Showing 60001 words to 63000 words out of 495987 words

Chapter 21 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

sai  faman    ya'bawa   juna  bak'ar  magana  suke   cikin kunar rai  ,
A matukar  fusace  Aliyu  ya  katsewa kisna   hanzarin  "na  fiki  son  rabuwa  dake    mumy  nima  na amince da tsarinta   mu  rabu  kawai  kowa ya huta  ,  dan Allah  mommy  ki  sanyawa  zuciyarki  salama  kiyi   hakuri   ki   bari mu  bar    rayuwar  juna  mu  cigaba  da zumuncinmu   shima   idan  zai  yiwu idan  kuma  bazai   yiwu ba kowa ya kama   kansa  ya fada yana  furzar da iska  mai  zafi  daga  bakinsa , wannan maganar  data  sake dokan kunnuwan mumy  yasa  taji wani  mummunar faduwar  gaba  ya sake ziyartar jikinta , qirjin  mumy  ya  dinga  baguwa  da  tsananin karfi , duk wani tashin  hankalin  da take kokarin dannewa  acikin zuciyarta sai daya fito  fili  saboda  babu abinda ta tsana a rayuwarta  kamar taji  maganar   rabuwa  a  bakin   Aliyu  dan na  kisna mai  sauki  ne  tunda sakin  ba a hannunta   yake  ba ...."

Aliyu  ne  ya fara  lura  da  yadda  jikin mumy   ke   karkarwa  kamar  mazari   yayi   saurin   rikota cikin tsansnin  tashin  hankali  yana kiran sunanta   "mumy !mumy!!! dan  girman  Allah  mumy  ki kwantar  da hankalinki  ".a  hankali   ta kai  hannu  ta dafe daidai  qirjinta  da taji yana mata  wani  irin  zafi  da  bugawa  " Please Karki   min  haka  wallahi bana son na rasaki  bana  son  wani abu ya sameki a dalilin  rabuwata   da kisna  idanunta   suka   fara  rufewa  sakamakon kalmar rabuwar daya sake maimaitawa  "mumy  Please  ki tamaineni ki  bude  idanuki me kike so  ayi  yanzu ? " duk abinda kike so a shirye  nake  zan  miki matukar zai sakaki  farinciki  cikin tsananin tashin  hankali  kisna  take furta mata haka kafin  daga  baya  Aliyu ya kwantar daita  akan katifa  ya  mike cikin sauri  gaba-daya ya  rud'e ya  gigice hawaye sun cika masa kwarnin idanunshi    tamkar  ba wannan  Aliyu   mai karkarfar zuciya ba  ya fita daga d'akin  , itama kisna hankalinta  yayi  matukar tashi dan  kusan  tafi  shi shiga  tashin  hankali,   take  ta fara data sani maganarta da bata furta kalmar su rabu da mumy bata shiga damuwa ba  ,wani  sabon  hawayen   ne  yazo   idanunta ya  fara zuba  akan  kuncinta tamkar an bude fanfo , a  hankali ta  fara rera kuka mai ban tausayi  ,ta sake riƙe hannun mumy  dake  cikin nata gam yayinda hawayenta  yaki tsayawa sai faman kuka  take da  kiran  kalmar  "na shiga uku     cikin  tsananin tashin hankali "mumy  na tuba  bazan sake ba, bazan sake furta kalmar rabuwa da ya Aliyu ba  tunda  bakya  son rabuwarmu , " ki  taimakeni  dan Allah  karki  mutu  ki  barni a gurinki  kawai nake samun farinciki da kwanciyar hankali   idan kika  mutu   kika barni rayuwa  zata min  muni,  sosai take kuka tana rike da hannun mumy itama mumy ta rike hannunta gam hawaye na gangaro mata ... ....."

Zuciyar  Aliyu   na matukar zafi ya dawo   d'akin    hannunsa  rike da goran  ruwa   bai  tsaya tsiyaya  ruwan a cikin cup ba ,ya ɓalle murfin goran da karfi wani zafi yaji ya   ratsa tafin hannunsa inda yaji ciwo  sai dai bai tsaya  kallon tafin hannunsa ba ,ya soma   shafa   ruwa  a fuska mumy  yana kiran sunanta , naunayen  ajiyar zuciya   ta  sauke  sannan ta  dinga sauke  numfashi  a hankali a hankali  "sannu  mumy   suka hada baki gurin furta mata haka da kyar ta gyada musu kai  idanunta  na  runtse   ,Aliyu ya  kamo  kanta  ya  kai goran ruwa bakinta   "ki  sha ruwa mumy  " .
Ta girgiza  masa kai  alamun  bazata sha ba  "dan  Allah mumy  ki rufa  min asiri  ki kwantar da hankalinki  ya kalli  kisna da idanunsa da suka rikice suka canza kala tamkar garwashin wuta  ya soma magana cikin zafin rai  "wallahi   Idan  wani  abu ya same mumy  a  dalilin furucinki bazan taba  yafe miki ba , kuma wallahi  bazan cigaba da zama  dake ba  dole  na yakiceki   ta  karfin tsiya daga jikina  domin nafi bukatar  rayuwa mahaifiyata  akanki  ya karashe maganar yana wurgi da rabon ruwa  ......."
kuka  kisna take sosai tamkar ranta zai  bar gangar jikinta  tana rike da  hannun mumy  Sun yi   matukar  tausayawa   halin da mumy  take ciki  , bazasu iya daukar halin  da zata shiga    a dalilin cikar burinsu  ba .......
Aliyu  ya  mike  da  hanzarin  zai  fita daga  dakin  domin kiran Samir dan sukai mumy asibiti  ta rike  hannunsa ya  dawo da sauri   ya   daura hannunsa  akan nata tare da zubawa mata  idanunshi kamar zai yi kuka  "mumy zanje na kira Samir ne mu kai ki asibiti"  sake  girgiza masa kai tayi    ta  zuba masa ido  cikin sarewa tace "karku  wani  kai ni asibiti alhalin   magani na gida , kune  damuwata muradi , idan zanganku cikin farimciki  da kwamciyar hankali wallahi  nima zan kasance haka"bazan  taɓa   yarda da   tsarinaku  ba  ,rabuwarku  wani babban  tashin  hankali ne  gareni bansan  me yasa nake son kasancewarku   tare da  juna  ba amma kafin na cigaba da magana ku amsa  min wannan tambayar  "?
ta soma yunkurin  mikewa zaune daga   kwance  da take jikinta na daukar zafi  Aliyu da kisna suka kai hannuwansu  da sauri  domin taimaka mata hannun Aliyu  ne  ya riga na Kisna  sauka a gadon bayan mumy sannan  hannunta  ya sauka akan nashi   saurin kallon kwayar  idanun  juna suka  tare da jin    faduwar gaba  mai tsanani zuciyarsu ta dinga bugawa a tare , zuwa wannan lokacin ko'ina ajikin Aliyu rawa  yake  yayinda zuciyarsa ke dokawa  da sauri  sauri fiyye dana Kisna , gabad'aya gabobin jikinsa sun yi sanyi, a hankali Aliyu yayi  saurin janye  kwayar idanunsa  a kanta  itama tayi kokarin dauke hannunta dake  kan nashi    suka  yi shiru  a tare suna  satar  kallon kwayar idanun   juna ,karamin bakinta ta turo masa   tana  kashe  masa idonta  d'aya  ..

abinda tayi ya bala'i  bashi  haushi sosai  and he don't want any dilemma with  her  ko sake kallon inda take bai yi  ba dan gani yake bata damu da halin da mumy take ciki  ba kukan munafurcinta data saba ne  ...
Cikin sanyin  jiki  ya kamo hannu  mommy cikin laulausan tafin hannunsa    tare da matsowa  gefenta sosai  itama  kisna ta  sake matsota  suka sakata a tsakiya  ya d'ago kanshi a hankali ya watsa mata harara itama batayi  sanya a gwiwa ba ta mayar masa  tana murgud'a masa baki yaji  tamkar ya  buge mata  baki ko janyo ta ya  yaryarfa mata maruka masu rai da lafiya   sai dai  ya kasa aiwatar da ko daya  saboda shi a  yanzu babu abinda yafi bukata kamar samun natsuwar mumy muryarsa a ƙausashe yace "malama ki dan matsa can mumy ta  samu wadataccen   iskaa  kin  wani manne  mata kina kokarin ....." 
      "kai ma ka matsa mana cikin ni da kai wa ya hanata shaƙar wadataccen numfashi ?  ta kasheshi tana zabga masa harara  " nifa bana son damuwa dan Allah  kowa yayi lamarin gabansa kawai    zai yi magana mumuy  tayi saurin d'aga masa  hannu alamun yayi shiru umarninta yabi bai sake cewa komai ba ,mommy ta numfasa sannan ta cigaba da magana a tsanake"  banason jin wata magana bayan amsar tambayar da zan muku yanzu  "tsakanin  kai  da  kisna idan  kun rabu  zaku iya  manta   junanku  har duniya  ta nad'e"?shiru  ne ya sake  biyowa  baya , hatra d'akin ya sake  daukar shiru tamkar babu wasu halitta acikinsa  kisna ta d'ago idanunta  a hankali ta kalleshi  dan ganin yanayinsa  wani kallo ya watsa  mata wanda yasa  take hantar cikinta kadawa , ta tabe masa baki  qirjinta  ya  bugawa  da karfin gaske .
"ina  tambayarku kun min  shiru  zaku iya manta  junanku  har abada  ?  Still shiru suka yi suna kallon mommy "Ni nasan bazaku iya manta  junanku  ba  har duniya ta nade da tunanin juna zaku mutu  amman idan amsarku   ta  kasance "eh  zaku iya manta  juna  sai  nasan  abun  yi  ........"

Jin yadda suka yi shiru yasa ta waigo  gefen da Aliyu  yake da gefen da kisna take makale daita tamkar zata mata numfashi  taga  suna kallon juna  tayi murmushi irin nasu na manya   "mai yasa  kuke kallon  juna ku bani amsar  tambayata mana kun  min  shiru  suka sake  yin shiru kowanensu na jiran yaji abinda  d'an'uwansa zai furta  "nasan baza ku iya amsa  min  wannan tambayar  ba bari na faɗa  muku abinda zai sa ku shiga  hankalinku wallahi  muddin kukayi kuskuren barin juna karshenku wahala mai tsanani ,kuma sai ta shafi rayuwar ya'yanku  saboda zaku raba musu hankula , saboda kai  Aliyu wata matar zaka aura kema Kisna  wani mijin zaki aura kuma duk wanda zaki aura bazai kai uban ya'yanki ba ,hakazalika kai ma nawal bazata zama tamkar Kisna agurin su Aryan ba ,da zaran ta samu nata  zata manta dasu  ba kowace matar uba ke rike masa yaya tsakani da Allah ba ta karashe maganar tana sauke numfashi da kyar Aliyu ya sake tashi ya dauki goran ruwan da yayi wurgi dashi yaga da sauran ruwa aciki ya mika  kai bakinta ta kurba tana lumshe ido "na gode muradi Allah yayiwa rayuwa albarka Allah ya yaye maka zafin zuciya ".
"gara kan kina yi kina masa addu'a, wannan zuciya kamar ta mutanen farko ,zuciya a wuya kamar kuturu ba'a  jin rarrashi  bare hakuri  kallonta kawai yayi ya furzar da iska   tare da jan tsaki ,ta watsa masa harara tana hura masa hanci dan ta sake tunzura shi ,a ranshi yace kiyi duk iskanci da kika ga dama ganin idon mumy ne  zamu hadu ne  .."
"Kana magana ne ? tayi maganar cikin jan hankali ."

"ke kisna ban son iskanci sa'anki  ne"? tayi shiru  "ki shiga hankalinki   dan kice  kika fara kawo zance rabuwa a tsakaninku  da muradi    bayan kuma kece za   kiyi   hakuri   dashi domin   kin zo gyara kuskurenki ne a gurin mutumin da  yake tsananin fushi dake dan iskanci sai kina fada masa magana "kiyi hakuri mumy  , "bani zaki bawa hakuri ga wanda zaki sake bawa hakuri nan kuma  yanzu a gabana saboda ko babu aure a tsakanin ki dashi d'anuwanki ne bai cancanci wasu abubuwa daga gareki ba , muryarta a raunana tace "to ..to kayi  hakuri  ".
"haka   ake  bada  hakuri  ki hada kalamanki  guri daya ki bashi hakuri ta  shagwabe fuska kamar zatayi kuka tace  "kayi hakuri ".. shiru yayi yaki magana dan zafin da zuciyarsa keyi  ba zai bar shi ya amsa mata ba .."Kisna na kiraki da babban murya karki sake zance rabuwa tsakaninki da muradi  saboda ina matukar sonku tare bana son ku rabu, rabuwarku daidai yake da shigata damuwa "Ni kuma zafin da zuciyata take akan shi fa  mumy ni kadai fa nasan abinda nake ji kar a waye gari a iske bana numfa........" Da ikon Allah babu abinda zai sameki  idan kika zauna dashi  tsakani da Allah zaki samu lada mai dimbin yawa   sannan  zaki jiyar da mahaifiyarki  dadin da bata bata  jin irinsa ba ,zata sake magana mumy ta dakatar daita kana ta maida hankalinta kan Aliyu .....
    "aliyu  wacece ni agurinka "? da kyar ya iya bude bakinsa muryarsa can kasa yace  "Mother " yana riko hannunta cikin nashi "tabbas ni uwarka ce shiyasa ma nafika jin haushi   akan  abinda kisna ta maka ,abinda tayi  ya balain  tsaya min a rai ya dameni ya daga min hankali saboda na fahimci halin daka shiga a lokacin  amman duk da haka yana da kyau  ka yafe mata  a karo na biyu  dan Allah ku fahimci mahaifiyarku ina son  ganinku cikin farinciki dan Allah ku zauna lafiya dan kwanciyar hankalina shiru suka yi zuciyarsu na dokawa da sauri  iska ya furzar yana Kallon Kisna  itama  shi  take kallo "mai yasa mommy zata masa haka akan kisna "? "Mai yasa zata sa igiya ta  daureshi akanta ? "Aliyu ta sake kiran sunansa  muryarta a sanyaye  kamar zata zubar da kwalla ," ka saki ranka  nasan  halinka  kana da tsananin  fushi da riko a cikin zuciyarka  wanda ba'a son muslimi  yana yin haka  ta  kamo hannu kisna  ta saka cikin na Aliyu  ta dunkule guri daya " ka yafe mata   wannan alfarmata ce na nema agurinka nasan  ko numfashinka nace ka bani zaka mallaka min bare kalmar baki  ,Shiru yayi har kusan second biyar "kayi shiru  muradi kace ka yafe mata ? Da kyar ya  sake buɗe baki yace "na yafe  amman darajanki ne  mumy  wani sanyayiyyen numfashi Kisna ta sauke tana mai godiya  ga Allah da ya furta ya yafe mata mumy tace "nasani  darajana taci kuma  na gode  ko alahira wani nacin arzikin wani Allah yasa muci arzikin Annabi Muhammad  Sallallahu alaihi Wasallama "ameen suka hada baki..."Sai  abu na gaba Kisna  zan  baki   wata  biyar  ki dawo  da Aliyu  daidai  ,kaima  Aliyu zan baka wata biyar ka dawo daidai da matarka idan  ba haka ba zan ɗauki mummunar  mataki akanku  wanda a karshe  bazai muku dadi ba, tana gama fadar haka ta mike da kyar  ta soma kokarin  barin dakin Aliyu ya mike zai taimaka mata tace "yi zamanka muradi  na gode zan iya takawa da kaina ya koma ya zauna yana furzar da numfashi .."

Mommy  na  tashi  daga mazauninta  Kisna ta mike cikin sanyi jiki ta biyo bayanta   ,mumy dake kokarin zama ta dubeta a tsanake tace  "me kuma kika zo yi ? " Maza ki  koma gurin mijinki  ki soma aiwatar da aikinki Allah ya baki nasara akanshi  muryata a shagwabe tace  "mumy wannan dan naki fa akwai wuyar sha'ani kanshi kamar kwakwa yake wallahi "ungo nan haka zaki daure , tun farko da bakiyi abinda kikayi  masa ba  kema kinsan  yadda kike so  zakiyi  a gidansa ,hakuri zaki kara akan wanda kike yi , ki sanyawa ranki ibada kike yi  kin san kuma duk abinda akace ibada ne dole sai an d'aure tare da sanyawa zuciya hakuri inshallahu ina ji ajikina zakiyi nasara akansa bazai sake wining zuciyarki ba "shikenan mumy adduarki ta Kara min karfin gwiwa daga sarewar dana yi da lamarinsa dan wallahi har na cire tsammani a kanshi "ba'a cire tsammani da rahmar Allah mamana ,kuma  inshallahu sai kinyi alfahari da mijinki wata rana mumy ta dan dauki lokaci tana bata shawarwari daga karshe sukayi sallama ta koma dakin yana nan zaune a inda ta barshi yayi tagumi
ta matsoshi  sosai  kamar zata shige  jikinsa sauran kaɗan  ta kwanto jikinsa tace   " maganar mumy   gaskiya   ne  bazamu iya rabuwa da juna ba sai dai  wallahi  na gaji da irin rayuwar da muke ka saki ranka mu zauna lafiya , ni dai nasan  a halin yanzu babu abinda nake son kasancewa dashi kamarka   bazan iya rayuwa babu kai ba , ina sonka aliyu  kaima nasan  kana sona "? tayi  maganar tana murza tafin  hannunsa dake cikin nata ..."No  i can't ya fada atakaice yana  furzar da iska  mai zafi tare da jan dogon   tsaki , shiru tayi jikinta na ɗaukar  rawa "you mean you don't love me "? "yes I do   ya  sake  bata  amsa a takaice ,ta sake matsoshi  tare da sanya kwayar idanunta cikin nashi,  d'ayan  hannunsa ta  kamo ta mikar dashi tsaye   "come with me ta nufi jikin  bango  dakin    dashi bai mata musu ba yayi  shiru  yana biye daita kamar wani karamin yaro  suna karasawa  ta tsaida shi tana fuskartashi tare da  kai hannuwanta duka kan wuyansa ta zagaye  tana jifansa da wani irin kallo mai kashe gabobin jiki  "meye  haka  kuma "?yayi magana yana kai hannunsa zai cire hannuwanta  dake zagaye da wuyansa "tsaya mana  ranka shi dade  ka ga  wani abu , ta cire hannuwanta dake zagaye da wuyansa  ta zuge zip din gaban rigarta   take dukiyar fulaninta  dake  cike  bammm sunyi wani luhu luhu dasu ga kyau ga haske ga taushi  suka bayyana a gabansa  "wowwww is beautiful  yaushe rabon na gansu ya  faɗa  acikin ranshi   amman  a zahiri tsaki yaja  yana kawar da fuskarshi  gefe kamar yaga mugun abu   ,ta kai hannunta  ta dawo da fuskarsa gareta ya sake dauke  idanunshi akansu "duk fa wannan  kayan marmari is  for you   Aliyu muradi   ".... "for me"? ya furta yana watsa mata  harara  "Yes of course  is for you don't you like it ta sake turo masa  su daidai bakinsa kasancewarta  doguwa sosai kaɗan ya rage  bata kamoshi ba yayi  saurin runtse idaunshi    qirjinshi na wani irin bugawa da karfin gaske  "stop all  this nonsense Kisna  it  not look beautiful ",kinsan wani abu "?ta girgiza masa kai tana  tura hannunta cikin vest d'insa har tayi nasarar  kife  yatsunta  a qirjinsa ya bude baki da niyyar  zai yi magana  ta muzra kan nipple's d'insa  duka tana wani  irin narke masa ajiki ...   ...tsarkewa yayi  ya soma tari  kamar wanda yaci wani  abu  mai yaji  take ta rude tana masa sannu  "na kawo maka ruwa "?Kai kawai ya girgiza mata alamun  a'a ya zare hannunta daga jikinsa ya nufi gaban mirrow  yana magana  yana kwance agogonsa sai lokacin ya samu damar fadar abinda yake son fad'a mata  " duk wannan abinda  kike yi   basa burgeni saboda bana jin komai ajikina  ji nake kamar namiji ne a kusa dani ,wallahi na gaji dake bazan dai  iya fitowa na fad'awa  mommy  bane dan  ita kadai   zan iya gama  rayuwata dake ba dan ina sonki ba,idan son samuna ne ma   wallahi nayi  nisa da rayuwarki zai fiyye min kwanciyar hankali.."

"look   I understand what's in your heart ,ba Sai ka faɗa min ba saboda idan da sabo na saba da wannan kiyayyar  ko zan iya baka    tukuici akan wannan kiyayyar "?yayi shiru yana Kallonta ta cikin mirrow  zuciyarsa na tsalle  kallon wawiya yake mata ita kuma tana masa kallon mara wayo   "bana bukata  kuma  karki  dameni  da shirmeki na banza on-expecting yaji ta sumbaci kumatunsa  ta juya  tana wata irin  shegiyar  tafiya  tana kad'a masa  jiki wanda ya zame mata jiki   a tsorace ya juyo  yana kallon  bayanta "kina hauka ne kike irin wannan tafiyar "? "Haukan sonka  ba  ta bashi amsa tare da juyowa suna fuskantar  juna "me kuma ya samu tafiya ta ? tayi magana tana   matsowa  a hankali ta karaso gabansa ta tsaya kirjinta na kadawa shiru yayi  tare da tsura mata ido kamar zai cinyeta  ganin taki ɗauke idanunta akanshi ya cire vest dinsa  yabi gefenta zai  wuce  Kawai yaji ta rungumeshi  a jikinta , hannuwanta ya sauka a 

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login