Showing 114001 words to 117000 words out of 495987 words
Chapter 39 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
sake furta min wata kalma sai na harbeki yanzu ya ciro bindigasa daga aljihunsa yana nuna sautin brain dinta da kyar mumy ta hadiye kukanta dan ganin halin da yayanta suke ciki yau ta shiga tsakaninsu tana bawa ema hakuri saboda tasan halin zuciyarsa zai iya aikata komai hayaniyarsu tasa Sadiq ya barke da kuka yana wuntsil wuntsil da kafafunsa ta dauki danta ta rungume tana rarrashi shi kuma sai tsula kuka yake "yar iska ki tsaya kina bata rayuwarki akan mutumin da bai san komai ba sai ashararanci mara cikakken ilimi ko ke mai kashe kanki ce ki huta akanshi bata sake tanka masa ba har ya bar dakin yana surutai mumy ta kamota ta zaunar daita tana kuka "dicter ki taimakeni ki kai dan nan gurin ubansa ko dangin ubansa mu zaman lafiya bazan iya daukar wannan maseefar ba ,a hankali mumy ta dinga mata magana wanda Sam baya shigarta dan bataji zata bawa haroon karamin danta koda zai amsa bare ya nuna bai so ....."
A daidai wannan lokacin da al'amura suka dagule mata ta kowani bangare babu sauki daga yan'uwa ta ko'ina zafi ne , ta samu labarin inda haroon ya koma a bakin wani abokinsa commander bata yi sanya a gwiwa ba ta amshi full address din inda yake ta tattara kayanta batare da tayiwa kowa sallama ba ta nufi Abuja ta sauka a yanya bata sha wahala gano inda yake ba tashin farko yayi mata hauka amman daga karshe dole ya hakura ba dan ransa yaso ba sai dan abokansa da suka saka baki tare da kai maganar gurin Chirman, chairman na gama jin dogon bayaninta tausayinta ya kamashi har kwalla ya zubar yace "yanzu me kike son ayi ?muryarta a raunane tace "idan da hali zan so ya aureni dan a shirye nake dana amshi muslimci chirman ya numfasa kana ya kalli haroon "kai yanzu wannan ba abun alfahari bane agurinka ta sanadiyyarka wani ya musulunta "? Haroon Yayi shiru yana tsotsa keya sai dai zuciyar nan nashi tamkar ta kama da wuta"kayi tawakalli ka yarda da hukuncin Allah kasan baka shirya haihuwa ba mai yasa ka kai kanka ga aikata zina ? Muryarsa a dake yace "bani na mata cikin ba taje gurin wanda ya mata dan tasan uban danta amman bani haroon ba ..
"kayi wa zuciyarka adalci haroon duk wanda yaga yaron nan yasan danka ne ka hakura ka rungumi rayuwarta ko dan darajan jininka , chirman ya dauki dogon lokaci yana masa nasiha a karshe ya muslintar daita ya tara mutane aka d'aura musu aure , abokansa isa sule tare da Usman suka kaita madaidaicin bukkansa da yake rayuwa aciki a bayan gari ,babban filli da wani ma'aikacin gwanati ya bawa chairman ajiya shine kowanensu ya dibiba yasa aka rufe da tambal aka maidashi daki sai dai shi yasa an cire masa bayi daga gefen d'akin sa ."
Da misalin karfe shida yamma ya shigo dakin lokacin daya daura idanunshi akan yaron dake kwance a saman cinyarta gabansa yayi mummunar faduwa saboda tsantsar kamaninsa da yaron dan duk haukan da yayi bai tsaya yayiwa yaron kallon tsab ba ,guri ya samu a gefen katifa ya zauna tare da rafka tagumi ya zuba mata ido yana kallon kyakkywar fuskarta tana jijiga yaron lura da tayi da irin kallon da yakewa yaron yasa ta yunkura ta d'aura yaron akan cinyarsa ta fice daga d'akin ta shiga bayin dake manne da bukkan tsaf an sumenteshi da breaking tayis hannu ta kai ta jijiga jarkan da ta gani a ajiye a bayin taji motsin ruwa ta tsiyayya acikin wani karamin botiki da ta gani sannan ta durkusa domin yin fetsari ,koda ta dawo dakin idanunsa na kan sadiq ya riko yatsun hannunsa yana kallonsa komai nashi ya dauko babu abinda ya dauko na mahaifiyarsa sai duhun fata , wani irin abu yaji yana bin jijiyoyin jikinsa , zama tayi ta fuskanceshi ya ɗan d'ago kanshi ya kalleta sannan yace "me zaki ci ?wani irin yanayi ta tsinci kanta , zuciyarta tayi sanyi cike da jin dadin maganarsa duk da tasan bai taɓa sonta ba itace ke haukan sonshi amman taji dadin furucinsa na yanzu ,murmushin jin dadi tayi tare da sake kallon inda yake zaune a takure rike da sadiq gabansa na faduwa ,matsowa tayi kusa dashi ta riko hannunsa daya, a hankali tace " haroon i love You ,i really love you haroon tun daga lokacin dana fara faɗa maka wannan kalmar da gaske nake yanzu ina sake maimaita maka ina sonka ba dan kudi ko ilimi da dukiya ba, ka soni karka dauki alhakin zuciyar da ke maka soyayyar gaskiya da gaskiya numfashi ya fesar cikin tsananin zafin nama ya zare hannunsa ya daura sadiq akan cinyarta dan idan akwai abinda yafi tsana yaji daga bakinta bai wuce wannan shirmen banza ba zuciyarsa a dagule yace "baki da wata amsar data wuce bana sonki kuma bazan taba sonki ba har abada sannan nan kusa zaki nemeni ki rasa bazaki sake ganin koda inuwata bace a rayuwarki , gaban dicter wacce ta dawo rashida a wanin da suka gabata ya dinga faduwa bakinta ya kasa furta komai tana kallonsa ya fice daga dakin sai jin motsin ruwa tayi hakan yasa ta fahimci wanka yake cikin mintunan da basu wuce goma ba , ya dawo dakin daga shi sai dogon wondo baki ya dauki towel ya goge jikinsa tana zaune tana kallonsa har ya gama shirinsa ya dauki riga army green da wondo baki ya saka ,ya d'auki wayarsa yasa a aljihu ya fesa turare infenity sannan ya kalleta cike da tsananin kiyayya yace "ki fadi abinda zakici akawo miki idan dare yayi ki kulle ko'ina saboda bazan dawo ba sai gobe zuciyarta na bugawa kamar zai fito waje saboda firgici ta yunkura ta saba danta a kafada wani irin tashin hankali ta sake shiga gabad'aya jikinta yayi sanyi bai tsaya jin abinda zatace ba ya sa kai ya fita tabi bayansa da kallon "da gaske dai haroon baya sonta ta dinga jin zuciyarta kamar zata tarwatse saboda tsabar zafi "dan Allah ka soni zafin yayi min yawa da me zanji tuni hawaye suka wanke mata fuska ,a gurin yan'uwansa babu sauki agurinka ma haka kusan wannan tashin hankalin yafi komai ciwo da rad'ad'i a zuciyarta ta kamkame danta ajikinta tana wani irin kuka shima kuka ya fashe dashi kamar yasan uwarsa na cikin damuwa , kuka tayi sosai bayan kamar minti talatin taji motsi ana sallama ta kwantar da danta ta fito daga cikin bukkar wani matashin yaro ta gani tsaye ya gaisheta cike da girmamawa sannan ya mika bakar ledar "gashi inji oga tasa hannu ta amsa tana masa godiya ya juya ta dawo cikin bukkar ta buɗe laidar takeway ta gani da ruwan Eva da pure water guda biyar masu sanyi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta zauna ta soma cin abinci bayan ta gama tayi wanka shi kuwa sadiq sai goge masa jiki tayi saboda babu ruwan zafi gashi babu risho a bukkar bama risho ba duk wani abun amfani babu a gurin ,bukkar daga katifa sai fanka da kwan lantarki sai school bag d'insa da jakar kayansa dake gefe ta ciro wayarta ta jona cajin wayarta ta kulle kofar saboda dare ya soma dan bakwai ta wuce da wasu yan mintuna ..."
Kamar yadda ya fada mata bai dawo ba sai washegari ya dawo motsin bugun ko'farsa ya tadata ta mike ta bude masa kofar tayi masa sannu da zuwa sannan ta matsa domin bashi hanya ya raba ta gefenta yana cire facing cap d'insa ya ajiye ya fada saman kafita ya soma bacci bai tashi ba sai kusan azahar yayi Sallah ya kira yaronsa isele ya kawo mata abinci shi kuma ya cigaba da baccinsa bashi ya tashi ba sai karfe shida na yamma yayi wanka kamar jiya ya fita a qalla sai datayi kwana bakwai wata mu'amular arziki bata shiga tsakaninsu ko motsa bakinsa baya yi haka baya kallon inda take bare sadiq da yake ganin shine babbar matsalarsa a arayuwa, duk abinda yake yana damunta amman bata da yadda zatayi dole take yin shiru ranar data cike sati biyu a bukkar ranar ta kudurta aranta zata shiga kasuwa ta siyo abubuwan bukata lokacin da yaronsa asele yazo kawo mata abincin tace zata bishi ya nuna mata kasuwa tare suka fita ya kawota kasuwa tayi amfani da atm d'inta ta siyo kayan amfani tukunya da slinder gas da duk abinda tasan zata bukata haka ma ta bangaren Sadiq ta siyo masa Pampers da madara dan nono baya isansa , koda haroon ya dawo gida domin shirin fita muguwar kasuwancinsa da yasa kanshi ya firgita matuka ya dinga mata wani irin kallo kafin daga baya yace "ke mene ne haka nake gani ance miki zama kika zo ne ko me "?
"Lokaci na baki fa yana cika zaki koma gurin iyayenki kisan yadda zaki daidaita dasu su amsheki da danki dan zamanki cikin rayuwar haroon daidai yake da siyawa kanki ticket din mutuwa cikin tsoro tace "dan Allah kayi hakuri ka barni gara na mutu tare da kai wallahi ina tsoron abinda yan'uwana zasu yi min sannan banason sadiq ya taso yaga irin tsanar daake masa adalilin zunubin iyayensa ta karasa maganarta tana kuka lumshe kyawawan idanunshi yayi sannan ya buɗe ya daurasu akan sadiq dake kwance yana wuntsil wuntsil da kafafunsa "me kika ce sunan yaron "?
"Sadiq ta furta tana kuka ya girgiza kai aranshi ya furta" wallahi dicter kin haukace a zahiri kuma yace " ubanwa yace kisa wannan dan naki suna to bari kiji ko sunan ubansa zaki saka masa bazan amsheshi haka zalika dangina bazasu amsheshi ba dan haka tun wuri ki kama gabanki dan bazaki yi rayuwa mai dadi dani ba saboda da gaske bana sonki "cikin tsoro tace "dan Allah ka daina cewa baka sona kalli irin kyautar da Allah yayi maka adalilina, kayi hakuri kayi alfahari dashi koda bazaka soni ba ka daure ka .."Babu abinda zaki samu agurina fa hankalina bazai taba kwanciya dake da wannan dan naki ba wannan dan naki na bar miki shi har abada dan bani da abinda zanyi dashi ya soma cire kayan jikinsa yana jifa dashi sannan ya fita tana tsaye kamar an dasata ."
ta dade tsaye tana tunani har sanda yayi wanka ya shirya cikin jallabiya brown ya daura facing cap baki da takalmi baki ya fice washegari ma haka ya shigo da safe tana zaune tana karanta littafi addu'oi mai fassara da turanci ,duk da bata sallah har lokacin amman tana fahimtar wasu abubuwa dangane da addani , shi wanda zai tsaya ya koya mata bai natsu ba bare tasan yadda zata tsaida addininta gabansa na tsananin faduwa ya fada saman katifa ya kwanta a gefen sadiq yana kallon fuskarshi photo capy dinsa sak jikinta a sanyaye ta rufe littafin hannunta ta hau saman katifar cikin tsoro tace" sannu da zuwa banza yayi mata ya runtse idanunshi ta kai hannunta jikinsa "bari nayi maka massaging da alamun ka gaji dayawa nan ma shiru yayi ta kai hannunta jikinsa ta soma mammatsa masa jiki zuwa nipples d'insa wani irin sanyi yaji yana bin sansar jikinsa saboda dadin abun daman kuma yasanta da yadda tasirin hannunta suke gurin iya massaging kafin kace me tuni yanayinsa ya soma sauyawa jin idan bai yi wani abu ba komai zai iya faruwa yasa ya mike daga kan katifar ya zira slippers akafarsa ya shiga wanka ya fito ya sake kwantawa bata daddara ba ta sake kusanto jikinsa tun yana dojewa sai gashi yayi balance cikin kankanin lokaci ya birkice mata zuwa wani yanayi na dabam bai san abinda ya aikata ba sai bayan daya gama sannan ya hankalta aiko ya rufeta da ruwan bala'in zatai magana yasa hannu ya d'agota ya ɗauketa da wani gigitaccen mari har guda biyu sannan yaja tsaki tayi dariya "banyi danasani ba sannan ban ji haushin marin ba da sannu Allah zai min maganinka dan banga dalilin da yasa zaka dinga min irin wannan kiyayyar ba ,ka gaugauta tuba akan abubuwa da kake min sannan ka canza rayuwa domin wannan rayuwar daka daukarwa kanka wata rana zakayi danasaninta , ko kuma nace zaka cutar da kanka sannan mutane irinku sune suke hana duniya kwanciyar hankali ina tabbatar maka daga rana mai kamar ta yau ka dinga kuskuren kusantata kenan ina addu'a a dukkanin shafukan rayuwata ya zamanto nice uwar ya'yanka a nan duniya duk macen da zaka kusanceta spam dinka ya zamo ruwa mara amfani ajikinta "ai kuwa kisawa ranki kinyi bankwana da farincikin sannan zan ladabatar da kazamar zuciyarki banza shasha kawai mara mutunci da kamun kai ana gudunki kina naci "komai zakayi kayi a shirye nake kuma bazanji haushi ba kai yanzu nafi bukatar kiyayyar akan soyayyar dan tafi dadi ,banza yayi mata yayi kwanciyarsa bai tashi ba sai lokacin da fitarsa tayi ."
******
Akwana a tashi babu wuya agurin Allah sai gashi har dicter tayi wata biyar wanda yayi daidai da watan sadiq tara a duniya yana gudunsa ko'ina haka yana gane babansa daya ganshi zai yi ta daga masa hannu ,wata rana ya daukeshi wata rana yaki kuma a wannan lokacin ta fuskanci ciki gareta ta shiga damuwa sosai sai dai tayi farinciki sosai aikuwa lokacin data gaya haroon taci wani abu wai shi duka ,duka yayi mata kamar zai kasheta tare da yi mata saki biyu yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "daman ni ban ɗauki aurenki da wani daraja ba dan dashi da babu agurina duk daya ne ,itama kusan hakan ce gareta sai dai ita ta yarda ta zauna karkashinsa ko ta wani hali ya dawo gallaza mata hatta dan abincin da yake bata ya daina wulakanci yau dabam na gobe dabam har bukkan yake kawo yamnatansa ya korota waje yayi iskancisa dasu duk ta kawo ido ta saka masa , kudadenta dake cikin account d'inta kuwa sunyi kasa sosai sai manage take damuwa ta taru tayi mata yawa saboda rashin samu cikakken kulawa ga yaronta karami ga cikin wata uku , haka tayita rayuwa acikin bukka a hankali har suka saba da isele gefe guda kuma cikinta na girma ,wata tara cif ta haihu ita kadai kamar haihuwar sadiq ta samu danta namiji shima mai kama da ubansa sak har ma yafi kama dashi akan sadiq saboda shine ya dauko farinsa sosai da tsarin jikinsa wannan haihuwar babu abinda ya kara mata a zuciyar haroon kamar bakin jini da zalar kiyayya suna zaune a daki isele ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ya dauki sadiq ya daga shi sama yana masa wasa shi kuma yana bulbulamasa dariya "kayi kani sadiq ka rage kiriniya ya fada yana kallon haroon oga wani suna aka sawa baby ne"?"Ban sani ba kuma karka dameni "esele ".
Dicter ta kira sunan esele " me ye sunanka na gaskiya ?Yayi murmushi sannan yace "Aliyu ""Ka iya radawa baby suna a muslinci ? yace mata "eh "Okay rada masa suna da Aliyu take esele yayiwa yaro huduba da Aliyu shi kuwa haroon ko ajikinsa shirinsa yake hankali kwance ciki farar riga mai gajeren hannu da bakin wando yana gamawa ya daura facing cap d'insa na gado ya fice.esele ya zauna cike da jin dadi , a hankali dicter ta dinga jansa da hira daman kuma sun saba sosai dashi tace "esele Wai aikin me haroon yake yi ne da bai kwana a gida kullum yana garaji "?
Shiru yayi mata har sai data sake magana sannan ya tsosa gaban goshinsa "a zahiri gaskiya aikin da oga yake ......nan ma ya sake yin shiru "ka faɗa min mana karka boye min komai ka ɗaukeni kamar yayarka nima kuma kamar kanina na daukeka aikin me haroon yake ?"A zahiri gaskiya oga dila coken ne wato hudar iblis ............."
MMN SUDAIS[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Page 19
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, volyal lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan ɗaya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096,
......." Koken ta furta a mutukar firgice tare da dafe qirjinta da duka hannuwanta , a tsoroce esele yace" ki rufa min asiri maman sadiq kada ki bari oga ya san na faɗa miki business dinsa zai iya ... .." saurin d'aga masa hannu tayi jikinta na kyarma "Karka damu esele babu abinda zanyi na gode sosai daka faɗa min gaskiya amman kaima shine sana'arka kenan "?Yayi saurin gyada mata kai alamun "eh " shiru tayi tana kallonsa zuciyarta na tsinkewa bata san sanda hawayen bakinciki suka zubo mata ba "ki daina kuka maman Sadiq da nasan zaki shiga damuwa a dalilin maganata wallahi ban