Showing 165001 words to 168000 words out of 495987 words

Chapter 56 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

matarsa , tsantsar kamaninsu a bayyane yake ,bakinsa ya soma motsawa bai kai ga fadar abinda yake son fad'i ba hajiya Aysha tace "realwan wannan shine yaron da'ake nema ko "? "Gashi nan na kawoshi sunansa Aliyu ".

Bai ce mata uffan ba ya juya cikin sauri yana magana "barin na kira salaha ta tabbatar da hakan, duk dai kamaninsa ma kawai zai iya fahimtar da mutun shi din wane ne , dawo wa yayi parlou'n rike da hannun salaha ai idanunta na sauka akan Aliyu ta kwace hannunta cikin na Alhaji realwan ta nufi inda Aliyu yake zaune cikin tsananin farinciki , shima Aliyu yana ganinta ya zabura ya mike tsaye ya nufata cikin tsananin farinciki suka rungume juna bai so ya sake daura idanunsa akan wani daya danganci dangin ubansa ba amman hakan nan a yanzu ya tsinci kansa cikin farinciki haduwa da kanwar mahaifinsa ....."
"Alhamdulillah Allah na gode maka daka bayana min muradin hajiya kayi muradina , Aysha babba wacce ake kira da ummi kasancewar sunan Hajiya dataci shekarunta basu wuce sha takwas ba jin Muryar Hajiya ne ya fito daita daga kitchen inda take kokarin daura abinci a tare suka yo suka yo kan mahaifiyarsu ita da Samir da madu har ma dasu mufida cikin tsananin murna suka zube jikin Hajiya salaha suna taya murnar ganin Aliyu ,"mommy shine aliyun da kuke nema ai mun gashi a gidan granny ? suka hada baki gurin fadar haka ,Hajiya salaha ta d'ago kanta tana duban muradi tana sumbatar fuskarsa ......"
murmushi Hajiya Aysha tayi bata yi kokarin yin magana ba,tana son sai sun samu natsuwa sannan tayi magana ,hajiya salaha ta dubi surukarta cikin sansar farinciki sannan ta dubi mijinta ta karashe da sauke idanunta akan Hajiya Aysha tana neman karin bayani "yau kimanin satinsa bakwai kenan agurina marwan ne ya tsintoshi nan ta kwashe komai ta fada musu ban da godiya ga Allah babu abinda mommy take tana shafa kan muradi shima murnarsa taki boyewa sai murmushi yake yace" mummy sauran anyata ina son ganinta "anyanka na ilo itama Allah ya kubutar daita ya lumshe lumtsatsun idanunsa yana sauke ajiyar zuciya "Allah sarki shiyasa tashi farko jininsu ya haɗu da Samir a she jininsu ne Samir ya rike hannu Aliyu cike da murna shima Aliyu ya rike hannunsa ,Kafin kace me mommy ta dawo daidai sai lokacin ta bukaci abinci, ummi ta mike ta shiga Kitchen ta shirya mata abinci ,bayan sun ci har Hajiya Aysha tayi musu sallama har jikin mota suka rakata sai da suka ga tashin motarta sannan suka koma cikin gida ....


Sukusuku ta dawo gidan har washegari bata sake ba tana jin kewar Aliyu a dan kwanakin da yayi mata ,tun daya zo gidan shi ke mata shara gidan gabad'aya wankewanke har ta fara aikensa domin ya soma gane guri tana zaune afra ta shigo parlou'n sanye da wando da riga duk bakake ta tsaya a gaban Hajiya Aysha "salamu alaikum "afra
"Na'am "
"Ya'akayi "?"Lafiya qalau granny yunwa nake ji abinci nake son naci "Afra bana jin dadi shiga Kitchen akwai taliya ki dan bararka kici "
Aysha ta kwa'be baki tana dubanta kafin daga baya tace "granny na gane tunda wannan shegen dan tsintuwar ya bar gidan nan kika daina walwala, jiya ma baki yi mana abinci ba "ke bana jin dadi ne yar taliya zaki bararka kici "ni fa yarinyar ce ban iya dafa komai ba ,kawai kin wani damu akan wannan kazamin yaron ,ni gani nayi ma kamar kin fi son shi akan ni da nake jikarki "shikenan yi hakuri kiyi yau kawai gobe zan dafa miki duk abinda kike son ci amman kar na sake jin kince wa Aliyu kazami ko shege dan tsintuwar,ba tsinto sa akayi ba shi din d'an'uwansu Samir ne yanzu haka yana gidansu "
bata rai "yanzu sai da kika kai musu shege ? Hajiya Aysha ta gyada mata kai alamun "eh " kuma nace karki sake ce masa shege dan halak " amman ai shine yace bashi da uba "kin ci uwarki da wannan maganar kaji min fitannaniyar yarinya mai kwakwar tsiya ina ruwanki ma idan shegen ne ? Afra ta yi shiru tana Kallon Hajiya Aysha zuciyarta cike da haushi "dan yayan maman Samir ne uwa daya uba daya kamar yadda dadynki yake da abbansu Samir "lallai ma granny din nan ta iya girba karya ita da aka tsinci yaro a gabanta sannan yanzu tace mata wai danuwansu Samir ne ta ina take tunanin wannan maganar gaskiya ce ? ta dai maidashi can ne dan tana son yayi rayuwar jin dadi da yanci ,kafafunta ta soma d'agawa a hankali ta shiga Kitchen batare da ta sake cewa komai ba ,sai dai a cikin zuciyarta ta qudurta komawa gidan alhaji realwan dan takurawa rayuwar Aliyu sai ta raba shi da gidan ta kowane hali ,bayan sati daya da komawar Aliyu gidan Alhaji realwan afra ta matsawa iyayenta lallai tana son zuwa gidan alhaji realwan karasa sauran hutunta da yayi saura , da fari mahaifiyarta kin amincewa tayi ganin ai hutun yazo karshe kuma ita bata son tana shigewa dangin mahaifinta dan ko gidan hajiya ma dole ce kawai hakan yasa afra ta daga hankalinta kullum cikin damuwa take kwana take yini tsabar bata samu damar ciwa Aliyu zarafi ba ,ganin damuwarta yasa mahaifiyarta ta amince mata ,sai dai da sharadin hutunta na karewa ta tattaro ta dawo ba sai tayita magana ba idan tayi kwana biyu ta dawo,tayita tsalle tana murna ta nufi d'akinta ta soma shirya kayanta a cikin yar karamar akwati ,ta bude jakar ratayarwata ta kwashe kayan kaliyarta ta zuba powder ailen white lips stick duk ta zuba a cikin mahaifiyarta na siya mata kayan kawaliyata ne kasancewarta babbar diyarta sannan ita kanta tana da tsananin son kawaliya shiyasa ta koyawa diyarta dan haka a shekarun afra ta iya tsara kwakiya sosai ga iya tafiya da rausaya kamar bishiya ,kullum fuskarta cikin kwaliya take an sha dukanta a school akan kwaliya sosai tayi kyau tayiwa mumnynta sallama tare suka jero da mummynta har jikin motar ta rakota tana mata fada" afra ban da rawan kai ki natsu dan Allah kinji ki zauna da kowa lafiya karkiyi tashin hankali da kowa ."naji umma karki damu kinji zan zauna da kowa lafiya Amman ban da wannan kazamin yaron sam bazan raga masa ba tayi murmushi tare da bude mata gidan baya ta shiga ta zauna ta maida murfin ta rufe direbansu ya ja suka bar gidan sai data ga mai gadi ya kulle get din gidan sannan ta juya ta koma cikin gida kai tsaye hanyar gidan Alhaji realwan suka ɗauka tana zaune a bayan mota zuciyarta na shirya mata abinda zata yiwa Aliyu idan taje gida ."

dareban ya sauketa a had'ad'd'en haraban gidan Alhaji realwan tana hakince a bayan mota kamar wata babbar yarinya cikin wani irin yanayi ta lumshe idanunta tana sake zurfafa tunaninta ,turare ta cire a cikin yar karama jakarta ta fesawa a jikinta ta bude murfin mota ta fito a hankali gabanta kawai take kallo tana taku kamar bata son taka kasa tana shiga parloun da Aliyu idanunta suka soma cin karo yana sanye cikin bakaken kaya wonda three quarter da rigar yan kwallo long selve kallo ɗaya suka yiwa juna kowane ya dauke kanshi ,yar farar dake fuskarsa ta ɗauke yana jin babu dadi a ransa dan bai mata da halinta ba ,tabe baki tayi ta samu guri ta hakinance akan daya daga cikin kujerun gidan a daidai lokacin direban ya shigo parlou'n hannunsa rike da akwatin kayanta ya ajiye a gefenta yana kallonta "sai yaushe zan dawo na daukeki '?
"Zan fadawa umma ta fada fuskarta a haɗe ."

tun sanda Afra ta dawo gidan Alhaji realwan Aliyu bai sake samun kwanciyar hankali ba saboda takurawarta bashi da ikon sakewa acikin gidan ,idan kuwa tana guri dole ne ya hakura da gurin ya killace kanshi a daki ko a lambun gidan saboda kallon wulakanci da aibantashi da take a cikin yaran gidan babu wanda bata fadawa a unguwar shi din dan tsintuwa ne kuma shege ne , a duk sanda Samir yaji ta fadi haka sai sunyi rigima daita , wani lokacin ma har da dambe suke yi da Samir yayi mata duka amman hakan baya hana gobe idan taga Aliyu ta furta masa bakar magana wanda shi ko kallon inda take bayayi sannan baya nuna alamun yasan da zamanta ,wani safiyar Lahadi wanda ya kasance weekend ce kuma bai fi sauran kwana uku ta koma gidansu ba ya badamasi daya dawo hutu daga kasar Austaraliya yace su shirya zai kai su shan ice cream Wanda shi saboda Afra ya shirya tafiya dan Allah ya jarabeshi da qaunarta tun haihuwarta ,ta shirya cikin hadaddiyar doguwar riga mai shegen kyau haka ma ummi ta shirya kisna cikin kanana kaya riga pinky da wando baki ta sanya mata takalmin pinky mai kalar kayan ta kama mata gashinta gida shida ta mika wa Aliyu ita "rike min ita muradi naje daki na dawo ya kai hannu ya amshi kisna wacce zuwanta hannunsa ke da wuya ta saka kuka tunda yazo gidan bata yarda dashi daman kuma shegen kiyuwa gareta bata yarda da kowa bayan mamanta sai yan'uwanta shima kuma baya son d'aukarta tunda ta fesa masa zawo ajiki "kinga aunty ummi dake haka yaji suke kiranta dashi bisa koyarwa mummy "Dan Allah amshi yarinyar nan bata son ina d'aukarta "kai dai muradi ka fadi gaskiya na lura dai tun randa aka yi maka wanka zawo kake gudun ɗaukar kisna ". Yatsina fuska yayi yana mika mata ita tana amsarta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya shi kuma ya juya zai bar parloun "wai kai bazaka fita bane naga baka shirya ba? tsaki yaja yace "gaskiya babu inda zani Sai kun dawo bata kawo wa ranta komai ba ta nufi daki ,Koda afra taga kowa acikin motar bata ga Aliyu ba sai taji babu dadi haka nan taji ranta ya ɓaci kamar tace ta fasa zuwa
A daidai haraban shoppright ya badamasi yayi parking motarsa kiran pijo ,daya bayan daya suka sauko ya badamasi , ummi ,Samir Muhammadu wanda suke kira da madu kisna duk ya'yan Hajiya salaha ne sai Zahra da mufeda ya'yan da mumuy ke riko .
a hankali afra ke taku wanda yake kara sa badamasi jin wani iri akanta yarinya ce sai dai Allah yayita da maseefar iyayi da yangar bala'in ,bata tsaya bin ta kan kowa ba ta samu guri ta zauna tana jiran karasowarsu ,sai dai hakan bai faru ba dan shigewa sukayi ciki ,batayi minti goma da zama ba sai ga ya badamasi ya dawo da yar fararsa yace "yar tsohuwar nan tunanin me kike yi haka "?
Yayi maganar yana mika mata abinda tafi so ice cream ta amsa tare da cewa "babu komai a shagwa'be kamar zatayi kuka "hannu ta kai kan itacen tsinke dake ciki ta dibi ice cream ta kai bakinta kamshinsa da gardinsa ya kaiwa kwakwaluwarta lumshe idanunta tayi tana buɗe idanunta suka faɗa cikin na ya badamasi daya tsura mata ido yana kallon kyawawar fuskarta .... "



Mmn sudais
[7/19, 5:32 PM] +234 803 631 5951: 💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Page 27

~TRUE LIFE STORY~

*PAID BOOK*

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

"Wannan  littafin na kudi ne  ,mai bukata karanta shi  zai  tura 500 ta wannan   account number  din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an  tura sai a turawa wannan number alert  +234 803 238 4602   domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne .  "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi  za'a iya tuntu'bar  Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos  lace da kamfala  ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da  chiganvy, volyal lace  duk akan farashi mai sauki ,ga mai  bukatar  siyan ɗaya ko sari  yayi magana ta wannan number 08059623096.


"Mummy ta dawo parlour'n ta iske afra ta cire uniform d'inta tana jujjuya kai ta bita da kallon mamaki sannan tace "ya naga kin cire kayan makaranta ?" cikin marairaicewar muryar tace "kaina ke ciwo mummy "karya take wallahi babu wani kanta dake ciwo , ba tayi assignment d'inta bane ai naji Sanda kike fad'awa mufeeda cewar kin tuna bakiyi assignment d'inki ba Kuma malamin Chemistry bai da mutunci dukan tsiya zai miki shine dan tsabar karya zaki ce kanki ke ciwo " ? inji cewar samir ya fada yana zabga mata harara "wallahi karya yake min mumy da gaske kaina ke ciwo wai ma ina ruwanka dani ne ? " ke mufeeda yaushe na faɗa miki haka ?" Allah mumy ki rabani da Samir idan ba haka ba zamu yiwa junanmu rashin mutunci . "to muyi mana yau muka fara rashin mutunci kece zaki sha wahala mai kan karas kawai ki dai tuba da karya dan Allah ya tsinewa mai karya".

mumy tayi murmushi sannan tace " kai Samir banason jan magana tunda tace kainta na ciwo babu inda zata ku kama hanya ku wuce Allah ya tsare "Mufeeda Zahra da suka wa mumy sallama dan tuni muradi yayi fita mufeeda ta riko hannun kisna nan fa ta fara zillewa itama bazata ba tunda aunty afra bazata ba , mumy tayi rarrashi ta lalla'bata amman taki ,cike da jin haushi Samir ya zuba mata rankwashi a tsakiyar kanta tare da ɗauketa ya rungumeta ajikinsa ya nufi hanyar waje daita ihu ta dinga yi tana kokarin saukowa amman ta kasa ya shiga gidan gaba daita tana rungume a jikinsa yana mintsini gefen cikinta , sauran kuma suka shiga gidan baya direba ya tada mota suka wuce, kisna aka fara saukewa sannan aka wuce dasu .."

Bayan tafiyarsu mummy ta shiga daki ta dauko wa afra maganin ciwon kai ta bata ta sha sannan ta kama sauran aikin gidan da ba'a karasa ba ,daman kuma haka take yi a duk sanda suka wuce school haka zata bi gidan ta sake gyara inda basu yi ba , bayan ta gama ta koma d'akinta tayi wanka ba ita da dawo parlour'n sai karfe ɗaya dan sai datayi sallah inda ta iske afra kwance akan doguwar kujera tayi mata sannu da jiki sannan ta samu guri ta zauna " cikin haka wayar mumy ta ɗauki kara batare data duba ba ta dauki wayar ta kara a kunnenta dan tasan mai kiran duk yanayin da mumy take ciki tana magana dady zai gane , hakan ce ta kasance ma yanzu yana jin muryarta sai daya tunhumeta tace "wallahi gajiya ce kawai , yayi murmushi yace" ko babu gajiya bakya gajiya da washhhhh , gashi kin hana a ɗaukar miki masu aiki ."karka damu aikin gidan nan guda nawa ne , ga yara mata kuma suna iyakacin kokarinsu ,bugu da kari nafi son su iya komai da kansu karsu je gidan miji basu iya komai ba ".

"wannan kuma gaskiya ne ranki shi dade Allah ya saka miki da alkhairi ,daman na kira naji muryarki ne naga shiru baki nemeni ba har yanzu ga aiki ya sani gaba ga rashin jin muryarki ,wannan sabon tayi masa ne tun suna ganinyar quruciyarsu har bisa yanzu da suka dan manyanta ,da zarar ya fita aiki wayarta bata yankewa gurin kiransa ,wani lokacin ma tana aiki waya na nanne da kunneta sun dade suna waya sannan sukayi sallama ta ajiye wayar .afra ta dube mummy tace "Allah sarki mummy dady na ji dake "mummy tace "idan bai ji dani ba da wa zai ji afra? "Biyayya da soyayya ta haifar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login