Showing 183001 words to 186000 words out of 495987 words

Chapter 62 - Cutar Kai Book Complete Hausa Novels by Aysha Bagudo.txt

...."

Karfe hudu da rabi daidai zahra ta shiga Kitchen yayinda afra da mufeeda suka soma aikace aikace gyaran gida kafin kace me sun gyara ko'ina gidan yayi tsaf daidai wannan lokacin ne Kuma mummy ta sanyo kai cikin parlou'n gidan ta dubesu tana murmushin tace "sannuku da aiki 'yan albarka sukayi murmushi su kace "yauwa mumy sannu da zuwa "yauwa ta amsa ta shige bangarenta ta shiga wanka bata dade ba ta fito ta sauya wasu kaya ta dauki wayarta ta fito parlour "ina su muradi ne banji motsinsu ba ko sun fita sanar tasu ne ?"Eh sun fita buga kwallo inji cewar mufeeda suna zaune suna kallo a zeeworld wayar mumy dake hannun afra tana buga game ta soma ƙara alamar kira mummy ta dubeta tana fadin "waye ? "Dady ne ta mikawa mumy wayar tayi sallama suka gaisa "ya kasuwan ?"Ya amsa da "lafiya yana jin muryarki kamar babu lafiya ?",Babu komai gajiya ce kawai "okay daman na Kira naji yadda kike ne sai na dawo ya kashe wayar nan suka ci-gaba da kallo suna hira kamar ya'yan data haifa a cikinta sai tayi musu abu sau dari batayiwa ya'yan cikinta ba ,ta tarbiyarta dasu kamar yadda uwa zata bawa ya'yan data haifa a cikinta bata ga abinda zata saka ita da yaranta bata basu sun saka ba har zaginta ake cewar bata san ciwon kudinta ba ,yaran suna wahalar mata da jikinsu ko masu aiki ta dauko iyakar aikin da zasu yi mata kenan sun wahalar mata da jikinsu ,shiyasa bata bambamtasu da yaranta har unguwa wata rana dasu take zuwa duk karshen shekara mai gidan zai bari su fita zuwa Saudiya ,Dubai chaina , egypt domin su huta yaranta yan hutu ne suna samun hutu yadda ya kamata ,yaran duk abinda suke so shi ake musu tun basu kai haka suke gurinta ba gashi har sun cika shekaru shabiyar suna tare ,matsala dai daya ce ita kuma daga afra ne da muradi ta rasa dalilin da yasa ta tsane shi duk da shi baya shiga tsabgarta a duk lokacin data yunkura zata dauki mataki sai taga idan tayi magana afra zata iya daukar abun awani matsayi ,ita kuma bata son tayi mata abinda zai taba ranta ta dawo gurinta ne saboda soyayya da shakuwa tunda babu abinda ta rasa a gidansu hasalima iyayenta na mugun ji daita sai abinda ta gadama take yi zamanta tare daita ne ma yasa ta rage shagwa'ba da sangarci , zata barta da Samir tunda tasan duk sanda tayiwa muradi rashin mutunci bazai kyaleta ba .."

Akan hanyar Kisna ta dawowa daga makaranta islamiyya ita da kawarta zinnira wacce bata wuce shekarunta a haihuwa ba ,Kisna ta cire hijab dinta tana wasa dashi itama zinnira ganin haka ta cire nata suna tafiya suna wasa kamar abun arziki sai Kisna ta ja ta tsaya tare da cewa "zinnira na daure miki wuya da hijab dina na jaki kamar rago dan muyi sauri ? batare da wani tsoro ba zinnira ta gyada mata kai tana murmushi aiko Kisna ta zagaye wuya zinnira ta daure ta soma janta da karfi , take zinnira ta fashe da kuka tana ƙoƙarin kwance daurin wuyanta amman ina Kisna tayi gaba har da dan gudunta tana murna zinnira na biye daita a baya tana cigaba da kukan ta kwanceta amman taki har suka shigo layinsu tana janta har da kiran " meeeeeeeeee "... tun daga nesa muradi dake tsaye da jahid ya hangosu ya dinga juya kai cike da mamaki zuciyarsa ta jagule kamar ya daura hannu akanshi sai data karaso kofar gidan tayi masa duban tsanake sannan ta kwance hijab dinta dake wuyan zinnira tasa hannu tureta "wuce gidanku joooooo. ... " kadan ya rage zinnira bata fadi kasa muradi yayi saurin tarota yana ƙoƙarin kamo Kisna da dayan hannunsa ta kwasa da gudu ta shige karamin get din gidan da sauri muradi ya mika zinnira gurin jahid ya biyo bayanta jahid na ƙoƙarin tsaida shi amman yaki tsayawa da dan gudunsa ya karasa shiga cikin gidan yana dube dube nemanta "lafiya muradi me kake nema ? "mumy ina Kisna "yanzu ta shigo da gudu halan wani abu tayi ? "babu komai ina ta shiga ? ta nuna masa dakinsu mufeeda , hanyar dakin ya nufa direct ya shiga bai ganta ba ya tsaya a tsakiyar daki rike da kugunsa yana kallon dakin dan gano inda ta boye ita kuwa Kisna tana cikin wordrobe din kayanta ta lullube jikinta da kaya jikinta na rawa saboda tsananin tsoro, dakin ya fara dubawa bai ganta ba wani tunani yayi Kawai ya juya ya fita daga dakin ya tsaya a bakin kofa yana fita ta buɗe ta fito tana kyalkyalewa da dariya har da girgiza jiki bata ankara ba taji shigowar mutun daki ta tsure tana neman gurin buya ya damki tsintsiyar hannuta ta juyo a mutukar tsoroce cikin wani irin matsefaffen tsana ta zuba masa ido tana turo masa baki "muje ki bawa yarinyar mutane hakuri , da kika daure musu wuyan yarinya zaki kashe musu 'ya ne? yayi maganar yana d'agata sama ya fito daita aiko ta saka masa ihu "wayyo mumy kice ya saukeni Allah bazan bata hakuri ba ai itace tace na daureta kamar rago "ai kuwa ko itace tace ki daure ta sai kin bata hakuri ko na zaneki yau " dan Allah kayi hakuri karka dakeni banaso bulala ka sauke bazan sake ba cikin tsananin tashin hankali take ihun bai sauketa ba sai da suka karaso falo inda ya iske zinnira da jahid sun shigo tana rike da wuyata mumy ta kamo zinnira tana duba wuyanta "muradi a she d'aure wuyan 'yar mutane Kisna tayi shine na tambayeka kace babu komai ? zo nan sai na zaneki yau mumy ta matsar da zinnira dake gabanta ta kai hannu zata damko Kisna muradi ya matsa baya kadan "Karki daketa mumy bari dai ta bata hakuri sannan tayi alkawarin bazata sake ba gaba-daya mutanen dake falon suka zuba masa ido suna kallonsa shi daya shigo tamkar mayunwacin zaki zaka dauka dukan mutuwa zai mata amman ya buge da iya hakuri zata bayar mumy kuwa wani irin tashin hankali da bakinciki ne ya dirar mata a lokaci daya saboda bata samu damar hukunta Kisna ba, muradi ya saki hannun Kisna tare da cewa "ki bata hakuri sannan kiyi alkwarin bazaki sake ba ya faɗa yana kallonta shiru tayi taki yin magana tana shesheka duk wanda ya ganta yasan tana cikin tashin hankali amman shegen taurin zuciya ya hanata bude baki a tsawace madu yace "ba dake ake magana ba kika tsaya kina kallon mutane ki bata hakuri mana ? ya kai hannu zai mareta muradi yace "no madu karka mareta mana zata bata hakuri "dan Allah yaya ka bari na dan mareta yarinyar nan ko na shake mata wuya taji yadda yarinyar mutane taji "muradi ya girgiza masa kai "matsalata daku kenan saurin hannu wallahi "kai da baka da saurin hannun ai gashi nan taki yin abinda kace saboda ta rainaka Samir ya faɗa yana shigowa falon " muradi ya rage tsawonsa daidai na Kisna tare da cewa "ki bata hakuri Allah baya son mutun azzalumi kuma mai mugunta idan bakya son Allah ya sakaki a wutan daya tanadarwa azzalumai tare da azaba mai radadi ki bata hakuri ita kuma ta yafe miki shinkenan kin huta da azabar Allah magana yake mata amman tamkar bada ita take ba gashi duk yadda yan'uwanta suka so hukuntata ya hana gabadayansu suka zubawa sarautar Allah ido suna kallon muradi dake rike da hannuwanta yana rarrashita da kyar Kisna ta bawa zinnira hakuri tana jan tsaki shima dan taji madu yace idan bata bayar ba zai dauko mata kyankyaso ...
muradi yaji tsakin da kisna tayi amman ya share ya mike a natse ya riko hannun zinnira suka fito waje jahid ya biyo bayansa yana cewa "kai wannan yarinyar da gani zatayi taurin kan bala'in da zuciya common hakuri sai datayi kusan minti shabiyar Allah ku tashi tsaye akanta "muradi na fita Samir ya waskawa Kisna mari "dan ubanki wa kika yiwa tsaki idan na sake jin kinyi tsaki sai na karyaki maza ki wuce dakin mumy ki kwanta a karshen gado ta kwasa da gudu ta shige dakin mumy tana kuka ta faɗa kan gado ta rufe idanunta da hannuwanta duka ....

A can waje ma bayan muradi ya sallami zinnira da sweet cigaba da magana Kisna jahid yake masa wanda har lokacin bai ce masa komai ba "Sai naga kamar kana biyawa Kisna wallahi ka bari a hukunta yarinya tunda kai baka iya hukuntata amman ka tsaya kana wani lalla'bata kamar kwai " "ka kasa fahimtata ne ni dukan mace ne banaso wallahi ina mugun jin tausayi mata bare Kisna yarinya ce karama idan ta saba da duka zuciyarta zata kangare har tazo ta daina jin tsoron duka "ai shinkenan Allah ya kyauta sai dai kasani wani dukan yana gyara mutun jahid ya karasa maganar yana masa sallama ya wuce da misalin karfe takwas na dare gaba-dayansu suna zaune akan dinnig table suna cin abinci ,yayinda da kisna ke zaune akan cinyar afra tana bata abinci tana ci tana zuba mata shagwa'ba ,can ta kalli Aliyu dake zaune ya gama cin abinci yana kallon sama tace "dady d'azu da bakya nan wannan ya kai ni islamiyya bayan nace bazani ba "waye wannan din "?mumy ta fada a matukar fusace yayinda kisna bata fahimci fushi mummy tayi ba ta sake narke fuska ta nuna muradi da yatsan hannunta "na sake jin kince masa wannan sai na cire wannan ɗan iskan bakin naki yayanki ne ba wannan ba ta karasa maganar tana buge mata baki aiko ta bare baki ta sauka daga kan cinyar afra ta soma birgima a kasa tana jiran dady yayi magana sai dai gani tayi ya mike ya nufi waje yana waya "au Dan ban miki duka ba shine kike birgima bari kigani mummy ta yunkura da sauri afra ta mike ta ɗauketa tayi daki daita tana cewa "ba yayyanki bane wannan bawa ne kuma ɗan tsintuwa shege ne karki dauke shi matsayin yayanki kinji baby na kisna ta d'aga mata kai .."


A parlour kuwa muradi bai d'ago ya kalli abinda ya faru ba duk da kunnuwansa sun jiyo masa komai tunanin abubuwa kawai yake , haka nan wani lokaci kwakwalurwasa zatayi ta tunanin mahaifiyarsa ,
yana mamakin yadda ta dauki tsawon shekaru bata kawo kanta garesu ba , sau tari idan sun yi waya da anyarsa jamila yana tambayarta ko akwai wani sako daga mahaifiyarsa sai tace" a'a sai dai su kan gaisa da sadiq wanda shima zuwa lokacin babu abinda yafi bukata da gani kamar daura kwayar idanunsa akan mahaifiyarsu ,yana son zuwa inda take sai dai rashin takamaiman sanin full address din inda take ke hanashi zuwa, ya dai san ita din yar benue ce a unguwar kankara amman a wani gida ?" Bai sani ba mahaifinsu ne kawai zai iya danganasu da inda mahaifiyarsu take , shi kuma har lokacin ba'a sanda inda yake ba ..
Mummy ta Kai hannu ta shafa sumar kanshi tana sauke numfashi sannan ta tsura masa idanu tace "ya'akayi muradi meke damunka tunanin me kake yi ?muradi ya dawo da kanshi daidai yana sakar mata murmushin karfin hali batare da yace komai ba ,sake tsareshi tayi da idanu "tambayarka nake kayi min shiru ko bazaka gaya min bane ?"Still shiru yayi mata tare da zuba mata idanu dan bai san abinda zai faɗa mata ba ,a ganinsa idan yace mata tunanin mahaifiyarsa yake zata dauka ko ya raina kulawar da take bashi ne shi yasa yaga gara kawai yayi shiru ,ganin har lokacin shi take jira ya fada mata damuwarsa ya ɗan kalli Samir yana lumshe idanunsa da suka dan canza tashi Samir yayi ya fice daga falon gabad'aya tashin Samir ya bawa mufeeda da zahra har ma da madu tashi suka koma kan kujera tare da maida hankalinsu kan tv naunauyen ajiyar zuciya ta sauke kana yace "mummy karki damu fa babu abinda ke damuna illa......."mummy Bata bari ya karasa maganarsa ba ta katse shi ta hanyar cewa "muradi ka saurareni da kyau bana son wannan dogon tunanin dake iya haddasa wa mutun ciwo idan wani abu aka maka ka fito ka faɗa min ina tabbatar maka akanka zan iya batawa da kowa dan haka ba zan rokeka ba umarni zan baka ya zamo dole ka faɗa min damuwarka ta karasa maganar a fusace ganin ran mummy ya ɓaci yasa jiki muradi yayi sanyi , zuciyarsa tayi rauni domin kuwa babu abinda ya tsana a duniya kamar yaga ɓacin ranta haka zalika babu abinda yafi so fiye da farincikinta sannan ya tsani ya bata mata rai yanayinsa kadai ta kalla ta fahimci yadda damuwarsa ta qara muradi ya kamo hannun mumy cikin nasa yayinda idanunwansa tuni sun canza launi cike da rashin kuzari cikin tautausan muryarsa mai sanyi da shiga jiki "kiyi hakuri mumy banason ganin ɓacin ranki abinda ke damuna ba wani abu bane wani lokaci ina jin rashin mahaifiyata a kusa dani karki ɗauka wai ko ban yabawa kokarinki bane a'a hakan nan dai nake kwadayin sake daura idanuna akanta "mumy ta sausauta murya tace "karka damu ina da tabbacin zata zo gareku ni kaina babu abinda nafi bukata kamar ku sake sanyata a idanunku da kuma nasan inda take da tuni na kaiku "Nasani mumy nasan ke din uwa ce mai daraja a gareni ya karasa maganar idanunsa na ciccikowa kamar zai yi kuka "kiyi hakuri mummy ban raina kulawarki garemu ba sai dai bansan dalilin da wannan tunanin yaki barin zuciyata da tunanina ba "...
Mumy ta saki naunayen ajiyar zuciya tace " ka kwantar da hankalinka wannan ba wani abu bane tunanin mahaifiyarka dole gareka ko ni idan kace min ka manta daita zan ji babu dadi a raina ka cigaba da addu'a idan da rabon zaku sake haduwa Allah zai yi dalili sai lokacin ne ya saki jikinsa sosai "Allah yayiwa rayuwarka albarka a kasan makoshi yace "ameen ."..Cike da kulawa mumy tace "da fatan dai tunbin dan kwallo ya cika da abinci muradi ya da'ura kansa akan kafad'an mumy yace "mumnynah na koshi babu sauran space daga bayanta taji Muryar Alhaji realwan "idan an gama da dan lale sai azo a Bani abinci mummy tayi kayataccen murmushi tace "Allah ya bawa ranshi ya dade hakuri muradi ya tashi ya nufi bangarensu a daidai lokacin dady ya karaso mummy taja Masa kunne "zauna ka ɗauki siriki amman har yanzu baka canza ba "ta yaya kike tunanin zan canza tunda kema baki canza ba kullum kina cikin salon jan hankali , mummy tayi murmushi wanda ya bayyana kyawawa hakuranta masu haske irin na muradi ta tsaida idanunta akan shi tace

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login