Showing 426001 words to 429000 words out of 495987 words

Chapter 143 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

duk abinda ya zuba a bangarenta sai da uwarta tasa aka fitar dashi aka saka wanda suka yi mata order ,ai kuma tana jin a nan gidan nawal zata zauna sai tayi wata biyar sannan ta biyosa cairo nan fa sabon bala'i ya tashi ke in takaice miki sai da nawal tayi mata kuka sannan ta hakura haka ta karaci fadanta tayi shiru amman muradi yace bai canza ra'ayinsa dan tun kafin su kawo wannan matsayin ya sheidawa nawal din wannan kuskurenta ne da bata sheidawa iyayenta ba , dana masa magana cewa yayi na barshi kawai ai tunda suka nuna basa son zamanta a gidan nan tare dani sai ta zauna ko kuma a fasa auren gbdy ."

naunayen ajiyar zuciya kisna ta sauke tana kallon mumy tare da sakin kasalallen murmushi ta matso kusa da mumy sosai "mumy a she kunga tashin hankali? ,ba kaɗan ba mamana ,yanzu jiya ma sai da kanwar uwarta ta kirani a waya wai a fad'awa muradi bangaren nawal din yayi musu kaɗan su gaskiya gidan suke bukata gbdy shine nake jiran idan ya huta zuwa gobe zan masa maganar ,abar musu gidan gbdy ke sai ki zauna a tsohon gidanku idan an gama biki " mumy ta k'arasa maganar cikin rauni "ni dai Allah yasa karsu rabani d'ana shi yasa nake son ki kwantar da kai kiyi hakuri ki rikeshi da kyau , ladabi da bibiya tsafta da kwaliya mai daukar hankali iya girki nawal bata fiki komai ba hasalima kin fita mamana , ki rike mijinki da kyau karki yarda kiyi sakacin da zaki rasashi , muddin muradi ya bar hannunki ya bar hannuna kisna , ina tsananin son muradi son da ban san yadda zan misalta miki ba , bazan juri a rabani dashi ba dan zan iya shiga mummunar hali muddin aka rabani dashi ."mumy ta gama magana jikinta a sanyaye matuka ."

naunayen ajiyar zuciya muradi dake tsaye a bakin kofar d'akin ya sauke daman zai shigo ne dan yi mata sallama yaji suna magana har zai juya sai kunnuwansa suka jiyo masa maganar mumy akan kanwar maman nawal , sosai hankalinsa ya tashi Idanunshi suka kada suka jajir sannan suka cika da ruwan hawaye tsabar bakinciki "nima ina sonki mumy , kuma inshallahu babu macen data isa ta rabamu muna tare muddin rai "ko yanzu sakon ya iso gareni kuma zan dauki mataki akai bazan yarda a tozarta min ke ba, ya cigaba da tsayuwa cikin tsananin damuwa da tashin hankali kafafunsa suka masa nauyi , gbdy yaji auren nawal ya fita akansa tamkar yace ya fasa .. "kisna karki yarda ki fito da kishinki fili kamar yadda na fada miki tun kafin kizo kasar nan, banason kiyi abinda za'a yi Allah wadai dake ,ki danne duk abinda zaki ji komai mai wucewa ne "inshallahu mumy bazan baki kunya ba zanyi duk abinda kike so " , muradi ya juya a hankali yana daga kafafunsa da kyar zuciyarsa banda tuttukin bakincikin babu abinda take , sun dade suna tautaunawa kafin daga bacci barawo ya kwashesu ." Muradi
na isa gida ya kira number nawal dan yaci mata mutunci ,ya kara fahimtar daita shi din ba sokon namiji bane yadda ya tsara gidansa haka yake so kada wanda ya canza masa tsari sai dai Kira kusan uku yayi mata bata dauka ba dan haka ya hakura da zumar gobe zai je gidan da kansa zuciyarsa na zafi ya kwanta sai dai ya kasa runtsawa saboda tsananin tausayin mumynsa da kisna ya dade kwance yana tunanin kisna ya fara missing abubuwan da take masa da suna tare da yanzu tana makale ajikinsa tana wasa da sansar jikinsa jiki a sanyaye ya janyo pillow ya matse ajikinsa gam yana furzar da iska mai zafi ,ita kuwa nawal tana sane taki daukar kiransa saboda haushin ya sauka a kasar tun a wanni takwas da suka gabata bai kirata ba ..

washegari tun da asuban fari ya shigo gidan mumy sakamakon rashin natsuwar zuciya da tunanin kisna ya kwanta , kai tsaye d'akin mumy ya nufa yaci sa'ar bai isketa ba sai kisna ya gani kwance akan gado ta lullube jikinta da bargo mai taushi iya fuskarta kawai ta bari , ya karaso Idanunshi na kanta ya zauna a bakin gado tare da tsura mata Idanunshi tsawon lokaci ya ɗauka yana kallonta batare data sani ba ya lumshe Idanunshi ya bude a hankali yana jin wani irin yanayi mai zafi akanta bai san sanda ya yayi kasa da bargon ba "ya subhanallah ya furta a kasan makoshi sakamakon ganinta cikin kayan bacci wacce ta bayyana qirjinta , kisna ba dai kyan jiki ba , yaji kamar ya kai hannunsa ya soma shafa dukiyar fulaninta amman ya kasa ya zarce da riko laulausan tafin hannunta ya matse gam cikin nashi tare da runtse ido yana kokarin ya kice fargaban nuna mata irin qaunar da yake mata a hankali ta bude idanuwanta akan kyakkwar fuskarsa tana masa kallon mamaki saboda bata taɓa kawowa zuciyarta hakan ba kokarin tashi ta fara yi ya kai hannuwansa jikinta ya kwantar daita tare da girgiza mata kai alamun ta cigaba da baccinta still Idanunshi na kanta, ya kai hannu ya shafa gefen fuskarta yana lumshe mata Idanunshi masu rikirkita mata lissafi mamaki ne ya kamata ganin yadda yake kallonta tamkar ranar ya fara ganinta a hankali ta furta "world best are you okay ?, lumshe mata ido yayi kawai tare da dage mata girarsa daya yana shafa wuyanta zuwa qirjinta dake cike da dukiyar fulanin wadan da basu da niyyar faduwa ."

muryarsa a kasalance yace "ki ci-gaba da baccinki babu komai na shigo naga yadda kika tashi ne "ya rabbi koda mafarki nake ?,ta furta hakan a ranta tana murza idanunta gaba-daya ta kasa boye mamakinta hakan yasa ya sake damke hannunta yana sakar mata tautausan murmushinsa mai kashe jiki da bugar da zuciya hannunta ya kai bakinsa ya shiga sumbata , ta lumshe idanunta "wayyyohhly Allah ,ya Allah idan mafarki nake karka farka dani daga wannan kyakkyawan mafarkin ta furta a fili cikin siririyar muryarta jin abinda tace ya yaye bargon gbdy ya shige ciki ya kwanta yana fuskantarta tare da janyota jikinsa zuciyarsa na bugawa da karfi akanta ya matseta gam yana runtse idanunsa yana jin dumin jikinta kusan minti biyu tana matse ajikinsa sannan ya sausauta rungumar da yayi mata a daidai lokacin ta bude idanunta ta zuba masa kwayar idanunta dake cike da rauni taga Idanunshi a rufe suke ruf tamkar mai yin bacci shigewa jikinsa tayi sosai tare da daura hannunta akan qirjinsa daidai kan nipples dinsa tun bata kai ga murzawa ba jikinsa ya soma sheking ya dinga jin kamar an jonasa da wutar lantarki."

yayi shiru yana sauke numfashi har lokacin gani take tamkar mafarki take ba gaskiya bane , hannunta dake kan qirjinsa ta soma yawo dashi ajikinsa addu'a yake Allah yasa karta kai ga murza kan nipples dinsa dan muddin tayi haka komai zai iya faruwa dashi a dakin mamansa , ita kuwa gaba-daya hankalinta yaki kwanciya sam bata yarda ba ,gani take mafarki take yi dashi , dan haka ta gyara kwanciyarta ta koma bacci canzawar numfashinta yasa ya fahimci ta koma bacci , ya mike ya sauko yana daidaita natsuwarsa sannan ya fita a dakin ya wuce gida bai sake neman nawal a waya ba haka zalika itama bata nemeshi ba nan ya sake kufula zuciyarsac tazo wuya dan yasan taga missed call dinsa ."

Kisna ba ta farka ba sai gurin goma na safe sai dai bata fito ba ta cigaba da kwanciya akan katifa tana tunanin abinda ya faru a tsakaninta da muradi wanda ta kasa gasgantashi ," shin gaske ne shine yazo mata a zahiri ko kuwa mafarki ne ? tana nan kwance a d'akin mumy hayaniyar yan'uwanta data soma jiyowa ne yasa ta sauko ta dauki hijabi dinta ta zura ta fito falo suna ganinta suka hau murna dan dai Allah ya jarabesu da tsananin qaunarta itama babu abinda take sai murna ganinsu saman kujera ta zauna daya bayan suka gaisa ta maida idanunta kan muradi qirjinta na bugawa da matsanancin karfi abinda ya faru ya sake dawo mata "kai bashi bane mafarki ne yaushe zai wani bata lokacinsa mutumin da babu abinda bata masa dan karkato da hankalinsa gareta amman yaki hasalima nunawa yake tamkar bashi da feelings , mikewa tayi a hankali ta nufi doguwar kujerar da yake zaune yana cin pepe soup na kaza da ruwan tea , yayi kamar bai ganta ba muryata a hankali ta fito "ina yini world best ?'ki duba lokacin har yanzu muna safiya ya faɗa fuskarshi a yatsine ta zuba masa ido zuciyarta na bugawa da sauri sauri bata ankara ba taji ya janyota jikinsa yace "zauna kici abinci dan nasan baki karya ba har yanzu ,yanzu kam zata iya gasganta abinda ya faru a tsakaninsu idanun jama'a dake falon ya koma garesu, nan take taji wata irin kunya from no where ta rufeta shi kuwa ko ajikinsa dan ko kallon inda suke bai yi ba ta gyara zamanta tana cewa "a koshe nake ya kai bakinsa cikin kunnenta wanda a zahiri zaka dauka magana yake mata amman abun ba haka bane iskan bakinsa kawai yake busa mata wanda ya haddasa wa jikinta mutuwa tsigar jikinta suka dinga mikewa gbdy ta maida tunaninta kanshi ta mance inda take, kallonsa tayi taga Idanunshi akanta .
gbdy mutanen dake falon suka sa dariya samir yace"easy fa dan'uwa karka manta inda kake kana gaban surukanka ne "naunayen ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "me kuma nayi ?, sannan su waye surukain nawa ?,nan duk yan'uwana ne dan haka karka dameni, sabuwar hira ce ta barke tsakaninsu aunty ummi ta kalli kisna tace "zamu sabon gidanku tun da'aka bude bamu je ba ko zaki kafin ku tare ? da kamar tace bazata ba sai taga zasu iya daukar abun wani iri dan haka tace "shikenan bari naje nayi wanka kafin na dawo kuma kun gama shiryawa "wani shiryawa zamuyi ai mu a shiryenmu muke ke dai jeki shirya bari na shiga naga aunty rukayya jiki a sanyaye kisna ta mike taje tayi wanka ta sako doguwar riga milk colour mai dogon hannu tayi rolling kanta da mayafin rigar tayi kyau sosai kamar ka sureta ka gudu falon ta sake dawowa inda ta iske granny tazo suna hira dasu muradi tana ganin kisna tace "sannnu alankosa "ke tsohowa kinzo kenan da mita "babu wani mita ke wacce irin matace miji ma yaci abinci bazaki zo ki dauke masa kwanu ba? , kisna tasa dariya "naga alamar tsohuwar nan sai na miki da gaske zaki sakar min mara to aike zan maida mai wanke wankenmu shiyasa naki kwashewa yanzu ma ki tashi ki kwashe kije ki wanke ,granny ta kalli muradi "kaji abinda wannan sokuwar matartaka take cewa dan rashin kunya to kuwa zan sa muradi ya gyara min zamanki daman ga amarya nan shigowa zaki gane baki da wayo ,"kinji tsohuwa da wahala ni ina ruwana da wata amarya ko ajikina dan daita da babu duk daya ne agurina mijina ne a gabana ta karasa maganar tana dariya muradi ya ɗan d'ago ya kalleta qirjinsa na bugawa "anya ma kuwa ba yaudari kanshi yake ba daya amincewa zuciyarsa tana son shi ?'idan mutun yana son abu ai dole yana kishinsa amman ita kalleta ko ajikinta, koda yake ai mumy tace karta nuna tana kishinta wata killa shiyasa ta fadi haka tuno haka yasa zuciyarsa ta samu natsuwa ."

"ai kuwa zan kwance mijin gbdy tunda kinfi sonshi da kowa "aha kungan min tsohuwa da kishi to shi me zai yi da tsohuwa world best ko kana sonta ? ta juya tambayesa tana tsaresa da idanunta masu rikirkita masa lissafi ya girgiza mata kai alamun a'a "me zanyi da wata tsohuwa yaro ai sai da yarinya tsoho sai da tsohuwa gaba-daya suka kwashe da dariya mufeeda tace " kamin dade granny sai a daina zakewa ko "Inna lillahi Kai da kanka muradi kake fadar haka ? Inji cewar granny tana marairaice fuska
,yanzu har munzo lokacin da zaka shigarwa wannan jairar to bari nayi maza na kama gabana tun kafin ku taru ku min dukan tsiya daman saboda kai nazo tunda yanzu kafi son matarka dani nayi nan ta yunkura zata mike muradi yayi saurin cewa "no no hajiyata da wasa fa nake ai kece sarauniyar mata , kinyiwa kowace mace zarra a zuciyarta Allah dai ya qara miki lafiya da nisan kwana "ameen muradi Allah yayi maka albarka ya albarkaci zuriarka "ameen hajiyata suna cikin hirar aunty ummi ta katsesu "to muje muyi sauri kusan akwai abubuwan da zamuyi idan mun dawo gabadayansu suka nufi haraban gidan suka bubbude mota suka shiga kai tsaye sai doping estate mai gadi yana ganinsu ya bude musu tafkeken get din gidan dakeansu suka shiga sukayi perking suka fito daya bayan daya. shiru kisna tayi tana kallon haraban gidan tunda ga nan zaka fahimci yadda muradi ya kashewa gidan kudi lallai gidan yayi kyau sosai har ya zarta yadda mumy ta bata labari babu inda basu shiga ba sai bangaren nawal wanda ke kulle kuma mukulli na hannunsu suka zagaya ko'ina babu abinda ya dauki hankalinta kamar gurin guym da gurin wasan yara swiminpool komai dai masha Allah suna tafiya suna hira acikin gidan aunty ummi ta kalli kisna "ke kisna ni kuwa ina son tambayarki ,kisna ta tattara hankalinta gareta tare da cewa "ina jinki ".

" wai meke faruwa a tsakaninki da uwar dakinki naga tun jiya da kika sauka a kasar nan bata zo ba anya kuwa lafiya?, kuma yanzu sam bakya maganarta irin da , shiru kisna tayi tare da lumshe idanunta dan ta fahimci wacce aunty ummi take nufi, sosai hankalinta ya koma kan abinda aunty afra taso mata Allah ya kubutar daita yanzu haka data tuno hankalinta yayi matukar tashi gabanta ya shiga faduwa muryarta a tsarke tace "aunty ummi dan Allah karki kara min maganarta dan ko mai sunanta banason ji , tana gama fadar haka su mufeeda suka karaso gurin "lallai akwai gagarumin abinda ya faru ba kuwa zanyi shiru ba ana gama bikin nan dole na hadaku naji abinda ya hada uwar daki da yar daki su mufeeda suka sa dariya ban da kisna da gabanta ke dukan uku uku sai gurin karfe biyu saura suka dawo gida lokacin gidan ya cika da mutane yan kai kayan an bubbude akwatina ana ganin kaya Kai tsaye daki kisna ta shiga ta kwanta , karfe hudu daidai Aunty rukayya ta shigo dakin tana cewa "auta kwanciya kika yi bazakije kai lafe bane ?,gaskiya da wahala bazani ko'ina ba ,ke kuwa da kinje meye aciki ai hakan ma zai sa su fahimci baki da mu da auren ba "koma ma me zasu fahimta su suka sani babu inda zani aunty rukayya ta juya ta fice daga dakin ita kuma ta mike ta shige bayi domin dauro alwala . "
Karfe biyar daidai suka tafi kai kayan lefe na gani na fada acikin hadaddiyar motar latest ferari sabuwa dal zuwa gidansu nawal , komai na girma akayi haka suma an mutuntasu yadda ya kamata mahaifiyar nawal taso taga fuskar mumy ,dan tun da taji ance ba itace uwarsa ba tasan dole za'a daita dan cike take da haushinta gani take kamar itace ta bukaci nawal din ta zauna daita sai dai akayi rashin Sa'a bata zo ba , iyakacin manya kawayenta ne da wasu daga cikin yan'uwan mijinta sai hajiya rabi dasu aunty ummi .

Tsawon kwana biyu kenan muradi bai sanya kisna a cikin Idanunshi ba tun washegari ranar da suka zo haka nan yaji abun ya tsaya masa arai sai dai ya basar ya cigaba lamuran gabansa ,
bangarenta itama bata samu zama ba cikin sauri ta nufi dakin mumy wanka tayi ta fito sannan ta tsara kwaliya mai kyau cikin kayan da mumy ta dinka mata wayarta ta dauko ta duba saboda tana bathroom taji karar sautinta ta dauka ta duba taga har 10 missed calls babu suna kamar karta ta kira sai tayi tunanin ta kira taji ko waye dan haka tabi number ,ana dauka aka fara da mita "haba kisna meye rayuwar duniya baki neman mutane wallahi da ace ina da numberki da tunin na nemeki "tayi murmushi sakamakon fahimtar ko wacece mai maganar tare da sakin wani ihun murna tace" allah sarki basma wallahi na canza waya ne tun lokacin baya daga baya abubuwa sukai ta faruwa dani nayi missing komai nawa shiyasa bancin haka ai kinsan dole zan nemeku tunda bani da wasu kawayen da suka fiku ".
"Haka ne duk naji abinda ya faru dake lokacin bana kasar dana dawo nayita neman numberki ban sameki ba in takaice miki har gidanku nazo ban iske kowa ba sai masu ainkinku , na dade ina neman numberki ban samu ba sai dazu naga yayanki madu shine na amsa ya shekaru daya ya yarana suke ?,duk muna lafiya ya nawa yaran suke ? tam gamu dai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login