Showing 111001 words to 114000 words out of 495987 words
Chapter 38 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt
sunanta a tsanake cike da tausayawa ,ta kasa amsawa sannan ta kasa d'ago idanunta saboda hawayen dake cikinsu "duk naji abinda ya faru tsakaninki da haroon amma mai zai hana kiyi hakuri ki bari a cire cikin so that daga baya sai a san yadda za'a yi idan ma auren zaku yi sai kuyi ,kinsan mu addininmu ya haramta mana aure da ciki "
Kai tsaye girgiza masa kai tayi alamun ta sani kafin daga baya ta soma magana cikin kuka "nasan da haka Abdul sai dai bazan iya zubar da ciki ba , dan yarenmu bama zubar da ciki idan mutun yayi ganganci zubarwa kuwa sunansa gawa dan mutuwa zai yi ta fadi haka dan kare kanta da kuma tsiratar da cikin jikinta dan ita tana tsananin son abinda zata haifa wa haroon . bata yi auni ba taji saukar zazzakar muryarsa a kausashe cike da tashin hankali yana cewa "aikuwa Ki sawa ranki zaki mutu nan kusa dan wallahi bazan amshi cikin jikinki ba kije ki san yadda zakiyi dashi ya k'arasa maganar a fusace yana ƙoƙarin barin gurin tayi saurin shan gabansa tare da riko duka hannuwansa hawaye na gangaro mata "haroon karka min haka ni bance dole sai ka aureni ba amman ka amshi cikin jikina a matsayin d'anka a zuciye ya fixge hannunsa daga cikin nata yana nunata da ɗan yatsansa alamun gargadi , abdul ya matso kusa dashi kamar yayi kuka yake duban haroon dan ba karamin tausayawa dicter yayi ba , babu yadda bai yi da haroon akan ya hakura ya amshi cikin ba hakan ba zai zama da wata matsala ba hasalima babu sisinsa da zai kashe akan cikin amman haroon yaki yarda yace "shi bai tashi haihuwa da kowace mace ba koda kuwa da macen da zuciyarsa ke so ce bare ita da bai taɓa jin digon sonta acikin ransa ba .."
Tun da ya soma magana idanunta ke kansa tana ci-gaba da zubar da hawayen bakinciki "me ta rasa da haroon ya kasa fuskantar lamarinta"?" ta haɗa komai da duk wani cikakken namiji zai bukata daga cikakkiyar macen data amsa sunanta ,kasa hakura tayi ta sake matsowa garesa cikin narke fuska ta durkushe a gabansa nan fa hankalin mutane ya karkata garesu suka zuba musu ido suna kallonsu , cikin rawar murya take magana jikinta na rawa "haroon zuciyar dicter ta makance akanka, zuciyarta bata taɓa tsintar kanta cikin yanayi irin wannan ba , ka tausaya mata karka barta babu abinda zuciyata take buƙata kamar ta mallakeka ,
zanyi komai akanka dan bana son yadda soyayyarka ta ladabtar dani ta labdatar da abinda ke cikina , idan zuciyarka ta makance akan kiyayyarta bai kamata idanunka su makance akan tilon dan d'an da zaka fara samu a duniya bayan dogon lokacin daka ɗauka kana tarayya da mata kala dabam dabam cikinsu babu wacce ta dauki cikinka bare har tayi niyyar haifa maka sai ni da kake jin tsanata fiyye da kowace mace a duniya , idaniyana sun makance akanka haroon duk da kiyayyarka gareni ammna har yanzu rayuwata na kaunarka da tillon danka ko yarka dana fi so fiyye da komai a rayuwata kai muslimi ne na zauna tare da muslimai suna da tawakalli da yarda da hukunci Allah komai suna daukarsa a matsayin kaddama ina rokonka ka yarda da kaddarar cikin nan mu barshi ya rayu da........"
" Enough dicter ya katseta a matukar tsawace yana mata gargadi da idanunshi, gabad'aya yanayinsa ya canza hatta kwayar idanunsa sun canza launi ji yake kamar ya shaketa ta mutu ya huta "mai yasa kike da taurin kai da nacin bala'in ? Shin ko kinsan duk wannan abinda kike yi baya sauka akan zuciyata bare naji shi a jikina? ciki dai nawa ne ko ? Tayi saurin girgiza masa kai tana marairaice fuska " to nace miki banaso bana bukata ki zubar ko kuma ki zama uwarsa da ubansa wannan kalmar itace silar bugawar zuciyarta "meye farinciki ka a rayuwa haroon da zaka nemi wulakanta jininka ? "Ina tabbatar maka muddin ka wulakanta wannan cikin bazakayi farinciki a rayuwarka ba saboda baka cancanci samun haihuwa arayuwarka bayan ka wulakanta ya'ya bilaadadin "ki min shiru stupid idan ba haka ba zan daga miki hankali zan baki mamaki ina ruwanki da ko duka ya'ya na wulakanta ? ganin suna maidawa juna magana cikin tsananin fushi da zafin zuciya yasa Abdul ya matso ya shiga tsakaninsu yana bashi hakuri da ƙoƙarin shawo kansa amman taurin kai irin na zarma ya matsowa haroon yaki fahimtar abokinsa haka Abdul ya hakura ba don rashin yayi masa dadi ba , suna kallonsa ya tsaida mai mashin ya haye ya barsu tsaye jigun jigun tamkar waɗan da aka yiwa mutuwa , Abdul ya dinga kwantar mata da hankali da bata tabbacin zai shawo mata kanshi a karshe ma zai dawo gareta nan kusa , da zantuttukan masu sanyi ya samu ya dinga kwantar mata da hankali ta nufi gidansu zuciyarta na rawa ..."
Daren ranar dicter bata runtsa ba babu abinda kwakwalurwarta ke yi sai tunanin nemawa kanta mafuta ,kanta kamar zai tsage akan tunani gabad'aya ta rasa abinda ke mata dadi damuwa ta samu kyawawan mazauni a cikin zuciyarta idanuwanta kuwa sun kankance saboda tsabar kuka har lokacin ma hawayen idanunta yaki tsayawa akan kyawawar fuskarta , ta kai hannu ta goge hawayen a lokacin da wasu zafafan hawaye suka zubo mata , kuma har lokacin bataji zuciyarta ta amince mata da zubar da cikin jikinta ba , har goshin asuba bata samu damar runtsawa ba, washegari taki fitowa har kusan karfe biyu jin shiru yasa mahaifiyarta ta shigo d'akin ta isketa kwance shiru ta lula duniyar tunani , hankalinta a tashe ta karaso gareta ta tambaye ko lafiya bata fito ba tace "kanta ke mata ciwo "shine zaki kunshe kanki a daki dan rashin sanin ciwon kai ,maza ki tashi akai ki hospital ta gyada mata kai tare da mikewa zaune ita kuma ta fito daga dakin , bayan mahaifiyata ta fita daga d'akin komawa tayi ta kwanta tana fidda numfashi sama sama yayinda duka hannuta ke kan cikinta da taji yana mata kugi alamun jin yunwa ranar haka ta yini da zazzafan zazzaɓi da yunwa ajikinta ko falo bata fito ba mahaifiyarta ta sake shigowa d'akin wanda lokacin tare suka shigo da likita ta nuna masa inda take kwance , ya ajiye jakar kayan aikinsa ya soma dubata tare da yi mata allurai da rubuta mata magani dan bayi tunanin aunata ba ya fita ...."
Tun daga ranar dicter bata kara samun lafiya ba tayi bankwana da farinciki duk abinda taci sai ya dawo ga miyo laulayi dai ya tasa gaba sai ɗaukar hutu tayi a gurin aikinta Abdul ma bai zauna a garin ba ya tattara ya kama gabansa saboda gudun abinda zai biyo baya, sai da cikin dicter yayi wata biyar cikin na shida sannan mahaifiyarta ta fahimci ciki gareta tashin farko tayi murna dan su a yarensu bawani abu bane dan mace tayi ciki , amman jin wai mai cikin yaki amsa kuma muslimi ne yasa hankalinta yayi bala'in tashi ta dinga zaginta tare da kiran zata gurbata musu zuri'a da muslinci , haka ma y'an'uwanta sanda suka ji labari suka hau bala'in tare da zarta hukunci akanta ko a zubar da cikin ko tana haifar abinda ke cikinta ta bar musu gidan da yaron basa bukatarsa cikin family dinsu hakan ya sake haddasawa dicter shiga damuwa kullum da tunanin take kwana take tashi tunda ema yasan da batun cikin kullum kafar na gidan yana surfawa dicter tujara iri iri yaki yarda a daidaita komai burinsa ta yarda a cire ciki ko kuma da zarar ta haihu ta bar musu gida "hawayen idanunta sunki tsayawa kalma daya ce dai ke fitowa daga bakinta "kuyi hakuri ku bar min cikina da zarar na haifa na yarda zan barku "wannan kalmar ke karyar da zuciya mumy tayi kukan zuci babu halin yin magana dan sai tayi kamar zata yarda da zaman dicter da cikin jikinta sai ema ya sake harzuka ya dinga zugeta tare da sauke mata kwando maseefa da bakaken kalamai ya nuna mata itace ke daure mata gindi ,fita yayi daga d'akin cikin bacin rai mumy ta bishi tana masa magana cikin harshensu "me kake son nayi ema ? "Ni kaina ba farinciki nake da wannan cikin ba "to me yasa kike zuwa kina tarewa a gurinta kina nuna tausayawarki gareta alhalin kinsan babban abun kunya ta aikatawa danginmu idan kin yarda da zamanta mufa bazamu lamunta ba gara tun wuri musan abun yi ki zaba ko mu ko ita? mumy tayi shiru zuciyarta na zafi duk maganarsu tamkar a cikin kunne dicter suke yi sakamakon biyo bayansu datayi domin sanin matakin da zasu sake dauka akanta "daga yau karki sake zuwa inda take matsawar kina son mu zauna lafiya, mumy ta sake yin shiru tana kallonsa "shirunki ma kawai amsa ne ya sa kai ya fita ya barta da ciwon zuciya .
tun daga ranar mumy bata sake shigowa inda dicter take ba sai dai hankalinta na kanta tana tura mai aikinsu ta Kai mata abinci tana lura da duk wani motsinta rashin shigowar mumy yasa zuciyar dicter ta fara ciwo saboda kadaici yayi mata yawa , domin dauke kafar da mumy tayi daga shigowa dakinta babban tashin hankali ne gashi bata samun mai kwantar mata da hankali ba , kullum cikin damuwa take .
da wani yammaci ta kunshe kanta a tsakankanin cinyoyinta tana kuka mara sauti mai tattare da bakinciki halin da take ciki mussaman yadda Haroon yaki abinda yake cikinta bata san yadda zatayi da rayuwarta da cikin jikinta ba tana jin kamar ta zubar da cikin ta zauna da yanuwanta lafiya ta huta da balai sai dai wankakkiyar zuciyarta na kwabarta da aikata haka ,a lokacin ta sake yin baki ta Rame gabadaya ta fita haiyacinta saboda rashin samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali , ita kanta mumy zuwa lokacin ta soma nuna tausayin diyarta ta damu sosai da ramar datayi ga ciki gabadaya damuwa ta aureta kana ganinta kasan tana cikin damuwa dan dai bata son nunawa ne kada manya yayanta su dauka da gaske tana goyon bayan dicter ne, kuka take sosai tun daga lokacin da cikinta ya tsufa bala'in ema da sauran yan'uwansa ya karu kuma a lokacin ta hakikancewa kanta yanuwanta baxasu amince da zamanta da abinda ke cikinta ba a gidan sai dai ta kudurcewa kanta bazata rabu da cikinta ba ,zata haifa kuma zata rayu dashi ko bola ne taje su rayu amman bazata taba biye musu ba bare ta wulakanta abinda zata haifa , dan bata sani ba ko cikin jikinta kadai zata mallaka a rayuwata ."
sannu a hankali ta cigaba da renon cikinta har sanda ta haihuwa ta samu d'a namiji kyakkyawan gaske wanda yaci sunan abubakar wato sunan yayan haroon tana kiransa da sadik , limamin unguwar su ta samu ta koro masa bayanin cewar uban yaron muslimi ne dan haka tana buƙatar a saka masa sunan Muslunci bayan limamin ya gama jin komai ya tausayawa rayuwarta da yaron sannan ya bukaci sunan da take buƙata tare da karanto mata sunayen maza a Muslunci har yazo kan Abubakar sadiq nan ta tuna haroon ya taba faɗa mata yana da yaya Abubakar , a hankali ta cigaba da bawa yaronta kulawa sai dai kullum da abinda take gani daga y'an'uwanta wanda bata tsamaci hakan daga gare su ba, ta ɗauka kaunar dake tsakaninta dasu zatasa zuciyarsu tayi rauni su kaunaci abinda ta haifa sai gashi a dalilin tilon d'anta sun sake tsanarta da nuna mata ita din ba kowa bace garesu gashi shima uban ɗan ya nuna duk duniya bashi da makiyiyar data wuceta ,tun mahaifiyarta najin haushin yaron da bai ɗauko komai nata ba sai na ubansa ta dawo ta soma sausauta mata da fahimtar kowa da irin tashi qaddarar ,bazata rabu da tilon diyarta ba amman dole a fitar da yaron daga gidan dan ganinsa nasata jin bakinciki mara misaltuwa kuma hakan na hura wutan bala'in a gidan .
tana tsakiyar katifarta a zaune tana bawa yaronta ɗan wata hudu zuwa biyar nono, yayanta Emanuel da mahaifiyarta suka shigo d'akin ta d'ago kanta a hankali ta zuba musu ido tana jiran taji abinda ya shigo dasu " yau ne watanni dana baki suka cika tun bayan haihuwar ki ki ɗauki wannan yaron ki kaiwa ubansa ki dawo mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka gabatar a tun farko idan kuma kinki amincewa da tsarinmu sai ki tattara ki bar mana gida ki bi ubansa dan ba zamu zauna tare da dan muslimi kuma wanda ya nuna baya qaunarki , bancin ke ƙatuwar wawiya ce ta yaya zaki shayar da wannan dan bayan ubansa yaki amincewa dashi sannan ya nuna rashin kulawarsa gareki".
"yaya zanyi da rayuwata "?ta fada cikin raunin murya "ku min uzuri dan Allah ni kaina ban tsamaci irin wannan rayuwar ba ,sai dai kusani ko na kai masa yaron nan babu abinda zai yi dashi tunda ya nuna baya bukatarsa a rayuwarsa ,sannan meye ribar na bayar da tilon d'ana na dawo na cigaba da rayuwa tare daku batare dashi ba? " ina son dana Kuma duk runtsi zan rayu dashi koda kuwa zanyi rayuwa akan bola ne, ina rokonku kada ku bari wannan al'amari ya farraka tsakaninmu ,ba kowace uwa ce zata iya rayuwa babu d'anta ba dukkaninku iyaye ne ku misalta haka akan kanku , "mai yasa zaku zama makiyana akan abinda bai kai ya kawo ba "? "Mommy ke fa uwace kin fi kowa sanin yadda ya'ya suke a zukatan iyayensu ke kanki bazaki so rabuwarki dani ba, Ki duba kiga yadda kike jina aranki ,yadda kike mutuwar sona a zuciyarki yadda kike ji akaina haka nake jin soyayyar dana araina koma nace fiyye da irin son da kike min saboda ni na samu gatan da soyayyar iyayena wanda d'ana ya kasa samu daga gurin mahaifinsa gabad'aya jikin mommy yayi sanyi ta dukar da kanta sai hawaye sharrrrrrr sharrrrrrr ..........
"ema ya kalleta a fusace "bafa zamu cigaba da zama dake da wannan dan ba , ai da ɗan iskan yaron da yayi miki ciki bai gudu ya bar garin ba da sai yasan yayiwa miki ciki dan tuni zan sa bindigata na harbe shege ko ya kai wa uwarsa dan ta goya , sati daya na baki ki san abin yi dan mu fiki shiga kunci da bakinciki wannan abun kunyar da kika yi wai ki rasa wanda zaki yarda kiyiwa ciki sai muslimi duk fadin garin nan kin bani kunya dicter banyi exepecting haka ba yana gama fadar haka ya juya fuuuuuuuuu ya fice daga d'akin sosai take kuka sai dai har lokacin zuciyarta batayi nadamar haihuwarta ba mumy ta zauna kusa daita ranta duk a jagule sai dai ta rasa me zata fada mata .."
Bayan kwana biyar din da ema ya bata ta soma shirya kayan Sadiq a cikin jaka tana kukan zuci tana tunanin sauran kwana biyu kwanakin da ƴaƴanta ya bata da inda zata ga haroon yayinda mumy ke rakube a gefenta rungume da sadiq tana kukan zuci dana zahiri ta ya zata rayu batare da diyarta ba dicter na cikin hada kayanta ema ya bude dakin ya hankado labule ya shigo mumy na ganinsa tayi saurin ajiye Sadiq akan katifa jikinta na rawa suka zuba masa ido suna kallonsa gabansu na faduwa balle da suka ga ya tokare a bakin kofa sai huci yake, addu'a dicter ta soma yi acikin zuciyarta "fatan baki manta ba jibi ne kwanankinki zai cika a gidan nan ki tattara ki bar mana gida dan baxaki reni Dan musmulimi a gidan ubanmu ba idan kuma kinki zaki nacewa zaman gidan nan zamu kawar dake da wannan yaron mu huta take mumy ta tsure tana cigaba da kallonsa "kisa kake nufi ema ko me ?
Ya watsa mata idanu "kisa kuwa ko zaki hana ne ? Ta girgiza masa kai alamun aa"babu abinda ya dace daita sai mutuwa ,take dicter tayi luuuuu zata fadi akan Sadiq mumy tayi saurin tallabota abun haushi suma ta so tayi amman suman yaki zuwa dan haka ta zuba masa ido cikin wata irin gigitan jin abinda yace zuciyarta na dokawa kuka ya kufce mata "yaya yanzu har munzo lokacin da zaka iya kasheni akan wannan matsalar?
a fusace ya d'aga mata hannu "dan ubanki akwai abinda yafi dace wa dake bayan mutuwa ? " idan mun kashe danki zaki dangwama kina ganin bakinmu idan mun kasheki mun bar danki zai rayu tare damu abinda bazamu so ba kenan kinga gara ku tafi gabadaya tunda kin zabi rayuwa dashi sai lokacin mumy ta sanya baki cikin tsinkewar zuciya da tsoro "haba ema bai dace kana fada mata haka ba idan kayi haka kayi ..
Yayi saurin katse mumy "bazamu fa bar wannan munafukar ba,sai dai ta zabi daya cikin biyu ta kaiwa mai da dansa ko suyi mutuwar kasko mumy ta zaro ido tana dubansa jikinta na rawa hawaye ya zubowa mumy a lokacin da dicter ta zube gabanta tana kuka irin kuka a kausashe "kada ku min haka ko addinin muslinci babu inda akace zaa kashe mutun dan yayi ciki da Christan ,dan Allah karkayi haka wannan jahilce ne kai da zaka tsayawa rayuwata akan dana daya zamo qaddara a rayuwata kai ne .... "dakata ya daga mata hannu kenan kin zabi muslinci akan addininki tunda har kina ganin a muslinci bazaa iya yin miki haka ba ? "Tabbas na zabi muslinci akan addinina kuma ina daf da amsa a fusace yace "ki min shiru wawiya makaryaciya kawai ki fita idona kafin na karyaki dan ubanki kin dade baki amshi muslinci ba , kuka sosai take na bakinciki wannan tsanar da yanuwanta suka mata "kada ka cutar Dani Kai danuwana ne idan kayi haka Allah bazai barka ba haka dicter ta dinga furta masa magana cikin muryar kuka tana ajiya magana zai dauka "anya kuwa yaya kana da digon imani a zuciyarka ?"kana tsoron Allah kuwa ?"idan kika