Showing 174001 words to 177000 words out of 495987 words
Chapter 59 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
ido suna Kallonta cike da mamaki . "zaki zo da wahalar kenan ko ? inji cewar madu "ai kai ne wahalallen tayi saurin dakatar dashi ,kun wani zo nan kuna ta ɗaukar hoto ko a samu wanda zai kirani ai nasan duk sharrin wannan ne ta k'arasa maganar tana nuna Samir "sannu gimbiya saboda ana jin tsoronki ne za'a zo kiranki alhalin kinsa hakan zata iya faruwa dole idan anzo za'a yi hoto , ke da kika san kina son d'aukar hoton me yasa kika ....."?
"Ya isa abar maganar haka inji cewar ya badamasi zo nayi miki hoto my queen ya ciro wayarsa iPhone xx max , tabe baki Samir yayi tare da cewa " yar wahala kawai ke dai idan baki ja mutane faɗa ba bakya jin dadi yar rainin hankalin kawai ". hotuna sukayi sosai daga karshe tasa ya badamasi ya siya mata wani ice cream ,Samir ya dauki ice cream mai chocolate da kayan motsa baki "bari na d'aukarwa muradi ".da sauri ta matso kusa dashi ta tsaya "ka jika da iyayi yana son sha me ya hana shi zuwa "?"Ina ruwanki da rashi zuwansa ko kice zakiyi kayansa zuwa gida"?Tace "kai ne zaka yi kayansa amman dole nayi magana tunda bakina ne ta fada tana yatsina fuska "to babu ruwanki dani idan ba haka ba zamu raba hali yanzu anan "to mu raba mana sai me tsoronka nake ji "?"Kufa gayawa yarinyar nan ni ba sa'anta bane idan ta raina kowa karta ce zata rainani ..."
ya badamasi ya riko mayafinta
"muje my queen Samir fa kaninki ne ki daina biye masa fixge mayafinta tayi tana masa wani kallo "ta ina ya zama kanina bayan akwai wattanni a tsakaninmu ya bani wata biyar fa ta karasa maganar tana nuna masa yatsunta biyar "naji ni ba wannan nake nufi ba idan lokaci yayi zaki fahimci abinda nake nufi ya sake janta Suka nufi inda motarsu take Suna shiga haraban gidan ranta yayi bala'in ɓaci saboda cin karo da fuskar muradi da tayi cikin shirin zuwa masallacin sanye cikin jallabiya baka kafin ya karaso inda motar take pake ta jefa masa wani mugun kallo tana harararsa tare da jan tsaki ta runtse idanuwanta saboda bata kaunar ganinsa a rayuwarta ya ɗan tsaya yana jiran fitowar Samir ta fito daga gaban mota tana yatsina fuska haka nan taji zuciyarta ta bugu lokacin da tayi kusa dashi ".
Aunty ummi ta fito da kyar muradi ya mika mata hannu alamun ta miko masa Kisna "yauwa muradi dan Allah kai ta dakin mumy suka jera tare da Samir yana fada masa yazo masa da ice cream kai tsaye dakin mumy suka shiga ya kwantar daita akan gado ya cire mata takalmi dake sanye a kafafunta Samir na bashi labarin inda suka je suna ƙoƙarin fita daga dakin mumy ta fito daga bayi tace "yauwa muradi zo nan kai kuma Samir kira min ummi har da madu ma ya fito cikin sauri tare suka dawo Mumy ta kalli muradi tace "abinda nake son fad'a maka duk inda kaga kawunka garba ko bature Karka kallesu bare su ganeka , kuma bance ku fadawa wani daga cikin dangina dake garin nan cewar an ga muradi ba " gaba-dayansu suka gyada mata kai alamun sunji "oya kuje kuyi sallah suka fita ummi ta nufi dakinsu su kuma suka wuce massalaci ."
karfe bakwai daidai duk suka hallarar a parlour Samir ya mikawa muradi roban ice cream din daya zo masa dashi ya amsa ya bude yaga ice cream din ya narke duk yayi kunfa daga sama ,Samir dake zaune gefensa ya leka cikin roban saurin dafe goshinsa yayi "ya narke ko ? amman banji dadi ba wallahi shi yasa nace kasha kafin kaje massalaci kaki". ita kuwa afra ranta fesa da jin abinda Samir yace "Allah ya qara ai ka iya gulma da iyayi gara daya narke naga karya sha ta mike daga zaunen dake ta shiga Zariya a cikin parlour'n tana jin dadi saboda hango ɓacin rai mai tsanani a kwayar idanun muradi,a hankali muradi ya ajiye roban ya tashi ya bar gurin ya koma dakinsu yana danne zuciyarsa dake masa zafi yana da tsananin hakuri amman zuciyarsa bata daukar wulakaci, yana da juriya amman kuma yana da taurin kai mai tsanani akan abu , idan ya kafe akan abu ko me zai faru sai dai ya faru amman bazai rusuna ba shifa akan afra za'a iya nemansa a rasa gara yayi rayuwarsa a wani bagiren da bai da kowa kuma babu wanda yasanshi zai fiyye masa kwanciyar hankali hawaye ya zubo masa saboda baya qaunar rayuwar waje kullum zuciyarsa na cike da tarin bakinciki rashin sadiq a kusa dashi baya son wannan yawon da yake " Samir ne ya shigo dakin yaga ya haɗa kanshi da bangon dakin yana sheshekan kukan zuci dana zahiri dan yana hango yadda bayansa ke motsawa , ya zuba wa bayansa ido kafin daga baya ya karaso gurinsa ya dafa shi tare da juyo dashi suka fuskanci juna muradi ya tsura masa ido yana huci qirjinsa har dagawa yake , tsawon mintina ko motsi bai yi ba bare a saka rai zai yi magana illa dauke hawayensa da yayi ,a fusace Samir yace "wai bazaka takawa yar iskar yarinyar nan burki ba ta fita harkarka dan fa taga kana kyaleta ne kazo muje kaci ubanta ya janyo hannun muradi yana ƙoƙarin fita daga dakin amman fur muradi yaki takawa ya tsaya Samir ya juyo ya zuba masa ido cikin ɓacin rai "ka kwantar da hankalinka Samir ni gidan ma zan bar mata rayuwata bata son yawon damuwa "idan ta isa tasa ka bar gidan nan shege nake ai ba da kudin ubanta a gina gidan nan ba bare ka barshi saboda ita," itace zata tattara ta bar gidan ta koma gidansu ka daina raga mata yar iskar yarinya ce wallahi , baka ga tunda naci ubanta muka dawo daidai daita ba , muradi ya sake tsurawa Samir ido a zuciyarsa yace "bazan iya cacar baki da mace ba bare dambe tsakanina da mace ido ne , Samir ya dade yana rarrashin muradi ganin yadda ya shiga damuwa yasa muradi yace "zan zauna darajan wannan soyayyar da ka nuna min kadai ta hanani aiwatar da abinda zuciyata ke gaya min akan zamana a gidan nan rungumeshi Samir yayi yana sake jin kaunar muradi a ransa ."Kowa a gidan yana ji da auta Kisna da sun dan samu dan canjinsu akanta yakarewa , shima muradi yana son daukarta dan Allah yayisa da son kananan yara sai dai Kisna bata yarda dashi tana ganinsa zata gudu shi kuma ya bita yana ɗaukarta zata fashe masa da kuka dole zai sauketa yana qaunar daukarta amman bata yarda dashi".
Afra na gama hutunta ta tattara ta koma gidansu ba dan ranta yaso ba, dan taso ta zauna ta cigaba da takurawa rayuwar Aliyu wanda bai san ma tana yi ba , komawarta gida ya haifar mata da zazzaɓi dan ranar data koma a daki ta wuni zur kwance babu inda ta fito har zuwa washegari haka ta dinga Allah Allah su sake samun wani hutun tattara ta koma gidan Alhaji realwan dan taji dadin zaman gidan ,zuwa ya badamasi biyu gurinta kuma a lokacin ya shaidawa dan'uwan mahaifinsa cewar yana son Afra da aure idan ya gama karatu yayi hakan ne dan kar abawa wani kafin ya dawo tunda yawanci a gida ake zabawa yaran family dinsu miji , alhj marwan yaji dadi sosai ya tabbatar masa Afra bata da wani miji sai shi inshallahu ,zuciyarsa cike da farinciki da soyayyar Afra ya koma kasar Australia ."
Aliyu ya samu sauyi rayuwa sosai domin kuwa da za'a koma makaranta dashi aka koma don cigaba da karantunsa na gaba da primary sai dai an sha fama dashi ranar dan lokacin da aka tambaye dady sunansa dana mahaifinsa dady yace " haruna Aliyu take muradi yace a'a " benedicter rashida Aliyu yake amfani dashi Alhaji realwan ya girgiza kai yana murmushi sannan ya ciro wayarsa ya kira mumy tace " ka barshi a yadda yake so din ko kuma yayi amfani da sunan dasu Samir suke amfani dashi " kina nufin sunana ?tace "eh " hakan fa bai yi ba duk lalacewar haroon mahaifinsa ne taya zaki ce haka ? "ya zamuyi kenan nasan halin muradi da kafiya can ilo ma haka aka sha fama dashi kar a zo ana samun matsala ne Alhaji realwan yace "zakayi amfani da sunana ?muradi ya gyada kai alamun "eh "tun a ranar muradi ya canza Komai nashi zuwa sunan Alhaji realwan, ajinsu samir aka saka shi saboda tabbatar da kokarinsa da malamai sukayi ."
sannu a hankali aka sake samun wani hutun zango shekara wanda zasu yi wata biyu kafin su koma makaranta , a wannan zuwa hutun da afra zatayi ne ta tabbatar wa mahaifiyar idan taje gidan Alhaji realwan taje kenan bazata sake dawo ba sai dai tazo kawo mata ziyara nan take mahaifiyarta taki yarda da wannan tsarin tace "sai dai taje hutu ta dawo amman batun zama gabad'aya babu shi , ita kuma tace "bata yarda da zuwa hutu kawai ba tafi son zama gabad'aya ai kuwa mahaifiyarta tace sai dai ta hakura gabad'aya, suna cikin wannan hali Alhaji realwan ya kawowa d'an'uwansa ziyara da yammacin ranar , domin tautaunawa akan kasuwancinsu na kasashen duniya dana nan gida Nigeria, yayi murmushin jin dadi a lokacin daya ji rigimar Afra dan haka bayan ya gama abinda ya kawoshi yace ta shirya kayanta daita zai wuce ran mahaifiyarta bai so ba amman haka ta hakura ta barta dan bazata iya musawa alhaji realwan ba Suna isa gidan tun daga haraban gidan take ihun kiran sunan mufeeda ....
itama mufeeda ta kwaso da gudu da zahra a daf da shigowa parlour'n suka haɗu suka rungume juna cike da murna ganin junansu suka karaso parlou'n suka zauna akan kujera suna maida numfashi mufida ta riko hannuta "afra zo muje dakinmu ki ga yadda dady ya gyara mana an canza mana komai dake cikin dakinmu ".
"Kai dan Allah ta fada tana mikewa tsaye ba dan taso ba sai dan damuwar da mufeeda tayi daita dan jininsu ya hadu sosai ."
rike hannun Afra mufeeda tayi har suka shiga dakin sannan ta saki hannunta "wooooowwww kai amman dakin ya qara kyau sosai anan zan zauna dan nazo kenan Bazan koma ba sai dai kai ziyara "dan Allah da gaske kike "?"Allah kuwa take mufeeda ta rungumeta ajikinta suka faɗa saman katifa suna murna komai na dakin milk colour ne Sai wordrobe da akayi musu mai ruwan chocolate colour , suna rungume da juna zahra ta shigo d'akin "idan kun gama rungume juna ku gabatar da sallah kuzo muci abinci ". "okay suka hada baki gurin fadar haka sannan suka shiga bayi tare Afra na tambayar mufida "ni kuwa ina wannan dan tsintuwar ban ganshi ba".? "Mummuy ta aikesa amman kinsansa babu wasa bare bata lokaci yanzu zaki gansa ya dawo "na so ace yana nan na soma guma masa wahalalle kawai ta karasa maganar tana kwashewa da dariya "dan Allah ki fitar harkarsa baki ga shi ko kallonki baya son yi ba"
"Kar ya kalleni mana Shima yasan abinda zai faru idan na kama shi yana kallona ". bayan sun gabatar da sallah suka fito tare dakin mumy ta shiga ta gaisheta ta fito rungume da Kisna suka fara cin abinci jollof din shinkafa ce wacce taji kayan hadi suna gama ci ta kwanta akan doguwar kujera ta daura Kisna a ruwan cikinta can bayan kamar minti goma ta mike ta koma daki daga kwanciya naunauyen bacci ya ɗauketa ."
Kamar yadda mumy ta fadawa muradi akan kar ya nuna kanshi hakan ce kuwa ta kasance duk inda zai ga Bature da garba baya kallonsu har ya kara girma yayi wayo basu san muradi yana gurin mumy ba a tunaninsu yana hannun yan fashi ....
Bayan shekara biyar
Sai ga sadiq yazo Lagos tare da mai gidansa domin yin aikin panapiter a matuwaf bayan ya gama abinda ya kawoshi gidan Alhaji Garba ya shiga nema ta hanyar address dinsa daya amsa dan tun a ilo yace idan ya gama abinda ya kawoshi a gidan takwaransa zai sauka idan ya huta sai ya nemi inda muradi yake , bai zo da wata mummunar shiga ko wani mugun yanayi ba tsab abunshi ga tsananin kamarsa da mahaifinsa daya sake bayyana yatsun kafafunsa ne kawai na mahaifiyarsa sabanin muradi da komai na haroon ya dauko sai bambanci halaiya kallo daya matar Alhaji garba rabi tayi masa tasan dan haroon ne ta tarbeshi cike da kulawa ta bashi abinci bayan yaci yayi wanka.
lokacin da yaran gidan suka dawo daga makaranta ta shiga nuna musu sadiq "ga takwaran babanku yazo daga ilo yaran ma sukayi murna sosai da ganinsa sai dai akwana daya sadiq ya raina kanshi dan fatata Alhaji garba yayi masa "me ya kawo ka gurina ? kan sadiq a sunkuye yace "nazo wani aiki ne a matuwaf nace nazo mu gaisa daga nan na ...."dakata dakata banason jin dogon bayani tashi ka bar min gida kar na kara ganinka a kofar gidana bare a cikin gidana dan halak ma yan fashi sunyi gaba dashi bare kai dan gaba da fatiha maza ka koma inda ka fito bama nemanka ko ka tafi gurin wannan ɗan iskan ubannaka hjy rabi tayi ta ƙoƙarin hana alhj garba abinda yake kokarin aikatawa amman yace sam bai yarda ba sadiq bazai kara ko second daya a gidansa ba ....
a kofar gida sadiq ya hadu da Abubakar yace "ina kuma zaka da jaka ? ya tambayesa yana kallonsa goye da jaka "zan koma inda na fito ne ko kasan gidan mama salaha "? Abubakar ya daga masa kai "yauwa na gode sosai dan Allah bari na baka wani sako jakarsa ya bude ya ciro diary din mahaifiyarsu da yayi cel d'insa da takarda mai ruwan kasa "dan Allah ka bawa Aliyu "Abubakar yayi shiru yana tunanin waye Aliyu a gidan mumy salaha ya gama tunaninsa tsab bai gano wanda yake nufi ba "gaskiya bansan aliyu a gidan ba "muradi fa dan ana kiransa da muradin hajiya kayi "eh nasan muradi kana nufin kaninka ne muradi ? sadiq yayi murmushi yace "eh dan allah ka taimakeni ka bashi wannan sakon naso zuwa da kaina amman ina jin tsoro kar naje can ma a koreni kamar yadda aka min nan yayi maganar a gaugauce "Abubakar ya girgiza masa kai "mumy bazata koreka ba ka bari zan kaika gidan "a'a na gode sosai ba sai naje ba zan je matuwaf nabi motar da muka zo dashi zuwa ilo ya mika masa ya wuce abubakar ya bi bayansa da kallo cike da jin tausayinsa kamar yayi kuka shi dai yana ganin muradi a gidan mumy salaha amman bai taba sanin dan kanin mahaifinsu bane sai yanzu ya dauka dan family mijinta ne , shiga cikin gidan yayi inda mahaifinsa ke bala'in da kunfar baki ",haba baba me yasa zaka koresa bayan jininka ne yanzu kasan inda zashi daka koresa ..?"dan Allah kace ya dawo ya zauna anan tunda ma dan'uwansa na gidan mumy Alhaji garba yayi tsuru tsuru yana kallonsa cike da mamaki "yanzu sai da salaha ta nemo yaron nan ai shi tunda akace ya bace yayi hamdala sun rage iri gyada kai yayi sannan ya shige dakinsa "gaskiya anya abinda baba yayi bai da kyau "kai ma karamin yaro kasan bai da kyau bareni na rasa me yasa babanku yake yin haka ? a ranar Abubakar yaje gidan mumy sai dai bai nemi muradi ba ya bawa mumy sakon sadiq sannan ya koro mata duk abinda mahaifinsu yayiwa Sadiq ta fashe da kuka tana cewa "wayyo Allah me yasa baka kawo min shi ba " sadiq din ne yaji tsoron zuwa tace karku koresa amman yace min matuf zashi d'ago kanta tayi sai ganin muradi tayi tsaye a gabanta idanunsa sunyi jawur alamu sun gama nuna mata yaji komai ta yafitoshi da hannunta sai dai zuciyarsa yazo wuya ya kasa daga kafafunsa ,hawaye ne ya shiga zubo masa yana son dan'uwansa shi kadai yake da yakinin yin rayuwa dashi tunda har wannan lokacin bashi da labarin mahaifiyarsu ko ma wanda yasan inda yake basu sani ba mumy ta mike ta kamo shi ta nufi ɗakinta dashi ta zaunar dashi tana karfafa masa gwiwa akan rayuwa "ka zama mutumin kirki muradi domin bawa wasu kunya kada dauki dabiar mahaifinka ka jajirce a rayuwa duk haroon ne ya jawo wa sadiq wannan rayuwa gashi bansan inda mahaifiyarku take ba wallahi da ni da kaina zan nemota kayi hakuri kaji kuka take shima yana yi ta mika masa sakon sadiq ya amsa ya kamkame ajikinsa yana cigaba da kuka yana mai tsanani tausayin dan'uwansa Gara shi yanzu mumy zata masa komai shi kuma tun farko shine yaki da yanzu suna tare ranar wuni yayi da dacin rai tare da kewar mahaifiyarsa da dan'uwansa "..
A hankali muradi ya cigaba da