Showing 318001 words to 321000 words out of 495987 words

Chapter 107 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

kara ta kuma kwallawa muradi dake zaune still a parlour ya shigo d'akin da sauri "ya Allah "ya furta saboda ganin ta sake sumewa bai tsaya wata wata ba ya sureta ya sata a mota zuwa asibiti ba karamin rudewa yayi ba ganin yadda ta dawo kamar bata da rai cikin kulawa nus suka amsheta zuwa ciki, Dr Hafsat balarabe ce ta soma ƙoƙarin dubata bayan ta gama dubata ne ta fito ta nufi office dinta muradi ya biyota zuciyarsa na tsinkewa cike da nadama dan bai san lamarin zai kai da haka ba , yaja kujera ya zauna a gabanta yana fuskantar likita "ko zaka iya tuna abinda ya firgitata ? Yayi saurin cewa "eh "ta d'ago tana kallonsa tare da neman ƙarin bayani batare da bata lokaci ba ya fada mata komai girgiza kai kawai tayi sannan tace "to a gaskiya dai tayi doguwar suma amman inshallahu zuwa nan da wani lokaci zata farka muradi yace "na gode tare suka sake fitowa suka shiga dakin da Kisna take kwance likitan ta isa inda Kisna take kamar wacce ta mutu ta sake dubata ta fita shi kuma ya tsura mata Idanunshi sai tausayinta ya kamashi haka ya tasa gaba yana kallonta zaune a bakin gadon da take kwance hannunsa rike da waya, sai wajen asuba ta farka shi bai ma sani ba sai daya d'ago suka hada ido yace "sannu"Ta kawar da kanta taki kallonsa sannan taki amsawa koda likita taga babu abinda ke damunta ta sallameta suka koma gida ya fito daga mazaunin direba yana kokarin zagayowa ya bude mata kofa ta fito ya kai hannu zai rikota ta goce tana buge masa sannu "dan Allah malam banason shishigi ance maka bazan iya tafiya bane da zaka wani rike min jiki salon kaji dadi "ta k'arasa maganar tana jan tsaki ..

shiru yayi yana kallonta a ransa yace "me kuma yayi sauri ba rike hannu ba jikin ma gaba-daya na gani karewar rike hannu ta sake jan tsaki tayi gaba ta barshi , juyawa yayi ya fita daga get din gidan ya shiga bangaren Samir ya fada masa a asibiti suka kwana sai dai bai fada masa dalilin zuwan nasu ba zee tace "ai da ka tashemu mun tafi tare ,ita kuwa Kisna bedroom din muradi ta shiga dan tsananin tsoro ya hanata ko kallon kofar ɗakinta ta watsa ruwa ta kwanta akan gadonsa tana sauke numfashi saboda kamshin turarensa daya kaiwa hancinta ziyara tana kwance tana karewa dakin kallo zee ta shigo ta kawo mata tea mai madara ta sha tana zaune byn ta sha suna hira da zee muradi ya shigo ya zauna a gabanta ta yatsina fuska tana kawar da fuskarta gefe zee ta mike ta fita, shi kuma ya tsura mata ido kamar me tunani wani abu can ya bude baki cikin sanyayyiyar muryarshi yace "ki tashi ki koma d'akinki dan..."tun bai k'arasa maganarsa ba ta dakatar da shi tare da mikewa ta sauko ta tsaya a gabansa tana masa kallon sama da kasa sannan tace "Allah yasa gidan ma dungurungun na ubana ne bare wani d'akin banza , kai ne maye gidan to abunka da ba'a saba ba ba'a gaji arziki ba an samu daga samu za'a damu mutane " tana gama fadar haka ta fice daga d'akin tana ja masa tsaki , sai dai tana isa falo qirjinta ya dinga bugawa da karfi dan wani sabon tsoro ne ya bijiro mata sadaf sadaf ta soma tafiya kamar wata barauniya ta tura kofar ɗakinta tana kallon cikin dakin bata ga komai ba dan haka ta kusa gbdy ta shiga ta tsaya daga bakin kofar dakin tana tunani "anya kuwa ba mafarkin kyankyasai nayi ba jiya ?"no tayi saurin girgiza kanta ido da ido fa na gansu suna yawo acikin dakin nan gaba-daya tayi confused ta rasa gane takamaiman gaskiya sai dai ganin har kusan awa daya tana tsaye cikin d'akin bata ga komai ba ta ɗan saki jikinta ta fito daga d'akin ta cigaba da abubuwanta sai dai bata yarda tayi zaman dakin ba bini bini tana falo ko kitchen wuni ranar kusan a falo da kitchen tayisa dan ko da zee ta dawo anan ta isketa, suna tare da zee har yamma anan zee tayi girkin dare ta zuba musu nasu ita da muradi a kula ta tattara nata ta koma part dinta , yayinda zuwa lokaci Kisna ta mance da wasu kyankyasai tana jin kiran Sallah magrib ta mike ta shiga ɗakinta ta cire kaya ta daura towel iya cinyarta ta shiga wanka kamar daren jiya tana fitowa ta sake arba da kyankyasai sai farrrrrr suke a bangon d'akin wani razannaniyar ƙara ta saki ta fito daga d'akin da gudu zuwa parlour inda muradi yake zaune zaman jiran yaji yau kuma me ya korota gabansa ta k'arasa ta tsaya dafe da qirjinta ,
tsura mata Idanunshi yayi ganin yadda surar jikinta suka bayyana ga rabin tsayayyun brest dinta sun yi hake hake a saman qirjinta sai sheke suke , ya runtse Idanunshi yana shafa goshinsa muryarta a tsarke tace "kaje ka fitar min da wad'ancan kyankyasai a d'akina suna can kamar kudin cizo " ajiyar zuciya ya sauke ya bude Idanunshi fesss akanta yana mata wani kallo rainin hankali sannan ya mike ya nufi d'akinsa ya barta nan tsaye ai da gudu ta biyo bayansa tana kuka "wallahi bazan iya kwana a d'akin ba ka bani aron d'akinka na kwana kai kuma ka kwana a parlour da mamaki ya tsaya a tsakiyar d'akin yana kallonta da jallabiya sanye ajikinsa ya cire jallabiyar ya ajiye ya saura daga shi sai farar vest da gajeren wando iya cinyarsa "idan zaki kwana ki kwana anan ko parlour bazan hanaki ba amman batun na baki daki wannan ne kuma baki isa ba dan babu wani daki da zan baki aro na koma parlour kafin ya sake yin wata magana ta juya a fusace taja masa kofar da karfi gim ta rufe yabi kofar da kallo yana murmushin mugunta ,
ko cikakken second biyu batayi ba sai gata ta sake dawowa a gigice ta maida kofar ta rufesu tana haki ...."

a hankali ta jingina bayanta da jikin kofar kwakume da towel a qirjinta ",ni dai ina ganin gara na kwana anan din dan har parlour'n ma kyankyasai ne wallahi "duk yadda kika gani" ya faɗa yana d'aga mata kafad'a tare da hayewa kan gado ya kwanta abunsa yana kallonta ta gefen ido yana shafa qirjinsa zuwa kasan mararsa , ahankali bacci ya dauke shi tana ganin haka ta lalla'bo ta kwanta ajikinsa tare da takure jikinta waje daya ta dade kwance ajikinsa batare da bacci ya d'auketa ba sai gurin karfe daya bacci ya fixgeta a hankali ya farka ya ganta makale dashi tana fuskartashi yayinda towel din jikinta da take kwakume dashi ya ɗan zame saman brest din masu haske suka bayyana take jijiyarsa tayi wani irin tsalle ta cika sambal, kallonta yayi kawai yana girgiza kai sannan ya sauko ya shafa jijiyarsa ya gyara mata kwanciya ya shiga bathroom, wanka da alwala yayi ya fito ya dauki jallabiyarsa ya zura kan boxes dinsa ya tada sallah ya dade zaune bayan ya idar da Sallah yana kaiwa Allah kukansa cikin bacci ta soma magana a gigice tana kiran wayyyohhly zan mutu gasu nan zan mutu " sai acikin kunneshi a natse ya mike ya k'araso inda take ya kunna wuta mai haske yana jan gajeren tsaki ya janyota jikinsa "Malama ki yi addu'a duk kin cikawa mutane kunne addu'a ya shiga tofa mata dan gaba-daya a tsorace take cikin kankanin lokaci ta dan samu natsuwa yace ",kwanta a jikina babu mutsu ta kwanta tana kwakumeshi cike da tsoro ranar dai kwana tayi firgita har sai da yayi dayasanin shigo da kyankyasan da yayi ya jawota jikinsa sosai ya rungumeta tsam yana shafa kanta zuwa gadon bayanta saboda ganin yadda ta rude sai firgita take ,batun jikinta da brest din ma bata takansu dan ga tsayayyun brest dinta nan muraransu yana kallo kan nipples dinta jazur dasu ajiyar zuciya kawai ya dinga saukewa ya runtse idanunsa yana jin wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa ajikinsa gaba-daya duk wani kafa na gashi dake kwance ajikinsa sun mike tsaye yrrrrrrrr ...... ji yake kamar ya kamosu ya tsotsa ko yayi massaging dinsu amman yasan muddin yayi kuskuren yin haka sai wani mummunar bala'i ya samesa gara ya hadiye abinda yaji akanta a haka suka kwana tana makale ajikinsa basu yi wani isashen bacci ba sai bayan asuba bacci ya saceta aiko bai yi shirin zuwa office ba sai daya tabbatar daya fitar da duk kyankyasai sannan yayi filit din d'akin ya fita ya koma d'akinsa yayi wanka ya shirya ya fita office koda ya dawo tana d'akinsa ta kulle .."

Ya murd'a kofar dakin yaji shi a kulle ya tsaya shiru yana kallon kofar da mamaki akan fuskarsa kafin daga baya yayi knowcking ,daga cikin d'akin tace "waye ne ? yace "kizo ki bude min zan dauki wasu abubuwana "bazan iya tashi ba kuma kar adameni sarkin matsala da shishigi kawai sai wani bare bare kakeyi duk ka gama makircinka ka kyaleni mugun nufinka akanka zai kare ta karashe maganar tana jan tsaki naunauyen numfashi ya sauke sannan yace "to ki bani dakina ki koma naki na cire miki kyankyasai nayi filit din koina "bafa zan fito ba na bar maka d'akina har abada ka turo min wasu daga cikin kayana ta window dan ni na dawo nan kenan"..


"na shiga uku naga ta kaina na jawo kaina maseefa yanzu kuma irin rayuwar da zanyi kenan ? ya fada a fili sannan ya juya yana shafa goshinsa ta sauko daga kan gado ta dawo bakin kofar dan bashi amsa "baka ga komai ba banza munafukin Allah kawai banda wulakanci duk gidan nan a rasa inda kyankyasai zasu shiga sai dakina ? " wai bama kace zaka sakeni ba uban me kake kira jira har yanzu ? " ka sakeni mana nima na huta da jaraba " rashin mutunci da zagi iri iri ta dinga antayo masa daga cikin d'aki yayi shiru yana kallon kofar dakin
"shi dai yaga ta kanshi ya aurarwa kanshi abinda ya dame shi ,d'akinta ya shiga yayi wanka ya saka wasu kayan dan dama su aunty ummi sun raba kayansa gida biyu wasu na ɗakinta wasu na nashi dakin saboda yawon kayansa ya feshe ilahirin jikinsa da turarenta ya ɗauki jakar computer dinsa ya bar mata gidan gaba-daya bai dawo ba sai wajen tara na dare yana can gidan Samir dan ragewa kanshi damuwa idan kaga Samir ka ga muradi kasan akwai bambancin mai yawa a tsakaninsu saboda yafi shi samun kulawa ta kowani bangaren ,yayi haske yayi kyau sosai kana ganinsa kasan tuni ya dade da angwancewa sabanin shi da kullum cikin matsaloli rayuwa da tashin hankali yake ..."
Yana dawowa gida ya balla kofar ya cicibeta ta saka masa kara tare da cizon bayansa tana ihun "ka saukeni" amman yaki yace "na cire miki komai yanzu babu kyankyasai "
Tace "wallahi a'a ni bazan shiga d'akin ba ka saukeni bazan shiga ba "baki isa ba wallahi tunda na cire miki dolenki ki shiga ina dalili zaki takurawa rayuwata an fada miki nima na damu dake ne ? " Ko ance miki tsoronki nake ji ?" sai daya kaita har ɗakinta ya direta akan gadonta ya fito da sauri kafin ta fito ya shige dakinsa ya kulle tayita bugun kofar da iyakacin karfinta tana kuka tamkar wata marauniya zagi da tsinnuwa kuwa ya sha shi shi dai bai kulata ba har tayi ta gaji daga karshe bacci ya dauketa agurin ."da asuba daya tashi daita yaci karo tana kwance a bakin kofa ta takure jikinta guri daya ya tsaya kawai yana kallonta a ransa yace" iya wahala kawai duk bala'in ki akanki zai kare bazaki kasheni ba , ya kulle kofarsa ya dauketa ya shiga dakinta ya kwantar daita ya wuce massalaci a qalla sai da tayi kwana biyu sannan ta dawo haiyacinta dan har wata doguwar ramar tayi tsabar tsoro da firgici .."

*******
Bayan sati daya

Da misalin ƙarfe uku na ranar juma'a yana zaune cikin motarsa yana driving wayarsa ta dauki kara ya kai Idanunshi kan screen din wayar dake ajiye yaga sunan nasir ne ke yawo dan haka ya danna koren madanin batare daya dauki wayar ba dake Bluetooth na manne a kunneshi "hello nasir ina kan hanya zuwa gida yanzu ka shiga ka jirani ganin nan karasowa "okay Kai da Habib ne to ku shiga mana babu abinda zai faru just give min ten minutes ya fada yana disconnecting din Kiran .nasir ya kalli Habib "Wai mu shiga ciki ni kuma wallahi tsoron shiga nake "muje kawai " suka nufi kofar shiga parlour'n suka tsaya habib ya kai hannu yayi kwonking Kisna dake zaune a parlour tana kallo a zeeworld ta mike da kyar tana cewa "waye ne yayi kwnoking daya ai sai tsaya kou " haka zai cikawa mutane kunne ?" tana buɗe kofar taga nasir da Habib tsaye wani mugun kallo tayi musu sannan tace "uhmmmm me kuma kuka zo yi ?"habib ne yayi karfin halin cewa gurin muradi muka zo Amman gashi nan ..."dakata dan Allah kun dai zo kwadayin da kuka saba kunci ranan nan kunji dadi shine yau ma kuka lallabo kuka sake dawowa to baya nan sai ku juya ku koma inda kuka fito dan yau ko yana nan bazaku ci ba masu kwadayi da leke leke gidajen mutane a haka zaku kare " tunda ta soma magana zufa ke karyo musu gbdy suka rasa abinda zasu ce mata dan bakinciki sai dai gaba-daya ilahirin jikinsu tsuma yake tana cikin magana sai ga motar muradi ya shigo haraban gidan yayi parking ya fito tun daya hangota

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login