damuwa irin wannan ba tabbas haihuwar Musa ya zame masa maseefa saboda duk shi ne yaja masa cin mutunci , a hankali ya ringa share hawaye sannan ya mike ya shiga ciki ya sanarwa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login