Showing 153001 words to 156000 words out of 495987 words
Chapter 52 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
zan yi ina ruwanka da ka wani hayayyako min kana zaro min ido kamar zaka cinye ni "?
tsaki yaja ya wuceta, directly ya tunkari d'akin mummy Yana k'arasa wa bakin kofar d'akinta yaja ya tsaya yayi sallama ,mumuy dake zaune a bakin gado hannunta rike da waya gama wayarta kenan da Hajiya asabe isuhu gra, ta amsa masa sallamar tare da bashi umarnin shigowa ,muradi ya shigo cikin dakin ransa a 'bace ,cike da matsanancin qaunarsa mumy ta d'ago kai tana kare masa kallo cikin shirin fita buga kwallo yake , ta janyo hannunsa ta rungumeshi a gefen jikjinta cikin murya mai cike da tsantsar qauna tace "lafiya muradina na ganka haka wa ya taɓa min dana in ci mutuncinsa dan bana son ganin wannan fuskar haka cike da damuwa ? " faɗa min meye damuwarka dana "?mumy ta karasa maganar tana zare shi ajikinta ta shafa kanshi cikin shaukin qaunarsa, "faɗa min waye ya 'bata maka rai "babu kowa mumy haka dai nake jin babu dadi a raina".Naunayen ajiyar zuciya ta sauke ta riko hannunsa "duk lokacin daka ji haka ka dinga karanta "allahumma lasa'ala illa maja'altahu sahla wa anta taja'alul huzna Iza shita sahla kaji yarona ".
Ya gyada mata kai alamun yaji sannan yace " nazo na faɗa miki zamu agege studio ne "bakwa gajiya da buga kallo nifa bana son wannan kwallon nafi son Ku Maida hankalinku gurin karatu "karki damu mumy ball bazai hana mu karatu ba nifa ina ganin kwallo zanyi da zarar na gama karatuna na secondary zan nemi club zaro ido mumy tayi sannan tace "Nida babanku burinmu ku karanci kasuwanci saboda nan gaba duk ku zaku maye gurbinsa tunda shi wancan yaki kasuwanci "shinkenan mumy karki ji komai duk abinda kuke so shi zamuyi "a'a babu takura idan kun fi son kwallon ai shinkenan zama ku iya hada biyu din suka jiyo sautin Muryar Alhaji realwan yana shigowa dakin murmushi mummy tayi sannan tace "kana ganin hakan zai yiwu "?"Sosai kuwa "
"To shikenan Allah ya taimaka ya nuna mana lokaci "Ameen alhaji realwan ya fada yana duban muradi idan ka dawo kaje dakina akwai wasu kaya akan gado na fito dashi ka goge min kaji dan albarka "ya gyada kai ya kalli mummy "Sai mun dawo "
"Okay Sai kun dawo dan Allah kubi a hankali Allah ya tsare ".
"Ameen ya amsa ya fita daga dakin yana tafiyar da kyar har ya fito parlour'n inda kunnuwansa ya dinga jiyo masa abinda Afra ke fad'awa kisna yar shekara biyar zuwa shida a duniya "kinga muradin dan tsintuwa ne fa sannan ba danuwanki bane kamar yadda na sha faɗa miki Karki yarda da maganar mummynki data ce yayanki ne, yayyenki sune ya badamasi, Samir da madu aunty ummi amman banda wannan, da idanuna dadyna ya tsintoshi a kan titi sannan da bakinsa ya fadawa granny shi din shege ne bashi da uba ,bashi da bambancin da mai aikin gidan nan ,baki ga irin aikin da yake ba a gidan nan ba kamar bawa "?kisna tayi shiru tana jinta a daidai lokacin da muradi ya karaso tsakiyar a parlour'n yaja ya tsaya yana dubanta ,zuciyarsa tazo iya wuya yana jin kamar ya shakota yayita dukanta har sai ta daina numfashi , gabad'aya kanshi ya kulle, ya rasa me Afra take nufi dashi ,zuciyarsa na aiyana masa ya kira ya badamasi ya fada masa abinda take masa ayita ta kare tunda ya lura shi kawai take dan shakka a gidan yayinda wani bangaren na zuciyarsa ke hanashi kada sanadiyyar hakan da zai yi ya janyo zumuncinsu ya samu matsala , garin neman gyara komai ya kwa'be."
"me ye ka wani tsaya kana kallona dan ina fad'awa yarinya gaskya ,a yadda nake jin tsanarka wallahi zan iya lalata maka rayuwa ta faɗa cikin karfin hali ,yayi shiru yana mamakinta karamar yarinya daita amman idan ta zaro magana sai ta kusan tarwatsa zuciyar mutun "duk abinda zakiyi kiyi amman ina tabbatar miki bazakiyi nasara akan Aliyu ba ,dan Aliyu ya zame miki karfen kafa ,ya za me miki ciwon ido babu yadda zakiyi dashi acikin gidan nan saboda dakikancin irin naki shekararki shabiyar a duniya amman ki zauna kina bata tunanin yarinya yar shekara shida ." ya fadi haka yana karasowa inda suke zaune ,ya kai hannu zai dauki kisna , yaji saukar duka a hannunsa kisna ce ta buge masa hannu tana janye jikinta daga nashi "Murmushin jin dadi Afra tayi sannan ta mike tsaye "dani daita zamu hanaka jin dadi acikin gidan nan ,duk inda kayi acikin gidan nan sai mun hanaka sukuni da kwanciyar hankali , ta soma d'aga kafafunta kisna na rungume a kafad'anta tana kallon Aliyu a kyamace ,jiki a sanyaye ya fice daga parlour'n inda ya iske Samir yana tsayuwar jiran fitowarsa shima sanye yake da kayan kwallo , kallo ɗaya Samir yayi masa ya fahimci akwai damuwa atattre dashi yayi saurin karasowa inda yake ya riko hannunsa yana tambayarsa sai dai kamar kullum amsa daya ya bashi "babu komai ya sa kai ya dumfari get din gida, shima ya biyo bayansa suka fita tare ,har kusan shida da wasu yan mintuna suna filli suna buga kwallo , duk da Aliyu yana ta samu nasara akan abokan karawarsa hakan bai wanke masa zuciyarsa ba, tunani yake tare da kudurta abinda zai yiwa Afra wanda zai sa ta fita hanyarsa tayi rayuwarta yayi nashi , ana tashi kai tsaye gida suka nufo suka yi wanka suka sauya wasu kayan suka nufi masallaci ."
****""
zaune mummy take a cikin katafarin parlour'n Alhaji realwan mai ɗauke launika dabam dabam da kayan alatu ga kujeru da suka zagaye parloun ac mai sanyaya d'akin tv jikin bango plasma ga na'ura ta dabam mai bada sanyi da zafi parlou'n ya hadu sosai dan kusan yafi kowane parlou'n dake cikin gidan tsaruwa duk wani mai rai da zaran ya so cikinsa dole ya yaba tsaruwansa ta mike akan duguwar kujera tana bacci,bacci ya kwasheta ne yayinda da ta kunna talabijin tana kallon tashar mbc action ana wani Film mai dadi da take so dan haka bata san lokacin da barci ya ɗauketa ba afra ta shigo parlou'n tace mummy ta jita Shiru alamar tayi bacci can mummy ta farka tace "lafiya naji kira sama sama "kika ce unguwa zaki na tasheki karfe uku "?
Murya can kasa mummy tace "jiran direba nake yi duba min ko ya dawo "
"Ai ya dawo yayi sallama kina bacci kina ina nace masa kina sitroom "
"Yanzu yana ina ?"Yana kan kujera a waje yana jiran fitowarki "
Ta tashi ta shiga ban daki domin wanke fuskarta ita kuma afra ta fito ta dawo palo mumy ta fito tasa ma fuskarta hoda ta kawo katon hijab d'inta ta saka ta dauki jaka ta rike ta fito daga sitroom zuwa babban parloun gidan ..
Daf da zata karaso tsakiyar parlou'n ta hango muradi hannunsa rike da safa da uniform, ya dungure kan madu dake zaune yana buga game shi kuma Samir yana kwance akan tays rike da waya yana danne danne a facebook "an wanke muku kaya kwashewar ma sai anyi muku ya take kafar Samir daya har sai da Samir ya saki qara ya zuba masa duka ya tsallakeshi ya shiga daki ya buɗe wordrobe ya zuba na madu ya fito daga dakin yana rera wakan naramarly a daidai lokacin da mumy ta karaso filin falon , "kai Samir ka dinga mentain din safarka tunda baka da jimirin wanki , muradi ya Kalli mumy yace "mummy Kinga safana ko datti baya yi wallahi kamar bana sawa ,hatta abokaina a school suna kokawa dani kafin mummy da Samir sun yi magana Afra tayi tsigil tace "ai kan mage ya waye an tashi katon kazami an dawo ........."
Mmn sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 26
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
"Dan Allah malam ina ruwanki ?" dake yake maganarsa da zaki wani tsomawa mutune wannan banzar bakin naki mai mugun wari? "bakin nawa ke wari? " ta fada a hassale tana zabga masa ƙatuwar harara ."au ke da baki sani ba ? " to bari kiji na faɗa miki wallahi kina buɗe bakin sai dummmmmm ....."ko karya ne zahra yayi maganar yana duban zahra dake zaune tsuru tsuru jin abinda Samir ya fada saurin girgiza kai Zahra tayi "ni dai ban sani ba karka sani a cikin maganarku ."Kin san gaskiya malama kawai bakya son faɗa ne dan karta miki bala'inta data saba amman dai gara ki faɗa ko ma samu wannan 'yar rainin hankalin ta shiga taitayinta ta daina shiga abinda babu ruwanta ."
take afra tayi narairai da idanu zatayi kuka dan taji maseefar haushin abinda Samir ya faɗa ya rasa irin zagin da zai mata sai wannan mumy ta sauke naunauyen ajiyar zuciya ta kai hannu ta dafa kafad'an afra dake cika tsana batsewa tace " Samir abar maganar haka karka sake cewa bakinta na wari "itama ki faɗa mata ta daina shiga tsabgar muradi idan ba haka ba zan cigaba da fada mata duk abinda yazo bakina kai har mutane zan fad'awa cewar bakinta na rawa"
"Shikenan zan mata magana zata daina "afra ki daina kinji diyata dan ku zauna lafiya shima muradi tamkar d'anuwanki ne tsaki taja a cikin ranta tare da cewa "Allah kiyaye ya zama dan'uwana "ni na fita amman ba dadewa zanyi ba, ku kular min da yarinyata idan ta dawo daga school a bata abinci ayi mata wanka a shirya ta zuwa islamiyya ,
kai kuma muradi kaje min gidan hajiya asabe ka amso min kudi tana gama fad'ar haka ta soma tafiya gabad'aya suka ce mata sai ta dawo".
Ko bayan fitar mumy Samir gaba yasa afra da sharri iri iri har "cewa yayi tana da warin kashi an gaya miki tsanar muradi shine abu mafi sauki a zuciyarki sam bazan yarda da haka ba kina masa zan dauki mataki tunda shi bazai iya ramawa ba ya fi tsawon minti biyar yana zaginta "tsanarsa tsanace da bazan taɓa dainawa ba araina i hated him so much musamman yanzu tsakanina dashi zallar kiyayya ce "akan wani dalili zaki tsaneshi ?"
"Me yayi miki ki faɗa min idan ya taba miki wani abu ne sai na sashi ya rokeki ki yafe masa? "Babu abinda yayi kawai dai bana son shi ...."Kar Allah yasa ki so shi zo ki kashe shi tunda bakya son ganinsa wawiya kawai samir ya dinga zuba mata ruwan bala'in babu shiri ta mike ta bar gurin "yar rainin wayyo kawai gara ki kama kanki tun wuri wallahi idan ba haka ba sai zaman gidan ya gagareki mai kan karas kawai ."
gabad'aya suka kwashe da dariya ban da muradi daya fita daga parlour'n zuwa nasu bangaren dan shiryawa ya tafi aiken mumy , "gaskiya Samir baka yi ba wallahi "dana yi me kenan ? "da kace afra na da wari baki da warin kashi bayan kasan ba haka bane "oho kenan a barta kullum tana yiwa muradi abinda ta ga dama yadda take yar'uwarki bakya son 'bacin ranta haka nima muradi dan'uwana ne bazan yarda ta dinga masa abinda ta ga dama ba . "Ai dukkaninsu yan'uwanka ne idan kana yin haka za'a iya samu matsaloli da dama " tsaki ya ja yace " an dade ba'a samu matsaloli ba ya cigaba da danne danne sa a facebook har sanda muradi yaje ya amso sakon mumy ya dawo ya ƙara karfin ac parlour'n saboda gumin dake tsatsafo masa ya tsiyaya ruwa a glass cup ya zauna akan kujera yana sauke numfashi tare da balballe botiran gaban rigarsa da hannu ɗaya yayinda d'ayan hannunsa ke bakinsa yana shan ruwa "
Samir ya waigo inda yake zaune yace "nayi addining number's dayawa fa bayan fitarka har nayi adding Wanda kace kar nayi ,na gama komai amman an buge account din ,"okay Sai da kayi searching wani kenan to kai me ya kai ka bayan nace karka yi ?"
"Ai na cire wannan hoton da kace kar na kara amfani dashi ,"ina wanda nace kayi seach inji cewar muradi "to ai kace dashi jahid zayi amfani dashi "Wanda kasa tun farko fa "? "Yana nan samir ya bashi amsa yana cigaba da danne dannensa a facebook " shi zaka cigaba da amfani dashi "okay idan dai wannan ne ai ina da hotunanta dayawa na wayana "muradi ya runtse idanunshi sannan yace " sai kayi amfani dashi kawai ka huta wanda jahid ya baka ma babu mai amfani dashi ."
"bai san kan abun bane halan "? Inji cewar zahra "ina fa ya sani yana damun kanshi a banza duk an ciye masa 'yan kudinsa ai wannan yahoo din adashin da babu kwasa ne sai an ci bakar wiya an kashe kudi sannan ake samu muradi ya k'arasa maganar yana murmushin gefen baki , "to kai haka ake yahoo din idan baka iya ba ka hakura mana sai kace dole sai kayi zahra ta fada tana kwashewa da dariya "rabo dashi a kina ganin Samir shegen son kudi ne da gashi yana ta kashewa yahoo kudinsa dan ya samu kudi gashi har yanzu bai samu komai ba sai wahala . "hoto ma da kake ganinsa shege tsada ne dashi wallahi, idan kaje ka bawa wani wayarka yaje ya kwashe maka hotunan shikenan ,dan hoto ma idan kana dashi zaka iya siyar dashi da tsada " shiga hankalinki Zahra babu ruwanki da aikina , bar muradi ya faɗa min komai zan hakura amman ke