Showing 261001 words to 264000 words out of 495987 words
Chapter 88 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
koma ki zauna har sanda ya badamasi zai dawo ya sallamemu ya k'arasa maganar yana dauke Idanunshi akanta sai lokacin ta soma magana cikin fushi "wai ina ruwanka dani ne ka kyakeni na tafi duk inda nake so ni wallahi na tsaneka saboda kafiye shishigi ya sake d'ago Idanunshi da suke a Lumshe ya saukesu akanta sannan ya budesu fess yana watsa mata wani kallon ta shiga hankalinta "ban taba damuwa da tsanarki ba saboda nima ba sonki nake ba saboda damun iyayena da kike baki cancanci a soki ba tsanace tafi dacewa dake sai dai duk da hakan bazan kasa saka ido akan gurbatattaciyar rayuwar da kike son jefa kanki ciki ba dan haka ki koma ki zauna tun raina bai ɓaci ba ya karasa maganar yana dauke Idanunshi akanta tare da controlling din fushinsa dan idan ya cigaba da kallonta fasa mata kai zai gabad'aya da irin kallon tsanar da take masa kin zama tayi kamar yadda yace har sanda wata nurse ta shigo office din ta dauki wasu file ta fita da sauri
batare data tsaya kulle kofar ba cikinsu babu wanda yayi yunkurin isa ga kofar har ya badamasi ya dawo ya iske su haka hankalinsa a matukar tashe yace "ba dai guduwa zatayi ba ?muradi ya girgiza masa kai alamun a'a sannan ya mike tsaye yana tura wayarsa cikin aljihu "muje ka sallamemu muce gida "okay muje suka fito tare har kisna suka tsaya a bakin kofa ya kulle suka karaso reciption ya shiga dakin magani shi kuma muradi ya daga wayarsa dake ringing yace "ya'akayi Samir ?"Okay kaje kawai ina hospital tare da Hajiya kayi yana fara magana ta juya cikin sanyi jiki ta fito zuwa haraban asibitin tana waige waige shi kuma ya cigaba da wayarsa "kuyi komai da jahid idan na dawo zanyi handling din komai da kaina katse kiran yayi cikin sauri juyowar nan da zai yi yaga wayam babu ita babu alamunta waige waige ya soma bai ganta ba yayi saurin kwankwasa kofar dakin da ya badamasi yake ciki da sauri ya bude yana tambayarsa "ya'akayi muradi ina kisna ?
"banganta ba da sauri ya fito suka yo waje tare suna nemanta cikin tsananin tashin hankali ita kuwa tana fitowa haraban asibitin cikin sanyi jiki tunanin komawarta gida take dan idan akwai abinda ta tsana bai wuce kulleta da aka yi ba kamar wata barauniya tare da hanata rawar gaban hantsi gashi ita a halin yanzu babu abinda take ji sai radadin rayuwa su barta tayi life dinta mana saboda me zasu takura rayuwarta ta durkusa kasa tana kukan zuci tana kallon kasa inda idanunta ya sauka akan wani karfe ta dauka tana kallonsa "idan ma sun kulleni zan iya amfani da wannan karfen gurin bude kofar na fito na kama gabana bazasu sake sakani aciki rayuwarsu ba tana cikin zance zuci taga tsayuwar mutun a gabanta yana haki ta mike tsaye tana hura hanci a ranta tace Sarkin shishigi kawai "muje ko yayi maganar yana damko tsintsiyar hannunta ya soma tafiya daita yana neman layin ya badamasi ta damke karfen hannunta sosai tana biye dashi tana zaginsa a jikin mota ya iske ya badamasi tsaye "a ina ka ganta ?
"bani key kawai kayi tafiyarka zan dawo maka da motar kasa aiwatar da hakan yayi yace "no muje na saukeku suka shiga motar akan hanyarsu ta dawowa gida haka kisna tayita sake sake yadda zata gudu har suka iso gida tunani take kai tsaye ɗakinta na bq suka nufa ya bude ta shiga an sharesa fess sai kamshi yake ta zube kasa ta soma rera kuka mai ban tausayi qirjinta na wata irin zafi ya badamasi ya bita da kallo "kukan me kike yiwa mutane ai irin rayuwar da kika bukata kenan gashin nan kuma kin samu tunda bazaki zauna lafiya ba ki cigaba da zaman cell Kinga ko yanzu kin cuci kanki shi wanda kike gudu saboda shi yana can .."no ya badamasi bani key kayi tafiyarka babu mutsu ya mika masa ya fice shi kuma ya shigo cikin filin dakin yana kallon yadda hawaye ke tsiyaya a kuncinta "me kike so ki faɗa min duk abinda kike so wallahi a shirye nake nayi miki shi dan ki kwantar da hankalinki dana mu ? ta d'ago idanunta dake cike da kwalla "ka kai ni gurin Musa shi kawai nake son gani ina son sani halin daka jefa shi ya mutu ne ko yana raye ya tsugunna a gabanta yana kallonta zuciyarsa na tafasa "ki kwantar da hankalinki yana raye har ma yana yawonsa ko'ina bayan dukan danayi masa na kai shi hospital shida dan'uwansa na biya kudi Naira dubu dari uku dan a duba jikinsu ta dinga kallonsa tamkar mutum mutumi a gabanta zuciyarta ta cigaba da bugawa da sauri da sauri wani irin mutun ne shi yayi barna ya gyara ? "Ki ciresa a ranki ki cigaba da rayuwarki dan ko kin koma garesa babu abinda zai yi dake saboda ya tabbatar min da haka yanzu haka ma ya manta dake jin maganarsa ta karshe yasa ta soma tsine masa da mayar da kalmarsa ta karshe akansa "bazai taba mantawa dani ba saboda yana sona tayi maganar cikin kuka "sai ki cigaba da son sa a inda kike ya juya yayi tafiyarta tare da kulleta .."
Daren ranar bata runtsa ba ta dauko karfen data zo dashi daga hospital ta soma kwakule karfen kofa sai dai har kusan biyun dare batayi nasara ba a haka har bacci ya dauketa a cikin kwananki kullum sai kisna ta kwakwale kofar sai dai karafen kofar suna nan daram babu alamun motsi yau tsawon kwana biyu muradi bai shigo inda kisna take ba saboda ayyukan office da suka sashi gaba shi da samir sai dai shi duk abinda yake hankalinsa na kanta da kula da abincinta wani lokaci ma har fada mumy da dady suke masa kan yadda yake nuna kulawarsa gareta shi kuma sai ya fada musu itace zata sa ta kwantar da hankalinta har ta fahimci cewar lallai ahlinta na sonta ba wai kiyayya ce tasa ake son rabata da yaron da take so ba .
a hankali ya bude kofar dakin ya shigo tana kwance tana ganinsa ta mike zaune idanunta a kasa har ya karasa shigowa dakin ya durkusa a gabanta ya daura hannunsa a saman kanta "hajiya kayi ykk fatan kina cikin koshin lafiya ? Shiru tayi taki cewa komai illa hannunsa datayi kokarin cirewa daga saman kanta "kada ki cigaba da sanyawa ranki damuwa akan qaddararki wanda ke karya min zuciya kullum na fita ina jin babu dadi a cikin raina saboda na baro kanwata kulle cikin matsanancin damuwa hakan na karya min zuciya har na zubda hawaye a duk sanda na tunoki ta kalleshi da sauri cikin waro ido sannan taja tsaki a ranta "kullum baka rabo da sabon shishigi ya kura mata ido yana son karantar wani abu daga gareta amman ya kasa "ina son ki cigaba da karatunki da rayuwa kamar kowa wani alkwari zaki min nasa baki a sake ki ? Tayi shiru tsabar miskilanci tana kallonsa "kinyi alkwarin zaki zauna lafiya bazaki damu kowa ba ?tayi saurin gyada masa kai ganin ga damar fita zata samu "shinkenan zan samu dady muyi magana dashi cikin satin nan yanzu me kike so ? Tayi shiru a qalla na minti goma sannan cikin sanyayyiyar muryarta tace "a fitar dani daga dakin nan yau saboda dakin na bani tsoro "idan an fitar dake bazaki ko'ina ba ? Ta sake gyada masa kai alamun "eh ya saki murmushin farinciki "nayi murna sosai ko babu komai hankullan iyayenmu zai kwanta zasu yi farinciki sosai idan kika kwantar da hankalinki zamuyi alfahari dake zan fadawa abokaina ina da kanwa mai hankali da jin magana da tausayi duk maganar da yake ta bayan kunneta yake bi burinta ya fitar daita kawai "kin yi shiru fatan zaki cika alkawari ta kakalo murmushin dole tace " nayi"
ya mike tsaye tare daita yana rike da tsintsiyar hannunta yana tafiya yana magana cikin sanyayyiyar muryarsa "kece komai na rayuwarmu fadar matsayinki agunmu abune mai matukar wahala da bata lokaci abinda nasani kin tafi a kashi casain a cikin dari na al'amuran rayuwarmu a fili yake mata maganar dan kwantar mata da hankali mumy na zaune a falo taga shigowarsu sai da taji gabanta yayi wani irin mugun faduwa take jikinta ya kama rawa muradi ya karaso da sauri tare da zaunar da kisna gaban mumy "dan girman Allah mumy kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki nasan nayi laifi amman babu abinda zai biyo baya sai alkhairi kulle da muka taru mukayi wallahi bashi ne mafuta ba sannan tayi min alkawarin bazata sake aikata abinda tayi ba mu bata dama har yanzu yarinya ce da bata san ciwon kanta ba haka ya dinga kwantarwa da mumy hankali ta numfasa tana sauke ajiyar zuciya mai karfi ya kalli kisna ki bawa mumy hakuri tare da tabbatar mata bazaki sake ba "kiyi hakuri mumy bazan sake ba "Allah yasa mamana Allah ya yaye miki yasa karshen wahalar kenan nima ba'a son raina kike kulle ba ta karasa maganar tana janyota jikinta ta rungume tana kuka muradi yayi shiru yana kallonsu sai suka tuna masa data shi uwar daya rasa wanda har lokacin bai daina jin radadin ciwon rabuwa daita ba dan'uwan daya daura rayuwarsa akansa shi kuma yabi sawun mahaifinsu bashi nan yau bashi can kullum addu'a yake Allah ya kawo masa shi dan ya inganta rayuwarsa kamar yadda mahaifiyarsu ta bukata rayuwarsa akwai ciwo mai radadi mumy ce kawai ke sanyashi farinciki shi kuwa me zai mata ya biyata daya wuce kyautata mata da dawo da diyarta cikin haiyacinta cikin kwana biyun da aka fito da kisna ta soma neman hanyar gudu sai dai babu hanya saboda takunkumi da'a ka sa ta ko'ina sosai ta saki jikinta da muradi kamar gaske hakan kuwa yayi masa dadi har ma da kowa dake cikin gidan afra ce kawai ta fahimci ba dan Allah take abubuwan da take ba ,sosai muradi yake ji da kisna ya dinga mata abubuwan da yasan zai kara kwantar mata da hankali da iyakacin karfinsa daya ga tayi shiru zai ɗauketa ya fita daita yawo yayi mata siyayya mai yawa ya dawo daita gida yau ma kamar kullum ya ganta tayi shiru ya kalleta sosai ya gano tana cikin damuwa dan haka ya dauketa ita da zee sai wani hadadden boutique ya siya musu kananun kaya masu yawa sai dai na kisna yafi yawa yayinda a zuciyarta take tsine masa dan son mantar daita muradin zuciyata haka ta dinga daurewa tana musu biyyayar karya da bin umarninsu yanzu har waje take fita ta zauna ta sha iska a base dinsu muradi ita da kawayenta gabad'aya kowa ya sakankace daita cewar babu batun gudu ta bar gida kowa murna da farinciki yake kisna ta shiryu taimako kuwa har lokacin mumy ba daina amsar mata ba ...."
******
Zaune kisna suke a babban falo gidansu ita da kawarta zinnira sai ga muradi ya shigo ya wuce dakin mumy zinnira ta kalleshi "yayanki na matsefar burgeni idan na girma irinsa zan aura "ki dai ce kina son shi kawai ?"a'a idan na girma nace fa nan kisna ta hau zaginsa "ni wallahi babu abinda zanyi da irinsa ya fiyye shishigi gashi shege ne fa zinnira ta zaro ido "ki daina fadar haka babu kyau suna cikin hira can kisna muskuta tace " zinnu mu bar wannan hirar tashi muje kofar gida wallahi yau tsokana nake ji "tsoka kuma kisna ? zinnira ta fada tana waro ido waje tare da dubanta dan tasan halinta "gaskiya bazani ba gara muyi zamammu anan kawai yafi "to sarkin tsoro na fasa muje mu sha iska "babu wani tsoro dan duk tsorona ban kai naki ba tunda ke common kyankyaso tsoronsa kike har yanzu " da wayo da dabara kisna ta janyo zinnira suka fito dan ita tana da manufarta na fitowa a ranar lokacin da suka fito babu kowa akan bancin dasu muradi suke zama ta kalli tarin robobin dake jere da fanfon kofar gidansu lokacin ba'a kunna ruwa ba taja tsaki "kai wadan akwai yan wahala fa jefa tun ba'a kunna ba sun wani yayyabe fanfo suna nan zaune har aka kunna ruwa ya soma zuba sai gasu rahma da kanneta hadiza da aysha makaftansu ne da wani yaro yinka shi kuma opposite din gidansu yake rahma ta karaso inda kisna take ta bata hannu suka gaisa dan tasan halinta da tsokanar bala'i muddin ta shareta bata mata magana ba akwai matsala dan zata iya janyo abinda mai gadi zai fito ya koresu bayan sun gaisa ta koma gurin fanfo nan su rahma suka tara botikansu suka fara diban ruwa bayan su diba suka ce wasu su diba kafin su dawo kasancewar botikansu nada yawa da suka jera akan layi da zarar sun dawo zasu janye kowaye akan layi su diba dan yawon botikansu ke samar musu ruwa da wuri bayan sun dawo sai ga yinka da gudu zai dibi ruwa alhalin yasan da tarin botikansu rahma ,rahma tace" a'a yinka ai ka iske botikanmu ne a nan You can't fash water oooo nan suka fara diraging dashi ai kisna na ganin haka ta mike tsam ta isa gurin tana kallon yinka a yatsine kafin daga baya ta karfi bawon rahma ta ture na yinka ta tara shima bai duba wai fanfon gidansu bane ya tunkude bawon rahma dake rike a hannu kisna nan suka shiga tunkude bawon juna suna cikin haka nan take zuciya ya zo ma kisna ta kai masa mari Shima bai tsaya wata wata ba ya kai mata mari jin zafin mari yasa kisna ta cukumesa suka fara dambe take sauran yara suka shiga ihu da kururuwa neman dauki bata san ta iya naushi ba sai ranar yana kai mata naushi tana kai masa data ga alamar yafi karfinta kawai ta silale kasa ta suma aka zuba mata ruwan duniya amman taki motsi alhalin nomal dinta take da gudu zinnira ta shiga gida dan sanarwa mumy tare suka fito gabad'aya da mutanen gidan har muradi mumy ta tsaya a bakin get shikuwa muradi yana zuwa ya girgiza kuncinta shiru sai ya juya yana tambayar zinnira bata boye masa komai ba ta fada masa yana gama ji kawai ciccibeta ya saba a kafadansa ya nufi gida daita take mumy ta razana ta biyo bayansu kamar ma bata motsi nan kisna ta sake sake jikinta kafin kace me gidan ya cika da mutanen unguwa har iya yinka tace "yeeeeee yinka oti pomo lomo oti she leshe surutu kawai take tana dukan yinka tana bada hakuri aka sake kwarawa kisna ruwa amman still taki tashe a zuciyarta tace sai na sha madara kuma sai kun biya kudin asibiti sannan na gudu mumy tace "muradi kira badamasi "a'a bari muje asibiti ya fita cikin sauri ya
juya kan mota Samir ya cicibota aka kaita asibiti Victoria saboda shi yafi kusa dasu ana zuwa asibitin ba'a wani bata lokaci ba ta farfaɗo washegari sai ga iya yinka da kayan shayi niki niki bayan tasha tea ta kwaba madara ta sha sosai sannan tace likitan da yazo duba da rana "dan Allah kayi discharging dina plz na komai gida likita yace "a'a har kin samu lafiya ke da aka kawoki kin fita haiyacinki ya fada yana dariya dan shima yaso ya gano suman karya tayi tun jiya amman ya share kwanata daya da yini da yamma aka bata sallama daga asibiti ta faki idanun mumy ta gudu bata tsaya a ko'ina ba sai gidansu musa kallonta yayi cikin bakinciki ganinta duk da ba wai ya daina sonta bane amman ba zai cigaba da soyayya daita saboda yana shan wuya ganin irin kallon da yake mata ya sata qarasowa daf da shi wani sabon mummunar tashin hankali ne ya sameshi ,wani daci rai me tsanani ya rufeshi kamar ya rufeta da duka haka yaji amman ganin ta zube kasa tana kuka a gabansa yasa zuciyarsa shiga rudani yayi tunani gara ya lallabata ko kudantarta yayi tunda yasan ko sama da kasa zasu haɗe baza'a bashi aurenta ba dan haka ya kamota jikinsa babu alama jin kunya atare daita ta rungumeshi bayan kamar minti goma suka bi ta kofar baya suka bar unguwar basu tsaya a ko'ina ba sai a omole estate gidan wani kanin babansa dake zaune a Canada mai gadin ya sansa Musa sosai ya barsu suka shiga kusan awa daya suna tare daita suna abinda suka saba kafin daga bisani ya barta ya dawo unguwa dan gudun zargi .."
Can asibiti kuwa bakaramin tashin hankali yan gidansu kisna suka shiga ba a lokacin da suka nemeta suka rasa wasu na ƙaryata guduwa tayi yayinda wasu ke cewa guduwa tayi shi kuwa muradi tuni ya yarda ta gudu din ne dan babu inda basu duba ba acikin hospital din ba ko taje Shan iska ne sai dai wayam babu ita babu alamunta "ai sai dana fada maka kuskure kayi gurin fito da wannan mara jin magana na rantse da Allah wannan karon sai na balla mata kafa sambatu kawai Samir ke faman yi suna tafiya da muradi wanda ya rasa me zai ce illa furzar da iska " kenan duk plan ne sumar da tayi "? Ya tambayi kanshi a daidai lokacin da suka dawo inda su mumy suke, runtse idanunwansa yayi da suka sauya a take yana controlling natsuwarsa na wasu sakwanni kafin ya budesu akan inda ya barta gabad'aya ya rasa da wani kalma zai yiwa mumy dake gefensa tana girgiza kai da furta kalmar "Inna lillahi was Inna ilaihi raji'un bayani dan kuwa shine silar faruwar komai "kiyi hakuri mumy ban ..."babu komai